Hausa NovelsNihaad Complete Hausa Novel

Nihaad 59

Sponsored Links

💖 NIHAAD 💖

59

Mami na fitowa bangaren Janar Aunty Hassana ta bi ta da kallo ganin yanda take kuka, can ta kalli Aliyu da shi ma ya bi ta da kallo yana tsaye parlon, Aunty Hassana ta bude hannu murya kasa kasa tace “Lafiya na ganta haka?” Aliyu ya daga kafada yace “I don’t know….” Aunty Hassana tayi shiru, can ta mike ta nufi bangaren yayan nata da sauri, A parlonsa ta samesa yana dube duben wasu takardu, ta nemi waje ta zauna da damuwa tace “Yaya lafiya naga Aunty fatima ta fito tana kuka?” Janar ya daga kai ya kalleta yace “Toh me ya hanaki bin ta ki tambayeta? Ko ita ta turo ki ki tambayeni?” Aunty Hassana ta ɗan yi yaƙe tace “Haba ai bata ma tsaya ta saurareni ba, kawai dai i was just worried ganinta da nayi cikin wannan yanayin shi yasa na fara shigowa nan, amma bari in je in sameta” Tana fadin haka ta mike har ta nufi kofa sai kuma ta dawo tace “Ya jikin Khalil din Yaya?” maimakon ya amsa mata sai ya daga wayarsa dake ring wanda wani babban sojan ne ke kiransa, kofa ta nufa ta fita daga parlon duk kanta a daure, to lafiya ta fito tana irin wannan kukan kamar warce uwarta ta mutu, ko dai sakinta yayi? Tunanin hakan ba karamin dadi yayi ma Aunty Hassana ba, da ace bata yaɓa mata magana bane dazu da ta shigo parlon da sai ta bi ta bangaren nata, amma yanzu da kunya ai ta bi ta, kyaɓe baki tayi a ranta tace “In ta yi wari ma ji dai” Daga haka ta tafi bangarenta don Aliyu ma ya bar parlon. Mimi na zaune gefen Mami duk hankalinta a tashe ganin yanda Mamin ke kuka, tace “Ko ma menene don Allah ki daina kukan nan Mami for the sake of ur health” Mami dai ta kasa daina kukan da take, she still can’t believe abubuwan da Khalil ya gaya mata, ita in particular zai yi fooling haka? Ita zai yaudara haka ya kawo yarinya for almost 2 months tana gidan sai yau ne zai bude baki yace wai matarsa ce, ta ina hakan zai yiwu? Ai bazai taɓa yiwuwa bane tunda ba film ake acting ba, zata nuna masa ita ta haifesa ba shi ya haifeta ba, Ta jawo wayarta for the 4th time ta kira Aunty Maryam amma bai shiga ba, har ta tashi zata dau mayafi zuwa gidan Hajiya Safeenah sai kuma ta tuna to idan ma taje can din kukan me zata ce mata tana yi? Me zata ce mata ya faru? Ai bata jin zata iya sanar mata da wannan mugun abu da Khalil ya aikata, haba wannan ai abun kunya ne, Mimi ta fashe da kuka tace “Mami na tambayeki me ya faru kin ki gaya min, kuma sai kuka kike, don Allah kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki koma menene” Mami ta fashe da sabon kuka tana fatan da ma ace duk wannan abun mafarki ne….. Tun bayan fitar Mami khalil ya kasa komawa ya kwanta, gaba daya hankalinsa yayi mugun tashi, bai ki ya ga fushin Abbansa ba, amma baya wasa da fushin Mami, he strongly detest anything that will make her angry, bai taɓa zaton haka zata dau al’amarin nan da zafi ba, he never expect that from her, he was thinking Abbansa ne idan yaji zai kusan harbesa, sai yaga Abba ma bai dau issue din personal ba, sai Mami da ya dau hope ya daura mata yana ganin ko wani bai goyi bayansa ba ita zata goyi bayansa dari bisa dari, A hankali ya zare drip din hannunsa ya sauka daga saman gadon duk da yanda yake jin jikinsa ya nufi