Hausa NovelsHausa NovelsTabarmar Kashi Book 2

Tabarmar Kashi Book 2 Page 50

Sponsored Links

 

Book 02 Page 50

“An gaya miki kowana ayu ne irinki?, besides mani ba auren zama nayi ba wannan shine last aikina da zanyi na gama zama a wajen” dariya sosai afifa ta saki harda kama ciki, sanann kuma daga bisani ta samu guri ta zauna. Dariyar ta qular da sãahar

“Waye kikema dariya haka?”

“Astagfirullah,da wanda ya tsargu nake” ta fadi tana fuskewa. Bata taba gain wauta zalla irinta sãahar din ba,da gasken gaske autar ce ta gaske, duk yawan buda sagonnin toufeeq da yadda fuskarta kan saki a duk sanda ta gama karanta sagon afifan na karance da shi daga jiya zuwa yau din,amma duka wanna ta tattara ta ture, itakam zataso taga ya wanna drama zata kaya.

_muma zamu so mu gani ni da jama’ar zafafa_??

Sai säahar din bata sake cewa komai ba don vau
din bata jin kowanne wasa da afifan zata yi mata zaiyi tasiri, amma hakanan maganar baby din data fada saita tsaya mata a rai. Ta yaya zata samu wani baby?, bayan ko kafin ta taho tayi period, kuma zuwa next week take sanya ran zuwan next period dinta,sannan ko a yanzun tana jin cramps a mararta, amma idan ya tabbata fa baby dinne? ta yiwa kanta da kanta tambayar,sai kawai ta samu kanta da subucewar murmushi a fuskarta wanda ita kanta batasan dalilinsa ba.

Kurba uku kacal ta yiwa tea din taji ya cika mata ciki fal, qamshin madarar dana Lipton din ciki yana son hautsina mata ciki,sai ta ajjiye tana duban afifa dake cin abincinta tuquru kan jiki kan qarfi. Kaman zatace wani abu sai kuma ta janye idanunta, tuni afifan ta ganta, murmushi ta saki

“Bestie wannan dan naki acici ne Allah”

Sai da dukkansu suka jira afifan na kusan minti
ashirin ta gama lodin abincinta sannan suka fita farfajiyar hotel din,inda taxi din da zata garasa dasu asibitin su ukun take jiransu.

Ko a hanya ma shuru ne nata,tayi nisa a duniyar
tunanin me ranar ta vau zata haifar musu? farinciki ko
akasin haka?, abinda ke qara sanyaya mata gwiwa daya ne,dukkan sakamakon da zai biyo baya ITACE SILA ALKHAIRI KO AKASINSA.

Da gudu fadeela ta sauko daga saman gadon ta
rungumeta tana kiran sunanta

“I missed you anty N” sosai sãahar ta rigeta hawaye
nason zuba a idanunta amma tana danneshi, ta tsugunna a hankali ta rungume fadeelan cikin jikinta hawayen na zartowa. Har an aske area din da za’a yi mata surgery din. Tsanar hajiya garama ta sake cika a zuciyarta sanda fadeelan ke fadin

“Abby bazaizo na ganshi ba?” Banda gudun sharrinta, ta yaya za’a yiwa fadeela aiki irin wannan toufeeq baya gurin? baima sani ba?.

“‘Zaizo in sha Allah my fadee, kada ki damu”

“Yaushe anty?” Ta sake tambayarta tana rungume a jikinta

“Yau in sha Allah” taji afifa ta fada tana riqe hannun fadeelan a tausashe. Ajiyar zuciya säahar din ta saki, har a ranta taji dadin yadda afifan ta kubutar da ita, don batason viwa fadeelan qarya.

Migewa tayi ta aza fadeela din saman cinyarta tana jin labaran da take bata na nurses din dake kula da ita,da sauran abubuwan da ke wakana a asibitin duk sanda ta tafi gida.

