Hausa NovelsSakayyah Complete Hausa Novel

Sakayyah 29

Sponsored Links

 

*LITTAFIN SAKAYYAH NA KUDINE KO KIN GANSHI A WASU WURAREN DA BA CIKIN GROUPS NA DANA BUƊE NA SAKAYYAH BAto na satane, 1k ne kacal kuɗin littafin SAKAYYAH yar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa a kanki 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276, kiyiwa Allah da Manzonsa ku dena fidda min littafina, in dai kin san kin sayane dan ki turawa wasu, dan Allah ki gaya min in mayar miki da kuɗinki🙏🏻🙏🏻Dan Allah nace ba dan niba*

 

Isrnejny. Moddibo kuwa cike da mamaki da tsoro ya maimaita 200 Millions asaman laɓɓansa, he can’t believe or imagine zasu iya tambayar wannan maƙudan kuɗin how cames kidnapper zasu tambayi kuɗin fansa kamar sun sace ɗan shugaban ƙasa.

Rintse idanunsa yayi tare da cije labɓansa na ƙasa lokaci ɗaya jijiyoyin kansa suka tashi sukayi ruɗu-ruɗu dasu.

Dafe kuncin Hajiya Karima tayi da hannunta duka biyu kana ta kyale baki tare da cewa.

“Ohh Allah ya kawo mu wani zamani ka haifi ɗa sannan wasu ƙartin banza da wofi su saka kasa ke sayan sa bafa Millions biyu ba, Ba ashirin ba, Ba hamshin ba, Ba ɗari ba,  har Millions ɗari biyu sai kace abin Masifa ko dan sunyi zaton Jameel ɗan Aliko ɗan Gwate ne, shi, ka haifi ɗa kasha wahalar ciyar dashi shayar dashi tufatar dashi biya masa makaranta sannan ace ka sake siyan sa”.

Dafe kai Abba yayi da duka hannunsa biyu baki ɗaya ilahirin jikinsa rawa yake kar-kar-kar tamkar mazari  yayin da idanunsa suka kaɗa sukayi jawur tamkar garwashi.

Dai-dai lokacin Hajiya Turai tashigo baki ɗaya tayi zuru-zuru da ita. Idanunta sun kaɗa sunyi jawur dasu ganin halin da Abba ke ciki yasa tace.

“A’a Alhj Lafiya Subhanallah”.

ta faɗa tare da nufar Bedroom ɗin sa ta da buɗe drawer ta ɗauko naganinsa ganin alamar hawan jinjinsa ne ya tashi tare da manna waya akunnenta bayan kamar second uku tace.

“Hello Dr Muktar dan Allah kazo yanzu ina ganin kamar hawan jinin Alhj ne ya tashi”.

Cikin raunin murya Abba ya ɗago kai ya kalleta tare da cewa.

“A’a ki bari ba sai Dr yazoba, ki bani maganin kawai”.

Kai ta gyaɗa kana cikin sauri ta zuba masa ruwa a glass cup ta miƙa masa tare da bara masa maganin karɓa yayi ya afasu  abakinsa ya haɗiye.

Sannu a hankali ya fara maida numfashi sama-sama yana jin bugun zuciyarsa tare da sarawan da kansa keyi ya fara raguwa amma still hannunsa na dafe da kansa.

 

Ɗago Idanunsa yayi tare da kallon Moddibo daya zuba masa Idanu kana ya kalli gefen damansa Hajiya Turai ce durƙushe Idanunta cike da hawaye  lumshe idanunsa yayi kana ya shiga tunani kwata-kwata kuɗin dake cikin account ɗinsa tsuran kuɗi, gaba da baya Million Sha biyu ne wanda yake tunanin da sun cika Ashirin zai bawa M Jameel saboda ya habɓaka Company daya bashi, da ƙarfi ya sake rintse idanunsa tare da dafe kansa tuno wa da yayi acikin Million Sha biyu ma akwai cikon kudin hajji nashi da na matansa da zai cika ta, baki ɗaya tunaninsa ya tushe ina yasan zai fara kai kadaransa asiya masa su cikin gaggawa kuma da daraja sannan abashi kuɗin cikin tsanananin tashin hankali yace.

_“Ya Ilahi ya lillahi ya mujibud da’awati ya hayyu ya ƙayyum bi rahma tika astaghisu lahaula wala ƙuwwata illa billahil aliyul azim”_.

Abin da yake maimaitawa kenan asaman laɓɓansa.

A hankali Moddibo ya matsa kusa dashi cike da tausayawa yace.

“Colm down Abba ka nutsu ka kwantar da hankalin ka everything will be fine by the grace of Allah”.

Cikin sauri Abba ya riƙo tsintsiyar hannun Moddibo tare da cewa.

“Aliyu Why should I find 2 hundred Millions?”.

Aliyu mai zan fitar in sayar dashi cikin gaggawa in Samu kuɗi?.

Aliyu bani da ko Million ashirin acikin account ɗina,kaji kuɗin da suka kira fa”.

Kallonsa kawai Moddibo keyi cike da tausayinsa Cikin raunin murya Abba ya cigaba da cewa.

“Aliyu kwanan nan na cire kuɗi na siya filin nan kuma shima gaba ɗaya filin dana siyeshi 25 Million ne da ace suna nan kaga kuɗin akwai ɗan gwaɓi ahannu na”.

Sai kuma ya sauƙe numfashi tare da sake damƙe hannun Moddibo acikin nasa kana yace.

“Ina da kadaran da zan iya sayarwa amma ta yaya awani lokaci zan samu ace ansiya se anbani kuɗina sannan na wane”.

Kasa ƙara sa maganar yayi kawai saiya janye hannunsa dake cikin na Moddibo ya rufe fuskarsa yana mai furta.

_“Allahumma Ajirni fii musibati wa’ahlifli khairan minha Hasbunallahu wani’imal wakin La’ilaha Illah anta subhanaka Inni kuntu Minal zhalimin”_.

 

Hajiya Karima dake dafe da kuncinta ta ɗago kai tare da kallon Abba kana tace.

“Alhj ai dole dama za ayi ciniki dasu idan yaso sai anemi ragi”.

Moddibo kuwa kai ya girgiza tare da kallon ta kana yace.

“Idan da ace sunzo mana da sauƙi da kuma Imani acikin zancen zamu iya hakan amma fa kiga yanda idan sunyi magana sai su yanke mana kiran baza su tsaya suji ta bakin muba sai sun kwana ɗaya ko biyu kafin su sake kiran mu”.

Da ƙarfi ya runtse Idanunsa tare da cije labɓansa na ƙasa kana ya cigaba da cewa.

“Basa tunanin shin wani irin yanayi ko hali zamu kasance aciki ba yaya zamuyi, da wannan kuɗin da suka kira”.

Ya ida maganar cikin raunin murya.

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe kana yace.

“Nima abinda nake tunani kenan idan nace musu babu zasu iya yiwa Jameel Illah”.

Girgiza kai Moddibo yayi tare da cewa.

