Hausa NovelsTUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 19

Sponsored Links

 

 

 Fitowana ke nan daga
dakina zuwa falo muryan ummace ke fadin ki dauki kayan abincin nan ki kaiwa su
Abban ku a falon shi daga nan ki tambayeshi idan suna bukatan wani abin ki kai
masi.

  Ja nayi na tsaya a
wuri daya ina kallon ummah din dake magana dani lokacin kafin nace da ita ummah
wani abincin kuka girka masu a nan kuma ?

   Ina su gwaggo sunce
an girka masu a gidan hjy ai to Abbah ku yace kada a kawo a nan zamu girka ai
kinga ni yaune kawai zan basu abinci daga gobe hjy maimunace zata basu har su
bar garin nan don dole nasan dai ya koma zuwa Monday ai.

    Badon naso ba na
dauki abincin dake a shirye nida Tani muka nufi part din Abba din Tani ta tsaya
daga kofa nice na fara shiga da kayan abincin ciki da sallama a bakina.

    Suna zaune saman
kujera daya zaune a hade jin sallamana yasa Abba ya dan gyara ga yadda suke
zaune din na nufi wajen dinning dinshi yace kawo muna nan zaifi.

   Na juyo nazo
gabansu a kasa na aje saida na aje
abinci kafin na dago ina gaida Abba da ina wuni Abba mama kuna lafiya
ina ita umman nakune nace tana side dinta na juya wurin matar data kafeni da
idanu nace mommy ina wuni ?

  Lafiya kalau yan
mata wanan mamatace itace na sakawa sunan hjyn mu Abba ya fada na mike nafito
na karbi na hannun Tani ta juya ta koma ita.

    Na kai gabansu na
aje ina jin Abba na mata bayani take fadin wanan na ganta dazun a part dinsu su
wa yancan ne ban samu ganin su ba.

   A nan na gane sunki
yarda data gansu ke nan son nasan suna gidan dai weekend bamu fita zuwa ko ina
ki turo min umman taku Abba ya fada.

   Na koma na isarwa
Ummah da sakon Abba na dibi abinci na koma saman doguwar kujera na zauna na
fara ci ina kallo ummah tace kina da dabi,an son zama a nan kici abinci ga
wurin cin abinci can ki bari.

    Hakan baisa na
daga ba naci gaba da kallon da nakeyi din tare da kannena naji ummah tace min
dazun da kukaje gidan hjy abinda takewa ke nan ashe ta nuna maku jan ido ga
zuwan  ku.

    Bansan meya yasa
hjy take wanan halin ba haka ko kudin da ku nazo daga gidan mu oho barta kawai
na iya fada ai dole tunda tasan gaskiya take takewa duk abinda mutum yayi don
kansa ai.

    Can naga ummah
tamike ta fita ni dai har muka gama kallon mu muka shige ban fito wajen ba ban
kuma san lokacin data dawo part din ba don na kai kannena daki na rufo kofan
daga ciki data shigone ta rufe kofan.

    Washegari misalin
tara na safe wayana ya dauki kara ina kwance lokacin ban tashi daga barcin
safen da nakeyi ba na lalubo wayan na kara a kunnena bayan na dauka.

   Muryan Ahmed naji
yana min sallama na karba mai muka gaisa yake fadin badai baki tashi ba har
yanzun daga barci ba zarah  ?

   Murmushi nayi ina
fadin yanzu dai aikatashe ni brother yace manya ke nan har wana  lokacin mutum yana kwance yana barci ?

    Nayi murmushi yake
fadin  zahar don Allah idan ba damuwa
zanzo gidan kune na karbi kudin nan dake hannun ki zamu shiga kauye ne mu sayo
wake da gero don azumi daya kawo jiki.

   Nayi shawara na
sayo su da kudin tunda lokacin sayan su ke nan yanzu nabi wanan riban da zan
samu OK na fada kudin suna nan yadda ka bani su ban taba ba ai.

