Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 76

Sponsored Links

CHAPTER 76

Gudu yake shararawa shide fatan sa ya’isa dawuri kafin wannan hoda data shaƙa yasake ta,sai daf da sallan isha’i suka isa suna shiga garin ya sauke ajiyar zuciya direct wani katafaren gida yanufa yanayin horn mai gadi leƙo yana ganin sa yabude masa yashiga da motan sa yayi parkin kai tsaye bakin tap din dake tsakiyan wasu furanni yanufa alwala yayi yafita zuwa masallaci sai da yayi sallah sannan yazo.

Har sannan bata farka ba,saida ya geshi ya bude ƙofan wani falo sannan yazo bakin motan yabuɗe bayan mota ya dauko ta kaman wanda yadauki ƴar tsana ya shiga da ita hadaɗedden falon da bakajin komai sai sai sanyi ac da wani dadɗan kamshi daya cika falon kwantar ta saman kugera 3sitter harya miƙe tsaye ze tafi yaji ta riƙe masa hannun komawa yayi yazuba idanun saman kyakkyawan fuskarta kallon ta yake ko kiftawa babu beta sanin yarinyar haka take da sassanyar kyau ba sai yau ya shagala da kallon ta jin zuciyan sa na motsawa yasashi saurin kai ɗaya hannun sa ya zare daya hannun sa cikin nata ya mike yashiga toilet dan watsa ruwa.

Alhaji sunusi yashiga mummunan tashin hankali ko yanzun duka sun halarta a guest house dinda suka saba haɗuwa duka sun halarta idan kacire Alh badamasi .

Alhaji surajo ne yamiƙe rai a ɓace yake magana inda yake cewa”sunusi nasan kafi kowa sannin manene ƙa’idan ƙungiyar mu kasan wace irin tafiya muke amma koda yaushe anfi samun matsala ta ɓangaren ka”amma ranka yadaɗe oga kasan ba lefina bane ko?nima badason raina hakan ke faruwa ba.

“Dallah rufa mana baki Alh bashir yace rai a ɓace ya daura da cewan kuma kasan ɓatan Ishaq yana daga cikin mummunan kaddara mu barin sa wajen mu kasan barin sa yana rayuwar ƴanci babban barazana ce garemu dama dukiyar mu baki ɗaya”kuma saida akace dakai mukaishi matsafa ko dawanau mubarshj can arinka masa alluran mahaukata amma kaƙi tunda kace bakason yanzu a kashe shi,alh shehu ne yake wannan maganan.

Miƙewa Alh sunusi yayi tsaye yana cewa”ina ganin dr da muka bawa contrack ɗin alluran nan yaci amanar mu,ni sai yanzu ma nake tunawa da sharadin shugaba yazama mun dole in nemo Ishaq ko wani dake da alaƙa dashi.

“Ya batun saka hannun da alh badamasi ze wa wannan takardun kasan fa idan basaka hannunsa muka samu da farko ba komai namu baze tafi daidai ba”kaman de yanda ishaq yayi maka tsawon lokaci da muka dauka muna ƙillace dashi sai daga baya muka gane takardun duka kaddarorin sa dukka sunan matar sa dakuma babbar ƴarsace har yanzu munkasa sani ina suke aina suke rayuwa kai ko kamanin ita yarinya ba wanda yasani cikin mu balle musaka anemo mana ita.

“Sannan ita ma matar damuke ta murnan munsameta sakacin ka da rashin kulawanka yasa munrasata rana tsaka,kuma duk da hakan baka tunanin komai kai auren ƴarka kasa gaba,tom bari kaji yanzu haka alh badamasi an aiko masa da sammaci daga babban kotu”kotu ya ambata a kiɗime”eh kotu yasake amsa masa kuma baka da labarin wannan ɗin ko?

Saida ya sharce gumi daya tsastsafo masa a goshi ya haɗiye wani ƴawu mai kauri tukun ya gyaɗa ma ogan nasu kai.

Wata uwar harara Alh surajo yamasa yace”dama tun farko saida mukace baza muyi wannan tafiya da kai ba kanace kace zaka iya gashi baje ko ina ba asirin mu naneman tonuwa.

Yakare maganan yana huci cike da bacin rai idan yatuna cikin ƴan watanni sunyi asaran million of naira sai yaji mugu mugun haushin sa gashi duk abunda ƙungiya ta ginɗiya masa ba wanda yacika cikin sharuɗan ta.

“wai kai surajo me matsalan ka danin ne alh sunusi yace yana miƙewa rai a ɓace dama tun shigowata ƙungiyar nan nasan basona kake ba,take faɗa ya kaure tsakanin su kaman zasu bawa hammata iska saida shugaban su ya tsawatar sannan suka nutsu suka zazzauna bayan ya umurcesu da haka.