“Abba kar ma kace musu babu sai muyi ƙoƙari duk yanda zamuyi mu haɗa kuɗin nan muyi ƙoƙari mu basu”.

Ahankali Abba ya furta.

“Ya Salam”.

Hajiya Turai kuwa cikin matsanancin kuka ta kalli Moddibo kana ta maida kallonta kan Abba tare da cewa.

“Ai abayar ɗin yafi Alhj duk wani abinda kake dashi ka sashi akasuwa kawai asamu asayar akarɓo Jameel meye fi maka Jameel aduniyar nan Alhj, kawai asayar da komai akai musu kuɗin akarɓo shi”.

Cikin sauri Hajiya Karima ta kalli Hajiya Turai kana tace.

“Kamar ya asaida komai Hajiya Turai kifayi tunani akan abinda kike faɗa idan aka sayar da komai muku mu murayu aya kenan?”.

Sai kuma ta maida kallonta kan Abba kana ta cigaba da cewa.

“Alhj ya za ayi ɗauki irin wannan maƙudan kuɗin amulmula abasu kaga idan wa’annan ƴan Kidnapping din da suka kinnafe Jameelu sunji dadi an basu abinda suke so to wasu kuma ai sauran ƴaƴan zasu zo su kwashe”.

Ta ida mgnar tare da sauke numfashi kana ta cigaba da cewa.

“Suma sauran ƴaƴan sai aje a kinnafesu su kuma idan kuɗin da za’a fanshe su bai rage ba ya za ayi kenan.

A gaskiya wannan ba shawara bace ace za aɗauki wannan maƙudan kuɗin abasu sai kace ba asha wahala wajen ne mansu ba”.

Ahankali Moddibo ya ɗago kumburarrun Idanun sa ya kalli Hajiya Turai dake dafe da ƙafaɗan Abba tana sharɓan kuka kana ya maida kallonsa kan Hajiya Karima data zabga tagumi.

Girgiza kansa yayi.

Sosai hankalin Abba yayi masifar tashi yama rasa wani irin tunani zaiyi Aransa ya gaza tantance abin cewa.

Sannu a hankali idanunsa suka fara lumshewa jikinsa ya saki  baya yaja tare da gyara kwanciyarsa akan 3sitter tare da lumshe idanunsa  Atake Bacci ya ɗauke sa sabida magungunansa da Hajia Turai ta bashi yasha sun jiƙa sunbi jininsa.

Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da miƙewa kana yai musu sai da safe tare da ficewa yashiga motarsa kai tsaye gidan Ummi ya nufa.

Awaje yayi Parking motarsa kana ya fita iska na kaɗa ko wani sashe na jikinsa ahankali ya murɗa handle din ƙofar ya tura bakinsa ɗauke da sallama ya shiga.

 

Idanunsa suka sauƙa akan Ummi dake zaune kan Sallaya hannunta riƙe da Carbi yayin da Malam Ahmad ke zaune gefenta yana rarrashin ta.

Ganinsa yasa Ummi ta ajiye carbin dake hannunta kana ta maida hankalinta kansa,Anutse Moddibo ya ƙara sa tare da miƙawa malam Ahmad hannu sukayi musabaha kana ya koma ya zana agaban Ummi.

Jin Sallamar sa yasa Asma’u da Bashir suka fito daga Bedroom tare da zama gefe da gefen Ummi ya zamana sun sashi a tsakiya kana cikin raunin murya suka gaishesa atare zuwa lokacin shima Bashir kuka yake sosai duk yayi zuru-zuru.

 

Ahankali Ummi ta zubawa Moddibo Idanu kana cikin sanyin murya tace.

“Babana ya akayi sun sake kira?”.

Kai ya gyaɗa tare da sun kuyar da kansa ƙasa kana yace.

“Eh”.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.

“Me suke buƙata?”.

Still Kansa na ƙasa yace.

“Ummi kuɗi suke so”.

Numfashi ta fesar kana tace.

“Kuɗi suke so?”.

Kai ya gyaɗa amma bai ce komai ba.

Cikin tsira masa ido tace.

“Kuɗi kamar nawa suke so?”.

Cikin rauni ya kalleta kana ya kalli malam Ahmad, Asma’u da Bashir ya fesar da numfashi tare da cewa.

“Ummi kuɗin suna da yawa kuɗin da suke buƙata sun wuce zatonmu”.

Gyara zama tayi kana tace.

“Toh Meye amfanin kuɗin mahaifinsa?, Meye amfanin kuɗin Babansa?,Menene amfanin duk tattalin da yake yi!?”.

Girgiza kai Moddibo yayi kana yace.

“Ummi kuɗin sun wuce tunanin mai tunani!?”.

Ɗa gowa Ummi tayi tare da tsira masa ido kana tace.

“Kamar nawa suke buƙata Babana?”.

 

Cikin raunin murya da alamar sarewa Moddibo yace.

“Ummi har Million ɗari biyu suke buƙata”.

Cikin wani irin yanayi mai cike da rauni, tsoro, mmki Ummi taja ajiyar zuciya kana ta maida kanta ta jingina da jikin kujeran da Malam Ahmad ke zaune tare da lumshe Idanunta kana Muryanta na rawa tace.

“Ƙarya sukeyi ba kuɗin suke so ba so suke su kashe min Jameelu lallai Mahaifinsa mai arziƙi ne amma be kai matakin da za’a matsesa lokaci ɗaya ace ya fito da Million ɗari biyuba, kawai dai yaudarace suke mana anya ma Jameelu yana raye kuwa?”.

Cikin sauri Moddibo ya girgiza mata kai kana yace.

“Yana raye Ummi ina ji ajikina J yana raye kuma na faɗa miki munyi magana dashi”.

Girgiza kai tayi tare da cewa.

“Yau da suka kira kunyi magana dashi?”.

Shiru yayi yana kallonta amma baice komai ba.

 

Kallonsa Ummi tayi cikin muryan kuka tace.

“Babana ka faɗa min gaskiya tsakanin ka da Allah yau kunyi magana dashi?”.

Girgiza mata kai Moddibo yayi tare da faɗin.

“Ummi ba muyi magana dashi ba, amma naji muryan J ƙasa-ƙasa yana cewa Abba abasu duk abinda suke so”.

Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da rintse idanunsa kana tace.

“Babana ka tabbatar gaskiya kake faɗa min?”

Jinjina kai Moddibo yayi kana cikin sanyin murya yace.

“Wallahi Wa rabbul Khaba Ummi naji muryan J ƙasa. yana magana bawai sun bashi bane amma naji yana magana”.

Kuka Asma’u da Bashir suka fashe da shi atare kana lokaci ɗaya suka haɗa baki wajen cewa.

“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n ya Allah ka kuɓutar da Yah Jameel Ubangiji kada ka basu ikon cutar dashi ya Allah kaine gatanmu Yah Jameel shine ka wakilta da isar mana gatanmu ya Allah ka karesa da karewaka”.