Awarsu guda nurses biyu suka shigo dakin nasu,cike da kulawa da sanin darajar mara lafiya suka shaida musu zasu shirya fadeela za’a shiga da ita theater room din. Dukkansu dai jikinsu yayi sanyi, banda ita abinka da yaro da kuma quruciya, tana ta yiwa säahar hira ita kuma tana qoqarin boye hawayenta. Har suka kammala shiryata hannunta yana cikin na sãahar, ba ita ta sake mata hannu ba har sai data isa gofar theater room din. A hankali ta zame hannunta cikin nata, amma idanunta cikin na fadeelan. Duk yadda taso dakewa ta kasa, muryarta na rawa tace

“Allah yasa ayi lafiya a gama lafiya fadee na,in sha
Allah,in sha Allah from this day kin rabu da wannan lalurar rabuwa ta har abada. Murmushi kawai fadeela tayi mata,idanunta gyar bisa fuskar säahar din har suka maida gofofin suka rufe suka daina ganin juna.
Afifa ce ta matso tana dora hannunta akan kafadar saahar din

“Wannan damuwa ta isa hakanan-karkije ki yiwa kanki illa fa, damuwa a irin situation dinki bata kamaceki ba,an viwa mutane bila’adadin surgery din nan,kuma alhamdulillah they’re healthy and safe,suna rayuwarsu vanzu kaman kowa,ya riga ya zama tarihi ma,samu guri ki zauna” sai taja hannunta suka zauna saman kujerun dake shirye a gurin.

Sannu a hankali sakanni suka juye zuwa mintuna, mintuna suka juye zuwa awanni, awa ba daya ba har biyu shiru,zuwa lokacin sai ta dinga jin kamar hankalinta nason barin jikinta, da gyar ta iya daurewa aka cinye awanni uku cur.

Tuni duk wani fata nata ya yanke, confidence dinta ya soma zagwanyewa tsoro da firgici, ta waiwaya ta dubi afifa data dawo daga cin abinci, abincin da babu yadda batayi da sãahar din tazo suci ba amma tace ba zata iya motsawa ko nan da can ba

“Bestie lafiya kuwa? 3hours fa” dan murmushi ta sakar mata na kwantar da hankali

“Ba komai in sha Allah, suna aikinsu ne” kasa zama tayi,sai ta mige ta koma dakinsu ta daura alwala,sannan ta dawo gurinta,ta bude qur’anin cikin wayarta ta fara karantawa gasan ranta ko hakan zai taimaka mata ta samu nutsuwa komai qangantarta.

Sannu sannu sai gashi an sake shafe wata awa
dayan har da rabi, adadin awanni hudu da rabi kenan,zuwa lokacin karatun kawai takeyi, amma gefen lafayarta gaba daya ya jiqe da hawaye, idanunta kuma sun tasa sunyi jajur, kamar yadda fuskarta ta hada jaa musamamn wajen hancinta zuwa habarta, abinka da farar fata. Duk iya hilatar da afifa zatayi tayi matan amma kuma bata samu nasara ba dole ta zuba mata ido ta shiga tayata da addu’ar itama cikin zuciyarta.

Sajjad ne ya shigo gurin, ya tsaya daga baya ya yiwa afifa alamar tazo da hannu,dukka tana kallonsu,amma hankalinta baya kansu, har zuwa sanda afifan taie sukavi magana qasa qasa sannan ta sake dawowa wajenta,shi kuma ya juya ya fice a hankali.

›Wasu mintuna arba’in dinne suka zo suka wuce duka akan idanunta dake a rarrabe tsakanin qur’aninta da gofar theater room din.

A hankali gofar ta bude, abinda ya kusa tsayar da bugun numfashinta saboda wata qaqgarfar faduwar gaba. Ko ina a jikinta rawa yakeyi sanda likitan ya bayyana a gofar dakin. Zumbur ta mige har wayar hannunta na subucewa ta fadi a gasa, dukkan idanunta a kansa tanason zuwa ta riskeshi taji daga bakinsa amma tsananin tsoron abinda zataji daga gareshi ya hanata aikata hakan.