kofa ya fita, Janar ya daga kai yana kallonsa, tunda khalil ya kallesa sau daya ya dauke kai ya nufi kofar fita daga babban parlon, Janar yace “Hey Mr Man, koma ka kwaso drips din da magunguna da ka bar min a dakin….” Khalil ya juya ya koma dakin ya kwaso duk kayan treatment din nasa ya fito, Janar ya bi sa da kallo sai kuma yace “Ita yarinyar da ake magana akai tana ina?” Tsayawa khalil yayi kamar baxai juya ba sai kuma ya juyo yace “Can gidana” Janar yace “Tana ciki aka kulle gidan?” Khalil yayi shiru, Janar ya dau wayarsa zai kira daya daga manyan sojojin dake tare da shi, Khalil yace “Daga gidan Mami take yanzu” Janar yace “Toh wa ya bata izinin zuwa? Sannan wa ya kai ta har ya bude mata gidan?” Shi dai khalil bai ce komai ba, can dai ya juya ya fita daga parlon. Hajiya Amina ce tayi sallama cikin parlon Mami, Mimi tayi saurin tashi don kofar bedroom din a bude yake ta nufi kofa ta fito tace “Ina yini Mama?” Hajiya Amina na kokarin kutsa kai ta shige dakin tace “Lafiya lau ina Hajiyar?” Mami tayi kamar bacci take, hakan bai hana Hajiya Amina karasawa cikin dakin ba, tace “Hajiya rasuwa aka min nace in zo in gaya maki” Babu yanda Mami ta iya haka ta bude idonta ta mike zaune tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, wa ya rasu?” Hajiya Amina na kallonta tace “Makociyar kanwata Nana, kinsan muna mutunci da matar, yau ta rasu wajen haihuwa” Mami tace “Allah sarki, Allah ya ji kan musulmi” da mamaki Hajiya Amina tace “Lafiya na ganki haka Hajiya?” Mami tayi yake tace “Wallahi bana jin dadi ne” Cike da damuwa Hajiya Amina tace “Naga idanuwanki sun kumbura kamar warce tayi kuka? Kukan me kike haka” Mami tace “Har da baccin da bana samu yanzu” Hajiya Amina tace “Ayya, Allah ya sauwake, ya Khalil ya kara ji duk da na shiga bangaren Janar din ban gansa ba” Mami ta daga kai da sauri tace “Baya can?” Hajiya Amina tace “Aa ya fita gaskiya kuma ai ruwan bai ci ace ya kare ba” Mami bata kuma cewa komai ba, Hajiya Amina ta nemi waje ta zauna, duk wani salon bugan ciki babu wanda bata yi ma Mami ba ko zata samu hint din abinda ke faruwa a gidan amma Mami sai kaucewa take, gashi ita dai bata ga ana hada kaya ba alamar anyi saki, ta dai gaji da zama ta mike tace “Toh Allah ya kara lafiya Hajiya, bari in je in ci gaba da abinda nake yi” Mami tace “Toh Nagode” Daga haka ta fita daga dakin, Mami ta dau wayarta da sauri ta shiga kiran Noor, har ya katse Noor bata daga ba sai ga shi ta biyota, Mami ta daga tace “Khalil yaje gidan ne???” Noor tace “Aa, amma muna hanya Mami, Sojojin ne suka ce Abba yace su maida mu gida” Mami tayi shiru ta ma rasa abinda zata ce, can ta katse wayar kawai, ta kara dialing number Aunty Maryam ko zata sameta amma still baya shiga, to ina ta shiga haka??? Tun da Nihad ta ga anguwan da suka shigo jikinta ya kara yin sanyi taji kamar ta fashe da kuka, a duniya babu inda take jin bata son ganin kanta irin wannan gidan da za su, har cikin ranta bata son gidan, ta dinga kokarin ganin hawayen dake taruwa idonta bai zubo ba amma ina, sai da ya zubo, ita dai Noor na zaune ta daya end din tana ta danna wayarta, har suka iso gidan bayan an idar da sallan magrib, Noor ta bude motar ta sauka tana kallon Nihad dake dannar kanta kar ta fashe