Kanwar Matata 4
🦜 *_K’ANWAR MATATA_*🦜
_Matar Sayyadee_
_Wattpad @Matar_Sayyadee_
☀️ *ZAFAFA WRITER’S ASSOCIATION*☀️
Page 4
“Ah’aaa! Yaya haka, menene haka kuma zuwa da sassafen na sai kace karb’an kud’in bashi? Ni fa bani son irin wannan naci tun ba’a je ko’ina ba.” Fad’in Lami wacce fitowarta kenan daga d’aki baki duk miyan bacci. Bayanta kuma Aina’u ce ke mik’a tare da hamma babu addu’a sai wani “umm’iyyyyyyy!” Take fad’i kamar k’atuwar rago ko kuma bijimin sa. D’aya daga cikin matan wacce sai jijjiga take yi, ga dukkan alamu tafi kowa a cikin su hassala tace, “To dama uban me zai kawo mu wannan wulak’antaccen gidan wanda babu albarka cikinsa in ba tsautsayi ba. Banda fitina da jawowa kai jidali irinta Umar Farouq, menene abun so a cikin y’ay’an gidan nan wanda gaba d’aya kowa ya gama sanin karuwan gida ne su.” D’ayar siririyar cikin sy tayi saurin cafe zancen wajen fad’in, “Aunty Bilkisu ai gansama-gansaman zaurawar gidan nan sun wuce karuwan gida, don ni kam ba zan Kira su da y’an mata tunda tun daga kan babbar har k’aramar babu wacce bata san dad’in d’a namiji ba.” Saurin cafe zancen k’aramar cikin su tayi tare da fad’in, “Yo aunty Halima ai ga zahiri tunda kina ganin shegu ta kowani lungu na gidan an ajiye. Kai Allah yai wadaran naka ya lalace. Wallahi ko wucewa ta kwar gidan nan ban k’aunar yi balle har in tako k’afata cikin gidan nan.” Lami kuwa dake tsaye suke fad’in duk abunda yazo bakinsu, wani shewa tayi tare da nuna wacce aka kira da aunty Halima tace, “Alhamdulillah, ko yau na fad’i na mutu za’a nuna abunda na bari ace Allah sarki ga y’ay’an wance da ta bari. Ke kuwa fa? Ko b’ari kin tab’a yi ne? Idan fitsari banza ne, kaza tayi ma. Kuma y’ay’ana Kainuwa ne, babu yanda aka iya dasu. Duk wani munafurcin ku da k’ananun maganganunku, kanku zai koma.” Aunty Halima wani tsalle ta daka kamar za tayi wasar y’ar gala-gala sannan ta bugi k’irji kare da fad’in, “Haihuwa idan har irin taki ce Lami, kada Allah ya bawa ruwan maniyy d’in mijina isa ga mahaifata. Ai da Haihuwa irin y’ay’anki wallahi gwara b’arinsu. Lami haihuwa irin taki ko, na gwammaci har in koma zuwa ga ubangijina ban ajiye ko kwai d’aya a duniya ba. Kuma ki bud’e kunnuwanki dakyau kiji, idan har ni k’anwar mahaifiyar Umar Farouq ce, to wallahi auren sa da Sarah sai dai bayan raina. Domin Na’ima har gida taje ta samu mahaifiyar Umar ta fad’a mata y’arki da ake son mak’alawa d’ana, tana d’auke da ciki. Dama kuma banda hauka da rashin hankali, mai Farouq zai ci da d’iyar karuwa, tubabbiya wacce sana’ar danginsu kenan karuwanci! Mun bar maku duk wani abu da aka kawo gidan nan da sunan naiman auren y’arku, sai dai amma ki sani, babu aure tsakanin zuri’arki da namu zuri’ar.” Wani irin rushewa da kuka Sarah tayi jin abubuwa da Aunty Halima take fad’i