Lokaci daya kuma gabanta ya sake faduwa fiye da na dazu sakamakon tsintar muryar da bata taba zaton ji ba. Da wani irin sauri ta juya tana kallon qofar farko ta shigowa gurin.

Sajjad ne gefansa kuma toufeeq, nadeeya na biye dasu. Sanye yake cikin wasu lafiyayyun suit da aka saqa da asalin zare me daraja na vicuna giviut fabric.

Kalar suit din data dace da kwantacciyar fatarsa da hutu da kulawa suka ratsata. Idanunta ta sauke kan fuskarsa,abinda ta hanga wani irin shimfidadden bacin rai tare da cushewar fuska,ainihin kamanninsa na cikakken miskili kuma fusataccen MT JARMA take gani muraran, hakanan cikin sassarfa yake takowa fiye da sajjad da nadeeya. Kamar ya sani ko yaji a jikinsa tana kallonsa. Nasa idanun va zube a kanta sanda idanunsu suka sarqe cikin na juna sai taji gafafunta sun fara rawa, bugun zuciyarta ya garu ainun, mararta ta daure tamau yana sake kusantota tana jin kamar ana juyata daga hagu zuwa dama, daga gaba zuwa baya. Sai ta fara gani dishi dishi lokacin da mararta tayi wani mugun murdawa dai dai lokacin kuma da likitan ke magana da harshen jamusanci

“Wo sind Fadeelas Verwandte? Folgen Sie mir ins Büro, es gibt etwas sehr Wichtiges, das ich Ihnen sagen mochte (ina ‘yan uwan fadeela?,akwai bayani me matuqar muhimmanci da zanyi muku”. Idanunta ta dauke daga kansa tana mayarwa kan likitan dake nufar office dinsa da sauri sauri. Ganinta yana sake zama dishi dishi toufeed na kusantota idanunsa a kanta,lokaci guda kuma taji wani abu me dumi yana ratsa jikinta sannan ya zarto zuwa qafafunta ta cikin lafayar jikinta,sannan ya taba takalminta ya kuma fara sauka a farin marbles din dake shinfide a gurin.

Idanunta takai kai,wani irin abu ya daki
kwanyarta,jini ne, irin jinin da ta taba gani kenan sau biyu a rayuwarta,zamanin rayuwarta a gidan adam,zamanin da take mararin haihuwa da samun iri, yau ga na uku na fita daga jikinta wanda shi kuma wanna bata da tabbacin jinin meye?. Ruf idanunta suka gama fullubewa, tayi baya gaba daya zata zube a wajen,saidai tsananin zafin naman da toufeeq yayi ya hana hakan faruwa.

Cikin zallar tashin hankali ya tarota ta fada a jikinsa. Tuni afifa ta taso kanta, itama nadeeya ta garaso da sassarfa, shi da su kowa na kiran sunanta da garfi hankali tashe, toufeeq din yana jijiga kafadunta,saidai ko alamar motsi batayi ba. Hankalinsa a matugar tashe yake duban jinin dake zuba daga jikinta,sai ya dauketa cak kawai ya wuce office din likitan da gaggawa.

Suna shiga likitan dake rataye lab coat dinsa ya waiwayo,zuwa lokacin tuni ya shimfideta saman gadon dake dakin,cikin rudani ya juye harshen jamusancin shima yana cewa

“‘Der Arzt hat ihr schnell das Leben gerettet, ich weiß nicht, was mit ihr passiert ist (Dr ka ceto rayuwarta da hanzari bansan me ya sameta ba)” da gaggawa ya danna wani abu sai ga nurses har biyu sun shigo, ya kalli toufeeq

“Sir, geben Sie uns einen Arbeitsplatz?(sir ko zaka bamu guri muyi aiki?)” Kai toufeeq ya girgiza,yana tsaye qyam a gabanta hannunsa cikin nata,yana jin wani tashin hankali na ratsashi

“Ich kann nicht rausgehen und ihr vor meinen Augen irgendetwas antun(bazan iya fita ba,kuyi mata komai a gabana)”. Yadda suka karanceshin sunsan ba zaya fita din ba,abu daya yayi dole ya sake mata hannu don ya basu damar gabatar da aikinsu,ya koma baya kadan hannunsa zube a aljihun suit dinsa, idanunsa da suka sauya launi saboda tsananin tashin hankali qur a kanta tamkar an gaya masa yana janye idanun zai rasata.

