SANA'O'IN

ASAN MUTUM AKAN SANA’AR /FAWA/ BY MSZ.

Sponsored Links

                                   FAWA 

Sana’ar fawa, sana’a ce da take da tsohon asali, kuma sana’a ce da kowa da kowa Zai iya yinta babu wani haram ci ga wannan sana’ar kuma mafi akasarin ma su yin sana’ar a yanzu gadarta suka yi saboda iyayensu da kankanin su ma yin sana’arsu ke nan saboda dadewa sana’ar.

  Yadda a ke samun ma su ƙaramin ƙarfi a kowace sana’a haka a ke samu acikin mahauta, kuma idan an sami wanda yake da nasibi cikin sana’ar sai kaga ya na daga cikin Manyan attajiran garin duk girman garin .

  Ma su wannan sana’a su na da zabi akan sana’ar su wanda suka riki dabbobin da ransu suke siyarwa, wasu sakan yanka dabbobin su sai da su a gutsartsari, wa su kuma a gashe, ko a tsiresu ko ai kilishin su sai ai amfani da shi, ma su wannan sana’a su kan taimakawa kansu Kuma su taimaka wa Al’umma, don ba kowane ya iya tsire ba ko kilishi ba. kuma kilishi ya na da wani sirri akan ajiye shi ya Shekara bai yi komai ba .

    Mahauta wasu a gashe suke siyarda naman . baban abin sha’awa in ka sami mahauci yasan sana’ar fawa sosai, Sai kaji ana fidda fida sunayen ko wace tsoka, ko wani sashe daban -daban da kuma amfaninsu.

   Acikin kayan cikin dabba akwai su koda da hanji da timbi da saifa da hanta da zuciya da sauransu abin da ba’a rasa ba, haka kuma yakin naman akwai (Bishi),da (Ƙwanduwa)da (Yafi) da(Tanka)da (Wujiya)da(Tozon)da (Awaza)da(Namijin nama)da (Farin makari)da(Tantaƙwashi)da(Karfafa)da sauransu. 

      mai karatu ana zamu diga aya sai mu hadu a sati na ga wata sana’ar da ban.
         Daga naku 
      musa s Zage

Leave a Reply

Back to top button