KUDIN RUWA DA BASHIN BANKI

{KUƊIN RUWA DA BASHIN BANKI A MUSULUNCI} KASHI NA HUDU.

Sponsored Links

                         KASHI NA HUDU

            MA’ANAR RIBA DA HUKUNCITA         

               KAFIN ZUWAN MUSULUNCI 

                      Gabatarwa 

Daga naku 

musa s zage

Ma’anar Riba:- Ita Riba Kalma ce ta larbarci. Don haka asalin ma’anar harshen larbarci ita ce dadi ko kari a cikin konewa ne  Abu.

Wanana ita ce ma’anar wannan kalma a harshen larbarci.

Yayin da yahudawa sukai kaura daga inda suke, suka kuma zauna a madina da wadansu waurare a jazirar larabarwa ;sai suka koyawa larabawa bayar da bashi da sharadin kari ga Wanda zai karba.

    Don haka sai larabawa suka rika kiran wannan kari da ake  

shardanta wa mai karbar bashi da sunan Riba.watau Ruwa a yanzu.

            NAU’OIN RIBA TA JAHILIYAR

                           LARABAWA 

Yin bayani game da na’o’in Riba wadda larabawa jahiliyya suka yi mu’amala da ita abu ne muhimmi. Domin Kuwa yin haka shi zai kara bayyana mana ma’anar Riba. 

Ya Kuma fayyace mana  Ribar da Muaulunci ya tarar Larabawa suna yi ya hana su. Ga dai nu’o’in kamar haka;

(¡) Bayar da Bashi days kari:- Wanda sukan yi ta hanyoyi iri hudu

1- Hanya ta farko ita ce, yarjejeniya tsakanin mai bayar da bashi da mai karbar bashi a kan Karin da za’a yi kan dukiyar, lokacin biya. Al jassas ya ruwaito cewa: “Hakika Ribar da larabawa suka fi yi ta kasance kari be ga zinare da azurfa zuwa lokaci .

 Yakan zama gwargwadon yawan abin da azurfa zuwa lokaci.  Yakan zama gwargwadon yawan abin da aka bayar bashin.

 

2- Hanya ta biyu ita ce biyan kudin ruwan duk wata, alhali asalin dukiyar yana nan. Idan lokacin ya cika sai kawai a dawo da asalin dukiyar. Idan kuwa Wanda ake bin ya kasa biya, sai a kara masa lokacin a kuma kara kudin.

3- Hanya ta uku ita ce, ta bayar da bashin ruwa zuwa wani lokaci. Idan Wanda ake bi ya kasa biya sai a yi ta ninka ruwa. Al-Alusi ya bayyana cewa: “Mutum fiye da daya sun rawaito cewa:Akan bayar da bashi ruwan ne zuwa wani lokaci. Idan lokacin ya yi sai Wanda ya bayar da bashin ya ce:kara min kudin na kara maka lokaci. Haka za su yi kowane lokaci har dukiyar ‘yar  kadan ta yi ta karuwa.

4- Hanya ta hudu ita ce ta bayar da  bashin da sharadin in an kasa biya’ asalin dukiyar zai nunka. Idan dinare dari ne ya zama Dari biyu. Idan lokaci ya sake yi ba a biya ba sai su zama danare Dari hudu. Haka za a yi ta yi kowace shekara. 

(¡¡) Yin Kari a huldar  ciniki sabo da jinkiri:   Idan lokaci biya ya zo aka kasa biya, sai a yi kari akan kudin kayan. Kamar yadda wahbu dan Amru ya bayyana a cikin hidubarsa lokacin ganin ka’aba. Inda ya nemi larabawa da su sanya dukiyar da ba su yi cinikin Riba da ita ba, 

(¡¡¡)Yin kari yayin musayar abubuwa: Wanan Ita ce wadda Annabi (S.A.W)

YA HANA .watau wadda ake kari yayin musayar dinare da dinare, azurfa da azurfa, Sha’ir da Sha’ir alkama da alkama da dai sauransu.

  Kamar yadda y zo a hadisi. Larabawa suna yin irin wannan musaya, ba su san Riba ce ba sai da Annabi (S.A.W) ya haramta ta .

(iv)Yin mugun kari a kayan sayarwa ga wanda bai san yadda kasuwanci ke ciki ba . watau mutum ya shiga kasuwa bai san ƙimar kuɗin abin zai siya ko zai sayar ba .sai a sami wani ya zalunce shi.

  Ya siya kayan sa da muguwar araha ko sayar da muguwar tsada . Dalilin haramcin wannan shi ne hadisin da Baihaki ya rawaito daga Anas .Inda Annabi (S.A.W) Yesu ke cewa:

” yaudarar wanda bai san kasuwanci ba Riba ne ” . AMMA anan mallamai sun. ce a nufin yin haka zalunci ne.

 Ni kuwa , ina ganin mu dai bar shi a matsayin wani nau’i na Riba wanda Annabi (S.A.W) ya hana kamar yadda ya hana ribar musaya  watau ya hana su saboda a kauce wa ribar jinkiri.

ana  zamu diga aya sai mu hadu a Kashi na gaba .

Daga dalibin

        ku 

musa s Zage

   ceo page

Domin Karin bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan za’a cigaba da kasancewa wannan wensite mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauransu, 

Ana iya subscribe ta hanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode.

    sai mu hadu a Kashi na gaba….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button