Bakar Ayah Book 2Hausa Novels

Bakar Ayah Book 2 Page 7-8

Sponsored Links

Page 🖤7••8🖤

 

 

Lokacin data shiga Sayyada-tateen tana zaune akan carpet ɗin falonta,da kwanon tuwon semo a gabanta miyar kubiyah,kana shiga warin yajin daddawa zai bugi hancinka.
Labari suke tayi da wata mai aikinta wacce take itama dattijuwace ta manyanta,labari suke tayi tana warfa lomar ɗumame hankalin ta kwance kaman tsumma a randa.
A bakin ƙofah Lylah tayi sallama tareda shigowa cikin falon,kallo daya Sayyada-tateen tayi mata tacigaba da taɗinta wanda sukeyi akan Ruwan kogi na ƙauye.
“To dakika shigo bazaki zauna ba kika tsayamin akai kaman naci miki bashi,mai ya kawoki wajena ma da sanyin safiyar nan oho,dan nasan ta Allah bata kawoki ballanta ta annabi,saidai ta allaro”
Duk sababin da Sayyada-tateen takeyi babu wanda Lylah ta tanka,don ba wannann ne ya kawota ba,burinta shine bata Hajiya zeenah a wajen Sayyada-tateen ɗin,ita kuma tasamu shiga sosai,ta hakkanne take ganin zata fara takunta na farko,wajen karbar ragamar gidan daga hannun ta.
“Uhm iyah ya ƙafar taki,ina fatan tayi sauƙi koh”
Miƙa ƙafar Sayyada-tateen tayi tana kallonta,wacce take luwai da ita kaman bata tsofi,magana tayi da tuwon a bakinta.
“Hmmm ƙafata bazata durƙushe da wuri ba,domin nayi mata horo mai tsanani na tafiyah,dan daga ƙyauyenmu har Samunaka nake zuwa a ƙafah…..ohh wato soma kuke nima na koma kaman Aliyu ku samu yadda kuke so ko,ta Allah to ba taku ba ehe”
“Ahah iyah niba wannan ne yakawo ni na,dama wani zancene nake tafe dashi mai muhimmanci wanda naga yakamata ki sani”
“In ma wannan zancenne da audillahi yayi min na zakiyi aiki a company bazan yarda ba,nice nan nace ban yarda ba,inkuka shiga aikin maza wazai kuma rike muku gidan,matan da suke gidannann bazasuyi aikin gwannati ba,dan kunka daulah bazaku kawomana tsarin nasara ba sam….. Yo ke Laure mai za’ayi da matar datake aiki a wajen maza,mu zamanin mu ina muka san haka sai su,su a dole ga ɗaliban nasara”
Shuru Lylah tayi tana kallon Sayyada-tateen,gaba ɗaya ta hanata tayi mata bayanin abinda ya kawota,in tafara magana saita cafe tayi wani layin daban,abin duk ya isheta.
“Iyah nifah ba wannan ne yakawoni ba,Hajiya zeenah tana can ta aurowa Jabeer wata mata daga can Gembu,yarinyar bata san tarbiyyah,yanzu haka zancen danake miki yanzunnan shigowarta cikin gidannan,wai tun jiya tabaro garinsu ita kaɗai,a hotel ta kwana na cikin gari,yau kuma tashigo cikin gidan. Ko Hajiya zeenah bata gaisar ba tanufi sashenta,shikamma mijinnata aka ce koh Kallonsa wai batayi ba,har fah mai aiki ta takawa ƙafa a shigowarta”
Shuru Sayyada-tateen tayi da kunne tanajin maganar da Lylah take da zubomata,wanda ta tariyo da wajen mai aikinta indo.
Tana gama bayanin Sayyada-tateen ta tafa hannu tafara sallallami.
“Lahaula wala ƙuwata yau ni Sayyada inagani abu,ke laure wai wannan zance haka yake?”