  Na sani yace min
nazo ba matsala na karba kazo mana idan kazo saika kirani nafito na fada yayi
min godiya ya kashe wayanshi a lokacin nima na mike na daga gado inda na boyesu
sunan  yadda na barsu na dauko tare da
bude wardrobe din na na ciro wani envelop na ciro kudi a ciki na hada dasu na
mayar da sauran a ciki.

    Bandaki na shiga
na kewaya na fito na daura gyale akaina lokacin wayana ya dauki kara wata kila
dama yana kusa da unguwar tamuce dama.

   Na dauka ina fadin
gani fitowa ina daga wajen get ya fada nace ka shigo kawai ciki zan fito yadda
nake dagani sai dogon riga da gyalen dana daura a kaina na fito.

   Na hangoshi a cikin
shiga irin na kauyawa da suke shiga daji da wani hula aja akanshi saidai yana
hangoni ya fara cire hulan a kanshi ya nufoni fuskanshi dauke da dan murmushi.

    Muka hade muka
kara gausawa na mika mai kudin zakace wani takardane yadda ledan suke don yadda
na shiryasu a ciki.

  A daidai lokacin su
Aisha tare da Rukkaiya suka fito daga cikin gidan namu ko su san sunga mutane a
wurin basu nuna muna hakan ba.

   Daga inda muke yake
fadin ina kwanan ku Rukkaiya ta wani kalloshi tasa kai ta wuce mu yace toh ga
manya gaisuwan ma sai angadama ake karbawa a gidan ku.

    Murmushi nayi nace
yanzun kauyen zaka ke nan yace dana bar nan mota nacan mun fara taruwa sai mu
daga Allah ya tsare na fada naji karan bude kofan fitowa again.

    Mamace ta fito
naji gabana ya fadi ras na juya ina gaida ita tayi dan jim kafin ta amsa tana
wucewa zuwa wurin motar dasu Aisha suke shiga ko ta shiga baya sukaja suka fice
a daidai fitan su naga duk sun kallo mu suna magana.

   Yai min sallama
shima ya tafi na juya na koma ciki a falo na samu ummah tsaye suna hada abin
karyawa ita da Tani nasan sun makara ko kuma aiki yayi masu yawa lokacin.

    Ummah ta juyo tana
fadin yaushe kika fita daga nan nace yanzu wani ne yazo amsan takarda a wurina
nakai mashi .

   Amma kinsan Abban
ku yana gari kika fita haka ko ai yanzun na fita na bata amsa kizo ki kai kayan
nan falo nasan kila sun tashi suna jira yanzu.

    Nace to na fara
daukan kayan zuwa falon Abban mu nayi sa,a babu kowa a falon har na gama jerawa
na juya zan fito naji an bude kofan matar ce ta fito na juya ina gaida ita
tace.

   Aa kece ashe ina
jin mitsine ina ciki na leko nace eh da kara fadin ina kwana ta amsa min cikin
murmushi tare da fadin sannu da kokari ki gaida ummah taki kafin na shigo gaida
su.

   Wanka na fito duk
da ina jin zuciyana a wani irin don ba dadi ko farin ciki a zuciyana mai na
zauna ina shafawa naji wayata ta dauki ringing na duba Ahmad din ne ya kirani
na dauka.

    Yayi sallama na
amsa ya fara fadin nazo na bude kudin naga sunfi wanda na baki a jiya yawa eh
na sani nima bansan me zanyi dasu ba na baka ka kara don naga kana bukata .

   Amma zarah hakan
zai iya hadani dake don kudi ba ayi mai haka Allah dai ya bada sa,a na fada
yace amin yanzu kim aramin dai na kara ke nan nace eh aro din na baka.

    Amma kuma ban faye
son  kudin wani a cikin sana,ata ba abin
dan uwa aibana aani bane na bashi amsan na kashe wayata naci gaba da shirina
rana  shigar atampa nayi dinkin riga da
buje.

