Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 61

Sponsored Links

CHAPTER 61

Jujjuya ledan data tamiƙa masa yafara sai can yace”hajia gaskiya aikinki mai saukine sannan da wuya abunda yasa nace haka nide nawa zubawa ne kawai amma sakashi yaci wani abun ko yasha wannan badaga ni bane dan haka shine wuyan da nace,dole sai annemi wanda ze ja hankalin sa yaci abincin ko kuma yasha juice ɗin,shin kina da wanda ze aiwatar miki da wannan ko babu idan babu ko kinga xubawan asarace.

Saurin ƙatseshi tayi ta hanyan ɗaga masa hannu tace”banason jin an anbaci asara nan”to hajia ga shawara kice da amaryar tayi iya yinta dan ganin ta bashi koda juice ne yasha”shawara mai kyau tace dashi harta juya zata tafi sai kuma ta juyo tace dashi ka kula wajen zubawan kar wani yagani”baki da matsala inde wannan ne kede kiyi ƙoƙarin dan ganin yasha ko yaci wani abun shine kawai daga haka sukai sallama da cewa sai yajita.

Tana barin wajen daddy ishaq ya ƙwashe da dariya yaron sa kamilu ya matso kusa dashi yana cewa”oga da alama waƴan nan mutanen basuda imani haryanzu idan bacin haka yaushe asiri yake tasiri aiko yayi naɗan wani lokacine”ai kamalu basu sani ba kuma bazasu san kuskure da suke tabƙawa ba harsai ranan da reshe ya juye da mujiya tukun zasu sani,ai yanzu idona nakan duk wani motsin su kafin a gama wannan bikin ko zan samu nasaran ƙusawa cikin masarautar su ko kuma sai yayi shiru…..”karka damu oga in sha Allah saikayi galaba a kansu wannan karon Allah yana tare da mai gaskiya yafaɗa cike da bashi gwarin gwiwa”hakane ya amsa yana komawa ciki.

Hajiya mariyah gaskiya keɗin gwaskace shiga irin wannan ƙatsurgumin dajin wallahi tunda muka tafi bansamu nutsuwa ba harsai da naga munshigo gari kuma cikin gida sannan naji hankalina ya kwanta,dariya sosai hajiya mariya tayi tana kallon hajia shema tace”ai bari shema nima kaina dayace mu fita a hankali karmu taka musu yara suna wasa wallahi karfin hali kawai nayi amma da kin lura lokacin zakiji yanda cikina yake ƙuji wallahi dariya suka kece dashi a tare sannan hajiya mariya ta kwalawa mai aikin ta kira ta kawo musu abinci da abun sha,saida sukaci sukai nak sannan suka daura sabon hira dakuma yanda zasu ɓullowa basma tabawa Ahmad koda juice ne yasha kada asamu matsala dan sanin halin basma da shashancin kartasa muyi zuwan banza.

“Kaman kin shiga zuciyana kin gani abunda nake tunani kenan nima shema tunda boka yabani maganin hanyan da zanbi nazuba masa a abinci nake ta tunani to wannan an wuce wajen dan fitan da nayi da muka shigo ai naje nasami wanda zemun wannan aikin ne saide shima ce mun yayi nashi mai saukine wanda zesa ya danci wani abu ko shan waje abun shine kawai.

Ɗan shiru sukai kaman masu tunanin wani abun sai can hajia shema tace”yauwa gawani shawara ki kira ita basman yanzu,ba musu kuwa hajia mariya ta dauki waya ta kira basma bugu daya biyu sannan aka ɗaga tunma kafin tayi magana tace”kisameni a ɗakina yanzu”to mummy kin dawone?”eh na dawo yi sauri kizo karki batan lokaci muna tare da mummynki shema kuma tafiya zatayi yanzu”tom mummy gani nan zuwa daga haka ta katse wayan tana kallon salaha tace”ina zuwa yanzu mummy nakira na daga haka tasa kai tafita daga dakin tabar ƙawayenta da mai makeup dasuka gayyato.

*********
Wow kinga yanda ƙunshin nan yamiki kyau kuwa?gaskiya na dade banga wanda gyara ya amshi jikinta ba farat ɗaya irin ki,takare faɗin haka fuska ƙunshe da murmushi.

Murmushin ita Aisha ta maida mata tace”kai hajia karki saka kaina ya kumbura naringa jina a sama,dariya tayi tana riƙe haɓa tace oh ƴar nan dan ma kinsamu na yaba to bani ba bari wanda yakawokin yazo dan nasan shima kansa sai yayaba yakuma karamun da tuƙwici dan wannan gyaran babbar harkace dukda yace keɗin ƙawarsace amma ba komai nasan ze yaba kuma dan Allah ko raran aurenki karki mance da nan kizo ko gayyatana kiyi har gida zanje namiki gyara na musamman na amare tsawon sati biyu zamuyi wallahi sai kinga yanda jikinki ze dawo tamkar balarabiya ai ingaya miki munan bama wasa wajen inganta aiyukanmu kayan mu masu ingancine dan daga sudan muke oder nasanma dole yallaɓe yayaba irin kyaun da kikayi”hajia kenan kita wani yayaba aiko be yababa ni nasan aikinki yayi tunda naji wasu ƴan canje canje ajikina ba karya.