Kallon su yayi ɗaya bayan ɗaya sannan yace” hukumar NAPTIP tasakomu gaba kan wannan harƙalla tamu duk da ba wanda yasan mune muke aikata abubuwa da suke zargi amma ina jiye mana tsoron faɗi wannan karon dukda tunda muke bamu taɓa faɗiwar ba,kuma bazamu yarda mufaɗin ba gaban maƙiya suma dariya.

amma ɗazu nakejin labari da ɗuminsa kan cewa akwai jimi’insu mai ƙwazo da hazaƙa idan yakama aiki bayaji baya gani harsai yaga karshen abun harin sa.

Sannan baya karɓan cin hanci matukar akan aikin sane gobe zeyi resume a office dinsu dake abuja dan haka inason kai Alh sunusi katura idon mujiya ya gane mana shin waye shi?ya sunan sa yake dakuma hoton sa adireshin inda yake da zama duka harma da sunan da yakekan card dinsa ya amsa da”an gama oga sannan suka miƙe baki dayansu banda ogan nasu dakuma alh surajo.

Ahmad bayi yanufa yana sakarwa kansa shower saida yagama cuɗa jikin sa da sabulun sa mai daɗin ƙamshi da tsada sannan ya dauraye jikin sa da ruwa yafito jikin sa daure da towel yana goge kansa da ƙarami gaban dressin mirrow yanufa ya dauki oil dinsa mai tsada dakuma ƙamshi yasoma shafawa sama sama saida yagama ya dauko jallabiyan sa milk colour ya feshe jikin sa da turare yafito zuwa falon har zuwa sannan Aisha bacci take bata farka ba.

Kaman de ze zauna sai kuma ya fita daga falon zuwa compound ɗin gida yanufi wani part dayafi girma cikin gida dan gidan part uku ne dashi amma dayan nan shine babba dan nan part din mai gidan ne da iyalan su,ɗaya na kusa da wanda Ahmad yake ciki kuma na babban yaron gidan ne kuma abokin ahmad din sai bq da masu aikin gidan ke zama a ciki,matar gidan ƴar uwace gun alh badamasi ƴar gwaggon sace kuma ita ɗayace a gidan sai yaranta da mijinta wanda kusan yawanci baya garin yafiye tafiye tafiye yau yabaya garin nan gobe baya garincen hakade yake harkokin sa da yawan tafiya ƙasashen ƙetare.

Ahmad yayi zama a wannan gidan sanda yazo wani aiki tsawon shekara biyar kafin ya dan tsagaita da aikin nasa sakamakon bayanan su da wasu daga cikin su ke fitarwa ga abokan adawan su ana dan basu ihsani sukuma suna bi suna kashe masu mutane wannan dalilin yasa hankalin Ammin sa tashi ganin yanda akewa ma’aikatan na NAPTIP kisan gillah tare da iyalansu,dan haka ta matsa dole yabar aiki ya koma gida da zama shine fa yabude A&B travels agent da A&B fashion dakuma boutique shekara uku kenan yanzun ma zeyi join aikin ne saboda kawo karshe masu aikata ta addancu da mumanan ɗabi’u safaran miyagun ƙwayoyi safaran yara mata kai harma da maza dakuma ta makamai masu linzami,ya dauki alwashin sai yakama koma wanene saiya shefe babinsu a doron duniya.

Saikuma ya wanke mahaifin sa daga zargin da akemada mahaifin sa yanason ya wanke shi a idon duniya.

Duk dashi mahaifin nasa yaɓoye masa bayason yasani amma faisal yatura masa da komai in details yakuma karanta komai daki daki koda ze rasa nashi rayuwan yayi alkawari sai yakawo karshen GAGARA BADAU da akace shine shugaban wannan tafiyar.

Ya tsaida tunanin sane sanda ya ƙaraso ƙofan babban falo gidan hannu yakai a hankali yabude yashiga da sallama wata mata macece aƙalla zata kai shekara hamsin hakimce tana zaune saman ɗaya daga cikin kugerun da sukaiwa falon ƙawanya tana kallon wani movies da ake haskawa a mbc2 gefen wata yarinya buduwarce kwance ta daura kanta saman cinyar matar tana danne dannen da wayan ta.

Amsa sallamar tasa sukai kusan a tare fuskokinsu yana nuni da zallan mamakin su”yaushe a gari amadi?inji matar itako yarinyar ƙwaɓe fuska tayi cike da shagwaɓa tace”shine baka ko gayamun a waya kana hanya na gyara ma ɗakin ka ba.