 

Numfashi Malam Ahmad ya fesar kana cike da tausayawa yace.

“Asma’u ba kuka ya kamata kuyi ba addu’ar mu Jameelu ke buƙata idan kuna kuka ya kuke so Ummin ku tayi?”.

Cikin sheshsheƙan Kuka Asma’u tace.

“Abba Yah Jameel fa Yah Jameel yana cikin mawuyacin hali Abba kaji  fa maƙudan kuɗin da suke buƙata Abba ya za’ayi mu samu irin wannan kuɗin mu karɓo Yah Jameel Abba Ina tsoron kada su cutar mana dashi”.

 

Girgiza kai Malam Ahmad yayi cikin sanyin murya yace.

“Insha Allah da izinin Ubangiji babu abinda zai samu Jameelu, ko wani bawa da kalar tashi ƙaddaran tun kafin a haifi Jameelu Ubangiji ya zana masa ƙaddaransa muyi masa addu’ar Allah ya sauƙaƙa mana zafin ƙaddararsa”.

Jinjina kai Moddibo yayi yana jin wani irin azabebben zafi aƙirjinsa.

Kallon Moddibo Malam Ahmad yayi kana yace.

“Moddibo mai Yakamata ayi acikin wannan al’amarin!?”.

Moddibo da kansa ke ƙasa ya ɗago ya kallon Malam Ahmad a hankali yace.

“Malam abinda yakamata kawai afara cuku-cukun neman kuɗin nan sai muga abinda zai kasance”.

 

Girgiza kai Ummi tayi still tana jingine da jikin kujera tace.

“Babana ina zamu samu kuɗin nan Million ɗari biyu fa da ace Million biyu suka ce koni kaina ma zan bada su”.

Ta faɗa tare da ɗaukar wayarta tayi checking balance kana tace.

“Gashi yanzu anan ina da Million ɗaya da dubu ɗari huɗu da hamsin da ɗaya sannan kuma ba matsala gobe in Allah ya kaimu zan tafi cikin.

Taraba zan kai gwala-gwalaina”.

Sai kuma ta ɗan tsaya, jin numfashin ta na yankewa, da ƙarfi ta fizgo numfashin tare da cije labɓanta na ƙasa hawaye cike da Idanunta murya na cike da rauni ta cigaba da cewa.

“Zan saida su inga nawa zan samu ajikinsu zan haɗa harda na Asma’u sannan, motata itama zan saidawa muga nawa zan samu awurina”.

Jingina kai Malam Ahmad yayi kana cikin sanyin Murya yace.

“Har gidan nan ma asashi a. Kasuwa asayar dashi”.

Kallonsa Moddibo yayi tare da girgiza kai kana yace.

“A Malam ayi haka”.

 

Kai Malam Ahmad ya gyaɗa kana yace.

“Asiyar Moddibo menene Jameelu baiyi mana ba aduniyar na, kasancewar sa atare damu shiyafi mana komai”.

Ahankali Ummi ta ɗago kanta tare da tsira masa ido hawaye na bin kuncinta ta sani fili dai filinsa ne halalinsa mallakinsa, amma baki ɗaya ginin dake ciki Jameel ne ya musu bayan yasa an buge tsohon ginin taɓon.

Girgiza kai tayi cikin rauni tace.

“A’a ba sai anyi haka ba bari muga abinda Mahaifinsa zai samu”.

Girgiza kai Malam Ahmad yayi tare da kallon Asma’u da Bashir da har zuwa lokacin suke kuka a hankali ya fesar da numfashi tare da cewa.

“Ni dai na sadaukar da wannan gida ga.

Jameelu wallahi na yafe masa shi duniya da lahira na amince asa shi akasuwa muddin za a samu masu siya, to asa shi akasuwa  mu samu muga aƙalla dai awajen mu ace an samu Million goma kuɗin zaifi gwaɓi”.

Sun kuyar da kai ƙasa Ummi tayi hawaye masu masifar zafi suka zubo mata.

Hannunta Moddibo ya riƙe cikin sanyin murya yace.

“Ummi dan Allah ki daina wannan kukan idan kina kuka muku ma ya zamuyi Ummi babu abinda J ke buƙata awajen mu face addu’a ganin ki awannan yanayin naya sake raunatamana zuciya”.

Kai Malam Ahmad ya gyaɗa kana yace.

“Sosai ma wannan kukan da kike Fatima saidai ya haddasa miki wani ciwon amma babu amfanin da zaiyi dan Allah ki daina ki cigaba da yi masa addu’a. shi kansa ba zaiso ace kina masa kuka ba”.

Kai ta gyaɗa tare da share hawayen ta kamar yarinya kana tace.

“Na daina Insha Allah zan cigaba da yimasa addu’a Ako da yaushe”.

 

Saida Moddibo ya tabbata ta daina kukan kafin ya mata sallama ya fice cike da tausayinsu Driving yake ahankali har ya isa gida yayi Parking kana ya fito ya rufe gate din tare da wucewa sashen Innayi bakinsa ɗauke da sallama.

Kwance ya samu Innayi cikin Yanayin damuwa gefenta da Radio tana sauraro wanda ɓatan M Jameel ake sanarwa.

Miƙewa tayi ta zauna tare da amsa Sallamar sa kana tace.

“Moddibo ya labarin Jameelu?”.

Cikin sanyin murya yace.

“Innayi sun sake kira ɗazu”.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.

“Toh kunyi magana dashi yana cikin ƙoshin lafiya?”.

Girgiza mata kai yayi  kana yace.

“A’a Innayi bamuyi waya dashi ba amma bisa duk kan Alamu J baya jin daɗin zaman wajen can”.

Ahankali Innayi ta jingina bayanta da jikin bango kana ta matsar da Radio gefe tare da cewa.

“Dama Moddibo ya za ayi yaji daɗin zaman wannan wajen. kasan yanayin da yake ciki ai dole bazai ji daɗin zaman wannan wajen ba amma me suke buƙata?”.

 

“Innayi kuɗi suka nema”.

 

“Kuɗi suka nema to aisai abasu aje a karɓe shi”.

 

“Innayi kuɗin da suka nema na fitar hayyacine!”.

 

“Kuɗi har nawa suka nema? Da zai zama na fitar hankali”.

Dafe goshinsa yayi kana yace.

“Innayi Million ɗari biyu suka nema kuma cikin ƙanƙanin lokacin fa”.

Ita kam Innayi baki ɗaya lissafin ta sincewa yayi jin maƙudan kuɗin tama rasa nawane, kallon Moddibo tayi tare da cewa.

“Dubu ɗari biyu?”.

Kai Moddibo ya Girgiza tare da cewa.

“A’a ba dubu ɗari biyu bafa Million fa Million ɗari biyu”.

Daga kanta sama tayi alamar tunani sai kuma ta kallesa tare da cewa.

“Million biyu?”.

Still girgiza mata kai Moddibo yayi kana yace.

“A’a Million ɗin goma, ashirin, hamsin, ɗari, ɗari da hamshin har ɗari biyu”.

