HARSHEN HAUSA

ASALIN SAMUWAR TASHE A KASAR HAUSA.

Sponsored Links


 Barka da zuwa wanan shafin namu mai albaraka .

     Gabatarwa 
         Daga 

Posted by DIDDIGI

                  TASHE A KASAR HAUSA

An kirkiro tashe don gyara tarbiyyar rayuwar Bahaushe ne – Farfesa Lawan Danladi Yalwa
Daga Isa Muhammad Inuwa, Kano da Bashir Musa Liman.

A yayin da watan azumin Ramadana ya yi kwanaki masu yawa da shigowa, har ma’ a  yanzu ake kokarin yin ban kwana da shi, lokacin gudanar da al’adar tashe tuni ya yi.

Wakilan Aminiya sun gana da masana a Sashin Nazarin Harsunan Najeriya da ke Jami’ar Bayero da ke Kano, inda suka yi bayani filla-filla kan ma’anar tashe da kuma darussan da yake koyarwa. Ga yadda tattaunarwa ta kasance:  

Farfesa Lawan Danladi Yalwa na Sashen Nazarin Harsunan Najeriya a Jami’ar Bayero ta Kano, ya ce: “Wani abu ne na gargajiya da aka jima ana yin sa, kuma ana yin sa ne a lokacin azumin watan Ramadana. An fara tashe a kasar Hausa ne, bayan zuwan addinin musulunci.
Tashe yana kunshe da fadakarwa ko wa’azi ko nishadantarwa.  Akan fara gudanar da shi ne bayan an cika kwanaki goma na farkon azumi. A takaice dai jigon tashe shi ne, don a gyara tarbiyyar rayuwar Bahaushe.”

 Wadansu mutane suke tashen ‘Ka Yi Rawa Kai Malam Ka yi Rawa, Ban Yi Ba’


Wadansu Mata suke Tashen: ‘Hajiyar Kauye’

Farfesa Lawan ya ce: “Galibi idan an cika goma ga wata, to a rana ta sha daya ga wata za a fara fitowa tashe. Yara maza da ‘yan mata suka fi yin tashe, amma kuma da akwai tashe na manya.

”Farfesan ya fadi muhimmancin tashe ga al’adar Bahaushe inda ya ce, yana koyar da abubuwa da dama da suka hada da koya wa yara tarbiyya da al’amura na rayuwa, irinsu ladabi da biyayya da hana hada ma da zari. 

Tashe yana koyar da neman abin kai da ma koya wasu abubuwa na magungunan Hausawa. 

Ya ce: “Tashe yakan koya wa yara mata tarbiyyar zaman aure da biyayya ga miji. A wani fannin kuma tashe yana nuna yadda Bahaushe yake kallon wasu kabilun, irin su Gwarawa, ta hanyar kwaikwayon su da nuna yadda suke gudanar da wadansu abubuwa na rayuwarsu


Daga nan sai ya bayyana takaicinsa bisa ga yadda a yanzu wannan al’ada ta tashe take bacewa sannu-a-hankali daga zukatan matasan Hausawa na zamanin yanzu. Ya ce: “A yanzu yaran ba su iya komai na tashe ba, sai abin da ba a rasa ba, inda galibi sai dai su dauki garewani da galalluka da jarkoki suna ta yin kida,  sannan su rika  tare masu ababen hawa suna tambayarsu kudi har sai sun ba su, sannan su kyale su.”


Farfesan ya ce ba komai ne ya kai ga bacewar tashe a zukatan yaran Hausawa na yanzu ba, sai zamananci da abubuwan zamanin ya kawo na bakin al’adu da sababbin salo na rayuwa.

  Ya ce a maimakon yaran su rika yin abubuwa na al’adar Hausawa da daddare, sai su bige wajen kallon talabijin da kallon Sinima da kuma zuwa gidajen rawa, wanda “wannan ne ya sa yaran yanzu da dama ba su san komai game da tashe ba, ko wasu al’adun yara na Hausa ba”.


