Hausa NovelsMr. Romantic Complete Hausa Novel

Mr. Romantic 7

Sponsored Links

*💋MR. ROMANTIC💋*
Multi dimensional story.

Page 7

Mamanteddy

Try to be grateful for what you have, instead of focusing on what you don’t have.

Hausa novel 📚 .

Gaba Ɗaya Hankalin Nihla ya karkata ixuwa hanyar fitowar Maleek . Sanye yake cikin shigar farin suit masu Masifar kyau hannun sa Ɗauke da brief case hatta takalmin ƙafar sa Fari ne irin white cover shoe mai ɗan budewa ta baya irin na maza , idanun ta ne ya sauka bisa suman kan shi wanda yayi tsawo da cika ko na wata macen Afrika albarka , yasa roba ya kuma tattare suman nasa , kai da gani kasan Rashin ji ya ƙare akan Wannan Matashi Wato maleek Jibo . Tsayar da ƙafarsa yayi bisa matakalan jirgin yana ƙare ma Excouts ɗin nasa kallo tare da shimfiɗa-shimfiɗan lafiyayyun motocin da suke a layi a jere kallo , dukan su kiran Combo cars Lamborghini bakaƙe .

Cikin Sauri biyu daga cikin Excouts ɗin shi suka nufo inda yake , yayin da Wani ya buɗe masa Wani irin lema na mataran rana , ɗayan kuma yana saka hannu tare da Amsan brief case din hannun shi . Takawa yake tamkar ɗan sarauta saboda mulki da isa , haka Duk Welcoming din nan nasa da suke Miskilanci bai basa daman yi masu magana ba har ya isa inda Nihla ke tsaye yana shirin wuce ta ne Muryar ta ya katse shi tana furta ” Welcome back to Nigeria”.

“Thanks”.

Amsan da ya bata kenan yana shigewa moton da suka bude masa , ganin suna kokarin rufe Murfin moton ne yasa Nihla Saurin kutsa kan ta da jikin ta tana shigewa tare da zama gyefen sa . A haka motocin suka fara barin Airport din ….Tafiya ce mai ɗan nisa suka fara Wanda har a wannan lokacin Maleek bai kalli inda Nihla take ba , don baya buƙatar hakan , isowan ta ma bai so ba ,bare kuma zaman da tayi Gyefen sa .

Laptop ɗin sa yake operating yana duba saƙonnin Jenny yana sakin murmushi da har sai da Faffaɗan Hushiryar sa na sama ya bayyana , wannan kuma ya jawo Hankalin Nihla izuwa inda yake kallo yana murmushin .

Ƙara fiddo da Idanun ta tayi waje ganin yanda Maleek ke kallon tsaraicin Jenny yana murmushi hankalin sa kwance tabbas abun nasa gaba yayi ba baya ba . Maganan ta taji a vedion tana cewa ” I miss you Maleek , komai nawa kewar ka yake yi , ka gani….Tana maganan tana tattaɓa masa Jikin ta da dukka wani inda zai motsa hankalin ɗa namiji . Lumshe Lulun idanun sa yayi yana ƙara ƙare ma suran jikin Jenny kallo wanda babu inda bai sani ba dama , sai ma abun da ita kan ta bata san tana dashi ba a jikin ta wanda shi kaɗai yasan da zaman sa .

“Maleek “Maleek wannan Wani irin iskanci ne ? Ace muna tare kake kallon vedion tsaraicin wata ? .

Muryar Nihla ya ji ya katse sa tana maganan tana numfarfashi tamkar wanda aka watsa mata ruwan zafi . Ba tare da ya juyo ya kalli inda take ba , yakai hannun sa yana rufe laptop ɗin kana a izzance ya Juyo yana kallon Nihla yana mai zuba mata manyan idanun sa wanda sai da jikin ta yayi sanyi , don wani tsaban seniority ta gani a ƙwayar idanun sa . Ni Sa’an wasan ki ne ? Ni maleek kike faɗa ma haka ?. Wacece ke ? Idan Abun da yafi tsaraici ne zan gani a gaban ki , ke ko da kuwa sex ne zanyi a gaban ki ke mutum ce na dauke ki? , Oga….! . Yayi maganan yana kallon inda driver din sa yake .

Cikin sauri Drivern ya Juyo don dama yasan halin isa da miskilanci na maleek baya taɓa kiran sunan su sai dai Oga ko Yallaɓai .

“Yes sir” .

Dakata anan .

Cikin Sauri Drivern ya kai hannun sa yana danna Wani abu mai kaman remote motocin ne duka kaga sun hau slow suna tsayawa a gefen hanya . Da Sauri Uxair Excout din maleek ne na hannun daman shi ya iso inda moton su yake yana buɗe side din maleek . “Sir “Ya furta yana jiran umarnin da zai fito daga bakin maleek ” .

Juyawa Maleek yayi yana kallon inda Nihla take kana yace Fice ki bani Wuri. “What?”Maleek na fita fa kace ? A gefen hanya zaka Watsar Dani ? . Ku fitar mun da ita. Ganin Uxair ya nufo ta yasa Nihla cike da baƙin ciki kai ƙafarta tana sauka daga moton a sarari tana furta “Ƙwarto kawai kuma Wallahi sai na faɗa ma Hajiya kaka duk abun da kake yi a yanzu ,da yanda ka wulakanta Ni a titi………………!

Kamin ta rufe baki ita dai taga tuni an rufe moton ne suna baɗe da ƙura, Wani irin ƙwallah ne ya ciko idanun ta na baƙin ciki da takaici . Wai Me yasa nake barin Maleek na mun irin wannan wulaƙancin ne ? Duka duka nawa yake ? Kuma da mane ya girme mun? . Mtswww. Tsaki taja tana cizan laɓɓan ta tare da tunanin ranan da Allah zai fado mata da maleek hannun ta . Nan take wata Zuciyar ta fara rarrashin ta da cewa ” Maleek muji ne na nuna ma Sa’a,bayan nan yana da kuɗi ,sannan yana duk wani abu da zaki so a nuna Miki shi a matsayin miji , Kiyi Haƙuri Nihla zaki rama duk abin da yayi miki. Hmmmm jan numfashi tayi kana takai hannun ta tana fara latsa nombobin…………..!

Yau ayi haƙuri da posting din babu yawa …nayi ne dai kar ace mmnteddy bata tayi typing ba . Kaman yanda kuka sani Nobel din na kudi ne .

Regular payment ₦500
Vip payment ₦1000
Zaku iya fara payment yanzu saboda a ko wani lokaci free page na iya yankewa, ga account number Dina da zaku tura kuɗin ku kai tsaye 6037312299 Mohammed A’isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932.

Leave a Reply

Back to top button