Gyara zama tayi tana fuskantar ta tace”yama kike da suna?”Aisha ta amsa mata da Aisha”yauwa Aisha kinganni nan niba karamar yarinya bace dazaku raina mun hankali kuna wani ɓoɓɓoye mun shi yace ke ƙanwarsace amma irin kallon da yake miki yafi karfin yah da kanwa,zakice na fadamiki wataran tabbas akwai soyayyarki na gani a kwayan idon sa,ƙila shima besan yakamu da son naki ba,amma nide abunda zance dake shine ki kula karkiyi wasa da wannan daman naki,sau ɗaya tak kake samun dama a rayuwa dan haka karkiyi sake wannan daman yabarki.

“Kaman yaa hajia?bayan mudin ba wasu masoyan bane babu komai tsakanin mu kaman de yanda kika fada ina ganin kawai hasashe kawai kikayi amma ina ni ina auren mutum kaman Ahmad ina ga gami,ai kinsan yafi karfina kota wani fanni,dariya hajiar nan tayi sosai saida ta tsagaita sannan tace”lalle Aisha har yanzu kina fama da yarinta amma in banda haka ina ruwan so da matsayi kyau ko muni so ba ruwansa da wannan karkiga matsayin da kikaga Ahmad yana da ya tsorata ki haƙiƙa ninasan koman daren dadewa Ahmad ze furta miki kalman so kar gayun sa da kuɗinsa ya tsorataki abu daya zan faɗamiki shine ki kasance wayayya ki kuma kasance ƴar gayu dan mace da gayu akasanta sannan kiyi kokarin sanin me dame yafiso me yafi birgesa sannan kuma meyafi sha’awa wani irin abinci ko abun sha yafiso arayuwarsa wani irin kwalliyane yafi burgesa ga ɗiya mace shin ma’abocin son saka ƙananun kayane ko yafi sha’awar kayanmu na hausa wani irin ƙamshin turarene yafi burgesa da ɗaukan hankalin sa,sannan uwa uba ki iya girki wannan shine babban makaminki ƴa mace duk kyaunki da iya ɗaukan wankanki idan vaki iya girki ba kinzama hotiho baki da sauran amfani sannan muhallinki yazama ko da yaushe ashare cikin ƙamshi.

“Hmmm wai hajia meyasa kike faɗamun duka wannan abun?kanta tsaye tace”saboda nasan wataran zeyi miki amfani kuma inason kifara rihazal daga yau ai tsakanin mata da mijinta babu shamaki idan yace yafison yaganki daga ke sai ɗan kamfai yi kokarin ki zauna masa hakan dan faranta masa”hajia mubar wannan maganan kawai dan ko ɗaya bana fahintarki,tafaɗa cike da ƙosawa dakuma gajiya da maganan dan hajiyar nan idan kabiyeta irin matan nan ne masu shegen surutu da son jin ƙwakwafi da son shiga sharo.

Basma tafiya take ma aikatan dake aiki a gida sai zubewa suke suna gaisheta duk inda ta wulga amma ko kallo basu isheta ba,tana gab dashiga ɗakin hajiarta suka kusa cinkaro da lantana mai aikin gidan nasu tafito daga ɗakin ɗauke da kayan dasu hajia suka gama cin abinci batayi wata wata ba ta zabgawa lantana mari da hankaɗata gefe tanunata da yatsa cikin ɓacin rai take magana”wace iriyar yarinya ce ke?kina tafiya kaman tunkiya kai a ƙasa tashiga dudduba jikinta taɗaura da kinyi sa’a da baki batamun jiki ba da yau sai kin raina kanki.

Lantana data maru dan marin yashigeta gashi kuma da tray a hannun ta balle tasamu zarran dafe ƙuncin ta sai hakuri take bata a zahiri amma a zuciya sai Allah ya isa datake jamata tare dayi mata mummunan fata a gidan auren ta”ɓacemun da gani sai warin baki kike anƴa yau kinma wanke bakin kuwa?cike da jin haushi lantana ta amsa mata dacewa”dayake man wanke bakin da kika sayumun sun ƙare tun wancan wata,dakamata wani irin gigitaccen tsawa tayi dayasa lantana zabura ta kwasa da gudu saura kaɗan ta ɓarar da kayan hannun ta,ganin yanda ta kwasa a guje yasa basma taɓe baki tana cewa kaga wani shashanci kuma.

