fasaha

Shi kasan Yadda Ake Hada NIN da Layin MTN, Airtel, 9mobile, Glo ta Hanya Mai Sauki.

Sponsored Links


Tun a watan Disamban 2020 ne Gwamnatin Tarayya ta umarci kamfanonin sadarwa su tilasta wa dukkan masu amfani da layuka a Najeriya bhada lambobinsu da Lambar Zama dan Kasa (NIN) a matsayin bangaren inganta tsaron kasa.


A baya dai an sha dage wa’adin a lokuta daban-daban, inda a dagewa ta karshe aka sanya ranar 31 ga watan Maris din da ya gabata.


Amma a cikin wata sanarwa ranar Litinin, Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, ya umarci dukkan kamfanonin da su kulle layukan da suka yi kunnen kashe daga ranar Litinin, hudu ga watan Afrilun 2022.


Pantami ya ce matakin na daga cikin tanade-tanaden aiwatar da dokar hada layukan da lambobin NIN.


Kamar yadda yazama wajibi dukkan wani layin waya sai an hada shi tare da National ID Card sannan zai cigaba da aiki kamar yadda ya kamata, Rashin hada layin da NIN ka’iya
jawowa a kulle layin gaba daya.

Bayan haka kuma kowane kamfani daga cikin kamfanin sadarwa MTN, Airtel, Glo da 9mobile sun bayar da
hanyoyin hade layin da NIN, hanyoyin sune kamar haka:

Yadda Ake Hada NIN da Layin MTN

Za’a iya amfani da wadannan lambobi *785# inka sanya
su saika danna kira zai baka dama kasanya lambobin NIN
wato National ID Card guda goma sha daya (11).

Ko KUMA ayi amfani da mobile app na MTN mai suna myMTN app,
shima ta cikinsa zai baka dama kahade layinka da NIN
Number.

Sannan kuma za’a iya shigar da bayanan NIN Number din
ta shafin yanar gizo gizo da MTN suka bayar DOMIN wannan aiki kawai, Danna wannan LINK.

https://nin.mtnonline.com/ .

Yadda Ake Hada NIN da Layin Airtal

Za’a iya amfani da wadannan lambobi *121*1# inka sanya su saika danna kira zai baka dama kasanya lambobin NIN wato National ID Card guda goma sha daya (11) ko KUMA ayi amfani da mobile app na Airtel mai suna My AIRTEL, shima ta cikinsa zai baka dama kahade layinka da NIN
Number.

Sannan kuma za’a iya shigar da bayanan NIN din ta shafi yanar gizo gizo da kamfanin Airtel suka bayar domin wannan aiki kawai, Danna wannan link

https://airtel.com.ng/nin/

Yadda Ake Hada NIN da LAYIN 9mobile

Za’a iya amfani da wadannan lambobi *346# inka sanya su saika danna kira zai baka dama kasanya lambobin NIN wato National ID Card guda goma sha daya (11) ko kuma yi amfani da mobile app na 9mobile mai SUNA My9mobile, shima ta cikinsa zai baka dama KAHADE layinka da NIN Number.

Sannan kuma za’a iya shigar da bayanan NIN din ta shafi yanar gizo gizo da kamfanin 9mobile suka bayar DOMIN wannan aiki kawai, Danna wannan link

https://9mobile.com.ng/nin/

Yadda Ake Hada NIN da Layin Glo

Za’a iya amfani da wadannan lambobi *346# inka sanya su saika danna kira zai baka dama kasanya lambobin NIN wato National ID Card guda goma sha daya (11) ko KUMA ayi amfani da mobile app na Glo mai suna Glo Café Nigeria, shima ta cikinsa zai baka dama kahade layinka da
NIN Number.

Sannan kuma za’a iya shigar da bayanan NIN din ta shafi yanar gizo gizo da kamfanin Glo suka bayar domin wannan aiki kawai, Danna wannan link

 
http://mobileapp.gloworld.com/glonin/home

     Kucigaba da bibiyar A Shafin mu Na Internet maisuna musa s zage domin samun Abubuwa Da Zarar Mun dora Don Su Amfanar Daku A Yau Da Gobe A Kowane lokaci.

Written by MSZ HAUSA.

Leave a Reply

Back to top button