“Eh ƙwarai kuwa Hajiya sayyada,ɗazu kam naji ma’aikata suna maganar shigowata nan wajenki zan kawomiki yaji”
Shuru Sayyada-tateen tayi dan yanzu tarasa ma kuma abin bafah,a jima tace uhmm……in anjima tace uhmmm. Sudai sunyi shuru suna kallonta sai ajajjaba abin takeyi.
“Wannan shine uhm inji kuturu,ke La’ilah(Lylah),tashi tashi muje yanzunnan ki rakani sashen ita zeenatun naga yarinyar,bazan lamunta ba,wannan ai shine iya shegen wai layyah da kare,muje ki rakani yau zata san takawo mana tantiriya zuri’ah,yo ko ƴar aikice ai ban lamunci wacce zatazo ta ruguza tarbiyyah ba,ballanta matar gida,hakan ma kuma ta Jabiru,shida yake babba a yaran gidan. Abin ai zai mana yawa shege da hauka,ga wata can bamu gama hucewa da tujararta ba,za’a sake takalomana wata kuma,so ake a maida min gidan ƴaƴa sansanin barikin taƙadarun mata?”
Tana tafe a hanya tana sababi,itadai Lylah bata ce komai ba sai binta take a bayah,banda dariyar jin daɗi ƙasa ƙasa babu abinda take.
“Ke la’ilah wai ina baban gidanne da jikinsa?”
“Kai iyah,nifah sunana Lylah,miye kuma wani la’ilah kaman zakiyi salatin,shekara da shekaru amma kinƙi kama sunan common suna”
“Kee Butar Ubaki,miye kuma comon wato zagina kikayi koh,dama kema bawani son ki nake ba,saida na hana audinllahi auroki ya tuƙe,da ƴar kyauyenmu ya aura da tuni suna nan da yaransu ina,Amma yaje ya auroki kin Haifi ɗa kaman gammo duk a kanannaɗe,ke anya kuwa Iskokai basabin danginku ma?”
Harara Lylah ta makawa ƙeyar Sayyada-tateen,wacce take gaba tana tafiyah tinkis tinkis sai surutu take zubawa kaman rediyo,dan takaici ma shuru tayi bata tanka mata ba.
Hajiya zeenah ta tashi kenan daga dinning zata shiga ɗakin ta Sayyada-tateen ta rafka sallama a ƙofar falon.
Maleekah ce ta taho da gudu tareda hugging ɗin Sayyada-tateen.
“Ohh my dear kakus,biyoni kikayi kinga banzo ba?”
“Hmm ai barni ɗiyar albarka,ba biyoki nayi ba nasan ai zaki je,wajen wannan tujararriyar uwar taki nazoni,naji wani mummanan batu yana zagawa”
Cuno baki Maleekah tayiwa Sayyada-tateen,dan dama daga ita sai Abdulmaleek,sukadaine ke shiri da ita a gidan.
“Haba kakus kodanni bazaki daina yiwa mommy haka bane,zanyi fushi dake fah”
“Ke kijim yarinya,yau ɗin hadewa zakiyi da iya kinunamin ni barece,yo yi fushin mana ai inada Audu ma idan kika tafi,bariki ga na zauna kafar nan tawa sai a hankali”
Kujera ta samu a falon ta zauna,gyalen dayake wuyanta tacire ta ajiye tareda kallon Hajiya zeenah.
“To haziƙa mandiyah babu iso kuma babu sannu da zuwa,gaisuwar ma saina roƙa ko me?”
Matsowa inda take Hajiya zeenah tayi tareda gaisheta,bata amsa gaisuwar ba dan dama ba ita ta kawo ta ba.
Ɗauke kanta tayi tareda kallon Madeenah wacce take tsaye tana kallonsu,dan ita dama bakasafai take shiga shirgin mutum ba ,inya shiga natane dai bazaiji da daɗi ba.
“To sarauta nima sarautancin zakiyi min,narasa cikinki ke da jabiru wayafi iyah shege”
