Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 63

Sponsored Links

CHAPTER 63

Can waje tafita inda bayawan hayaniya taje ta zauna haka kawai takejin tsanar basma har karkashin zuciyarta,tsana da da batajin tana mata irinsa wani irin baƙin ciki takeji aranta yanda ta ƙanainaye Ahmad dashima yake biya mata ko kunya babu da sunan rawa tsuka tayi tasakeyin ƙwafa taja tsaki yafi aƙirga duk yanda taso cire abun aranta kasawa tayi sai kawai tamiƙe tasake shiga can baya inda batajin motsi tana nan zaune tunani duk yayi mata bake bake acikin zuciya to wai ma mai hadinta dasu data zataringa damun kaita a kansu,wata zuciya tace kode kishi kike.

“Ina ina Allah ya sauwake nayi kishi a kan ma wani dalili zanyi kishinsa? saboda yana auren ki wata zuciyar ta bata amsa kinga kuwa dolene kiyi kishinsa hakade ta ringa surutai kaman wata zautacciya ita kanta batasan adadin lokacin da taɗauka nan zaune a wajen ba,ƙusƙus datake ji a bayan wasu motoci shi yaɗauki hankalin ta miƙa tanufi in takejin kaman magana na tashi daga inda take tsaye tana iya ganin mutane biyu duk da bata ganin fuskokin su suna tattauna wani abu abunda taji suna magana akai baƙaramin tada mata da hankali yayi ba,take hanjin cikinta hautsina taji wani jiri naneman ɗibanta kaman zata faɗi da sauri takoma baya dan karsu ganta bigewa tayi jikin madubin wani mota hakan yajayo hankalin su wajen daya daga cikin mutanen biyu yashiga cewa”waye waye a wajen?

Dube dube suka shigayi ita kuma tana ja da baya jin ɗaya yana cewa daya”karmu bari koma wayene ya kufce mana sai mun kamosa dan tabbas maishi yaji abunda muke tattaunawa,a ɗan rikice ɗayan yake magana yana cewa”dama saida nace maka muhadu a wani wajen kaƙi to gashinan yanzu asirin mu yana gabda to nuwa”kai shiru nace kai shiru ya dakawa ɗayan tsawa ganin yanda ya diririce duk ya firgice kai ba namiji bane abu kadan sai kanuna tsoronka a fili sai kace wata mace wallahi ko mace ba zatayi hakan ba,amma dubeka dan Allah abu ɗan ƙanƙanni sai kabi duk katada hankalinka sai kace kaine ɗaya mai rai ran nan fa guda ɗayace kuma kowama ɗayan gareshi.

Jin yanda ɗayan yakema ɗan uwan nasa faɗan yanutsu yabata daman rarrafawa dan neman wa kanta maɓoya tasan muddin tabari suka ganta to kashinta yabushe idan tace komawa zatayi inda tafito dole su ganta kuma su kamata idan suka kamata batasan abunda zasuyi mata ba,sannan yanda take ganin idon waƴan nan kashetama za su iyayi kuma sukashe banza ba abunda ba zasuyi ba dan kar asirin yatonu.

Neman maɓoya tashiga yi yayinda suma suke dube dube ido rufe dan ɗayan yana sake tabbarwa ɗan uwan nasa karka sake murasa koma wa

Rarrafawa tasomayi tana jada baya suma kuwa gadan gadan cike da tashin hankali suke nemanta bayan wanj mota tasamu taɓoya tana mai ajiyar zuciya can kuwa ta tsinkayo muryansu suna waya suna sanar wasunsu ansamu matsala akawo musu ɗauki dan basason koma waye ya kufce musu,ai kuwa tuni cikin Aisha ya ɗauri ruwa gashi bata da waya a hannu balle tayi tace akawo mata ɗauki,cikin abunda befi minti goma ba saiga zugan wasu ƴan daba da makamai rirriƙe a hannun su sai kafa wuƙaƙe suke suna kiran yau zasu sha jini,ji tai inama bata fito ba tayi zamanta ai ba lalle sai ta kalli inda suke rawan ba.