   Har na kwanta na
mike na nufo waje kitchen na wuce na dauko goran ruwa na fito ido muka hada da
amaryan Abba dake zaune a falon ummah tana fitowa daga bedroom din ta.

   Matar yar kwalisace
sosai don shigarta kawai zai nuna hakan kamar na shareta saidao na daure na
sake gaida ita ta amsa itama a cikin fara,a tare da fadin hjy ki bani yar nan
taki mu zauna tare da ita Abuja .

    Ayi hakan tana
karatu a nan ai Dear ya fada min ai a can kuke kuka dawo nan yanzu  wallahi ummh ta fada mun dawo gida saboda
yara su saba da yan uwa da al,adun mu na nan din ta fada kamar yadda Abba da
mama suka tsarata a lokacin.

   Abinda ummah ba ta
sani bashi don mama dake son dawowa gida da yaranta a lokacin yasa muma tasa
aka dawo damu kusa da ita don kada mu zauna birni suna gida su.

   Don dama Abujan
tace zata dawo Abban yace bai yarda da hakan ba shine tayi makarkashiya wurin
hjy inno kakarmu Abba yasa kowa dawowa gida.

   Murmushi matar tayi
kafin tace nayi mamaki keda kike da yara kanana haka kika yarda kika dawo nan
ba tare da yaranki sun samu wadatattacen ilimi ba kamar yadda yan uwansu suka
samu a can su.

   Nan ma ai sunayi ba
laifi bawa duk baya wuce kadaranshi ai in Allah ya nufa zasu zama wani abu a
rayuwa zasu zama din aiko mahaifinsu a nan din yai karatu har ya zama wani abu
yau a rayuwan shi.

   Hakane Allah ya
raya munasu ummah ta amsa da amin sai sukai shiru gaba dayan su don matar ta
kula da ummah bata da yawan surutu yasa taja bakinta itama tayi shiru .

   Waya Abba ya bugo
mata zata gaisa da wasu abokan shi yasa ta mike zuwa falon na Abba tavarwa
ummah part dinta duk ina dakina ban fito ba yinin ranan.

   Mama ko tana can a
family house din suna kwasa dasu gwaggo don takai karan gun hjy saita samu da
sanin tsohuwar da aka toshe wa baki da abin arziki akai auren ashe.

  Wana  yasa suka hargirse a wurin ta fara fadan
bakaken maganganu garesu suma suka shiga ramawa tafito hasale ta juyo zuwa
gida.

    Dije ce ta leko
daga daki sukai arba da akuyanta datayiwa suna da uwargarke da yau uwargarken
ta juye ta komawa dije wani abu na daban da Dije ta kasa fassarawa lokacin.

    Yauma tun fitan
Amadi gidan suke takon saka a tsakanin su dalili kuwa shine  ruwan kasarin da ya kwana Dije ta gyara masu
don Amadi yau sakkon fita yayi bai samu tsayawa yadda ya saba gyara masu ba.

   Ita kuma ganin ai
ruwan baiyi komai ba yasa ta gyara masu shi ta aje tana kokarin juyawa ta bar
wurin taji kamar an bangajeta ra dauka wani a bayanta mai karfi yayi mata wanan
bangazan .

   Allah ya gyara bata
kai kasa ba ta juyo taga uwargarke a tsaya tana ture ruwan cikin jarkan da kai
hakan bai mata ba tasa kafa kamar mutum ta ture ruwan ya zube a wurin.

  Da sauri Dije taja
baya a firgice don sai taga kamar ba akuya bace mutum ne ai gabanta don yadda
uwar garken ta nuna hasala a fil sai hakan ya ba Dije tsoro ya koma dakinta ta
shige sai lekowa takeyi daga cikin dakin tun safe ta kasa fitowa ta dan rage
aiyukanta na gida kamar yadda tasaba yi.

    Gashi kamar hadin baki
yau ba wanda yayi sallama a gidan ita kadaoce a cikin gidan sai dabbobin ta
dake kiwonsu inka debe uwar garke dake tsaye tun lokacin bata kwanta ba ta
kurawa kofan dakin Dije din ido babu kiftawa.