A bayyyane ta soma fad’in, “Shikenan, Farouq d’in ma ya sub’uce min. Dama na sani ba zan tab’a aure ba a rayuwata.” Ta fad’i hakane tana mai kaiwa cikinta duka da duka hannunta biyu. Lami kuwa kitchen d’in dake tsakar gidan ta nufa tare da d’auko katoton tab’aryarta mai nauyi da tsayi tayo kan su Aunty Halima don har cikin ranta taji zafin maganganun da aunty Haliman tayi mata. “Aunty Halima, aunty Halima!” Siririyar mai suna Najma ta kwad’a kiran sunan aunty Halimar tare da fizgo hannun aunty Bilkisu ta janye ta baya saboda kawo tab’aryar da Lami tayi. “Barta, barta ta jawowa kanta bala’i Najma. Wallahi ba zan gudu ba, karyar hauka take yi, idan ta isa ta buga min taga abunda zai faru da ita yau d’in nan.” Fad’in aunty Halima amma deep down tana jin tsoran kar Lami ta buga mata zabgegiyar tab’aryar dake hannunta. Lami kuwa k’ara yowa kansu tayi da tab’aryar ta d’aga sama zata kwad’awa aunty Halima da tayi k’arfin hali tak’i guduwa. Caraf taji an rik’e tab’aryar ta baya, a fusace ta juya suka yi idu hud’u da Sarah wacce idanunta suka kad’a suka yi jazur alamar tayi kuka. “Cika min tab’aryana ko inci ubanki cikin gidan nan!” Lami ta fad’i da k’arfi tana mai zarowa Sarah idanun. “Dan girman Allah Lami kar ki tab’a su, ki kyale su. Yanzu idan kika bugawa d’aya daga cikin su, RAI kuma yazo yayi halinsa, ya za kiyi?” Fizge tab’aryar tayi tare da fad’in, “To idan na kashe sai me? Ko kotu aka je babu wanda za tuhume ne don sune suka biyo ni har cikin gidana. Duba kiga cikin zuri’ar da kike son shiga, su kansu tun daga yanayin shigarsu zaki fahimci babu abun arziki a gidan. Daga ganin kayan jikin wannan shanyayyiyar matan (Tai nuni da aunty Bilkisu) kayan jikinta kwance ne. To a nan wajen mai na sama yaci balle ya baiwa na k’asa. Shashasha! Ni Allah ya yiwa Na’ima albarka da har taje gidan su Farouq d’in ta fad’awa mahaifiyarsa kina d’auke da juna biyu. Dama kuma nayi rantsuwa idan har ni y’ar Samuel da Debora ce ba zan tab’a bari kiyi aure da d’an iskan yaron nan ba. Sai gashi Allah ga kawo hanya mafi sauk’i. Ke bama shi ba, babu ke babu aure da kowani namiji a duniya nan.” Salati gaba d’aya su Aunty Halima suka d’auka suna tafi. “Eh lallai! Yau na tabbatar da ke d’in cikakkiyar arniya kuma bakatafiya ce ke. Kin fi k’aunar suyi ta gantali a titi suna yawon hotel-hotel suna kawo maki kud’i kina musu goyon shegu ko? Tirr! Shiyasa aka ce idan za kayi aure ka auri uwa ta gari domin ta haifo maka y’a’yana nagari. To kema kan ki ba tarbiyar gare ki ba balle ki bawa y’ay’anki tarbiyan.” Kamun Lami tayi magana, sai ga Na’ima da Nuratu sun shigo gidan a tare ko wacce hannunta rik’e da manya-manyan ledoji. Washe baki Lami tayi tare da fad’in, “Ka ga y’ay’an albarka wanda aka haife su tsiya na barci!” Baki sake su Aunty Halima suke kallon su Na’imar da sai wani yatsine-yatsine suke yi. “Lami akwai ruwan wanka kuwa a gidan nan? Don ni wallahi a mugun gajiye na dawo. Mutun hud’u suka yi ciniki na.” Amshe maganar Nuratu tayi