Hausa NovelsTUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 29

Sponsored Links

 

 

 

ZAINAB IDRIS MAKAWA.

[1/30, 7:07 AM] +234 701 497 9567: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

2️⃣9️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

Tafe suke ba wanda ya iya magana a cikin su don kowasu
zuciyar shi a jagule yake lokacin don abinda malamin ya fada masu game da
tafiyan nasu.

    Wani unguwa mai
nisan tsiya can suntubawa fita gari wurin wani tsohon bafilace suka fito wanda
akace ya shahara da asirin mata ko wani iri mace ke so idan taje wurin shi
tagama samun bukatanta don mutumin ya iya aiki sosai a cewan manyan matan gari.

    Saidai su tafiyan
nasu ya daure masu kai sosai matuka don kusan amsan shi daya da babalawon data
taba zuwa wurin shine lagos a baya ita da kawarta dan sanyin da taji shine
zancen hjy karima daya fada mata cewa ba zata taba haihuwa a gidan Abba ba
asalima dai baiga zama a tsakanin su ba nai tsawo a duban shi din.

   Wanan ya dan sa ta
rage jin tafasan zuciyar ta a lokacin saidai tunawa da zancen zahra din yasa
kuma taja tsuki a lokacin da bata shirya jan hakan ba a bakinta.

   Kallon ta yar nata
dake gefen mai zaman baza tayi tana fadin mekuma kika tuna kike jan tsoki nifa
dama damuwa kan wanan tsohuwar da Alh ya kwasone don sam ban damu da zancen yar
nan taku ba.

   Don nasan bata taba
kai diyan ki kaf dinsu a duniyan nan don me zaki saka damuwa haka akan yarinyar
nan ne wai maimuna ?

   Yarinyar da duk
inda kikaje akece maki akwai matsala a rayuwan ta tome ya rage kuma ki mata
yanzu ki barta can suji da matsalansu ita da uwarta su hakan ya shafa ai.

   Watau ya saude baki
ganewa ne tunda nasa ido ga yarinyar nan zahra naji Allah ya saka min tsanarta
tun tana karamar ta kwata kwata na tsani yar a raina wallahi.

  To ya zakiyi tunda
mai hadawa ya hada zaman ku a innuwa daya saiki kawar da idonki a kanta ki
mayar da ita da banza duk daya a gareki kiba kanki lafiya zaifi.

    Ko nace zanyi
hakan na kwatanta yadda uwarta ke taushe zuciyar ta wurin nunawa nawa diyan
kauna sai naji na kasa hakan ga duk yaran salma din .

   Bana son naga Alh
yana nuna masu kulawa ko wani nuna kaunan suma diyane a gareshi don Allah ya
gani banso ace wai salma ta haihu da Alh ba a gidan nan.

    Haka da yawa suke
ji kan yayan mijinsu saidai kowa na taushe zuciyar shine a zauna lafiya bakiji
manya sunce dan kishiya rikon mai hakkuri ba .

    Duk wacce kikagani
tana ji da dan kishiya dole akwai tabon haka a zuciyan ta yan kadan ne keyi
tsakani da Allah to ita taki mun kasa gane ko a wani ajin take do  komai wayaun ka baka taba fahintar salma.

    Munafuskace ta
gaske don baka taba ganin bacin ranta kome kuwa zakai mata zata iya hadewa ta
shanyewa cikin ta ta boye abin yai mata zafi koda kuwa mijin ne yai mata hakan.

  Ai taci sunan ta
kuwa salama son sunan ya dace da halinta mama saude ta fada a hankali taga yar
uwan na rage gudun motarsu taga tayi parking a wajen masu kayan marmari zata
saya.

   Tana tsayawa masu
kayan marmarin suka taso suna fadin hjy a sai kankana asai abarba wani kuma na
fadin hjy Apple ne ko kai don Allah wancan nake so na tsaya ta fada a dan
tsawace masu tallan suka fara ja da baya mai table din lemun ya taso yana dauko
leda tare da fadin na nawa za a zubane ?

    Zuba na dubu daya
sai Ayaba shima na dubu daya ta duka tana dauko kudi a jakkan kayanta tana
dagowa idonta ya sarke cikin na wani makaho dake zaune rike da sandanshi baiwa
kowa a wurin magana sai dai mika roba da yakeyi.

   Da sauri ta kawar
da kanta gareshi don sai halittan mutumin taga ya bata tsoro kafin ta dago kai
da niyar bawa mai kayan marmarin kudi sai ganin shi tayi bakin window motan
tsaye yana fadin.

    A taimaka saboda
Allah da Annabi matafiya Allah ya sauke lafiya tafiyan da akayi Allah ya mayar
da aniya ga mai ita sarkin da akayiwa ya sani.