Dafe kirji tayi kana tace.

“Million ɗari biyu?”.

Jinjina mata kai Moddibo yayi.

Girgiza kai tayi tare da cewa.

“Ban gane lissafin ba Aliyu”.

 

Lips ɗinsa duka biyu ya cije a lokaci guda kana yace.

“Ba zaki gane lissafin ba Innayi kuɗi ne masu tarin yawa suke nema”.

Cikin sanyin murya Innayi ta jujjuya kanta kana tace.

_“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Hasbunallahu wani’imal wakin Layukalliful nafsi illa wusɗaha_

Toh yanzu mai Baban nasa yace?”.

 

“Innayi Abbansa bashi da wannan kuɗin a ƙasa kwanan nan dama ya gama yi mana ƙorafi bashi da kuɗi”.

Lumshe idanu Innayi tayi kana tace.

“Ya Salam ya Ubangiji Allah ka dube mu da idon rahama, ya Allah ka yayemana ya Allah ka sauƙaƙa mana ya Allah ka tsare Jameel ka kare mana shi, Allah ka tseratar da wannan bawan naka”.

Cikin sanyin murya Moddibo yace.

“Ameen”.

 

Kallon second biyar zuwa bakwai Innayi ta yiwa Moddibo kana tace.

“To amma kai Moddibo mai kake ganin zakayi akai?”.

Still hannunsa na dafe akansa yace.

“Innayi akwai kuɗi awajena zan tattara su in haɗa su muga nawa za’a samu awajena”.

Kai ta gyaɗa kana tace.

“Yafi kam”.

Bayan sun sake tattauna ne Moddibo ya miƙe tare da  yi mata Sallama kana ya nufi Sashen sa ahankali ya tura Murfin Kofar shiga tare da mayarwa ya rufe.

 

Kana ya jingina bayansa da jikin da kofar tare da rintse idanunsa sautin murya M Jameel ya farayi masa kai-komo AJ bansan idan nakeba,

Lumshe danunsa yayu zuciyarsa na bugawa da masifar ƙarfi yana bada sautin dif-dif-dif cikin sauri ya buɗe Idanunsa jin muryan M Jameel na yawo a kansa yana cewa A.J A.J Kallon kan 3sitrer kurui ji yake kamar zaiga J dinsa a wurin, cikin raunin murya yace.

“J Why are you?, Zuciyata zata fashe ya Allah kaji ƙaina ya rabbil Izzati ka dawo da J garemu cikin aminci da salama ya Allah kada ka bawa waɗɗanan azzaluman daman cutar dashi”.

Ya kai 15 minutes yana mai jero Addu’o’in cike da rauni, kafin ya miƙe kamar wanda aka mitsina ya nufi Bedroom ɗin sa kai tsaye toilet ya shiga ya watsa ruwa kana ya ɗaura alwala ya fito ya kwanta bisa gadonsa yayi rigingine  duk da yasan cewa da wuya bacci ya ɗauke sa amman ya lumshe idonsa domin yau kwana uku rabon da ya samu wani wadataccen bacci sai wani irin azabebben ciwon kai da yakeji tamkar kansa zai rabe da ga wani irin sarawa da yakeyi yana bada wani irin sauti mara daɗi gau-gau-gau!.

A hankali ya bude idon sai kuma yayi saurin

Lumshe Idanun sabida sarawa da kan yayi masa.

Cikin zazzaƙan muryansa mai cike da rauni ya fara raira ƙira’ar Suratul Yusuf hawaye masu ɗumi suka riƙa fita daga idanunsa suna shiga kunnensa cikin wannan yanayin da cikar Sa’adatu da  karatun Alqur’ani mai girma ya samar masa, wani irin kiɗimemmen baccin da bai shirya masa ba ya sace sa.

 

Acan cikin baccin sa kuwa zaune ya hangosa akan wata.

Tattausan shimfiɗa cikin wani masha’hurin falo mai masifar kyau da ƙawa.

Sai dai kima yana ta dariya hartada karketawa, yayinda idanunsa kuma sunyi jawur jikinsa na rawa jin.

A hankali ya fara jujjuya kansa yana mai ci gaba da dariyar ya juyo kansa gabansa, jin alamar tafiya tare da wani ƙamshi daya ratsa hancinsa yasa ya ɗaga manyan idanunsa da sukayi luhu-luhu ya  sauƙe ganinsa akan Khausar dake zuwa garesa cikin wata iriyar ƙasaitacciyar shiga, ido ya zira mata ko ƙebtawa bayayi har ta isa garesa, a hankali ta zauna gefensa.

Tare da tsira masa manyan Idanunta masu haske wanda ke ciki da ruwan hawaye kana ta miƙa masa wani hankief fari ƙall mai masifar ƙamshin turare.

Ƙin karba yayi saima lumshe idanunsa da yayi wanda sai lokacin ya samu wasu irin tafasassun hawaye suka samu damar kwaranyowa, hakan yasake kawar da kansa gefe tare da sakin sheshsheƙa.

Ahankali Khausar ta matsa gabansa har suna shaƙan nunfashin juna kana ta sanya hankief ɗin ta shiga share masa hawayen cikin wata Sanyayyar murya mai cike da nutsuwa da kuma rauni tace.

“Yah Jameel Addu’ar mu yake buƙata ba kuka ba idan kai kana kuka.

Toh Ni kuma ya zanyi addu’a za muyi masa kaji ko Abu J”.

Ta ida mgnar da kiransa da sunan da ta raɗa masa, tare da faɗawa jikinsa ta fashe da sassayan kuka dai-dai lokacin kuma ya farka.

Kansa ya dafe tare da miƙewa ya shiga toilet ya ɗaura al,wala kana ya dawo ya shimfiɗa Sallaya ya fara nafillah yana cigaba da yiwa M Jameel addu’a.

Ba tare da yabi ta kan mafarkinba, domin yanzu kam idan da sabo ai yaci ace ya saba da yawan ziyarar kutse da nacin da Khaisar keyi masa cikin rayuwar baccinsa.

 

Washe gari Ummi ta tattara baki ɗaya Sarkoƙi, ta da ɗan kunnen zobe da awarwon Gwal nata dana Asma’u ta shirya ta tafi Tarata.

Tana isa kai tsaye babbar kasuwar su ta wuce kana tashiga shagon saida gwala-gwalai ta bayar aka gwada cikin sa’a ta samu sunyi farashi sosai kasancewar Manyan Sarƙoƙine nata dana Asma’u wasu nata tun tana gidan Abban Jameel ne, suka haɗa mata kuɗin ta Naira Million biyu da dubu ɗari huɗu da hamsin sukayi mata transfer dinsu.

 

Daga nan gidan kai tsaye gidan Ƙawarta Hajiya Salma Wanda mijinta ke saida Motoci yawanci awajensa M Jameel ke siyan mota ko kuma can zawa.