tare da fad’in, “Wallahi nima a gajiyan nake tib’is. Ni mutum d’aya ne ma ya d’auke ni muka tafi _Asa pyramid_, wallahi ko runtsawa banyi ba. Ruwan zafi nake buk’ata sosai in galgasa jikina.” Washe baki Lami tayi tare da fad’in, “Y’ay’an albarka, y’ay’an gwal kenan. Babu ruwan zafi amma yanzu nan zan had’a wuta na d’aura maku, ku shiga daga ciki naga alama babu k’arfi a jikin ku gaba d’aya duk kun yi laushi.” Su aunty Halima kuwa, wannan ta kalli wannan, sai wannan ta kalli wannan, haka su kayi tayi tsakanin su suna mamakin hali irin na Lami. “Way’annan kuma mi suke yi a nan gidan?” Fad’in Nuratu tana kallon su d’ai-d’ai. Sai da Lami ta balla masu harara sannan tace, “Wai zuwa suka yi su fad’a mana sun janye auren da suke nema na Sarah. Baki ganni da tab’arya a hannu ba, ai tahowa nayi in sheme y’an iska.” Gaba d’aya daga Nuratun har Na’ima kallon Aina’u suka yi tare da fad’in, “Ke dan ubanki tsayuwar mi kike yi da baku tare ke da Lamin kun kakkarya k’ashin bayansu ba!” Aina’u tayi wani tafi tare da fad’in, “Ai ni jira kawai nake yi Lami ta fara kai hannu kiga suga yanda ake yi a cikin gidan nan, don billahil lazi babu wacce zata fita da kaya a jikinta. Sai na tabbatar mun yi masu tsirara sannan mu hankad’a su waje.” Cire siririn gyalenta Na’ima tayi sannan taci d’ammara dashi tare da kallon Nuratu tace, “Maza je rufo mana k’ofar gida saboda kar su samu damar fecewa.” Da gudu Nuratun ta nufi k’ofa ta saka lock tare da sakata sannan ta dawo. Wani dogo sanda wanda aka ajiye a barandar d’akin mahaifinsu Nuratu ta d’auko, Na’ima kuma ta d’auko muciya, ita kuma Aina’u ta koma d’aki ta d’auko wata murd’ad’d’iyar bulala. “Inna lillahi wa’inna ilaihir raju’un! Nasiba sai da nace maku kar muzo gidan nan. Mu kira kawai a waya ya wadatar. Yanzu kinga d’aya daga cikin jahilci da rashin hankalin nasu ko.” Fad’in aunty Lubabatu wacce bata cika fitana ba, asalima ita taso abi komai a hankali amma Mama ta matsa su tafi su fad’a masu sun janye neman auren. “Wai nan tsoro kike ji? Ai wallahi sarkin yawa yafi sarkin k’arfi, mu biyar ne fa!” Fad’in Rahima wacce ita ma tunda aka fara fad’an bata ce komai ba sai yanzu. “Baki da hankali hala? Gidansu fa muka iske su. Wallahi mune a ciki ko kotu aka je!” Ko kamun wani ya fara magana a cikin su, Nuratu ta shak’o wuyar aunty Halima ta baya ta kaita k’asa. Ganin haka ya saka gaba d’ayan su suka hau Nuratu da duka domin ceton aunty Halimar don tana kaita k’asa ta hau dukanta da sandar da ta d’auko. Suma su Lami na ganin haka, sai suka hau kansu da duka. Aina’u sai zabgawa ko waccen su zambad’ed’iyar bulalan hannunta take yi, Na’ima kuma tana maka masu muciyar hannunta. Kan kace kwabo, kasancewa su Nuratun da makami a hannunsu, tuni jini ya fara sharara a goshin aunty Luba, Aunty Halima da Najma. Don sun fi kowa buguwa. Ga shaidan bulala ta ko’ina a jikinsu. Sarah kuwa gefe ta koma