   Masu mugun nufi ya
koma masu masu hassada halinsu ya bisu masu, , , haba malam muba tafiya muka
fito ba nan cikin gari muke mama saude ta fada a hasale don irin adduan da taji
yana fita a bakin shi.

   Mai sayar da
kaya  marmarin yace dasu ai malam mamman
kalar baranshi ke nan shi hjy ai fata na gari yai maku yanzu din Allah ya kaiku
gida lafiya.

  Motar mama data fara
jan motan tayi yasa ya kauce yana masu Allah ya tsare ya bar wurin yana binsu
da kallo har suka bacewa ganin shi ya koma bakin sana,arshi.

   Mama saude ta fara
magana tana fadin kinji mun mutumi wazai baka sadaka da wanan baran nasa wai
nufin mutum ya bishi kamar wanda yasan abinda muka fitoyi.

  Nima shinake tunane
mama ta fada irin mutanen nan ina tsaron haduwa dasu don wata kawata a lagas ta
taba yin gamo irin haka da kyat ta sha daga sherin su.

   Sai yamma sosai
suka isa gida suna magana daya sun shiga gida ana kiran magariba direct part
dinsu suka nufa mai wanki yana biye dasu da kayan tsaraban da suka sayo a
hanya.

    A sabule ya shigo
gidan Dije dake zaune a baki  murhu ta
dago ta dan kalleshi tana fadin yau da wuri haka ka dawo yace eh Dije yau munje
kauyene na dauko hatsi a can .

    Ledan da ya shigo
dashi a hannun shi ya aje a gaban ta yana fadin wanan naman na gani a can yai
min araha na sayo muna shi kinsan kauye suna da arahan komai su.

   Ledan ta jawo zuwa
gabanta ta fara buda tana fadin kace min dai yau dadine a gidan mun huta da cin
yan yama yama kwana biyu gata nan dai ki zuba ma,ishi kowa ya wadata yaci .

  Mikewa yayi ya nufi
wurin garke yana gyara masu dauri kafin daga can din yace Dije uwargarke dai ta
barmu da kewan ta kullun nazo wurin nan saina tuna da ita wallahi.

    Dole a tuna da
uwargarke sabo ba karamin abu bane don kusan shekara nawa ana tare da ita ba
zan manta ba a daren da mahaifinka zai tafine yazo gidan nan sallaman ka shine
ya bani fam biyar nayi ta boyonsu har suka kara taruwa.

   Saina hada na fara
sayan karo dashi ina dan kiwatawa sai na sayar nasai wani har kai ga sayo
uwargarke daga baya naji bazan iya sayar da ita ba don tana da shigan ciki a
jikinta lokacin.

    Kai kuma ka dauki
son duniya ka dora a kanta ance dabba baya dadewa to nidai kan uwarharke tayi
min halarci don ta haifa min diya da yawa inba daga bayan nan da ta zama juya
ba ta daina haihuwa nasan kuma tsufane tayi ya jawo hakan.

   Yanzun gashi ta
barmu don kanta tayi tafiyanta ai mun morewa wanan dabban sosai ko yanzu ta
barmu ai munci ribanta ko.

  Ballema bata tafi ba duk inda take idan ba
yankata maishi yayi ba zata dawo gidan nan in sha Allahu komai daren dadewa
kuwa nasan zata dawo garemu.

   Sororo Dije tayi da
ledan data dauka wanda ya shigo dashi da nama zata ta wanke tace haba dai Amadi
har son da kakewa uwargarke yakai haka yau kwana nawa da batan ta inane ba ace
min anganka kana nemanta ba ?

   Ni kaina na zaga
kaf gidajen unguwan nan na duba koda wanda ya ganta amma babu labarin ta ai ya
kamata ka hakkura haka ka fitar da rai a zancen ta kuma.

    In sha Allahuma
zata dawo don na yarda da hakan kuma an fada min hakan ma zai faru daga inda
take takemai kallon kanka daya kuwa Amadi ya gane me take nufi yace .

   Dije uwargarke da
kike gani alherice a garemu rabuwa da ita kinga zai muna jimame din haka kiyi
fatan Allah yasa ta dawo gidan nan garemu.

    Ta dawo wani gida
koka manta cewa a yanzu ita din ba mallakinmu bane wai da me itafa a yanzu don
me zaka dauki sin duniya ka dora a kan dabba haka wai ?

   Murmushi yayi daga
duken da yake yana fadin keba zaki gane hakan ba ai Dije amma nasan abinda
nakeyi ni tace to Allah ya kyauta kada ka koma dan bautan akuya na mutanen
kasan India.

   Suda kiri kiri
zasuga ta mutu su nemi wata suna mata bauta kuma daga baya ko su gina gunkita
su dinga bauta mata.