Farfesan ya ce mafita daya ita ce iyaye su tashi tsaye a kan kula da tarbiyyar ‘ya’yansu tare da ganin suna bin al’adun Hausa sau da kafa. Haka nan ya ce ya kamata Hukuma da sauran masu fada-a-ji, su tashi su rika fadakarwa tare da cusa al’adun Hausa a cikin zukatan yara da matasan wannan zamanin. Ya ce: “Abin takaici ne a ce dan Bahaushe bai san wani abu na al’adarsa ba, kuma kowa ya bar al’adarsa, ita ma al’adar tasa fa ta bar shi ke nan, idan hakan ta kasance sai ya zama Bahaushe ba shi ga tsuntsu, ba shi ga tarko.”

Shi ma wani manazarcin Hausa a Sashen Nazarin Harsunan Najeriya na Jami’ar Bayero ta Kano, Malam Tijjani Shehu Almajir, ya yi karin bayani a kan tashe, a cikin mukalar da ya gabatar, mai taken:
“Jigon Fadakarwa Da Ban Dariya A Cikin Wakokin Tashe”, a wajen taron farfado da al’adar tashe a Cibiyar Adana Al’adu da Tarihi ta Jihar Kano a makon da ya gabata.


Ya bayyana tashe a matsayin wata al’ada ce ta Hausawa wacce ta samu bayan zuwan musulunci; wacce kuma yara maza da mata da ma manya suke aiwatar da ita a yayin da watan Ramalana ya kai kwana goma.

   Asalin samuwar tashe  A kasar Hausa.

 Malam Tijjani ya ce: “Tashe ya samo asali ne daga yadda wasu mutane suka dora wa kansu tashin jama’a domin yin suhur, kasancewar barci yana yi wa mutane nauyi, har su kasa tashi don su yi suhur. Hakan ta sanya  wasu nau’in mutane da suka hada da almajirai, da wadanda kuma a lokacin ake ba su sadakar abinci suka rika tayar da mutane don su yi suhur, daga nan kuma sai maroka su ma suka shiga yin tashe zuwa gidajen manyan mutane don samun kyaututtuka.”

TASHEN DA AKA FARA YI A KASAR HAUSA .

 Ya ce, tun da yara ba sa iya tashi da asuba, sai suka rika yin tashensu da daddare bayan an sha ruwa.
Daga nan sai ya bayar da misalin jigon fadakarwa a cikin tashen Hausawa, inda ya fara da tashen: “TSOHO DA GEMU, YA TSUFA … KU TALLAFE SHI … YA TSUFA ...” Ya ce a nan ana koya wa yara muhimmancin jin tausayi da tallafa wa tsofaffi. Ya ce kuma a tashen: “NA CI NA KASA TASHI … BABA ZARI GARE KA “, yana koya munin zari da hadama ga yara, ta yadda za su tashi ba tare da yin halin hadama da zari ba.

A wani tashen kuma na: “WAYYO ALLAH! … BA MU KUDINMU … ” Malamin ya ce wannan yana nuna illar cin bashi ko kin biyan bashi. Inda kuma tashen: “JATAU MAI MAGANI”, yake koya wa mutane muhimmancin neman magani da nau’in magungunan Hausawa tare ma da dogaro da Ubangiji a wajen neman maganin, da yarda cewar magani yana wajen Ubangiji.


Ya kuma ce wakar tashen: “GA MAIRAMA GA DAUDU”, tana kunshe da koyarwa ta yadda ya kamata mace ta yi wa mijinta biyayyar aure, wacce kuma ake koya wa yara mata a cikin wannan tashen.


Daga bisani kuma Shugaban Kwamitin Amintattu na Cibiyar Adana Al’adun ta Kano, Dokta Sule Bello, ya bayyana bukatar a tattara kungiyoyin masu tashe, domin tattaunawa da su tare da ganin yaya za a farfado da wannan al’adar, kuma ta yaya za a gudanar da wannan al’ada ta tashe a yayin watan Ramadana na gaba. Ya kuma bukaci kafafen yada labarai, musamman gidajen rediyo da talabijin su rika yada tashe, domin yara ‘yan baya su koya kuma su rike shi.

Posted by DIDDIGI 

        DA

Tsangayar da ta himmatu wajen kulawa da killacewa da taskace abubuwan da suka shafi adabi da zamantakewar al’ummar hausawa.

                         Domin karin bayani

Domin Karin bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan za’a cigaba da kasancewa wannan wensite mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauransu,

  Ana iya subscribe ta hanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode.

written by ceo
       Page
musa s zage

Leave a Reply

Back to top button