GIRKE GIRKE

{YADDA AKE SARAFA NAMA } BY MSZ.

Sponsored Links
YADDA AKE SARAFA NAMA

      *DABARUN SARRAFA NAMA*

  Assalamu alaikum Warahamatullahi Wabarakatuhu.

               (Dambun Nama)

Dafarko zaki samo namanki zallah
bamai kitse ko ƙashi ba sai ki gyrashi.

 *kyan hadi sune:-

1-Albasa
2-Attaruhu
3-kayankanshi[Citta,kanunfari,masoro,cinnamon,maggi,gishiri,mangyada].

 bayan kin hadasu a tukunya ki zuba ruwa yadda naman zai hade da kayan da kika zuba su dahu sosai
bayan ya dahu kuma ya tsotse ruwansa.

saiki sauke hanya biyu ce:

1-ko in zaki iya ki cigaba da juyashi harya fara ragargajewa [yafi wahala]
kodai ki juyeshi a turmi ki daka.

2-ko kuma ki zuba a injin bature ki nika
daga nan saiki zuba mai a kasko yayi zafi kisa albsa ya soyu saiki zuba nikakken namanki
kita soyawa sai yayi yadda kike bukata
 daga nan saki juye a container mai tsafta.

yawwa daga nan sai diba kawai
nagode

Daga naku
musa s Zage

Rubutawa:-Binta Murtala[ummu Ahamd].

       DABARUN SARRAFA NAMA

*DARAJARKI ABINCINKI*

  *DABARUN SARRAFA NAMA*

                   (TSIRE)

1-kayan hadi

2-Nama

3-kuli kuli

4-barkono

5-Kayan kanshi

6-maggi

7-gishiri

8-man kuli

da farko uwargida zaki sami namanki amma banda kashi

ki gyarashi

uwar gida in kina bukata zaki iya samun harda mai kitse

saki yanyanka yadda kike bukata

saiki samu kuli kulinki

ki hadashi da kayan hadinki

bayan nan saki samu tsinkenki ki tsaftace shi

daga nan saiki tsirashi a tsinken bayan kin gama kidansa laima a jikin naman

saiki dunga sakashi a jikin kuli kuli kina dankarashi a jikin naman

sannan ki yayyafa man gyadarki a jikin naman

saki sa wayrki a wuta amma karki saka wutar da yawa

saboda karya kone

kuma ya gasu a hankali

in kuma uwargida nada

oven shikenan saiki saka tsiranki a ciki ki gasa.

akwai kuma wani method din zaki iya samun albasa da sweet paper.

[koran tattasai]

saiki yanyanka round round

sai dauko namanki daya albasa daya

sweet paper daya nama daya kigasa.

kinga Hjy kin bada style yadda zaki burge maigida.

ma’asalm

  Daga naku
musa s Zage

Rubutawa:-Binta Murtala[Ummu Ahmad].

br />

   2  DABARUN SARRAFA NAMA

°By Musa s Zage°

      *DABARUN SARRAFA NAMA*

                (*GAS *MEET)

kayan hadi sune:-

1-Nama zalla
2-Gishiri
3-Maggi
4-kanunfari
5-masoro
6-cinnamon
7-Albasa

Dafarko zaki samu namanki musanman mara kitse
saiki gayarashi,
amma inasi na sanar da uwar gida shi Gas meat yan bukatar albasa mai yawa
kuma baasa kayan miya
To idan kin gyara namanki saiki zuba kayan hadin dana fada a sama
[abinda yasa nace ayi amfani da kayan kanshi da albasa sbd shi Gasmeat in uwar gida tasanshi zakiga ba kayan miya acki idan kina bukatar yaji to masoro zai baki dandanon yaji amma bana barkono ko atturuhu ba]
kuma masoro yana da amfani ajiki ba cutarwa ba.

 Daga nan saiki sa kayan dandano yadda kike bukata
idan kinada tukunya ko kasko non-stick
saiki zuba. da albasarki mai yawa kusan daidai da naman saiki ta juyawa haryayi dan romo romo
kuma ya dahu
 uwar gida kinga
maimakon Alhaji ya tafi wani guri sayan Gasmeat to uwar gida ta iya
nagode.

br />  Daga naku
Musa S Zage

Rubutawa:-Binta Murtala{Ummu Ahmd}.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button