    Dariya ya kwashe
dashi ya gama gyara  gida ya koma gyaran
wajen gidan su ya dade a can wajen yana gyara kafin ya shigo cikin gidan ya
samu harta gama girki tana kokarin gyaran wurin.

  Karban aikin yayi
daga hannun ta koma kofan dakinta ta zauna tana fadin yaro da iya aikin mata
haka matar ka ta huta saika dinga miya ita tana tuwo ke nan.

  Daga duke ya bata
amsa yana fadin dukama zanyi mata ita ta huta kina ma zancen mata wa zai bani
yarsa garin nan an fara fada min cewa banda asali.

 Wane dan banzan ya
fada ma hakana wani irin zancene haka nake ji a bakinka kai mutane akwai iya
sheri garesu kaida ubanka ya bar garin nan yatafi ya barka a saman kafafun ka
biyu.

   Amma aiku kuka hana
inna tabishi yanzu ba gashi ta zauna garin ba da kunka hana tabin mahaifina ai
kun yarda tabi wani daga baya kuma.

   Kai Amadi shin
kanka daya kuwa a gidan nan koka fara shaye shayen zamanine da akeyi yanzu a a
zan bar yata zuwa wani nisan uwar duniya da banda kowa a can ni ina nan cikin
gusau zaune zama ?

   Ashe dama ni kaka
zargi da hanaka zama da mahaifin haka kawai nika daukan yata in mikata uwar
duniya ni ina nan nan niya gara dai su rabu din yafi min sauki da ace ya tafi
da ita can inda ba a sani ba.

   Kina fadin wai ba a
sani ba baku san garinsu ba kuka yarda yarku ta aureshi dole inga laifin ku a
yanzu don na daina jin zafin mahaifina da nakeji a baya yanzu laifin ku nake
gani.

   Shiru tayi tana bin
jikina nata da kallon mamaki kafin tace shiyasa kataho min da zancen shi
kwanaki ko ai tun lokacin na fara zargin da akwai wani magana a kasa da kake
son fito min dashi.

    To bari kaji garin
nan kaf ba wanda naji ya taba zuwa garin da yace ya fito saidai naji sunan
garin a gidan redio jefi jefi.

    Amma dai ai cikin
kasan nan yake ko koma ba kasan nan bane ya zama dole yanzu inje neman
mahaifina duk da yayi banza dani nan cikin duniya amma nasan dole ina ranshi
idan yana raye.

    Wa hwada maka ga
garin da yake da zama taka maimai ko nan daya taho ai a karkashin Alh Abu dan
canji ya zauna shina ma yayi auwalin aurene har muka yarda muka bashi ita.

   Daga baya da tahiya
tayi nisa yake fada muna shima bai san garin su ba ya dai yaba da hankali nena
ya tsaya mashi akai auren.

    Gara ma tun wuri
ka fitar da zancen shi a ranka don kila ma baya raye yanzu ni haka nafi sawa
raina don gaskiya inda Auwalu na raye nasan daya taho nan ko don kai.

   Dije ko bai raye
zanje yan uwanshi su san dani a a nika zama nan ana tsangwamata kan laifin da
ban aikata ba gara naje nasan asalina da anka fara fadin bani dashiya.

  Aiki ko ja a gabanka
zuwa wanan garin har uwar duniya don baka san iya kwanakin da zakayi a hanya
kafin ka kai garin.

  Zuwa lokacin yagama
hasala da kakar tasa don da ace Dijen tasan yadda zuciyar shi ke tafarfasa a
lokacin da bata yi wanan zancen dashi ba a lokacin.

   Damace gareshi a
yanzu don haka bai cewa Dije din komai sai shirin tafiya daya fara bayan ya
tambayu kan yadda zai kai kanshi garin mahaifin shi na asali.

   Tare da samun karin
bayanin yadda zai iya gano mahaifin nasa idan ya isa wurin wasu abokan hurdan
mahaifin nasa a nan gusau da yai zaman mutunci dasu a garin.

   Sallah asuba nayi
na zauna ina tulawa a wurin kafin gari ya kara haskawa na fara jin motsi a
gidan na mutanen gidan dake kara kaina a tsakar gidan ina jin motsin duk abinda
sukeyi saidai ban fito bane waje lokacin.

    Bayan na shafa na
mike na shiga bandaki wanka nayi don nayi saboda hakan don zuwa school dana
saba fita da safe dana gama azzakar saina mike na shiga wanka.

   Na fito na shirya
cikin dinkin atampa da akai min buje da riga na fito yar shar dani na mike na
fito zuwa falon gidan namu.

    Babu kowa a falon
saidai abinci da yan aiki suka jera a saman dining wata kafira da dan bujene a
jikinta ta fito daga kitchen dauke da wani katon dood warmer a hannun ta tanufi
dining din ta aje ta juyo sai lokacin ta ganni a zaune.

