ELECTION INEC

Saƙon Ɗan Takarar Gwamnan Kano na Jami’yyar PRP Malam Salihu Tanko Yakasai..

Sponsored Links


 Saƙon Ɗan Takarar Gwamnan Kano na Jami’yyar PRP Malam Salihu Tanko Yakasai


Alhamdulillahi mun ga sakamakon zabe da ya gabata, kuma mun karbe shi da Tawakkalin cewa dama Allah ne mai yi. 


Muna da kyakkyawar niyya ga jiharmu, kuma mun yi duk abin da za mu iya a yayin yakin neman zaben mu. Amma Allah bai sanya mu aka zaba ba. Duk da cewa ba mu ci zaben ba, amma mun sami nasarar samun magoya baya da suka gamsu da kudure kuduren mu. Ba karamin aiki ne ba ci gaba da kamfen na tsawon shekara guda, amma mun tsaya tsayin daka har muka kai karshe. Alhamdulillah!


Kwarewa, ilimi da fahimtar da muka samu yayin wannan yakin neman zaben ba za a iya ƙididdige su ba. Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa dukkan ni’imomin da Yai mana a lokacin yakin neman zabe. 


Ga ‘yan uwana, abokaina, shugabannin jam’iyyata da su kan su yan jam’iyar, ‘yan uwa da daukacin magoya bayana ina mai mika godiyata ga dukkan goyon bayan da kuka bayar. Na gode da addu’o’in ku, na gode da gudummawar ku na kuɗi da kayan campaign, na kuma gode da kalmomin ƙarfafa gwiwa. 


Abubuwan da suka sa na fito takara ba sai lallai ni zan aiwatar ba, duk wanda ya zama Gwamnan Kano nan gaba, idan aka bayyana sakamakon zabe a hukumance, ina yi masa fatan alheri kuma ni da kaina zan kai blueprint dina ga zababben Gwamna da fatan yayi aiki da wasu daga cikin tsare tsare mu a tafiyar da jihar mu gaba. 


Fatanmu shine Kano ta gyaru! Allah ya bamu shuwagabanni nagari a jaharmu masoyan mu, Ya kuma sa mu kasance mabiya na kwarai. Allah ya bamu hadin kai domin ganin Kano ta zama birni mafi girma a nahiyar Afirka. Wannan ya kasance burina koda yaushe kuma ba wai lallai sai ni ne zan zama wanda zai cimma burin ba. Allah ya taimaki Kano da Kanawa amin! Nagode.


Salihu Tanko Yakasai 

Dawisun Kanawa 

Masoyin Kano da Arewa da Najeriya.

Leave a Reply

Back to top button