 

Mai A dai-dai-tan na sauƙeta ta miƙa masa kudinsa kana ta shiga cikin tangamenen coumpund ɗin daya tsaru kai tsaye ciki ta nufa tare da Knowking ɗin ƙofar kana ta murɗa handle ɗin tashiga bakinta ɗauke da sallama.

Hajiya Salma dake zaune akan kujera ta miƙe cikin sauri kana tace.

“Hajiya Fatima sannu da zuwa ga wajen zama”.

Kai Mommy ta gyaɗa tare da cewa.

“Yawwa Nagode”.

Sannan ta zauna tare da sakin Ajiyar zuciya.

Bayan sun gaisane.

Cikin sanyin murya Hajiya Salma tace.

“Ayyah Hajiya ashe ga abinda ya faru da ɗana Jameel kuwa?”.

Cikin yanayin sanyin ɗaya zamewa Ummu jiki, ta gyaɗa mata kai tare da cewa.

“Ummm bari ke dai Hajia Salma duniya tayi min zafi”.

Cikin tausayawa Hajia Salma tace.

“Ba komai in sha Allah, kada ki damu Hajia Fatima.

Ubangiji Allah ya bayyanar da Jameel aduk inda yake Ubangiji ya karesa daga sharrin mai sharri”.

Cikin sanyin Murya Ummi tace.

“Ameen ya Allah ameen ya hayyu ya ƙayyum”.

Cike da tausayawa Hajiya Salma tace.

“Wallahi Koda wasa banji ba sai ɗazu da safe Alhj na duba jarida ya gani shine yake sanar min”.

Kai Ummi ta gyaɗa kana tace.

“Allah sarki ai yanzu anshiga kwana na huɗu kenan.

Uhmmm dama nazo kiyiwa Alhj Abdallah magana ne akan ya duba motata ya siya”.

Ajiyar zuciya Hajiya Salma ta sauƙe kana tace.

“Ubangiji Allah ya tsare Malam Jameel aduk inda yake”.

ta faɗa tare da shigewa ciki tsaye ta samu mijin nata yana ƙoƙarin fita Kallonsa tayi kana tace.

“Alhj Hajiya Fatima ce ta zo mahaifiyar Malam Jameel”.

Kai ya gyaɗa tare da cewa.

“Ikon Allah muna shirin zuwa kuma sai gata”.

Ya faɗa tare fitowa a tare, a inda Hajiya Salma ta barta anan suka sameta tayi ta gumi.

Ahankali Ummi ta ɗago jai tare da cewa.

“Alhj Abdallah ina kwana ya gida”.

Zama yayi kana yace.

“Lafiya lau Hajiya ashe kuma ga abinda ya faru da Malam Jameel”.

Kai Ummi ta gyaɗa kana cikin sanyin murya tace.

“Eh”.

Ajiyar zuciya Alh Abdallah ya sauƙe kana yace.

“Wallahi bamu da labari sai ɗazu ina karanta Jarida na gani nake faɗawa Salma tace itama bata da labari dake akwai wani fitar gaggawa daya kamani nace idan nadawo zan kaita da yamma ta gaishe ki”.

Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da gyada kai kana tace.

“Allah sarki dama Motata ce nazo ka tura adauƙa maka ka ga lafiyarta zan saidata in zaka siya”.

Ɗagowa yayi tare da kallonta kana yace.

“Motar da Malam Jameel ya siya miki nan?”.

Kai ta gyaɗa masa tare da cewa.

“Eh shi”.

Zaman hular kansa ya dan gyara kana yace.

“Amma ai motar bata daɗe ba Hajiya Fatima”.

Kai ta gyaɗa Muryanta na rawa tace.

“Eh bata daɗe ba Uzurin gaggawa ne ya kama Ni shiyasa zan siyar”.

Jinjina kai yayi tare da cewa.

“Aikam dama mota ce mai kyau sannan bai daɗe da sayanta ba za tura yaro yaje ya ɗaukota kuma yanzu mugama magana tunda abu na gaggawa ne”.

Cikin sanyin murya tace.

“Tun baka gani ba”.

Girgiza kai yayi tare da faɗin.

“Baki da matsala Indai wannan ne zan baki Million shida”.

Cikin sauri Ummi tace.

“Alhj har Million Shida kuma dama motar yana da tsada kenan?”.

Kai ya gyaɗa mata tare da zaro wayarsa acikin aljihu kana yace.

“Eh dama Million biyar ne haka ya siyeta toh nasiyeta biyar ɗin kamar yanda ya siya sannan Million ɗayan kuma na bada nawa gudunmawar Ubangiji Allah ya bayyana Malam Jameel”.

Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da cewa.

“Ameen ya rabbil izzati, ngd Matuƙa”.

Da sauri ta kalleshi jin yana cewa.

“Ki bani account number ki zan miki transfer”.

Kai Ummi ta gyaɗa tare da kiramasa number’s ɗin.

Atake ya mata transfer.

Miƙewa tayi tare da yi masa godiya sosai kana ta fito, har ƙofa Hajiya Salma ta rakata kana ta Wuce.

 

Kai tsaye tashar motar Gembila ta nufa, tana zuwa kuwa tayi sa’a mutun ɗaya ya rage, haka yasa ta shiga motar ta tashi.

 

Alhamdulillah sun isa Gembila lfy.

 

A hankali Ummi ke tafiya tana jin wani irin sanyi a ranta tare da Comfedance ga Million ɗaya da dubu ɗari huɗu da  dake account ɗinta ga kuma Million biyu da dubu ɗari huɗu da hamsin na Sarkoƙi kana ga Million Shida na mota ya zama tana da tsuran kuɗi ahannunta har Naira Million tara da dubu ɗari takwas kenan.

A hankali ta sauƙe wani zazzafafar ajiyar zuciya kana ta nufi gida.

Acan ɓangaren Moddibo kuwa ya haɗa duk wasu kuɗaɗe dake hannunsa ya samu Million huɗu da dubu ɗari biyu da hamshin kai tsaye gidan Ummi ya nufa yana Parking ɗin motarsa mai A dai-dai-tan sahu na ajiyeta atare suka shiga falonta.

Suna shiga Bayan sun gaisa Ummi tashiga Alart massage tare da miƙawa Moddibo wayarta tare da cewa.

“Babana ka kalli kuɗi sunyi gwaɓi”.

Amsar wayar yayi tare da Kallon Alart massage ɗin kuɗin kana ya sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.

“Masha Allah kuɗi sunyi gwaɓi bari na haɗa  dana wajena”.

 

Kallonsa Ummi tayi haka nan taji hawaye na ciko mata kwarmin Idanunta.

Cikin sanyin murya Moddibo yace.

“Ummi na wurina na bashi da yawa Million huɗu da dubu ɗari biyu da hamsin ne”.

Cike da tausayinsa tace.

“Toh Allah ya biya. Babana Allah yabamu yanda zamuyi Ubangiji ya saka maka amma ka rage wani abu aciki ka samu na kashewa”.

Girgiza kai yayi cikin raunin murya yace.