tayi ta rusa kuka don ita kanta ta samu nata rabon wajen ceton su aunty Halimar. Baba ne ya samu ya fito da kyar don k’afar na matsa masa da ciwo sosai. Yana fitowa tsakar gidan ya tsaya turus, don tun shigowar su aunty Halimar yake sauraran komai daga ciki yana share hawayen bak’in ciki. Babu wacce yake tausayi banda Saratu don ya san ba k’aramin damuwa zata shiga ba na fasa auren nan nata da ake shirin yi. “Ke! Nuratu, Na’ima, Lami, Aina’u, wallahi kamun na iso wajen nan ku rabu da mutanan nan. Ku wasu irin yara ne kamar dabbobi. Kai ko dabba baza tayi abunda kuke yi ba. Babu wawuya mara hankali a cikin su kamar ke Lami. Wallahi kuka yi kisa a cikin gidan nan, nine nan zan bada shaida duk a tafi a rataye ku.” D’agowa Lami tayi tana haki tare da fad’in, “To sai me idan mun kashe sun? Ai dama ni na jima da sanin ba k’aunar mu kake ba ni da y’ay’ana. Kana d’aka kana jin duk maganganun da matan nan suke fad’a min, amma baka iya fitowa ba, sai da kaji muna d’aukar mataki tukun zaka fito kana wani maganar banza da wofi, yara, ku cigaba da d’umamun su!” Ko rufe baki bata yi ba, su Nuratu suka cigaba da dukansu aunty Halima. Tsabar azaba aunty Luba kuka take yi tana basu hak’ura amma basu saurara ba. Baba kuwa dogaro sandar shi yayi tare da isowa inda suke ya d’aga sandar ya makawa Lami, sannan ya kuma d’agawa ya bugawa Nuratu da Aina’u, ya d’aga zai bugawa Na’ima, tayi caraf ta rike sandar tare da tura shi baya sai da ya kai k’asa k’afarsa ta markwad’e, Aina’u kuwa d’aga k’afa tayi dagangan ta take yatsun k’afarsa har da murzawa. Wani irin salati Baba ya saki tare da fashewa da kuka yana mai kai hannu kan k’afarsa da Aina’un ta mitstsike. Nuratu kuwa hannu ta saka ta dungure masa kai tare da fad’in, “Wallahi kar ka kuma ka kai hannunka jikina.” Da mugun gudu Sarah ta iso wajen ta d’auke Aina’u da gigitaccen mari, sannan ta kuma d’aga hannu ta zabgawa Nuratu da Na’ima mari, sannan ta kuma d’auke Aina’u da mari don a idanunta ta mitstsike k’afar mahaifinsun. “Dan uwarki ni kika mara?” Fad’in Na’ima tana mai nuna kanta, Nuratu kuwa muciyar dake k’asa ta d’auka ta bari Sarah dashi a fuska, nan da nan fuskan ya tashi, bakinta kuma ya kumbura ya soma fidda jini don har ta wajen bakinta dukan ya samu. “Allah ya isa shegiya y’ar iska! Kuma wallahi nima sai na rama!” Fad’in Aina’u tare da yin hanyar pamfo da gudu ta d’auko bokitin da aka cika ruwa aka ajiye tayo kan Sarah wacce ke tsugunne dafe da kuncinta da Nuratu ta buga mata muciya. Sai ji tayi shaaaaa an antayo mata ruwan sanyi tun daga tsakar kanta har cikin pant d’inta. Saurin kallon gefenta tayi inda Baba yake saboda jin wani ajiyar zuciya da ya sauke, sai tayi arba dashi a jik’e shataf, don ba ita kad’ai Aina’un ta jik’a ba har da baban. Baba kuwa kallon Aina’u da Na’ima yayi yana fad’in, “Ni! Ni ko? Ina mahaifinku zaku saka hannu ku ture ni har sai da ba kai k’asa