Hausa NovelsMr. Romantic Complete Hausa Novel

Mr. Romantic 8

Sponsored Links

*💋MR ROMANTIC💋*

Multi dimensional story🔞 .

 

Page 8

 

Maman teddy.

https://whatsapp.com/channel/0029Va5JfPf7j6g47cLhl807

 

**

Driver ta kira tana sanar masa da inda Maleek yasa aka watsar da ita babu mutunci bare darajawa Tamkar bai taɓa Sanin ta a rayuwa ba . Sosai Ran Nihla ya ɓaci kuma ta ɗauki Alƙawarin Sanar ma Hajiya Kaka duk wani Abu da Maleek yayi mata ,ciki har da kama vedion Tsaraicin budurwar tasa da ta ganshi yana kallo yana Washe baki da murmushi 😄 . Tana tsaye kusan mintuna Ashirin ne Drivern nata ya ƙariko inda take tsaye kaman karuwar ƙasar London don kaf shigar ta babu ɗaya na kirki .

 

Afuwan Hajiya Ayi hakuri na jinkirtawa. Salihu yayi maganan yana kai hannun sa tare da kokarin amsan jakar hannun Nihla. Wani irin ƙasƙantaccen duba tayi masa kana ta yamutsa baki a wulaƙance tace” Ya isa haka don Allah, bude mun moto mu wuce .!

 

Bai damu da tsawar da cin mutuncin ta ba ,don inda da Sabo to tabbas kwarai ya saba da Wannan tijaran nata . Buɗe mata murfin moton yayi tana shigewa ya rufe a zuciyar Salihu yana faɗin ” Ai mai maganin ku duka ya dawo , zaku gane Allah ɗaya ne , idan tijara ne da cin mutumci yafi ku iya sa , Shine dai dai ku Musamman ke da Yasmeen .

 

Tunanin uban mene kake yi ne wai?.

 

Muryar Nihla ya katse sa wanda cikin sauri ya furta ” Yi hakuri Hajiya ,yana maganan tare da shiga yana fara jan moton tare da ɗaukar Hanyar Gidan A halin Jibo .

 

**

RUGAR DAALA

 

Gaba ɗaya Billy ta rasa Walwalar ta bisa ga jin Furucin Fulanin Wannan Ruga, duk yanda taso tayi masu dabara Abun ya cittira wannan yasa ta don dole haƙura, amma sai tace da liman zata dawo bayan kwana biyu su ƙara tunani.

 

“Hasile ina ne zaki tafi ne haka?”.

Muryar Umma ya katse Hasile Wacce take Kokarin barin bukkan don bata san Umma zata tashi daga barcin da ya dauke ta ba .

 

Wani irin bugawa ƙirjin Hasile yayi don gaba ɗaya bata da gaskiya a al’amuran ta .

 

“Umma wurin ma’u Zani yanzu zan dawo “.

Kamin Umma ta kara mata magana tuni ta fice daga bukan ko takalmi babu sai Kallabi don Mayafi ma basa sakawa indai ba iyayen su bane ba mata .

 

Karo tayi da Ma’u wacce ta dade a wajen bukkan tana jiran Hasile , ke Ma’u mene kike yi anan ?.

 

Kallon Hasile Ma’u tayi kana cike da Raɗa tace ” Gafa su can sun tafi mutanen birnin .

 

Wani irin zabura Hasile tayi tana dafe kirji tare da fiddo da idanun ta tana cewa ” Sun tafi mene ? . Buɗe baki Ma’u tayi zata yi mata magana kawai sai dai ganin Hasile tayi ta fella da Gudu tana shiga ta cikin kararen tare da Daukar Hanya .

Ma’u meke faru ne ?. Ina ita Hasile? Muryar Umma ya katse Ma’u wacce tayi Saurin juyowa tana kallon Umma tare da yan kame kame .

 

Ma’u magana na keyi fa .

 

Umma yanzun zata dawo .

 

Kallon Ma’u Umman Hasile tayi tana Mata duban ban yarda daku ba . Kana tace , Ma’u me kuke kullawa? Zaku faɗa mun ko sai na saanar da Baffa Harɗo ?. Wani irin rawa jikin Ma’u ya hau kar² nan take ta fara rawar baki na marasa gaskiya. Dam..dama dama Hasile ne tace zata bi baƙin birnin can don tayi ilimi ,idan ta dawo zata koyar damu muma muyi ilimi .

 

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un….” Umma ta hau fadi tana nanatawa, Yadikko ne ta ƙariko inda suke tana faɗin ” Lapiya meke faruwa?”. Hummm Numfasawa Umma tayi cike da kawaicin su na Fulani ta kasa faɗa ma Yadikko halin da Ɗiyar nata ke kokarin jefa su .

 

Ganin tayi shiru yasa Yadikko Fahimtar wani Abin ne ya faru da Hasile wannan yasa ta saurin cewa ” Ma’u ina Hafsatu ? Ina Hasile ? Wani faɗan tayi ne ko mene?. Cike da Rawar jiki da tsoro Ma’u ta fara faɗa mata komai . Ai jin haka yasa Yadikko salati tana faɗin ” Kai wannan yarinya da akwai wauta! Ta sani ko mugaye ne ? Maza muje Mu sami su Baffa Harɗo mu sanar masu .