“Ummi wani abu zan rage idan ina da abinda yafi wannan zan ɗauka in bayar akarɓo J naje. nayi magana da dillalai gidan mu na sashi akasuwa in dai za’a samu siyansa akan lokaci.

Cikin sauri Ummi ta kallesa tare da cewa.

“Gidan ku kuma Babana!?”.

Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.

“Ummi Meye amfanin gidan mai zamuyi da gidan babu wani farin ciki acikisa.

Muddin J baya nan fa wanne farin ciki zamuyi. kuma komai da muka rasa zamu iya samu idan J ya dawo gare mu”.

Jinjina kai Ummi tayi, Account number dake wayarsa ya fito dashi ya mata transfer kuɗin tare da miƙa mata wayar karɓa tayi ta duba Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da kallon kuɗin Naira Million goma sha huɗu kenan cib.

Numfashi ta fesar tare da kallon Moddibo kana tace.

“Alhamdulillah Babana kuɗi sun cika Million goma sha huɗu bari muje gidan Abban sa tare”.

 

A hankali yace.

“Amma Ummi ki bari sai gobe muje wataƙil yau ba zasu kira ba sai goben, amma ni yanzu idan nafi ta zanje wajen Abba muji nawa aka samu awajensa”.

Kai ta gyaɗa cikin sanyi tace.

“Toh shikenan Babana Allah yasa muji al’khairi”.

Kai ya gyaɗa tare da miƙewa kana yace.

“Amin.

Toh shikenan bari naje yanzu”.

Ya faɗa tare da ficewa.

 

Kai tsaye gidan Abba ya nufa bayan yayi Parking ya fito tare da shiga Falon bakinsa ɗauke da Sallama.

Abba dake zaune kan 2 sitter ya jingina bayansa da jikin kujera ya amsa masa Sallamar cike da tausayinsa ya zuba masa yana ganin yadda yake tafiya duk ya faɗa acikin kwanaki huɗu ya rame yayi shafal.

 

Ƙara sawa Moddibo yayi tare da zama gefensa kana yace.

“Abba ina yini ya kuma haƙurin rayuwa?”.

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da cewa.

“Alhamdulillah Aliyu ya wajen su Innayi?”.

Kansa a ƙasa yace.

“Lafiya lau Abba basu sake kira ba ko?”.

Girgiza kai Abba yayi tare da fesar da numfashi kana ya runtse Idanunsa cikin sanyin murya yace.

“Basu sake kira ba Aliyu”.

Jinjina kai Moddibo yayi tare da cewa.

“Toh yanzu Abba kuɗi kimanin nawa aka samu awajenka?”.

Abba kuwa ahankali ya zame daga kan kushin ɗin ya zauna akan capet tare da fuskantar Moddibo kana yace.

“Aliyu na tattara duk abinda yake wajena kana duk wanda nake binsu bashi na tattarasu sannan na nemi temakon bashi duk wanda zan nemi temakonsu sunban bashi baki ɗaya kuɗin dana samu awajena Million hamsin da shida ne, iya adadin kudin dake hannu na kenan, duk ta inda zan buga na buga Aminaina ƴan uwana duk na nemi temako awajen su wasu sun bani kyauta wasu kuma aro na buga shine Million hamsin da shida”.

 

Jinjina kai Moddibo yayi tare da cewa.

“Toh Abba kuɗi dai sun ɗanyi gwaɓi gashi awurin Ummi an samu Million Sha uku yanzu kenan muna da Million Saba’in dai-dai a ƙasa.

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana yace.

“Alhamdulilah kuɗi sun fara taruwa Amma ɗari biyu fa suka ce gashi ko ɗari cikekke bamu samu ba”.

Cikin raunin murya Moddibo yace.

“Abba bari mugani idan sun sake kira sai mu rokesu su rage mana idan sun tallafa sun tausaya mana ko bashin banki ne zamu ci sai mu ƙara akai kuɗin ya cikata”.

Kallon sa Abba yayi tare da jinjina kai kana yace.

“Toh shikenan ba laifi Allah yasa mu dace”.

Ameen Moddibo ya amsa kana suka cigaba da hira har Misalin ƙarfe goma.

Abba najin ringing din wayarsa Yayi saurin zabura tare da picking kana yayi Sallama.

Daga ɗaya ɓangaren cikin bauɗaɗɗiyar murya mutumin yace.

“Alhj Bashiru ka haɗa kuɗin?”.

Cikin raunin Murya Abba ya gyaɗa kansa kana yace.

“Kuyi haƙuri bawan Allah dan Allah kuyi haƙuri wallahi kuɗin nan da kuka faɗa babu su awajena kwata kwata babu”.

Daga ɗaya ɓangaren mutumin ya juya  tare da kallon M Jameel dake zaune a ƙasa kana cikin wata dakakkiyar murya mutumin yace.

“Da alama dai mahaifinka baya sonka”.

Jin muryan mutumin agefe yasa Abba saurin cewa.

“Don Allah ku bani inji muryarsa”.

Cikin wannan bauɗaɗɗiyar murya Mutumin ya wurga wa M Jameel wayar kana yace.

“Gashi kaji muryan sa”.

Cikin sauri M Jameel ya cafke wayar tare da kaiwa Kunnensa kana cikin sanyin mai cike da rauni mai tada hankalin ɗan Adam cikin murya mai cike da galabaita yace.

“Abbana”.

 

Cikin sauri Moddibo ya karɓi wayar a hannun Abba kana yasa a handsfree tare da danna record.

Cikin raunin Murya M Jameel yace.

“Abba kabasu kuɗin Abba dan Allah ka basu abinda suke so ka fitar dani awannan wajen mana Abbana”.

Runtse Idanu Abba yayi kana yace.

“Babana zan fitar da kai ina nan ina har haɗawa kuɗin insha Allah zan fitar da kai amma Jameelu duka-duka kuɗin da muka haɗa anan Million Saba’in ne su kuma sunce Million ɗari biyu suke so”.

Cikin wata raunan’niyar murya mai cike da masifaffiyar galabaita da neman jin ƙai M Jameel yace.

“Abba a saida motocina duka sannan aduba ɗakina akwai kuɗi amma bai cika Million biyu bama dan Allah ahaɗa Abba abasu azo a karɓe ni”.

Cikin rauni ya runtse Idanunsa da hawaye suka cika kana yace.

“Abba bana son zaman nan babu daɗi ba Ummina ba A.J sannan kaima ba kai wuri ba daɗi dan Allah Abba ka basu duk abinda suke so kazo ka karɓe ni ku saida komai nawa a haɗo kuɗin”.

Kai Abba ya gyaɗa tare da ƙoƙarin hana hawayen sa zubowa kana yace.

“Babana Insha Allah zan zo in karɓe ka koda raina suke so zan basu amadadin ranka”.

Modibbo kuwa tuni wasu irin hawaye masu masifar zafi ke kwaranyo mishi tamkar mace.

 

Fisge wayar sukayi daga hannun M Jameel kana cikin wannan bauɗaɗɗiyar murya Mutumin yace.

