Dabarun Rubutun Waka

[DABARUN RUBUTUN WAKA RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA] BY MSZ.

Sponsored Links

 DABARUN RUBUTUN WAKA
   RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA
Kashi na farko
  Daga 
Nasir G Ahmad
Assalamu alaikum.
Wannan shiri, “Rubutattun Wakokin Hausa” zai rika zuwar muku a duk rana irin ta yau (Litinin), don tattauna dabarun rubuta wakar Hausa ga mai sha’awar farawa, da kuma inganta rubuta su ga wanda ke sha’awar kara kwarewa wajen rubuta su. 
A yau shimfida za mu yi, mako mai zuwa in Allah ya kai tai sai mu tsunduma cikin abin sosai.
RUBUTACCIYAR WAKA
 Zai yi kyau mu dauko abin daga tushe, wato daga bayani kan adabin Hausa.
Adabi a dunkule, shi ne duk wani abu da ya shafi ayyukan fasahar al’umma ta hanyar sarrafa harshe don samar da abokin hira, da nishadantarwa da debe kewa.
 Adabin Hausa ya kasu zuwa kashi biyu: adabin baka da rubutacce.
Adabin baka shi ne wanda Hausawa suka gada tun iyaye da kakanni. Shi da ka ake shirya shi, a fade shi da baki, a kuma adana shi a ka. Ya kunshi labarun baka, kamar tatsuniya, da zantukan hikima da sarrafa harshe, kamar karin maganganu, da wakokin baka, da wasannin gargajiya.
Shi kuwa rubutaccen adabi, ya samu ne bayan da Hausawa suka fara hulda da wasu al’ummomin, musamman Larabawa da Turawa. A rubuce ake shirya shi, a bayar da shi a rubuce, a kuma adana shi a rubuce. Ya kunshi rubutun zube (na labarai), kamar Ruwan “Bagaja,” da wasannin kwaikwayo, kamar “Uwar Gulma” da kuma rubutattun wakokin Hausa, wadanda wannan shiri zai rika magana kansu.
   Daga. 
Tsangayar da ta himmatu wajen kulawa da killacewa da taskace abubuwan da suka shafi adabi da zamantakewar al’ummar hausawa
    
   by  Musa s Zage.  
Domin samun wasu shirye shiryen mu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button