da kuka, A hankali Nihad ta bude motar ta sauka, Noor ta nufi entrance din gidan Nihad na biye da ita tana tafiya a hankali tana goge idonta, har sannan zafi take ji sosai idan tana tafiya, Noor ta jira ta har ta shigo parlon don Abba ya sanar mata suna isowa direct su nufo bangarensa, babu kowa main parlor din, Nihad na biye da Noor walking slowly har suka shiga bangaren Abba, Noor tayi sallama kafin ta shiga Nihad ta ki shiga ta tsaya bakin kofar gabanta na faduwa, Noor ta juya ta kalleta, Nihad ta sunkuya da kanta, sai kuma ta shiga cikin parlon, Sojoji ne su hudu a tsaye parlon Janar na basu instruction, Noor ta tafi saman kujera ta zauna don in dai ka shigo parlon Janar baya barin ka zauna a kasa, Nihad dake bin parlon da kallo ta rakube jikin tsadadden kujeran dake parlon tana kallon katon hoton Janar dake manne jikin bangon parlon yana sanye da kayan soja da hularsa, daga kasa an rubuta Lieutenant General Abubakar I Jikamshi, lokaci daya sojojin suka juya suka nufi wani kofar daban wanda ba sai sun bi ta babban parlon gidan ba zasu fita compound, Noor ta kalli Abbanta tace “Good evening Sir” maimakon ya amsa sai ya kalli Nihad yace “Ke ya sunanki?” Nihad sai da taji gabanta ya fadi don muryarsa kadai ma ya isa firgita mutum, Ta hadiye abu da kyar tace “Sunana Fatima” Yace “Yar wace gari ce?” Tace “Kano” Janar ya kalli Noor yace “Go and call me Ibrahim immediately” Noor ta mike ta fita daga parlon, ba a dau lokaci ba sai ga ta ta dawo bayan taje ta sanar ma Khalil Abba na kiransa, ta zauna tace “Abba yana zuwa” Janar na nuna ma Nihad kujera yace “Have a sit” Da kyar ta girgiza kai tace “Zan zauna a nan” A bit strict yace “Tashi ki hau kujera” Da sauri ta mike ta zauna saman kujeran ba tare da ta shirya hakan ba…. Khalil da ya fito part dinsa yana ganin Aunty Hassana ta daya staircase din tana saukowa ya rage pace dinsa, tun bayan da ya fito daga bangaren Abba ya shiga dakinsa bai fito ba sai yanzu, sallan magrib ma a dakin yayi, kuma har zuwa sannan banda shayi da Mimi ta kai masa babu abinda ya ci, Daga sama har kasa Aunty Hassana ke kallonsa, shi ko ya ki kallon direction dinta, can kawai ta nufi bangaren Janar ganin can din shi ma za shi, Khalil ya tsaya ya bi ta da wani kallo yaji kamar ya juya ya koma dakinsa, bude kofar Main parlor din aka yi, sai ga Aunty Maryam ta shigo da karamin trolly dinta, Khalil ya zaro ido yana kallonta ko kiftawa babu, Aunty Maryam ta sauke ajiyar zuciya ganinsa don duk tunanin ko Janar yayi masa wani abun ne da taji Mami na ta kuka a waya, ta nufosa da sauri tace “Ina Mami??” khalil ya kasa ce mata komai don ba karamin girgiza yayi da ganinta ba, ta karaso tana kallonsa kafin tace komai ya wara ido, cike da karfin hali yana murmushi yace “Aunty saukan yaushe? Ko dai dama kina kasar ne” Aunty Maryam ta galla masa harara tace “Ehh ina kasar, Mami idan bata daga ma mutum hankali ba bata jin dadi ai, ga dai ni Allah ya kawo ni lafiya, tana ina?? Shi kuma ya ga daman fitowa da kai daga guardroom din kenan….” Khalil dai sai zufa yake yana kirkiran murmushin yake ya kasa ce mata komai, duk maganar da take yi ma shi ba fahimta yake ba, Aunty Maryam tace “Ji wai ina maka magana kana min Murmushi kamar sha sha sha, tambayarka