“Hmmm kinga iya ni makaranta zan wuce inada defend dazanyi kanki ake ji,inna gaisheki ma naga ba amsawa kike ba,ina san gaisuwata saina ajiyeta saboda gaba”
Daga haka ta saƙala jakarta tabar falon,dama iliyah yana jiranta a mota.
“Ke zeenatu wajenki nazo naji dahirr daga bakinki,shin da gaskene kin aurowa Jabiru taƙadariyar mata? Kuma bada izinin kowa ba,bansani ba dangi basu saniba,yaushe yaron yazama naki ke kaɗai,a iska aka miki cikinsa bashida uba?. Wai kekam wacce iriyar uwace kam,kinfiso yaronnan yayi ta fama da bauɗaɗun mata”
Shuru Hajiya zeenah tayi tanajin Sayyada-tateen tana ta masifah,itadai batace komaiba.
“Kiyi haƙuri iyah yanxu kam koma menene yariga ya faru,sannan a matsayina na uwarsa inada dalilina akan hakan,saboda in matsala ce ba a taimakonka,in kayi ƙoƙarin gyarawa kuma sannan za’aje ana zundenka a gaba,ko kunya ba’aji”
Takarisa maganar tana kallon lylah,wacce take zaune a kujera tanajin abinda yake faruwa.
“To maganin haka iyah a kiramiki yarinyar mana ki ganewa idonki da kanki idan ƙarya akewa mutum”
Lylah ta fada da biyu,dan itama dama tanaso taga ya yarinyar take da idonta.
“Hakane kam zancenki la’ilah,ke Maleekah kije kice mata ina ƙirnata yanzunnan a nan sashen tazo ta sameni”
Amsawa Maleekah tayi tareda toh,ta fice daga falon.
Bayan kaman minti talatin suna zaune tadawo daga inda aka aiketan.
Shuru tayi tana kallon wanda suke falon tana zare ido,alamar taga abinda yashiga hankalin ta,tsaida idanuwant tayi akan mahaifiyar ta,tareda yimata alama da ido kan tayi magana? Ɗaga mata kai tayi da eh,wanda hakan yasa Maleekah tamayar da idonta wajen Sayyada-tateen,wacce tayi ƙamo tana jira taji mai za’ace.
“Uhmm Iyah naje nasameta a falo tana bawa wani yaro a cinyarta nono,……uhm ……uhm danace mata wai kina ƙiranta sai tace wai…..”
“Saitace wai me,anya kuwa ita kika gani,yanzu haka shirmenki ne,wacce amarya ce kuma budurwa za’a kawota da jinjiri”
“Wlh iyah itace wacce tashigo gidannan ɗazu a mota,bamuga dan bane inaga dan yana mota.
Cewa tace wai bataga wanda ya isa yasakata tashi tazo ba Ɗan ta bai ƙoshiba,saiki jira idan tagama kulada shi yayi bacci sai tazo,inkuma bazaki iyah jiraba ki haƙura”
Saurin tashi Sayyada-tateen tayi daga inda take zaune,saida Lylah dake gefenta ta maidata ta zauna,kuma daga yanda Maleekah ta faɗamata zancen tasan bazatayimata ƙarya ba.
“Yaunake ganin abu ni Maryamu,yau mai nakeji da kunnuwana,haka ta faɗamiki ki faɗamin,kin faɗa mata wacece ni a gidannan kuwa?”
“Eh nafaɗa mata Iyah,wani juya ido tayi ma da alama hakan bai dameta ba”
“Zo muje ki rakani wajennata dan malafar ubanta”
“Ahah iyah Sayyada,bai kamata kije ba,tunda tace zatazo ki bari tazo ɗin,daga nan sai a nuna mata iyakarta ,amma wannan kam bata goyu da zaniba”
Lylah tafaɗa tana alamun taya Sayyada-tateen jimami,nan kuwa a cikin ranta murna ce fall ganin faɗuwar guntun fadar Hajiya zeenah na tabb da rushewa a wajen Sayyada-tateen.