    A daidai lokacin
da Dije din ke lekawan ne a yanzu uwargarke din ke kwantawa a makwancinta
komawa Dije din tayi baya ta dafe kirjinta tana sauke ajiyan zuciya.

  Sai kuma raji
shigowan mutum gidan yana sallama da mamaki a fuskanshi yake bin gidan da
kallon ganin a yadda ya fita yabar gidan haka ya dawo ya samu gida kamar tun
safe Dijen bata leko wajen ba.

    Dijeh ya fada da
karfi kuma a razane yana sauri zuwa kofan dakinta sai gata ta leko a tsorace
don ta sheda shi din ta gani ko wani sukai arba da juna a hakan.

   Amadi kaine ashe ta
fada kamar a tsorace tana kokarin yunkurawa ta
mike tsaye lokacin yace wai lafiya kike kuwa Dije ? Tace balau ba kan
,  kadai huta a san nayi a gidan don ga
baki daya duk a firgice nake yau din nan.

   Me ke faruwa agidan
ne Dije ya sake tambayanta a gagauce, Dije ta dubeshi tace huta dai mayi
maganan daga baya barin dan fita in samo muna dan wani abu inciwa cikina ta
fada tana jawo tsunman gyalenta daga kofa a rataye.

   Tasa kai da sauri
ta fice gidan ko kallon inda dabbobin suke batayi ba ta fita da sauri ya bita
da kallon mamaki don yadda take jan kafanta mai mata ciwo kamar na dole takeyi
lokacin da sauri.

    Juyawa yayi wurin
dabbobin yana kallon su kafin yabi ko ina na gidan da kallo yasan duk da
tsohuwar nada ciwon kafa amma idan yai irin tafiyan nan na sammako ya fita bata
barin gida haka da datti saita gyara shi.

    Cikin dan lokaci
yayi tunane kardai yawan maganan akan uwargarke da tsohuwan keyi ya zamo
gaskiya fa shi bai kula ba har wani abu yazo ya samu kakar nashi saidaga baya
yayi daya sani akan hakan .

  Bin bayan Djje din
yayi wace ya samu a tsaye kofan gidan nasu kamar tana tunane Dije ya ambata
daga bayan ta cikin murya mai nuna yanayi.

    Ta juyo a firgice
taga shine ya karsso dab da inda take tsaye yana fadin Dije meye damuwan kine
wai  ki fada min don naga kamar a firgice
kike yau a gidan.

    Duban bayan shi
tayi kamar tana duba idan wani na biye dashi lokacin kafin taja hannun shi su
taka dan nisa kadan da gidan nasu kafin tace yau uwargarke taso kasheni Amadi.

   Kasheki Dije tace
kwarai nan ta kwashe komai yadda ya faru ta labarta mashi tare da fadin don
haka dole ka sayar da akuyan nan ko mu saketa tabi gari kawai taje duk inda
zata.

   Dan shiru yayi yana
kallon tsohuwar kafin yace baki ganin in muyi hakan munyi ganganci Dije akuya
nan fa ba zamun takeyi a gidan nan ba yanzun.

  Tana zama na amanane
a wurin mu yanzu yau idan mun saida ita maishi yazo muce dashi me ke nan ta
dawo mun koreta ko ta dawo mun sayar da ita ?

    Kiyi hakkuri kizo
mu shiga gida zan san abinyi kan hakan me zakayi ta tambayeshi a dan tsorace
tana kallon shi don jin me zai fada.

   Yace bari dai yanzu
koma ciki bari na gangara na sayo maki abinda zakici kafin motan kayana ya iso
nan da dan lokaci in zama busy ya fada yana kokarin wucewa.

    Ta jawo hannun shi
ba zaka barni da wanan abin ba a gida ni kadai kai subbahanallahi ya fada kafin
ya dan daga kai yana tunane a wurin na dan lokaci.