“Toh kaji dai abinda ɗan ka ya faɗa zamu baka dama ta karshe”.

Cikin sauri Moddibo da idanunsa ke rintse ya buɗe tare da cewa.

“Dan Allah! Dan Allah!! Dan girman Allah!!! dan darajar Annabi Muhammad (S.A.W) badan  muba kamar yanda kuka ce J nada mutunci da kamala toh dan Allah saboda wannan kamalar tasa ku rage mana kuɗin zamu yi muku duk kan biyayya amma ku faɗa mana abinda zamu iya kawo wa”.

Daga ɗaya ɓangaren shiru mutumin yayi  ba tare da yace komai ba kana bai katse kiran ba.

Cikin raunin murya Moddibo yace.

“Dan Allah kuyi haƙuri ku rage mana Insha Allah ba zamuyi gardama ba, amma kuɗin hannun mu munyi munyi sun kasa kai adadin da kuke buƙata mu samu su kai adadin da kuke buƙata wannan shine matsalar mu ku temaka ku ragar mana”.

Ajiyar zuciya mutumin ya sauƙe tare da cewa.

“Wannan Moddibo ne ke magana ko?”.

Kai Moddibo ya gyaɗa kana cikin sanyin murya yace.

“Eh”

Cike da gadara Mutumin yace.

“Toh shikenan ku bada Million ɗari da hamsin”.

Cikin raunin murya Moddibo yace.

“Mungode amma dan Allah ba zaku ƙara rage mana ba?”.

Cikin wata razananniyar tsawa Mutumin yace.

“Dan ubanka dan ka samu na zabge Million hamshin.

Atake to wallahi acikin Million ɗari da hamsin Naira biyar ba zamu rage ba kuma wallahi idan ku ka yarda kuka sake yi mana batun ragi kuɗi to wallahi akan ran Jameel domin kuɗi ne dai mu ki ya rayu ko ya mutu zamu samesu”.

Cikin tsanananin tsoro da kaɗuwa Moddibo ya dafe ƙirjinsa yayin da kansa ya sara da masifan ƙarfi.

Cikin tsawa Mutumin ya cigaba da cewa.

“Yanzu Moddibo gashi kayi magana dashi na ƙarshe wanda ko bacci yake yana kiran sunan ka gashi kayi magana dashi dan wataƙil shine maganarka na ƙarshe kenan dashi matukar dai baku haɗa kuɗin nan ba ku kasake yi mana batun ragin kuɗin to kayi magana dashi na ƙarshe kenan”.

ya faɗa tare da wurgawa M Jameel wayar.

 

Cikin sauri M Jameel ya cafke wayar tare da maƙalawa akunnensa kana cikin raunin murya yace.

“A.J”.

Cikin sauri da zaƙuwa Moddibo yace.

“J ina kake?”.

Girgiza kai M Jameel Yayi tare da cewa.

“A.J ban san inda nake ba ina Ummina!?”.

Runtse Idanu Moddibo yayi tare da taune lips ɗinsa kana yace.

“Tana lafiya J?”.

Cikin sanyin Murya M Jameel yace.

“J ka tabbata?”.

Cikin raunatacciyar murya yace.

“Na’am”.

jin haka yasa yaci gaba da cewa.

“Kace mata kada tayi kuka tayi ta min. Addu’a A.J ina sonka Ina son Ummina Ina son Abbana Ina Son Asma’u Ina son Bashir”.

Da sauri Moddibo ya dafe ƙirjinsa dake harbawa da masifan ƙarfi  cikin raunin murya M Jameel ya cigaba da cewa.

“A.J Ina son Khausar tashigo rayuwar mu”.

Cikin tsanananin rauni Moddibo yace.

“Na sani J nasan kana son mu muma muna sonka, kuma in sha Allah duk zamu kasance a tare, zata shiga rayuwarka J zan mutunta abinda kakeso J”.

 

Girgiza kai M Jameel Yayi still cikin raunin murya yace.

“Ngd A.J in kayi haka kayi min komai, kayiwa Ummina magana idan akwai wani abu a hannunta ta bayar ahaɗa azo a karɓeni awajen nan dan Allah katemaka min”.

Araunane Moddibo yace.

“Insha Allah J zan taimaka da duk kan iyawa ta da kuma duk kan damata J koda ace da raina ne zan fanshi ranka da rayuwarka Insha Allah zamu fito da kai”.

Jinjina kai M Jameel yayi tare da faɗin.

“Nagode Nagode A.J ina maka fatan al’khairi acikin rayuwarka ga Amanar Ummina, Asma’u, Bashir,Abba da…. ka kula dasu kafin in dawo sannan kada ka mance batun Kh”…

Fisge wayar akayi daga kunnensa tare da katsewa.

 

Dafe kai Moddibo yayi cikin wani irin azabebben rauni ya fashe da matsanancin kuka tare da miƙewa batare da yace komai da Abba ba ya fice yana fita ya shiga motarsa tare dayi  mata key.

Kana ya ciro wayarsa tare da dearling number Ummi tana ɗagawa  murya a raunace yace.

“Ummi”.

Cikin sanyin murya tace.

“Na’am”.

Cikin ƙoƙarin hana kansa kuka yace.

“Ummi munyi waya da J yanzu”.

Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe kana tace.

“Dagaske Babana?”.

Kai ya gyaɗa kamar tana gabansa.

Cike da tsoro Ummi tace.

“Babana to Meyesa kake kuka?”.

 

Fashewa yayi da kuka kana cikin sheshsheƙa yace.

“Ummi ina kukan rashin J akusa dani ne Ummi wanda suka sai motarki Alhj Abdallah kice ya tura Azo aɗauki motocina da na J  duka azo asiya ahaɗa kudin duka”.

Numfashi Ummi ta fesar tare da rintse idanunta kana tace.

“Sunƙi ragewa ko?”.

Girgiza kai yayi tare da cewa.

“A’a Ummi sun rage mana Million hamsin akai yanzu ya zama Million ɗari da hamsin suke buƙata”.

Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da cewa.

“Toh Alhamdulillah wataƙila zamu iya cin nasara”.

Cike da rauni Moddibo yace.

“Insha Allah Ummi da izinin Ubangiji”.

Ya faɗa tare da katse kiran jin wani kuka na neman kufce masa.

 

Kai tsaye hanyar gida ya nufa ba abinda ke yawo acikin kunnensa face sautin Muryar J ɗinsa yana isa gida yayi Parking tare da rufe musu gate.

Kai tsaye sashen Innayi ya nufa yana isa ya zauna abakin baranda tare da riƙe kansa da hannu duka biyu,

Kana ya fashe da wani irin kuka mai masifar ciwo a zuciya.

Wani irin azaban zogi yaji zuciyarsa na masa hadi da zafi da raɗaɗi yayin da wani masifaffen rauni ya lulluɓesa.

Innayi da bacci ya fara fisgarta ne, ta miƙe da sauri jin kamar sheshsheƙan Kukan Moddibo kana ta fito tare da Kallonsa yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ya ɗauki rawa cikin sanyin murya tace.