nake ina Mami??” Ya hadiye wani abu da ya tokaresa da kyar yace “Upstairs…” Dai dai nan Noor ta fito daga bangaren Abba, ta zaro ido ganin Aunty Maryam ta taho da gudu ta rungumeta tace “Aunty daga ina kike haka?” tace “Wallahi daga Uk, tun bayan da muka yi wannan wayar dake hankalina ya kasa kwanciya kawai nayi ma Abbansu Zeenah magana ya kuma bar ni na taho, me yasa Mami take haka don Allah, yanzu ba ga Khalil din ba, duk ta bi ta daga min hankali, haka kawai taje cutarta ya tashi a banza, komai baxata bi sa a sannu ba” Noor ta amshi jakarta tana Murmushi tace “Mu tafi sama Aunty, sannu da hanya” sai kuma ta kalli Khalil da sauri tace “Lahh Abba is waiting for you tun dazu fa yayanmu…” Bai ce komai ba ya nufi parlon yana tafiya a hankali, Aunty Maryam ta bi sa da kallo sannan ta kalli Noor tace “Tun yaushe ya sa aka sake sa?” Noor tace “Tun da safe, da Abban ya dawo ya sa a fiddo shi, kinsan ba shi da lafiya so he is under medication now” Aunty Maryam ta girgiza kai a ranta tana Allah wadai da mugun halin janar, sai kace ba ɗan da ya haifa ba, Sama ta nufa Noor na biye da ita a baya rike da karamin akwatin ta, dai dai kofar shiga parlon Mami suka hadu da Mamin, Aunty Maryam taji gabanta ya fadi ganin idanuwan Mami and how weak she looks, hankali tashe tace “Subhanallahi Mami, lafiya?? Me ya sameki haka?” Mami ta kasa cewa komai ganin er uwartata kawai ta fashe da kuka sosai tana girgiza kai, Aunty Maryam ta rungumeta hankalinta a mugun tashe tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Yaya me ya faru? Don Allah ki min magana What’s happening?” Cike da karfin hali Mami tace “Janar ya kira yana jirana a parlonsa, mu tafi can din….” Iyakar tashi hankalin Aunty Maryam ya tashi a lokacin, ita kanta Noor jikinta yayi sanyi sosai ta koma gefe ta dinga kallon Mami, Aunty Maryam ta kama hannun Mami ranta a dagule tace “Mu je parlon” yau ta dau alwashin sai ta ma Janar wankin babban bargo in har dalilinsa Mami ta shiga wannan damuwar take kuka haka, dama tara sa kawai take, tana rike da Mami zuciyarta na bugawa tace “Mu je parlon nasa” Mami dai na biye da ita kawai. Tun da Khalil ya shigo parlon yayi ma Aunty Hassana kallo daya ya nemi kujera ya zauna, Aunty Hassana bata fasa maganar da take ma Janar ba tace “Shine fa ta kirani wai bata sani ba ko ta maka wani laifin ne, kasan halin kauyawan nan da rashin wayewa yanzu yanzu sai su juya wannan lamarin, barin suna ganin ba uwa daya uba daya bane, to wani tsiyar suka taɓa kullala mana har Allah ya kawo mu iyanzu? ni nasan duk a kullace suke da kai tun da muka tare nan gidan shekara kusan shidda kenan babu wanda ya san inda muke iyaka idan zaka masu aike ka bani in tura masu, toh su ai ba haka suka so ba, sun fi so su yi ta maka zarya wasu in sun zo ma sai su shekara basu tafi ba ga ka shugaban kasa, Ya dikko ma ta kirani jiya….” Janar ya dakatar da ita yace “Kee Hassana, maganar da ta kawo ki kenan??” tayi shiru, yace “Toh bana son zancen, kowa ya dade bai yi tunanin dake ransa ba, clear??” Sai kuma ya dauke kansa ya kalli Khalil da idonsa ke kan Nihad, ita kuwa taki barin su hada ido ta sunkuyar da kanta gabanta na faduwa, Aunty Hassana ta gyara zama tana kare ma Nihad kallo tana mamakin ita kuma uban