TASKAR TARIHIN HAUSAWA DA AL'ADUNSU

Taƙaitaccen Tarihin Ibrahim Narambaɗa)

Sponsored Links

 Zai yi wuya a iya tantance haƙiƙanin shekarun da aka haifi Narambaɗa saboda dogon lokaci ko kuma rashin wayewar hanyar karatu da rubutu a ƙasar Hausa a wancan lokaci.
 Amma a hasashe, Gusau ya bayyana an haifi Narabaɗa a shearar 1875 amma shi Bunza ga na shi hasashen cewa ya yi an haifi Narabaɗa a shekarar  1890. Sunan Narambaɗa na Gaskiya Ibrahim. Ya samo laƙabin Narambaɗa ne daga sunan karyarsa Rambaɗa. Sunan mahaifinsa Maidangwale wanda shi kuma ya sami sunan ne daga  sana’ar sayar da alewa amma sunansa na Gaskiya Buhari. Mahaifin Narambaɗa fitaccen ɗan kokawa ne wanda ya shahara a lokacinsa. Asalin mahaifinsa mutanen Nijar ne, yawon karatu ne ya kawo su lardin Sakkwato don haka Narambaɗa a ɓangaren uba karatu ya gada. 
  Amma mahaifiyar Narambaɗa mutuniyar Badarawa ce mahaifanta makaɗa ne don haka Narambaɗa Karen makaɗa ne, kenan a nono ya sha kiɗa. In ana batun ƙabila kuwa daga uba da uwa duk Bare-bari ne.
Tun tasowar Narambaɗa mutum ne mai kazar-kazar don haka ma ya shiga harkar wasan samartaka sosai musamman wasan yara na lokacinsa ya yi wasan tashe da wasannin dandali na motsa jiki. Da ya ɗan tasa sai ya shiga wasan kokawa da na tauri.
  Narambaɗa ya yi karatun allo har ya kai ya sauka a hannun malaminsa mai suna Malam Shu’aibu, ya sa karatun sani har ya yi zurfi a cikinsa. Narambaɗa ya yi aure kuma ya samu zuriya.
    A ɓangaren kiɗi kuwa ya shahara kwarai mutum ne mai hazaƙar gaske yana da mu’amala da kyakkyawar dangantaka da hulɗa da jama’a wannan ya ƙara masa soyuwa a wajen mutane musamman Sarakai da Dagatai da ma Fadawa. Narambaɗa ya shiga harkar kiɗi da girmansa, wannan ya sanya kamalarsa da dattakunsa da ya sa  ake mutunta shi sannan shi ma a ɓangarensa ya ja girmansa . Duk da waƙar noma Narambaɗa ya fara har ya shahara a cikinta, ya yi suna musamman a ƙasar Gobir da Zamfara kuma wannan ne silar da ya sa manoma suka rinƙa kai masa gayyatar hira. 
 An ce farkon fara kiɗansa a fara shi ne lokacin da Galadima ya gayyace shi  a matsayin mai kiɗan fada ba kiɗan noma ba, kuma shi Galadima shi ya yi wa fadar sarkin Gobir tallarsa. 
    Narambaɗa bai samu shiga fadar Gobir ba sai a shekara ta 1927 da aka naɗa Tudu Muhammadu Na’ammani sarautar sarkin Gobir na Isa. Daga nan ya ajiye kiɗan noma ya shiga fada. Ubangidansa na farko shi ne sarkin Gobir Tudu Muhammadu Na’amani (1927-1935).
 Bayan rasuwarsa aka naɗa sarkin Gobir Ahmadu Bawa (1935-1975). Ahmadu Bawa ya shekara goma sha biyu bayan rasuwar Narambaɗa ba tare da  neman wanda zai gaji Narambaɗan a fada ba. Narambaɗa ya rasu ranar 30 ga watan janairu 1963.
Daga naku 
musa S Zage

Leave a Reply

Back to top button