“Inason ku bincika mun nan sosai kar maishi yatsare mutum ne kai koma addabane sai kun gurfanar mun dashi nan dan barin maishi haƙiƙa hatsarine garemu,oya rufe bakin sa keda wuya waƴan nan matasan samarin su takwas suka shiga neman ta harƙarkashin mota sai sun leƙa mota kuwa kona uban waye sai sun buɗeta sun duba in kaga basu duba mota ba ka tabbatar a kulle motan take,kaman yanda suke kusantota haka ita ma takeyin baya tare da canza inda take zuwa wani wajen duk ta tsure suna cikin wasan ɓoyan nan kawai ɗaya daga cikin su ya hangota ta madubin wani mota buɗe wagegen bakinsa yayi yana cewa”oga gatanan naganta dago kannan da Aisha zatayi sukai ido huɗu da wanda ya gantan miƙewa tayi takwasa a guje suna biye da ita a baya.

Ahmad da tun fitan ta yake hankalce da ita saide Basma ta kanainaiye shi taki barisa balle yasamu daman binta a baya,malika dake masa liƙi yama magana tabita abaya saide koda malikan tafita bataga inda tayi ba,harma parkin lot ta tafi amma bataga koda mai kama da Aishan ba,harma ta ƙarasa bakin get din hotel ɗin ta tambayi mai gadi koya ganta amsa mata yayi da gaskiya shi bega yarinya mai irin wannan kaman nin da ta ambata ba,tade sake dubawa ta aciki.

Komawa Anty malika tayi cikin hall din da ake gudanar da shagalin txt massage ta turawa Ahmad dake zaune kusa da amaryar sa sannan ta sanar da yah faisal Aisha fa tafita tun dazu kuma tafita ta duba bata ganta ba.”what tun taushe tafita ya tambayeta da damuwa saman fuskan sa”wallahi yayah nima bansan sanda tafitan ba,dan sanda a kakira ango da amarya nace tazo muje muyi liƙi tace bazata ba toni najeni sai yah Ahmad ne yace mun yaga tafita naje naduba ina zata,nabi bayan ta kuma ban ganta ba har bakin get naje batanan nama tambayi mai gadi yace bega mai kama da ita ba,takare maganan hawaye na taruwa a idanun ta”riƙo hannunta yah faisal yayi yana yace”cmon za ganta ne ba inda zataje kode takoma gida ne kinkira su kinji ko taje?”nah tace dashi amma bara yanzu nakira ciro wayanta dake cikin puse ɗinta tayi takira wayan Anty hajia har sau biyu tana ringin taƙatse ba’aɗagawa hakan yasa ta maida akalan kiran nata ga malik bugu daya biyu ya dauka ko sallamar sa bata amsa ba tace kawai yaduba mata gida ko Aisha tazo”batazo ba ya amsa mata kansa tsaye yadaura da cewa tundazu ina gida Anty hajia sun je kai kayan lalle gidan Alh sunusi sauran yaran kuma na gidan Ammi amma lafiya kike tambayan Aisha ko batare take da ku ba?”tare da mu take saide tun ɗazu tafita bamu ganta ba,danAllah twince ɗan duba kagano mana ko tashigo bada saninka ba,duk yanda ake ciki kasanar da mu”ok ya amsa yana mai miƙewa dan duba dakin su ko tana ciki bega shigowantan bane.

Ahmad dake zaune kusa da amaryarsa ta saƙale hannunta da nasa hannun duk shige da fice da faisa da malika keyi akan idanunta zuciyar fal murna dan cewama take tafi ruwa gudu yarinya duk tazo ta tarwatsamun farin cikina,amma yanxu ganin yanda ta hango damuwa saman fuskokin su haka kawai ta tsinci kanta da farin cikin kuma tafiyan nata saiya wanke mata da duka wani taƙaici da shiga dazu,miƙewa Ahmad yayi danufi zuwa gunsu yaji sake rike masa hannu tayi cike da kissa tana cewa”mine kaɗan zauna mana ganan ƙawayena xuwa muɗauki photo kafin ka tafi duk yanda yaso zullewa abun ya faskara kaman hadin baki dan ƴan mata da samari layi layi suke zuwa a dauki photo kowa kagani riƙe da ƴar wayar sa a hannu da kyar Ahmad yasamu kansa yamike yanufi su inda su Nawwar ke zaune shiɗinma karfi hali yayi bawai dan yan daukar hoton bs karewa sukai ba.

Da murmushi saman fuskar sa amma kana gani kasan ina kanta fuska shima Nawwar din maida masa da murmushin yayi fuskansa da alamun damuwa yace”haryanzu basu ganta ba sannan anyi waya gida ancbataje gidan ba,bama kowa a gidan sai malik to ƴar uwar tace yashiga yaduba ɗakin su ko tana nan bega shigan ta bane yanzun nan yakira yace gaskiya bata zo ba kuma har mai gadi yafita ya tambaya shidin ma cewa yayi yau tunda garin Allah ya waye beganta ba.