me take yau a parlon Janar, ita dama ba zancen da take ma Janar bane ya kawota, aa dalilinta na shigowa daban amma sai ta fake da wannan zancen, dai dai nan Mami da Aunty Maryam suka shigo parlon, Tsabar tashin hankali Khalil ji yayi dama kasa ta bude masa kawai ya shige, ya kasa hada ido da su biyun, Aunty Maryam tayi mugun mamakin ganin Nihad zaune parlon, can ta kalli Khalil sannan ta sake kallon Nihad din cike da mamaki, to me ke faruwa, ba Mami tace mata ta koma gidansu ba, yaushe kuma ta dawo nan, sannan me take yi a parlon Janar, Aunty Maryam ta kalli Janar dake kallonsu lokaci daya ta ɗan hade rai, babu yabo babu fallasa tace “Barka da dare Janar” Yace “Barka” Tana rike da hannun Mami suka tafi 2 seater suka zauna, Aunty Hassana sai kallon ikon Allah take, yaushe ita kuma wannan galallawar ta dawo kasar, Can dai tace “Sannu Maryam, yaushe a gari” a takaice Aunty Maryam tace “Daxu na sauka, ya yaran?” Aunty Hassana tace “Lafiya lau, sannu da zuwa” Daga haka duk suka yi shiru a parlon, Nihad dai sai kallon Aunty Maryam take, she don’t know if she should be happy or not, duk da damuwan da ya cika xuciyar Aunty Maryam haka ta mata murmushi, Nihad ta mayar mata da murmushin amma na karfin hali, cikin sanyin murya tace “Sannu da zuwa Aunty” Aunty Maryam tace “Sannu Nihad” Janar ya nisa, sai kuma yana kallon Nihad ya nuna mata Khalil yace “Wanene wancan?” Khalil yaji gabansa ya wani fadi, he wish rana irin ta yau baxai taɓa zuwa ba, amma dole ne ya zo, ya jinginar da kansa jikin kujeran da yake zaune zuciyarsa na bugawa, gashi dai duk da wannan tashin hankalin nasa yana jin takaici yanda za ayi magana a gaban Aunty Hassana, Ita kuwa Aunty Hassana sai gwaggwale ido take a parlon tana son jin dai me ke faruwa, Nihad ta kalli Khalil ta sunkuyar da kanta a hankali, ita ma har sannan gabanta faduwa yake sosai, a ɗan tsawace Janar yace “Ke magana nake maki, or are you deaf?” Lokaci daya hawaye ya kawo idon Nihad ta daga kai tana kallon Khalil, duk a tsorace take, da zaka kalli yanda kirjinta ke heaving sai ka tausaya mata, Janar ya kula da she is afraid kuma a rude take, Sai yayi calming voice dinsa yace “Fatima ko??” Nihad ta kallesa da sauri ta gyada masa kai hawaye na sauka idonta, ya nuna mata gefensa calmly yace “Dawo nan” A hankali ta tashi ta dai daita tafiyarta ta nufesa walking slowly, ta durkusa inda ya nuna mata, ya nuna mata saman kujeran yace “No, nan zaki zauna” Kasa kallonsa tayi ta mike a hankali ta zauna gefensa gabanta na faduwa kamar zai fito, Aunty Hassana dai sai kallon ikon Allah take, yau ga sabon salo, Mami dai kanta na kasa, Aunty Maryam kuwa sai kallon Janar take kamar ta shakesa ta huta…. Speaking Calmly Janar yace “Kinsan wancan mutumin dake zaune Fatima?” Nihad ta kara kallon Khalil ta gyada kai, Janar yace “To wanene?” Tana tsoron tayi shiru Janar ya mata ihu, sannan kuma ita bata gane kan tambayar Janar ba, she is just confuse, kamar ya gane she is confuse yace “I mean, meye tsakaninku Fatima?” Ta sake Kallon Khalil with her heart beating so fast, shi dai idonsa na kan Ac dake tsaye parlon baya ko kiftawa, a hankali tace “Ya zauna gidanmu” Janar na gyada kai yace “Good… What took him there?” Cikin sanyin murya tace “He was our