ko? Aina’u ni kika kwarawa ruwan sanyi a jiki har mitstsike min k’afa ko!” Sai kuma ya kalli Nuratu ya ce, “Nuratu ni kike saka hannu kina dungurewa kai kamar d’anki ko?” Ya fad’i hakan yana nuna kansa wasu zafafan hawaye na biyo kuncinsa. “Kuje! Duniya zata koya maku hankali.” Ya fad’i yana mai fashewa da kuka tare da k’ok’arin mik’ewa. Sarah kuka take yi sosai ganin yanda jikin mahaifinsu ke wani irin rawa kuma yana kuka sosai. “Lami dan ubanki kizo ki bani abinci yunwa nake ji!” Fad’in Safwan d’an Na’ima. Saurin kallon Lami Na’imar tayi tare da fad’in, “Yanzu Lami dama yaran nan basu karya ba? Haba Lami! Haba!! Wannan wani irin wulak’anci ne. Nafa bar komai na abincin yaran nan.” Marairaicewa Lami tayi tare da fad’in, “Yi hak’ura Na’ima, dama fitowa ta kenan domin in d’aura masu abincin sai ga wad’annan fitinannun mutanan sun shigo.” Kallon su Na’imar tayi tare da fad’in, “Zaku fita ku bar gidan nan ne ko kuwa sai kun sake ji a jikinku?” Babu wanda yayi magana cikinsu sai ma kama junansu da suka yi suka nufi k’ofar gida. “Sake ni Saratu kije ki bud’e masu kwar gidan ki basu hak’uri ki dawo.” Fad’in Baba yana mai share hawayen da suka kasa tsayuwa a idanunsa. Sarah bata sake shi ba sai da ta kai shi wajen barandarsa sannan ta nufi k’ofar gida da gudu, nan tayi arba dasu suna ta kiciniyar bud’e gidan. Hannu Sarah ta kai bayan sun bata hanya ta bud’e masu gidan tare da saurin kai guiwowinta k’asa ta shiga fad’in, “Aunty dan girman Allah kuyi hak’uri da abunda y’an uwana suka yi maku. Ku……” Katseta aunty Bilkisu tayi tare da fad’in, “Matsa mana a hanya mu wuce tun kamun nayi ball dake a nan wajen.” Aunty Luba kuwa saurin cewa tayi, “Mai ya kawo maganar Ball kuma! Ke jeki gida mun ji mun yi hak’uri. Bamu hanya mu wuce tun kamun shan ruwan mu a duniya ya k’are. Wannan da muka sha ma, ya ishe mu ishara!” Ta fad’i hakan tana mai bud’e gidan. Karaf gaba d’ayan su suka yi ido hud’u da Farouq dake k’ofar gidan. Da sauri Sarah ta mik’e tana kallonsa, kallon irin na bankwana. Najma kuwa tana arba dashi ta fashe da kuka tare da soma labarta masa abunda ya faru. Wani irin yunk’uri Farouq yayi zai fad’a cikin gidan ganin yanda jini ya b’ata gaba d’aya gaban rigar aunties d’insa da k’annan nasa. Saurin rik’osa aunty Luba tayi tare da fad’in, “Bada yawuna ba wallahi ka shiga cikin gidan na, yaran da har mahaifinsu duka suke yi, to uban waye baza su daka ba a cikin fad’in duniyar nan. Farouq dama inda kake nai man aure kenan? Wallahi, tallahi ko da ace yarinyar nan ba ciki bane a jikinta, kai da ita sai dai a lahira idan da rabon auren a can. Sam wannan gidan ba gidan had’a zuri’a dasu bane.” Sarah kuwa da sauri ta fito daga cikin gidan ta zube a gaban Farouq, ko kamun ta bud’e baki ya d’aga hannu ya wanke fuskanta da gigitaccen mari tare da nuna ta da hannu yace…………
_08128755583 WhatsApp only dan Allah. Ban da kiran waya._