HARSHEN HAUSA
{KO KASAN YADDA HARSHEN HAUSA YAKE BUN KA SA ‘A DUNIYA}
Sponsored Links
YADDA HARSHEN HAUSA YAKE BUNKASA A DUNIYA
(Kashi na biyu)
Daga:.
Rabiu Muhammad(ABU HIDAYA).
A KAN WANI FANNI KIKA KWARE A ILIMI?
Abin da goge a kansa a bangaren ilimi shi ne Kimiyyar harshe da kuma hanyoyin isar da sako ba da harshe ba. (Non-Verbal Communications).
WANI ABU NE YA BAKI MAMAKI A NIJERIYA?
To ni dai yadda na ga randa da ake zuba ruwa abin ya bani mamaki saboda yadda ruwan yake yin sanyi a ciki, sai kuma zuwa na garin Daura na je rijiyar Kusugu na ga kofar da Bayajidda ya shiga garin Daura, na shiga fadar sarkin Daura cibiyar Hausawa na ga gine-gine masu tarihi na Hausa wadannan abubuwa dana gani sun bani mamaki sosai, kasancewar labarinsu kawai nake ji sai ga shi yanzu na zo na gansu.
DAGA CIKIN AL’ADUNKU NA MUTANEN KASAR POLAND WADANNE NE SUKE KAMA DA NA HAUSAWA?
Tabbas akwai, misali yadda ake karbar bako a kasar Hausa da girmamawa a bashi kulawa sosai kamar wani sarki, to mu ma a can Poland haka ne,har muna da wata karin magana a harshen mutanen Poland cewa bako a gida kamar Allah a gida. Wato dole a karbi bako da hannu bibiyu dole a nuna masa girmamawa a yi masa murmushi da kauna sosai, kamar yadda Hausawa suke cewa bakonka annabinka. To wannan ya yi kama da al’adunmu sosai.
Sai dai kuma wani abin mamaki da na gani a nan shi ne mutum zai mikawa mutum hannu don su gaisa, sai ya noke, ya yi alamar risinawa kuma wai girmamawa ce amma mu a can hakan wulakanci ne mutum ya baka hannu ku gaisa ka ki ka yi masa haka.
MENE NE YA FI BURGEKI GAME DA DABI’UN MUTANEN NIJERIYA?
Abin da ya fi burgeni game da dabi’un mutanen Nijeriya shi ne yadda suke da son mutane, dalilin da yasa na ce haka kuwa shi ne, ranar lahadi na shiga sabon gari zan je coci, sai na tarar akwai layi don haka sai na dawo baya na tsaya, to a gefen da nake akwai wani mai shayi sai na ce ya bani shayi da madara na sha, bayan ya bani na sha, sai na dauko kudi zan biya sai yace ai an biya min, sai na yi mamaki, na ce wane ne haka? Na duba sai na ga wasu mutane a gefe suna yi min barka(dago min hannu) sai wani yace a bani biredi, sai na ce bana cin biredi na gode, sai ya dauko kudi ya bani sai na yi dariya nace ina da kudi na gode. To gaskiya irin wannan mutumci da aka yi min na ji dadi sosai kasancewata bakuwa a wurin, kuma na lura da hakan tabbatacciyar dabi’ar Hausawa ce son mutane don haka ya faru da ni a gurare da yawa mutane sun taimake ni.
A CIKIN ABINCIN GARGAJIYA NA HAUSAWA WANI ABINCI KIKA FI SO?
(Dariya)gaskiya ina son abincin Hausawa da yawa don nasan Dan wake, Dambu,Alala amma duk a ciki na fi son waina(Masa)irin ta shinkafa ina samu wannan ina ci sosai.
DAGA YADDA KIKE JIN LABARIN NIJERIYA YA KIKA GANTA BAYAN KIN ZO?
To mu a can muna gani a kafafen yada labarai ana gaya mana Nijeriya akwai boko haram ana fada babu zaman lafiya amma yanzu mun gani babu boko haram akwai zaman lafiya a Nijeriya sosai,
kuma wasu abubuwa da yawa da muke bincike a kansu sai da muka zo sannan muka gansu kuma mun samu banbamci da yawa da yadda muke jin labarinsu.
YANZU IDAN KIKA KOMA KASAR POLAND SAI KUMA YAUSHE?
To sai abin da hali ya yi, amma watakila ina iya dawowa shekaru kadan.
Na gode.
COPY RIGHTING
MUSA S ZAGE.
Tsangayar da ta himmatu wajen kulawa da killacewa da taskace abubuwan da suka shafi adabi da zamantakewar al’ummar hausawa.