driver….” Ba Janar ba har Aunty Hassana da su Mami sai da suka kalli Khalil da sauri, shi dai idonsa na kan Ac, Janar look a bit confused ya dinga kallonsa, can yace “Kamar yaya fatima?” Ta sunkuyar da kanta tace “Driving dinmu yake yi, Abbana na biyansa kudi” Janar yayi shiru for almost 30 seconds, can ya daga kai ya kalli Khalil, wanda shi ma Khalil din kallonsa yake this time around, su Aunty Maryam kuwa sai kallon Khalil din suke da mamaki, Janar ya dauke kansa ya sake kallon Nihad yace “For how long?” Nihad na jan fingers dinta a Hankali tace “For almost a year” Janar ya sake yin shiru, sai kuma yace “A gidan naku yake zama kuma?” Nihad ta gyada kai tana wasa da yatsunta tace “A chalet din gidanmu yake tare da sauran masu aiki a gidanmu” Lokaci daya hawaye ya kawo idon Aunty Maryam, Khalil ya rike kansa….. Janar dai yayi shiru kamar iyakar tambayoyin da zai ma Nihad kenan, bayan wani ɗan lokaci ya sake kallonta yace “Did u have an idea of nawa Abban naki ke basa?” Nihad ta kalli Khalil, a hankali ta girgiza kai tace “Nima ban sani ba” Janar yace “Sai kuma me ya faru da har ya taho dake garin nan?” Hawaye ya cika idon Nihad a hankali cikin sanyin murya tace “Abbana ya min aure da shi” Sai kuma ta rufe fuskarta jikin kujera tana kuka a hankali, Aunty Maryam tayi mutuwar zaune a inda take saboda yanda ta girgiza da abinda Nihad tace, ta dinga kallon both Nihad and Khalil a tare, with her mouth agape, Aunty Hassana bata san sanda ta mike tsaye tana kallonsu ba ita ma, Mami dai sai hawaye take ta kasa dago kanta, Janar ya dafa shoulder din Nihad yace “Wani anguwan ku ke a Kano?” Ta dago kanta hawaye caɓa caɓa a fuskarta cikin rawan murya tace “Nasarawa GRA” Janar yace “Ya sunan Abbanki?” A hankali Nihad tace “Alhaji Ibrahim Sadeeq” Janar yayi shiru yana gyada kai, can ya mike ya shiga bedroom dinsa sai ga shi ya dawo rike da Makulli a hannunsa, ya ajiye ma Khalil Makullin yace “Dauketa ku tafi can gidan naka, ku shirya gobe xa mu tafi kanon gaba daya” Khalil ya dinga kallon Abban nasa, Janar ya ɗan masa tsawa yace “Baka ji me nace bane” Khalil ya mike yana kallon Mami da ke ta hawaye, Ita kuwa Aunty Maryam tsabar shock ta kasa fa rufe baki, Janar ya kalli Nihad yace “Ta shi ku tafi Fatima, Allah ya tashe mu lafiya” A hankali Nihad ta mike har sannan hawaye na makale idonta, Khalil ya kalli Mami da kanta ke kasa, Sai kuma ya kalli Abbansa, Wani kallo Janar yayi masa, ya nufi kofa Nihad ta bi bayansa har suka fita daga parlon, Aunty Hassana dake ta wurga ido, tana rawan baki tace “Yaya, ban gane ya tafi da ita gidansa ba, kai ka yarda…..” Janar ya dakatar da ita yace “Fita ki ban waje Hassana”

*Kiyi kokarin sauke nauyin 500 akan ki Aunty and Mama*

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Via 07087865788

 

https://instagram.com/ruuscollections?igshid=MzNlNGNkZWQ4Mg==
Ruuscollections turaren wuta and more we got you everything scent,long lasting fragrance at very affordable price, change or complete refund if you don’t like any of our product in Sha Allah
Arabian,Traditional,English,Khumra ,Oil perfumes,Koleccha,Morphingmist,Roomfreshener,
Armpit powder, Mouth freshener,Laces ,Shoes,
Bags,Atamfa, 07025393114

Leave a Reply

Back to top button