“Ya dai Moddibo lafiya kuwa mai ya faru da Jameelu?”.

Cikin matsanancin kuka yace.

“Innayi ya zamuyi taya zanyi in.

Samu in taimaki J duk kan tattalina ya ƙare babu abinda zan samu in saida cikin gaggawa.

Zan saida tsohuwar motar  da kika siya min da wannan sabuwar da kuma na J duka za’a siyar sannan Innayi nasan koda an siyar dasu duka, kuɗin ba zasu ciki Million ɗari ba”.

Sai kuma ya kife kansa bisa guiwowinsa ya sake fashewa da sabon kuka kana yace.

“Innayi sunce idan muka sake neman ragi akan kuɗin kamar mun nemi akashe J ne”,.

Jingina kansa yayi jikin fillan dake gefenta tare da fashewa da matsanancin kuka hadda sheshsheƙa.

 

Cikin Sanyin jiki Innayi ta zauna kusa dashi batare da tace yayi shiri ko kuma ya daina kukan ba, domin  ta tabbata duk abinda yasa Moddibo kuka ba ƙaramin abu bane, kana idan har bai yiwa wannan abin kuka ba to mai zai yiwa kuka arayuwarsa.

Moddibo kuwa kuka ya cigaba da yi tamkar ransa zai fita har shidewa yake.

A ƙalla ya ɗauki Mintuna masu tsawo yana kuka kafin ahankali ya ɗago kansa tare da kallon Innayi kana yace.

“Innayi”.

Cikin sanyin murya tace.

“Na’am Moddibo”.

 

Cikin Muryansa daya dishe da kuka yace.

“Innayi ta wace hanya ce wace damace  wane daliline kike samu kike mana duk kan buƙatun rayuwarmu?

Innayi in dai har adana kuɗi kikayi in dai har basu ƙare ba Innayi ki fito mana dasu ki  taimakeni aceci J dashi”.

Jinjina kai tayi kana tace.

“Moddibo gaba ɗaya tattalin da mukayi na zaman rayuwar mu awannan yanki awannan gari a wannan ƙasar anje matakin da gaba ɗaya tattalin namu yazo ƙarshe sabida lokacin komawa muhalli ya kusan cimmmana”.

Sai kuma ta kalli Moddibo da har zuwa  lokacin hawaye ke bin Fuskarsa kana tace.

“Na tanadi komai ne domin sanin cewa muna da bukatar su kama daga karuntaka, ci, sha, Jinya, sutura.

Da dai sauransu to yanzu kuma lokaci ya tafi rayuwa ta juya abubuwa sun tafi baki ɗaya tattalin namu yayi ƙasa tsadan rayuwa ya cinye kaso mafi tsoka”.

Numfashi Moddibo ya fesar kana yace.

“Innayi koma wani irin tattaline shin babu ragowa ne ko kaɗan ne?”.

Kai ta gyaɗa tare da cewa.

“Akwai ragowa”.

Cikin kuka yace.

“Menene amfanin ragowan duk tattalin arzikin da kike dashi matukar dai ba zai fito atemaki J ɗina da shiba Jamelunki fa ya fito daga inda yake fa”.

Ya ƙare mgnar cikin ƙunan rai, domin gani yake kamar ma duk duniya ba’a damu da J ɗinsa ba.

Ita kuwa Innayi cikin tafiya wani sashi  nazarin Jinjina kai tayi tare da cewa.

“Bashi da amfani Indai bazan fito dashi ba, amma bari na fito dashi amma yanzu ka fara yin shiru tukunna kana kayi min al’ƙawarin cewa bazaka tambayeni komaiba akan duk abinda zaka gani”.

Kai ya gyaɗa mata kana yace.

“Innayi muga abinda zan fara samu awajenki tu kunna zanfi jin sanyi, ni yanzu a duniya babu tambayar da ke bakina daya wuce ina J yake , wanne hali yake ciki”.

Sai kuma ya fesar da zazzafan numfashi tare da cewa.

“Wallahi Allah ji nakeyi  tamkar naje na zauna abakin masallacai inyita bara asamu ahaɗa kudi in cikata in karɓo J Innayi ya zanyi”.

Cike da rauni Innayi tace.

“Ba zakayi bara ba Moddibo Bari muga abinda Allah zai mana”.

Kai ta gyaɗa tare da jan hannunsa suka nufi bayan ɗakinta inda randunan ƙasa ke ajiye.

Kallon Moddibo da har zuwa lokacin hawaye ke zuba a idanunsa tayi kana tace ɗaga min randan nan”.

Sauri kallonta yayi kana ya Kalli randan ƙasan tare da cewa.

“In ɗaga miki randa kuma?”.

Ba tare data kallesa ba tace.

“Kada kayi min musu idan na baka Umarni kabi”.

Kai ya gyaɗa cikin sanyin yace.

“Toh”.

Tare da ɗaga randan ya matsar gefe.

Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.

“Toh ɗaga  fantekar”.

Kai ya ɗaga tare da matsar da fantekar dake cike da ƙasa gefe.

Yana janye fantekar yaga ƙasan wajen alailaye.

Ahankali Innayi ta zauna agaban wajen Moddibo kuwa cikin sanyi jiki ya durƙusa agefenta.

Itako Innayi hannunta ta sanya ta fara tono ƙasan dake wajen ganin duhu agarin yasa Moddibo sanya hannunsa acikin aljihu ya ciro wayarsa tare da kunna tochligt ya haska mata inda take tonawan.

Innayi kuwa ahankali ta cigaba da tono ƙasan bayan ta gama kwashe ƙasan ya rage sauran wasu manyan duwatsu ahankali ta ciresu duka.

Cike da mmki Moddibo ya tsaida idanunsa akan  fafakekken rami an lailayeshi da siminti yana rufe da murfin tukunya kamar na lamba uku, da ɗan ƙarfi ta ɗago Murfin tukunya.

Cikin sauri  Moddibo yayi saurin rintse idanunsa da karfu sakamakon wani  haskene mai masifar sheƙi daya ɗauke masa idanu daya kashe  masa idanu,

A hankali ya kuma saƙe buɗe inadunsa, da sauri ya mitso ganin yadda cikin ramin ke sheƙi da ƙelƙeli mai ɗauke ido yake fitowa daga cikin ramin, acan ƙasan ramin kuwa cike yake da ƴan ƙananan sulallan gwala-gwalai wanda basu fiye yawa ba  sosai hasken ya ɗauke masa idanu saboda hasken wayarsa daya haske cike da tsanananin mamakin ya sunkuyo tare haska cikin ramin da kyau kana ya sanya tafin hannunsa acikin ramin ya ɗebo guda huɗu tabbas sulallan Gwalne…!

 

 

Littafin SAKAYYAH na kuɗine ko kin ganshi a wani wurin na satane. Ki biya ki karanta cikin Aminci 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA.

 

 

By

*GARKUWAR MARUBUTA*

Leave a Reply

Back to top button