Duk gaisuwar da mutane ke aikamasa babu wacce yasamu damar amsawa,kansa ya asama yake tafiyah har ya nufi office ɗinsa.
A hankali ya tura ƙofar ya shiga,bai zauna a kan kujerar aikinna sa ba ta hutu ya nufa ya zauna,ganin zaman bazai yi masa ba ya kwana yana kallon cilin,yarasa mai shin wanne tunani zayyi a lokacin.
Ya kai akallah awa guda a hakan,har bacci yafara ɗaukarsa,a sama sama yajiyo murya Khaleel yana bugar kujerar dayake kwance.
Ɗan firgita yayi ya farka tareda ware idanuwansa a kansa,tsuka yasake bamai sauti sosai ba.
“Khaleel yaushe ka shigo ban kulada kai ba”
“Uhm ina zaka kula kana bacci,mai cewa a dage da aikine yake bacci a office?”
“Kamawa tayi shiyasa,akwai wani abune?”
“Ahah bakomai,kawai lekowa nayi mu gaisa,sai kuma na ganka a kwance,amaryar taka ta iso ne”
Yamutsa fuska Jabeer yayi tareda kallon gefe,kana gani kasan baima da niyyar bawa Khaleel amsar dayake bukata.
Dariyah kana ya ɗora dacewar.
“Ashe Maleekah ba kayar take ba,data shaida min zuwan amarya,yanzu gashi nayi comferm da kaina”
“Kaga Khaleel serious mafita nake nema,inaga wancan shawarar daka bani zanyi amfani da itah,dan bazan iya rayuwa tsakanin wadancan matan ba,ni daga ganinta ɗazu sainaga ma kaman gwara Lubnah da ita,gabaɗaya batayi kamada mata masu zaman aure ba,beside ma tafi kama da sojoji ko kuma masu aikin bodyguard”
“Hhhh bodyguard kuma? To maizaihana ta dunga binka duk inda zaka tana baka kariyah,ni wlh dakukayi maganar ta har naji inaso inganta”
Shuru Jabeer yayi bai sake cewa komai ba,dan dama shi doguwar magana ba’a jininsa take ba,don Khaleel ɗinne ma shiyasa ya zauna yake masa maganar.
“Ni banajin zan iya wai abuma yanzu,idan babu abinda kake dan Allah kozaka rakani wani waje,akwai abinda nakeson nuna maka”
Fitowa sukayi daga suka office ɗin suka nufi wajen parking motoci,a motar Jabeer suka fita dan dama a kusa yayi parking ba wajen da ake yi ba.
Hanya suka hau suna tafiyah,Khaleel ne kaɗai ke surutunsa shi yana jinsa,saidai ko yaɗanyi dariyah ko yace uhm,babu abinda yake buri da muradi illah ya haɗu da ƙyaƙykyawar yarinyar data sace masa nutsuwa,bashida abinda yake so a yanzu illah tozali da fuskarta.
Ɗan murmushi yayi shikadai Lokacin daya tuno sanda ya kaɗeta,duk yadda yayi da ita ya taimaketa ƙin bashi dama tayi,hakan ba karamin burgeshi yayi ba. Yana cikin duniyar tunaninne yajiyo muryar Khaleel yana tambayarsa dalilin dayasa ya kawo su ƙofar gidan.
Bai sani yana cikin tunani she sun iso gidan.
Fitowa yayi a motar yanufi ƙofar gidan,yasan idan yaga bai bashi amsa ba ai zai biyoshi.