    Yanzun zo ki zauna
ga wuri naje in dawo yanzun nan yana jan hannun ta zuwa wurin dan dutsen dake
kofan gidansu a kafe inda wani lokaci suke zama ko masu tafiya su zauna asama
su huta akai.

   Zama tayi kamar
yadda yace din shi ya wuce can inda yan mata ke saida abinci ya sayo mata
shimkafa da salad da miya da nama yanka hudu sai ruwa mai sanyi daya riko mata
a leda lokacin tare da fantan kwalba.

   Ya dawo suka shiga
gida tare ya kaita har dakinta ta zauna ya fito ya diban mata ruwan wanke hannu
don yasan ba zata ci da cibi ba saida hannu.

   Saida ya tabbatar
da ta fara cin abincin a galabaice ya
mike ya fito sai wurin dabbobin nasu ya tsaya a gaban uwar garke daga
daki  inda dije take ta iya hangoshi
wurin yana gyara masu wuri.

    Ya zubar da ruwan
ya dauke roban ya wanke ya share wuri ya zuba masu abinci da ruwa duk a cikin
zafin nama da alama yana saurine a lokacin.

  Haba uwargarke keda
Dije ba hakan tsakani  ku ai karki manta
Dije itace farin ciki  gidan nan dani
daku duka baki dayan mu gidan ai Dijece gatan mu kin ture ta idan wani abu ya
sameta yau duk ya samemu ke na  ai.

    Ke kanki ina baki
girman ki na babba cikin yan uwa duk wani laifi ko wani abu kece babba ke, ke
dauka don haka kibar firgita min Djje don Allah ba lafiya ke ga tsohuwar ba kin
sani.

   Haba uwar garke bai
kamata haka  ba tsakanin ki da Dije sai
mutunci ai yanzu kibar mata abin dabo dabo tana firgita dake haka don Allah.

   Zaka ce da mutum
dan uwanshi yake magana a lokacin yana taba uwargarke magana sai ta mike ta
girgiza jikinta kafin ta dona kai a ruwan shan su tana sha .

   Bayan ya gama dasu
ya dawo zuwa dakin dije daga kofa ya tsaya yana mata magana Dije zanje na duba
na gani ko motar kayan mu ta iso na fake don nan nake son a kawo min su gida
tunda banda shago a kasuwa yanzu.

    To kayi niyya
Amadi Allah ya taimaka nima barim je gidan malam Tanimu harka dawo sai in dawo
gidan ta fada tana yunkurin tashi tsaye ya dawo ya tsaya yana fadin .

   Dije kardai ki
dauki wana zancen ki kaiwa makwabta shi suzo su fassara wanan magana  da wani manufa kuma daga baya.

   Kinsan yadda mutane
suke yanzu balle ana ganin na fara sana,an nan da kudin mutane sai su dauka ai
wani hali na daban na farayi yanzu karshe ma sai a camfa gidan nan kiga anzo
anki shiga daga karshe azo ana gudun gidan nan kuma.

    Hakane fa yanzu
lokaci ya canza ai gara daka kwabeni don kan abinda nayi niyar zuwa fadamasu ke
nan yanzu inda taimakon da zasuyi min su taimaka min dashi.

    Ba abinda zai sake
faruwa in sha Allah har inma ta hurhurane Allaj zai muna maganin ta balle yanzu
ina batun shigo da kayan nan kinje kin fadi hakan a take zasu camfa min ne kan
kudin tsafi nake amfani dasu.

    Alhalin kudin
mutane ne na aro na kara nake juyawa tace Amadi kudin wa ka anso yace naso maki
wanan bayanin kuma sai naga baki cikin hankalin ki yanzu idan na dawo zan fada
maki komai in sha Allah.

    Nan ya fice ya
barta tana zancen zuci ita kadai a gidan har ta dan samu fitowa ta gyara gida
saidai tanayi tana kallon inda dabbobin suke har taje ta sakamasu hayaki saboda
sanyi a wurin garken nasu.

Leave a Reply

Back to top button