Cikin lokaci gangani suka farfado xa ita daga suman da tayi sukayi goqarin tsaida jinin. Bai tsaya ba amma ya ragu,ganin hakan ya sanya likitan ya kunna na’urar scanning ya fahimci ne yakeson yi,sai ya matso gabansa

“Fass es nicht an, lass die Frau es ihrer Tochter antun, ich kann es nicht ertragen, das zu sehen(kada ka tabata,ka bari mace ‘yaruwarta tayi mata,bazan jure ganin haka ba)” likitan nada fahimta sosai da kuma saugin kai ya saki murmushi kawai ya matsa baya yana-sakarwa daya nurse din na’urar,har yanzu murmushi yakeyi sannan yace

“Du liebst sie anscheinend sehr, deshalb bist du so eifersuchtig auf sie(kana son ta da yawa da alama, shi yasa kake wannan kishin)” Kansa ya jijiga da qarfi don ya tabbatar masa da girman hakan cikin zuciyarsa

“extreme Liebe(matsanancin so)” ya amsa masa a taqaice.

Idanun likitan nakan allon computer din sanda take scanning din yana kuma yiwa toufeeq din bayani

“Kaine mahaifin fadeela?” Kai ya sake jinjina masa,sal ya waiwayo a nutse ya kalleshi, sannan ya saki murmushi, haka kawai yaji toufeeq yayi masa,ya miga masa hannu yana murmushin

“‘Ina tayaka murna,munyi aiki successful irin wanda bamu taba yin kamarsa ba,munyi nasarar cire sashen dake sakata jijiga in sha Allah daga yau zata rayu kamar kowanne mutum, amma zaku kula sosai da qa’idoji da kuma zuwa dubata har ta kammala warkewa duk da dai mun fahimci kamar any amfani da wasu magunguna a kanta da sukaso fadada ciwon ya taba wani sashen daban na qwaqwalwarta,wanda inda hakan ta faru ba zata taba warkewa ba, saidai taci gaba da rayuwa akan magani har qarshen rayuwarta,to sai kukayi dabarar tsaida maganin, abinda yayi nasarar hana afkuwar hakan,kuka kuma yi dabarar kawota akan lokaci akayi mata aikin,Glückwunsch(congratulations)”. Wani irin abu me sanyi ne ya sauka saman zuciyarsa tamkar ana sanya sassanyan ruwa ana wanke masa zuciyarsa. Cikin sanyin da mutuwar jiki ya migawa likitan hannu shima

“danke Doktor(na gode dr)”. Maida dubansa yayi ga saahar dake numfashi a hankali saboda allurar baccin da yayi mata bayan farfadowarta

“Wanne irin nau’in so zai gwadawa rayuwarta ne?” Ya
tambayi kansa da kansa,shi kansa baisan iya adadin sonda yake mata ba,ga wasu dalilai da suka qara rura wutar qaunarta me tsanani a ransa,shi kam bai sani ba baisanta yadda zai sarrafa wannan soyayya da qaunar da yakej) cikin qirjinsa ba.

“Setzen Sie sich, Herr (zauna yallabai)” likitan ya fada
yana dubansa, koda suka bashi seat din gaban gadontaya maidashi hannunsa cikin nata vana sake kula da dukwani motsinta

“‘Zamu bata daki itama,zuwa nan da awa sha biyu zamu tattara bavananta zamu sanar maka” likitan va fadi yana sake nazarin scanning din.

 

Zafafabiyar
??????????????

Leave a Reply

Back to top button