Hakan kuwa akayi biyo bayansa yayi daidai lokacin da wani yaro mai kimanin shekara goma yafito daga gidan,tsaidashi Jabeer yayi tareda tambayarsa babansa.
“Yana ciki barina ƙiramuku shi ”
Yana faɗin haka yakoma cikin gidan”
Bai daɗe ba suka fito a tare,yana ganin Jabeer ɗin yasaki fara’ah,yayinda shikuma yagaidashi cikin girmamawa.
“Ahh kune da safiyar nan,gidan ƙalau koh”
“Lfy ƙalau baba ya mai jikin toh”
“Jiki alhamdulillah dama ba wani ciwo ne sosai”
Bayan gaisuwar suna tsaye sunyi shuru,sunkuyar da kai Jabeer yayi yana sosa ƙeya,da alama akwai magana a bakinsa wacce yagagara furtawa.
Kulada hakan ta Malm Umaru yayi yasakashi cewa.
“Ahh yaro shigo daga ciki mana nan turaka ta ku gaisa da mai jikin koh?”
Aikuwa dama kaman Jabeer jira yake,da sauri yayi na’am da haka,ransa ƙall cikeda farinciki.
Duk abinda ake shidai Khaleel a tsaye yake tun bayan gaisawar da sukayi da mutumin.
Jan hannun Khaleel Jabeer yayi babu ko kunya suka shige cikin gidan.
Wani ɗaki aka kaisu na ƙasa,mai gajeren saman rufi,saida mashaallah a share yake tass babu ƙazanta a cikinsa.
Malm umar yana fita Khaleel ya zunguri Jabeer,dan dama jira yake dattijon ya fita. Cikin raɗa yafara tambayar sa cikeda muradin son ƙarin bayani.
“Kai bangane ba wai meyake faruwane,nan ɗin inane”
“Kai kam katsaya mana ka gani,”
Cikin ƙankanin lokacin Jabeer yabashi labarin haɗuwarsa da Jaleelah a taƙaice”
A zaune take a ɗakin mahaifiyar ta Inna Mairo,karatun hadda take wacce zata bayar da yamma.
Muryar babansu taji ya yana nemanta,hakanne yasa ta rufe ƙur’anin tafito.
Cikeda ladabi ta tsugunna tareda cewa cikin muryarta mai sanyi marar hayaniya.
“Baba gani”
“Yawwa dama wannan yaron daya kadeki ne yazo duba jikinnaki,ganin yanason magana dake yasa nace masa su shigo shida abokinsa kije ku gaisa ”
Shuru Jaleelah tayi kaman bazata ce komai ba,sai daya gama kafin tace toh.
Tashi tayi tashiga dakinsu ta ɗauko hijabinta,hanyar ɗakin babannata ta nufah,cikeda itama fargabar sake haɗuwa dashi a karo na biyu,tun ranar da suka haɗu yayi mata gizo dama.
Suna cikin magana tayi musu sallama cikin siririyar murya taahiga ɗakin kanta a sunkuye.
Shuru sukayi yayinda hankalinsu yakai kanta,amsa mata sallamar sukayi daidai lokacin da ta zauna a can nesa dasu.
“Yawwa ya jikinnaki,i hope babu wata matsala sosai koh”
“Eh babu,ban wani ji ciwo ba ai sosai,Allah ya tsare,nagode da kulawa”
“Ohk ba komai,banji sunan marar lafiyar ba”
Ɗan murmushi tayi wanda yasaka dimple ɗinta motsawa kana tace.
“Sunana Jaleelah”
Daga haka hirar ta ƙare sukayi sallama bayan Jabeer ya ajiye mata bandir ɗin kuɗi,shima bata karba ba,bashshi yayi a wajen suka tafi bayan sunyi musu sallama.