Da sauri yanufi kofa Nawwar namara masa baya sai latifa da itama takebiye dasu dama tuni khalid da sapwan na tare da faisal din.

********
Aisha da tun zuwan yah faisal da Anty malika na farko ta hangosu amma wani saƙandamin ƙato ya rufe mata baki saboda rashin imani wasu biyu daga ciki suka riƙe mata hannuwanta gudun kartayi wani ƙwaƙƙwaran motsin da zajita.

Nan da nan suka jata zuwa bayan wasu shuke shuken fulawa sukayi maɓoya acan lokacin da Ahmad ya nufo wajen da nawwar duka akan idon Aisha da wayan nan da samarin ƴan daban,haka suka shiga bube bube suka haɗu duka dasu faisal amma ba Aisha ba labarin ta har tsakankanin motoci Ahmad yaje har kusa da fulawowin saura kaɗan ya hangota kiran da malika tayi masa yasashi saurin juyawa gareta,wannan yabasu daman sake canza wani maɓoyan koda yasake maida hankalin sa wajen bega komai ba.

Faisal ne yaƙara so wajen yana cewa”kaga kai kaje gida tunda Anty hajia na gidan ku ko taje can ɗinne,ni kuma yanzu zanje office nakai wani report duk yanda ake ciki sai kaimun waya”ok ya amsa a taƙaice yana mai sake duba cikin fulawan nan shide haka kawai yaji yakasa yarda da wajen.

Haka duka suka fita suka shiga motocin su suka tafi sai a sannan wayan nan samarin suka sauke ajiyar zuciya itako Aisha wasu hawayene masu dumi suka shiga zubo mata tabbas tasan tata takare,ɗaya daga cikin sune yashiga cewa”maƙwa bara nafita bakin get nagani ko sun tafi dan naga kaman wannan gayen yaso ramfomu yanda yake yawan juyawan nan kaman ze sake zuwa nakeji.”Ko nima haka har jikina yafara sanyi da wannan lamarin anƴa ma kuwa ba cinnaka a cikin su?cinnaka suna nufin police”nimade abunda nagani kenan kiran sunan su yashiga yi ɗaya bayan ɗaya”jaami moro magaa bagaa duka kuyi sauri kufita daga nan kafin a ganomu mu muhaɗu a mahaɗa kai kuma bad boy yi maza ka kawo mana motan nan nan muyi maza mubar nan kafin susuke zuwa,yana gama fadan haka kaman kiftawa da bismillah duka suka watsa Aisha na ganin abun da suke niyar yi tayu yunƙurin guduwa saide ko taku biyu mai kyau batayi ba,wani ƙoto ya kwarfeta jikake timm tafaɗi a ƙasa tasaki wani gigitaccen ƙara wani irin zafine ya ziyarci hannunta data faɗa akai har ƙwaƙwalwanta taji wannan zafin.

Mota suka cusata yayin da wanda taji ankira sa da makwa yafizgi motan a 360 yafita daidai wata mota kiran honda baƙa tashigo wajen kaman zasu daki wannan motan driver yayi saurin ɗauke kan motarsa ganin hakan wanda yake bayan wannan hodan yace da driver sa”yi maza kayi reverse mubi wannan mota da alama basu da gaskiya”angama ranka ya dade ya amsa sannan shima driver wannan hondan ya juya kan motar cike da kwarewa ya mara musu baya gudu suke saman kwalta duka ababen hawa hanya suke basu ganin yanda suke shara gudu kai kace tsaren mota suke kaman a cikin shirin american film ɗin nan fast&furious ganin ana binsu a baya makwa yayi yaza yadau waya yakira ogan nasu da yabasu aiki wayan tana shiga dama shikan sa kiran nasa yake jira yana dauka”oga ansamu matsala ganan wani mota tana da bamusan ko waye ba yana biye damu abunda yasamu cewa kenan ga ogan nasa daidai motar tasu ta daki wata daf data lalace tana dauke da lodin kaya ji kake kiiiiiiiiiiiiiiii kau…

Masoyana abun Alfahari dake bibiyar wannan littafi a duk inda kuke a faɗin duniya ina muku fatan alheri.

Sannan ina mai neman afuwanku bisa jina shiru da kuke hakan yasamu asalina sabida rashin karfin jikina

Leave a Reply

Back to top button