 

Ɓangaren Hasile kuwa wani irin dakatawa tayi da gudun da take yi tana saka hannun ta tare da Numfasawa,don wani sanyi taji hango moton su Billy da tayi basu yi nisa sosai ba. Kasantuwar Hanyar babu kyau kwata ƙwata .

 

Cike da zazzaƙar Muryar ta take ƙwaɗa kiran Adda Bilkisu…! Wato Billy wanda basu san ma tana yi ba . Cigaba da gudu tayi tana ƙarawa tare da waiwayon bayan ta don tasan a ko wani lokaci Fulanin rugar na iya cimmasu idan labari ya koma kunnin su Baffa da Liman .

 

**

Barka da Hutawa Sir Maleek.” Muryar daya daga cikin ma’aikaciyar sa ya katse sa , wanda yake zaune bisa Resting chair idanun sa a lumshe. A hankali ya motsa laɓɓan sa ba tare da yayi wani motsi ko buɗe idanun sa ba , ya furta ” Ya aka yi?” .

 

Kira ne daga Part ɗin Hajiya Kaka . Ana zaman meeting kai kaɗai ake jira . Ware Lulun idanun sa yayi yana cewa ” Okay ” .

 

Simi Simi ta fice daga Resting room ɗin. Mikewa Maleek yayi daga Ƙwancen da yake yana zura Takalmin sa daga shi sai gajeren wando da t.shirt ya nufi part ɗin Hajiya Kaka .

 

Assalamu alaikum.

 

Yayi sallama yana kutsa kan sa zuwa falon wanda gaba ɗaya hankalin su ya karkata ya dawo zuwa gare sa . Iyayen sa ne maza da mata , sai yayyun sa da kanni kuma wanda suke cousins ne wasun su. Amin wa’alaikassalam.

 

Muryar Abba Bukar Alh.Jibo da Daddyn Lagos ya katse su suna amsa masa Sallamar ciki har da Hajiya kaka wacce take ta washe baki taga Jikan nata ya girma yanda take so , Aure babu fashi yanda ta kudurta.

 

Murmushi Take yi tana kallon sa tare da kallon inda Nihla take itama gaba ɗaya kallon ta ya kare akan Maleek ne .

 

Taufiq ne ya kalli Maleek yana masa alama irin nasu da hannu wanda shi kaɗai yasan me yace masa , wannan yasa Maleek hade giran sama da ƙasa don yasan zaman nan babu karuwansa daya ko abun da ransa ke so . Juyawa yayi yana kallon inda Nihla take tana wani murmushi nan take ya watsa mata wani irin kallo yana takawa cike da Issa yana zama inda Taufiq yake .

 

To Alhamdulillah tun da kowa ya hallara Hajiya kina iya fara maganan da kika taramu domin ta . Mshaaallh Muryar Hajiya kaka ya katse su cike da girma tana cewa ” Kaman yanda kuka sani , Magana ce daya yasa na tara ku duka , shine maganan Maleek da Nihla .!

 

Shiru Maleek yayi ko Ɗagowa baiyi ba bare su fahimci wani Abu daga gare sa . Tsawon shekaru uku nake so naga na kulla wannan Aure yayi Albarka tsakanin ka da Nihla , amma sai a Wancen lokacin kace baka isa Aure ba . Wannan yasa na bari har tsawon wannan lokaci, yanzu nasan komai Alhmdlh ,a kuma ko wani lokaci za’a tsaida lokacin aure ko Maleek?.

 

Ɗagowa Maleek yayi yana kallon Momyn sa Wanda tayi tsimi tana zullumin kar ya tubure masu. Kallon Hajiya yayi yana ɗan Murmushi kana yace ” Hajiya har yanzu Ban shirya Aure ba .

 

Kai Abdool Maleek Bama san Shashanci wani irin magana ce kake yi haka ?. Muryar Alh jibo ya katse shi cikin fushi da nuna ɓacin rai .

 

Eh Daddy ban shirya Auren Nihla ba ,saboda Ba ita nake so ba . Ammie ne tayi Saurin katse sa tana cewa ” Amma yana dakyau kayi tunani , ita fa Wancen yarinyar baka san inda take ba ,Bamu san komai nata ba , to yaya za’a yi mu saka maka ido kayi ta jiran Wacce…..A’a rabu dashi da Shashancin sa . To Ka sani Nihla ita ce wacce zaka Aura kowa ya tashi . Muryar Alh jibo ya katse na Ammi cike da Wannan furucin .

 

A’a Maleek ba yaro bane , babu mai masa dole . Hajiya kaka tayi maganan tana jan numfashi kamin ta cigaba da cewa ” Kayi tunani Maleek na baka Nan da Sati biyu ,duk abun da ka yanke kazo ka same Ni ka faɗa mun dagani sai kai .

 

Muryar Nihla ne ya katse su cike da Sangarta tana cewa ” A’a Hajiya Maleek bafa aure ne a gaban sa ba ,kuma karya yake yi yana cewa yana da Wacce yake so . Ko a America babu Abun da yake yi sai watsewar sa da Zina da Turawa………..!

 

 

 

*A page 10 Free page na wannan littafin zai ƙare , maza ki hanzarta kar ayi tafiyar babu ke,don wani labari sai Shigowar Hasile Rayuwar Maleek anan zai amsa sunan sa na MR.ROMANTIC kar ki bari ayi babu ke . Regular payment ₦500 ne kacal . Vip payment ₦1000 via 6037312299 Mohammed A’isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932*

Leave a Reply

Back to top button