Shuru Hilyaan tayi tana kallonta,dan taga mai zatayi idan ta gama bawa haidar abicinnasa,abinda tayi tunani ne ya faru,dan Bombee batada niyyar kiran da kakar mijinnata tayi mata.
“Amma anty maryam kinsan fah tana can tana jiranki,kuma kincemusu kina zuwa”
“Ohhh wai har yanzu suna jirana,kaii nifah tunda nayi tafiyar nan bansamu wani hutu ba”
“Idan kikaje kika dawo ai saiki huta,dan allah karki fara daga yanzu mana,tunda shekara zamuyi ki dan bari a ja lokaci mana kafin a fara”
“A fara me,me kika maidani ne,jarababbiya? To naji barina je naji mai zata bani take nemana”
Sungumar ɗanta tayi a kafaɗa,har taje bakin ƙofa taga Hilyaan bata tashi ba”
“Yana ganki a zaune,bazaki jeba ne”
“Ahah jeki dawo dangin mijinkine,ni inanan kidawo ki sameni,Allah ya takaita abinda zai faru a wajen”
Hilyaan tafaɗa tana dariyah ƙasa. Taƙaitacciyar harara Bombee tabata kafin ta nufi sashen Hajiya zeenah,inda Sayyada-tateen take zaman jiranta.
Shuru kakejin falon babu mai cewa komai,ajima kaɗan Sayyada-tateen taja tsaki,a ƙallah tayi sunyi cikin carbi.
Tashi laylah tayi tareda cewa.
“Uhm inaga wannan amaryar fah bazata zo ba tafi ƙarfin amsa ƙiranmu, nibarin tafi toh haka”
Tashi tayi zata bar falon,har taje baƙin ƙofar suka haɗa ido da Bombee,wacce ta dakko danta daga cikin mota ta nufo hanyar shiga sashen Hajiya zeenatun.
“Toh ga amarya nan ta amsa ƙiran bayan tagama shan ƙamshin”
Komawa tayi ta zauna babu ko kunya,saboda yanda gulmar san ganin mai zata kasance take cinta.
Kujerar da take facing Sayyada-tateen Bombee taje ta zauna,idan ido yana kisa daya kashe ta,amma ko a jikinta kaman an tsikari kakkausa.
“To kun ƙirayeni gani nazo,mai zaku bani”
Tafaɗa bayan tasaka ɗan ta cinyah tana kallon Sayyada-tateen.
“Kuyi sorry fah barku kuna jira,ɗana ne yake bukata ta,kunga kuwa bazan barshi ba nazo wani ƙiranku”
“Ɗanki wanne irin ɗa?”
Sayyada-tateen tafaɗa tana kallon Bombee dakuma Hajiya zeenah,wacce tayi shuru kaman ruwa ya cinyeta.
“Ɗa mana irin kowanne,ƴaƴan kala kala ne dama”
“Ton ina ubansa ko dangin ubansa dazakizo mana da ɗan wani cikin gida,oh yanzu dama zeenatun bazawara ta aurawa ɗannata,wanne wace irin badaƙala ce”
“Kinga ni bansan ubansa ba ballanta na wasu dangin ubansa,ni kaɗai yakeda kuma zan tsaya masa,menene a ciki ,sauran zancenki kuma bangane su ba”
“Bakisan ubansa ba,kina nufin kice mana shegene?”
“Haka dai kika ƙirashi,ni ɗa nake gani a gabana ,shege kuma ai zagine kawai”
“Hoɗan kekuwa ƴar nan suwaye iyayenki,sannnan wacce irin tarbiyya sukayimiki da ko ƙasashen Aranaku ba’ayinsa,aradu basai gobe ba gidannan zaki bari,tunda nake bantaba ganin tambaɗaɗɗiya yake ba,shege zaki kawomin cikin zuri’ah….hhhhh Kai Kai kai ke Maleekah ƙiramin meeting yanzunnan inason ganin kowa”
Ganin Sayyada-tateen tafara kuka ne yasa Bombee ɗaukar ɗanta,kana ta kalli Hajiya zeenah.
“Wainikma Hajiya zeenah aiki nazo miki kokuma fama da matsalar iyalanki? Tun wuri ki sanar musu su daina shafani cikin lamarin rayuwarsu,nima kuma batasu zan shiga ba,idan kuma ba haka ba zan nuna musu kala ta banida daɗi,musamman tsohuwarnan,haka kawai nagidanmu basuyimin ba wasu bazasu dameni su takuramin ba,kowa yayi rayuwarsa”
“Gabaɗaya suka kalli Hajiya zeenah tareda maimaita kalmar …”Aikeeh “… A tare.
Batada lokacin su ballantana samun lokacin yi musu bayanin tambayar dasukayi wanda dama bada ita suke ba,dan haka ta ɗora danta a kafaɗa tayi hanyar waje hankalin ta kwance kaman tsumma a randa.

_*SADI-SAKHNA CEH*_

___****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK 2_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31

Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150

______________****_______________

 

 

Leave a Reply

Back to top button