“Kedawa?Mominta ta tambaye ta sanda ta bude ɗakin ta shiga dan ganin yanda tayi kicin kicin da fuska”ni da wa in banda wannan shashashar mai aikin naki mummy wallahi bakiji yanda take hamami ba”kinga zauna nan ya’isa ni banji wani hamami da take ba,sannan kamata kibar wannan ɗabi’ar nan naki na wulakanta ƴan aiki tunda kinsa hakan yana daga cikin abunda Ahmad yatsana ke bazaki iya controlling temper ɗinki bane ba”mummy takira sunan tana wani marairaice fuska”to ai shikenan amma hakan yana daga cikin abunda bazamu nema miki mai aiki ba,dan gudun samun matsala tsakanin ki da mijinki,zatayi magana tayi saurin katsata da ga mummyn ku nan ki gaisheta tafiya zatayi yanzu dan su hanan su zo akan lokaci.

“Ina yini mummy ta gaisheta bayan ta juya tana fuskantar ta”lafiya lau baby ta amsa da fara’a kwance saman fuskanta taci gaba da cewa yau kuna da party babban harka tunda yau ango ze halarci wajen,dawani irin sauri takai tubanta ga hajia shema ta zaro ido danson jin ƙarin bayani eh ai ɗazu daddynki yakira mahaifin sa yamasa fata fata dan haka umurni yasamu daga wajen daddyn sa kai tsaye anjima zaki ganshi amma me kika tanadar masa dan ki burgesa?

Ajiyar zuciya ta sauke fuskanta dauke da mayalwacin murmushi tace”ai ni mummy nama rasa tacewa”ok to ni bara na baki nawa shawaran idan yazo kiyi kokarin ganin kinci dashi daga wani abu a wajen koda na shane daga hannunki hakan yana kara dankon kauna”inde wannan ne mai saukine zanyi kokarin ganin nabashi inde hakan ze burge shi,takare maganan cike da farin ciki”mezai hana ki burgesa saide idan bakiyi masa hakan ba cewar hajia mariya”haba mummy me zai hana inbashi wallahi bansan irin farin ciki danake ciki ba gaskiya mummy shema ba karamin burgeni kikayi ba yau ai wannan albishir ɗin naki yafi kugeran makka a wajena takare fadin haka tana miƙewa dan tafiya tasoma shiri dan a cewarta shirin na yau na musamman ne,tana komawa ɗakinta tafaɗa kan salaha tana dariya itama salahan tayata dariyan tayi dukda batasan me takema ba amma tasan komade mainene abun farin cikine yasami kawartata”salaha tayani murna yau mine zezo ya halarci partyn mu”wow karkice cewan salaha”wallahi kuwa ƙawata dalilin kiran da mummy tayimun yanzu kenan kede dole mu cancell wasu tsarin kicire wine dakika saka ciki dan ganin wine a wajen babban barazanace gareni sannan dan Allah ƙawata yi kokarin sanar da sauran yanzu babu shigan ƙananun kaya suyi amfani da wannan dogon rigar nan ta material dan mukara burgeshi ganan wayata ɗauki ki kira nakira kisanar dasu duk ta ruɗe take takasa tsaye takasa zaune gu ɗaya.

********
Saida akai sallahn magariba sannan Anty malika takawo mata riga da zata saka,wannan dogon rigar ta material da sukai faɗa akansa da basma haɗe da takalmi golden colour sai mahaɗan sa hand bag da ɗan yalolon gyale,Aisha na ganin Anty malika ta dan ƙwaɓe fuska kaman zatayi kuka cike da shagwaɓa tace”shine sai yanzu kika dawo bayan kinsa ko kuɗin motan komawa gida banda.

Ƴar dariya Anty malika tayi cike da zolaya tace”rabani da wannan ƙanwa ina ni ina shiga tsakanin mutum da matarsa,ko yanzu ma saida yakira yace nazo nakawo miki kaya kishirya sai kuma tayi ƙasa da murya tace dan Allah ki nutsu ayi miki kwalliya na burgewa dan so nake yau ki ƙarasa haukata wancan wawiyar kinsan hankali be gama isarta ba.

Kallon ta kawai tayi batayi magana ba dafa kafadanta tayi tace ke kwantar da hankalin ki bawani abun damuwa bane,nima kinga da shirina nazo dan so nake naje naganewa idona abunda takeson yayah Ahmad sai yaje dan haka so nake kiyi gayu iya gayu kamande wacce zata gasar kyau,ganin kaman Aisha bata da niyan tashi yasa Anty malika riƙe mata hannu tana tayi mata magiya kaman zata saka mata kuka har hankulan mutanen dake wajen yafara yuwa kansu saiga hajiar nan tanufo su tana tambayan yaya maike going anan ganin Anty malika yasata washe baki tana cewa ƴan biyu ashe kece”eh wallahi hajia ya aiki?ta amsa da fadin hakan tana kallon Aisha”lafiya lau fatan kin kawo mata kaya dazata canja?saurin amsawa malika tayi da fadin”eh hajia gashinan idan tasaka ayi mata makeup mara hayaniya dan yanzu nan zezo ɗaukanta.