Neman waje yayi ya zauna yace”ina yini hajiya mun sameku lafiya?”ƙalau ta amsa masa a taƙaice ta ɗaura da yasu Ammin naka da ɗan uwana”suna gaidaku ya amsa a gajarce yana ƙoƙarin miƙewa saiga baby safna ta rugo da gudu ta faɗa jikin sa tana dariya ɗagata sama yayi yana juyata sai dariya take ya sauke yana cewa”a’a bebin daddy angirma dariya tayi tana cewa”uncle A sai kawai katafi kayi aurenka kabar anty fauza kullum sai tayi kuka kuma tace ba zatayi aure ba ita kai zata jira….zaka jirata kaima?

Takare faɗin haka cike da yarinta dif wuta ya daukewa mami da ita kanta fauzan shiku Ahmad yi yayi kaman beji abunda tace din ba.

Shirin miƙewa yayi yana bawa fauza amsan tambayar da tamasa”ai zuwan bazata nayi wani aikine yataso mun,ɗaki kuma basai kin wahal da kanki ba nayi waya da sajid yasa saminu driver ya share,har yakai ƙofa hannun sa riƙe dana baby safna data maƙale masa mami ce tayi karfin halin yin magana ganin ze fita tace”bara yanzu nasa takawo maka abinci”ok yace yana fita sai kuma ta daura da cewa da kabarta kaga darene sannan kaida kayi dogon tafiya kana bukatar hutu ba surutu irin na safna ba kasanta da shegen surutu kaman aku.

Murmushi yayi yana kai kallon sa kan safna data noke kafaɗa sai kuma ya ɗago yana cewa mami idan takai abincin sai tadawo da ita daga haka yafice zuwa nasa part din deep down na zuciyar sa kuma yana ta tunano maganan safna duk da tafaɗa masane cike da yarinta tabbas hakane dan yanda yaga sauyawar mami da ita kanta fauzan sanda safna ke faɗamasa kenan tun tuni fauza sonsa take shi bemasan tanayi ba idan ko hakane akwai aiki dan zaman Aisha gidan nan ba lalle taji daɗi zama da su ba.

Yana shiga falon Aisha na farkawa tamiƙe zaune tafe da kanta tashiga dube duben dan ganin inda take take taware idonta dasukai mata nauyi ta zubesu a kansa tana dafe kanta dayayi mata naune”ina kakawoni?ina nane nan?tasake faɗa murya na rawa kafin yayi yunkurin cewa wani abu harta miƙe tsaye jiri taji na neman daukan ta tayi saurin komawa ta zauna sai kuma tarushe da kuka.

Baby safna sai kallon ta take idan ta kalli ahmad dake tsaye ko motsawa beyi ba sai kuma ta kalli Aisha dake zaune ta haɗa kai da gwiwa tana kuka”uncle A ita ma wannan kukan take dan bakajira ta ba kayi aure?

Tambayar tazo masa a bazata dan safna irin yaran nan ne masu shegen surutu.

Sai kuma tashiga takowa a hankali inda Aisha ke zaune tana kuka tace”kiyi hakuri kinji anty haka uncle A yatafi yabar anty fauza itama kullum sai tayi kuka kuma tace ba zatayi aure ba zata jira sa kema jiran nasa zakiyi?

Cak Aisha ta tsaya dayin kukan ta ɗago kanta tana kallon yarinyar waye kuma hakan?_wave kuma fauza?wa take jira duka wannan magan tana yinsane aranta ba kuma me bata amsa yanzu koda ta furta sannan kuma bata bukatan sanin.

idanuntane yasauka kan wata kyakkyawar budurwa ajin farko ƴar gayu kana kallon ta taga ƴar hutu hannuta riƙe da wata basket da aka rufe da farin ƙwalle ta shigo falon idanun ta kan Aisha da fuska caɓa caɓa ta jiƙe da ruwan hawaye”who is she?ta tambayeshi cikin sanyin murya.

shiru yayi mata kaman ma bashi take tambaya ba yanufi ɗaki yabarta tsaye baki bude ai fauza batasan sanda ta saki basket din hannunta ba tayi baya da gudu tana tushe bakin ta dan kar kukan datake riƙewa tun ganin sa datayi ya kwace mata a gaban wace batasan matsayinta agunsa ba ganin abunda fauza tayi hakan yabawa Aisha daman sake fashewa da sabon kuka tana cewa”tunda kasan auren wucin gadi mukai ba auren nunawa dangi ko wani abu bato to me naka nadauko ni kakawo wani gidan ka tashi ni kamaini inda kadauko wallahi ko yau na hana kowa bacci a gidan nan.

Ya faɗa tana miƙewa tsaye daga zaunen da take tanufi wani flower vase ƙato dake jirke a gefe da kyar ta kinkima daidai Ahmaf na fitowa daga ɗakin dan sabida kukan da take”K ..K kafin yakaraso inda take tuni taratse ta da ƙasa ji kake tasssss.

 

ALLAH YASA MUDACE.
[9/18, 9:29 AM] Ummahani: 💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

Leave a Reply

Back to top button