  Ina kwana mah ta
fada tana dan rage tsawonta kadan don ban girma a gareni na amsa ina kare mata
kallo tare da kyaman yadda na ganta nasan ba musulma bace.

  Don mu a lokacin
zaman mu gidan ummah bata taba yarda ta dauki yar aiki kafira ta jefa cikin mu
saidai musulma yar uwan mu da zata bamu tarbiya a tarevta dauketa tankar yarta
na cikinta.

  Idan zasu tafi kuma
a rabu a cikin mutunci da dadin rai ana kewan juna kamar kada su tafi amma
gashi yau arniyace a gidan take dan yawo da buje kuma cikin kazanta haka irin
nasu ko don ina kyaman hakane a raina bansani ba ?

  Hjy nakawo maki
abincin ki a nan ne ta tambayene cikin girmamawa nace no ki barshi idan na
tashi ci zan nemeki tace yes mah ta nufi kitchen inda suke aiki.

    Daga kai nayi na
kalli dakin ummah wanda a yanzu mallakin mommy ce wai sai naji zuwa Abujan nan
ya zame min dana sani don abin bakin cikin da nake gani a gidan ga zuwana.

   Karan budan kofa
naji yasa na dago kai mommyce tafito daga dakinta tana kokarin nufar dakin Abba
dake rufe sai kuma ta juyo ta dawo zuwa dining da nufin duba abinda aka girka
na breakfast.

    Kullan farko ta
bude ta rufe ta fara kwalawa kiran sunan wata da Tabitha daga can kitchen mai
sunan ta amsa sai gata da sauri hjy ta fara fadin banace idan kun gama ku fada
min kafin ku kawo kitchen wai meyasa ku bakwa jin magana ne ko koyaushe sai na
dinga nanata maku hakan ne ?

  Dauki kikai min daki
idan na gama zan kiraki fito dashi sorry ma Janet naba ta kawo ashe nan ta aje
ai ban manta da dokanki ba.

  Common dauki ki tafi
kin tsaya kina surutu tana fadi ta juya ta shige daki matashiyar matan tabi
bayan ta duk wanan abin bata kula da cewa ina falon zaune ba ta shige dakin.

  Gabana ne ya fadi me
za a jeyi da Abincin kuma a dakin mommy tsam na mike daga inda nake zaune din
na nufi dakina dana fito gado na haye na kwanta ina faman tunane.

    Barcine ya soma
daukana a hakan naji an turo kofa na bude idona mommyce  tashigo a cikin shirin ta na fita aiki ganina
na shirya tsam kamar mai shirin fita ta saki murmushi a fuskanta tana fadin.

   A, a my daughter
wanan kwalliyan haka rangas ko wani wurin zaki tafi dagowa nayi da dan murmushi
a fuskana na zauna ina kokarin sauka daga gadon tare da fadin ina kwana mommy ?

   Lafiya kalau ya
gajiyan hanya koda yake da alama kin sauke gajiyan ma ai tunda naga harkin
shirya haka fita zakiyine ta sake tambayana.

   A, a mommy ba inda
zani kawai dai haka na saba dashi damani na fada na koma saman gado na zauna
tace to ai hakan yai min dadi sosai don dama ga abinci can an gama sai ki fito
muci kafin Alh ya fita dama baku wani gaisa sosai ba jiya ya shige part dinshi.

   Mommy bana karyawa
da safe haka sai dai in an jima zan fito nace wajajen karfe goma kice min yar
tawa baturiyace kema kina irin tsarinsu ke nan dai ?

   A a mommy haka dai
na saba daman ni to ki fito ku gaisa da Abbanki yana falo zaune zan fada masu
kadasu kwashe kayan abincin sai idan kin karya din yanzu taso muje kafin ya
fita.

  Zaune Abba yake yana
waya tana fitowa yake fadin kinsan fa sauri nakeyi kin kuma je kin zauna abinki
can  sai gani na fito bayanta hakan yasa
yai shiru a lokacin.

   Har kasa nakai ina
fadin Abba ina kwana lafiya ya amsa min dashi yace ya gida ya kika barsu a can
, ?

    Kowa lafiya suna
gaida ku  amma ban samu zuwa gidan hjy na
sallameta ba don nasan zai tambayeni hakan.

    Ba laifi ya fada
yaci gaba da cin abincin shi da mommy din ta zuba mai wanan din kuma datasa
akai mata daki dazun.

  Ta juyo tana fadin
daughter idan kinzo karyawa wanan ferfesune a cikin cooler zakiji dadim shi
sosai ga Abban kinan ma zai sha kefa Abba ya fada naji tace ai kasan ban faye
cin kifi haka da safe ba.

  Kofa aka bude wasu
mata biyune suka fito a cikin shirinsu duk muka dago muna kallo  su .

 

Leave a Reply

Back to top button