Itade Aisha zaune take ko motsawa takasayi sai aikama Anty malika da harara take”Aisha tashi muje daga ciki ai da zafi zafi ake dukan karfe karki tsaya yin nawa haryazo yatsaya tsayuwar jiranki,wani irin haushi yake tasoma Aisha aranta kuwa cewa take mutum inba ya raina ma mutane hankali ba,me nawani sa muje shagalin bikin sa da wata,take taji wani abu nataso mata tun daga ƙasan zuciyarta yana lulluɓeta take tayi saurin kawar ta abun aranta tana faɗin toma wai ina ruwa da wani shagalinsu dama ita mai shagalin baki ɗaya dazan wani ji haushin su.

Rigar tasaka yayi mata ɗas a jiki yakuma fitar da shape ɗin ta saida akai mata makeup sannan hajiyar da kanta tayi mata ɗauri daya zauna mata daidai a kanta mayafin ta yafa mata a kafadanta takalmin tasaka irin half cover ɗinnan ce sai mahaɗanta hand bag masha Allah shine abunda ke fita daga bakin hajiar dama wacce tayi mata kwalliyar wankan turare akai mata gakuma ƙamshin turaren wuta dana dorot daya kama mata jiki,ita kanta Aisha sanda ta kalli kanta a madubi tsintar kanta tayi da sakin murmushi daidai tana kara juyawa gaban madubin tana karewa kanta kallo tare dakuma godewa Allah subuhanahu wata ala dayayi ta dakyan tsari da fasali maikyau badan wayonta ko dabaran ta ba,turo ƙofan ɗakin Anty malika tayi saida ta zarana da irin kyaun da taga Aisha tayi mata yau a ido duk da tasan ita din kyakkyawace amma bata taɓa sanin kyaunta yakai haka ba take ita ma tafara fadin masha Allah ke kinga yanda kikayi kyau kuwa wannan ai sai kisaka yah Ahmad fasa zuwa wajen shagalin ko kuma idan yaje yamance sunan amaryasa saide kawai muji yana kiran eashow eashow,dukan wasa Aisha takai mata ita kuma na gocewa tana dariya tace kidaurawa ƴar mutane hawan ruwa a banza cike da zolaya take maganan hajia ma tasamu abunda take so sai kaɗa baki tayi tana tambayan Anty malika”ince ko shidin shine wanda ze aureta?ƴar dariya Anty malika tayi duk yanda Aisha ke mata alama da ido kartayi magana amma saida ta tanka tace”hajia wato de zan iya cewa shiɗin mijinta tane duk da dukansu basu dauki abun da mahimmanci ba,haɓa hajiyar tarike kafin tayi wata magana sai wayan Anty malika yayi ringin tana dubawa taga yah Ahmad ne bisa layi tana dagawa bebari ko amsa sallamar da tayi masa yayi ba yace”ku fito muna waje daga haka yakatse kiran,kallon Aisha tayi datayi tsuru ta zuba mata ido tayi tace”mutafi ko kirarin da hajia tasoma matane yasata saurin fita daga ɗakin tanufi kofan fita waje daga babban shagon nasu Anty malika na biye da ita da ledar kayanta data canza riƙe a hannun ta sai hajiyar nan dake ta washe baki biye da ita tasan yau irin kyaun da Aisha tayi dole tasamu sallama mai kyau wajen ogan tunda taji ance matar sace.

Fitowa Ahmad yayi daga cikin motarsa yana daddan na wayan sa khalid dake zaune cikin mota shiya fara hango xuwan su Aisha kafeta da ido yayi a ransa yana ma abokin sa dariyar mugunta dan haka fitowa yayi daga cikin motar dan son ganewa idonsa wani irin yanayi abokin nasa ze shiga dan kullum bashi da magana sai cewa wannan ƴar jaririyar yarinyar su Ammi za suce matarsa saide ya yarda ze zauna da ita na wucin gadi kafin nan kowa ya kama gaban sa,gyaran murya khalid yayi da fadin”a’a malika harkun fito kenan tun ɗaxu muna jira kunason ɓata mana lokaci kaman bakisan yayan nan naki bayason yawan jira ba.
Yafadi haka amma idonsa nakan Ahmad daya sake baki da hanci ya zubawa Aisha ido tunda khalid yayi gyaran murya yakafe ta da ido besan sanda yafurta”wow beautiful ba.

Leave a Reply

Back to top button