Hausa NovelsTUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 45

Sponsored Links

 

AFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

4️⃣5️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

   Abu kamar wasa
karamar magana ya zama babba don mazajen su Aisha sunzo da lokacin da suke son
bukin su aahe mama kuma ta gama shiryawa hakan.

    Don haka zancen
auren su dai ya taso lokacin gadan gadan don kowa yasan lokacin buki a cikin
dangi duk da ba,a sani ba hakan bai hana in saka kaina a cikin zancen ba.

   Tunda gidan mune
za,ai sha,anjn bukin nima a bangarena ina nawa shirin a hankali abinda bamu
sani ba shine harda ni ake shirin wanan bukin wata rana ummah ce da girki ta
shiga gun Abba.

   Yake fadi a
gadarance ki fadawa yarki ta turo min wanan yaron yazo mu zauna dashi a cikin
mamaki umma ta kalli Abba din tace wani yaro ke nan fa ?

   Abba ya kalli ummah
fuska daure don anfi wata yana daure mata fuska hakanan daga ummah harmu babu
mai ganin fuskan Abban din a yanzu  idan
yana gidan.

    Wanan dan iskan
yaron data nace masa kika daure mata gindi a kansa kuma nayi nadama sosai a
rayuwana danayi sakaci har hakan ya faru dani.

   Mamakin ummah ya
kare a lokacin don haka bata san lokacin data bude baki tace da Abban kwarai
kuwa yadda kayi nadama nima hakan nake nadama a kullun a kanka.

    Mutumin da ya
kawoka gari bai damu da damuwan ka ko sanin halinda kake ciki ba sai son zuciya
da bata kawai kasa a gaba duk abinda aka fada maka a kanmu ya zaunu a zuciyar
ka.

  Kaje mun barka da
Allah duk wullakancin daka shirya zakui muna Allah yana sane da hakan maamah
dai yata ce don haka aka biyo ta gareta a kuntata min Allah yana tare da mai
gaskiya ko yaushe.

    Zuwa lokacin
hawaye ya gama wankewa ummah fuska ta juya ta fita daga falon suka hade da mama
da zata shigo tabi ummah din da kallo ta fada falon.

    Zaune ta samu
Abban din rashi a bace shima take fadin lafiya naga kowan ku haka rai a bace
dan tsuki Abban yaja yana fadin barsu kawai.

   Wai na fada mata
zahra ta turo min yaron nan shine take fada min maganan banza mama tayi saurin
fadin ita salma din yace ni suke son batawa suna a banza.

  Aidai shike nan
tunda kace su turoshi in ma wani abin ne su sukajawa kansu hakan ai kace kai
baka iya kwaban yaro sai duk abinda yayi daidaine gareka.

   Daga baya kuma azo
aga laifin mutane a banza hakan dai da kayi shine daidai din yanzu a hadata da
yan uwa a wankesu kowama ya huta yafi.

    Abban bai kara
magana ba don yadda yake jin zuciyar shi game da zancen a lokacin har ta gama
ta koma part din ta tana labartawa su Aisha abinda ya faru.

  Budan bakin Rukaiya
tace a,a nikan baso hakan ba gaskiya ga zahra dadai an barta ta fito da wanine
mama zaifi gaskiya..

    Wani harara uwar
da Aisha suka jefeta dashi Aishan tace aisai ki nema mata wanda kike ganin ya
dace da ita ko ki bar mata kabir din ki ta aura shike nan.

   Tasan cowon kantane
ita wanan din aida itace haka ya sameki farin cikin hakan zatayi a ranta tunda
yan iska suke gara na nuna ma salma bata kai ba wallahi .

   Haka zasu kare daga
ita har yar nata a cikin wahala da tsiya ko yaushe wasa take dani kawai bata
sanni ba har yanzu sai sunyi kukan jini da idanunsu gidan nan.

    Miji kan wane ita
tace ra fiku shi saidai ta nuna maku kyau da baida rana a gidan badai ta fiku
mijin nunawa tsara ba kan.

   Na dawo a gajiye na
san Abba na gari don haka ban warganta ba koda din dai bana tsayi saurin dai na
ranan yafi na kullun.

   Na iso part din mu
ina sallama duk da ummah na falon zaune nayi mamakin kin karba min sallaman da
batayi a ranan har na karasa na gaida ita ta amsa min da kyay da gani tana
cikin yanayin bacin rai sai naji ba dadi a raina.

    Haka na shige daki
na kwabe kayan jikina nashiga bandaki na dan jima na fito na saka kaya ajikina
falo na fito naci abinci lokacin ummah bata falon tana daki suna waya da hjy
karima lokacin.

  Don ta samu labari
shine ta kira ummah din suna maganan da ita kanzancen sai da batun sune na
kishiyoyi da bai karewa kowa nason ganin bayan dan uwa ko wani tashin hankali
ga dan uwa.

    Ta dai gama dadin
bakinta a lokacin sukayi sallama ta kashe wayan anyi kiran magariba na shige
ciki dama dabia tace bana fitowa inci abincin dare idan naci na yamma.

  Don haka sai ban
fito ba a ranan bansan wainar da ake toyawa a gidan ba ke nan don ummah tabi
shawaran hjy karima ta koma wurin Abba sunyi ba dadi ga zancen.

  Har Abba ke fadin an
fada mai ko kwanaki angan mu da Ahmed a bakin wani layi mun tsaya muna magana
dashi akwai zubar da mutuncin dayafi wanan.

  Meye dalilin sai mun
motan da yayi don in ta tsayawa da maza ya saya min ko don me zai saya min mota
ina yawan banza a gari.

   Don haka zai hadani
da yaron muje can mu karata kuma ummah ta sani zai saka dokoki masu tsauri a
kaina saina gane kurena na kin maganan shi da nayi.

   Wa,iyazubillah
ummah kan ta shiga tashin hankali don ranan kwana tayi buge bugen yawa saidai
kamar hadin baki magana daya ake fada mata cewa tayi min adduan Allah yasa
hakan shi yafi zama alheri a gareni.

   Karshe data kira
aminiyarta ita ta kwantar mata da hankali tayiwa ummah din nasiha sosai ta
lurar da ita abinda ta kasa hangowa a tunanenta.

   Hakan yasa ummah ta
kwantar da hankalinta taci gaba da al,amuranta kamar komai baya damun ta a rai
da safe ina dakina ina shirin fita makaranta sai gata ta shigo dakin nawa.

   Nayi mamakin hakan
sosai saidai a fuskanta na fahinci akwai maganan da take son muyi da ita
lokacin don haka na bar abinda nakeyi na dawo kusa da ita na tsuguna.

   Naji tace dani
bayan na gaisheta maamah mahaifin ku yace in fada maki ki turo wanan yaton
yanzo ya ganshi kafin ya koma  .

   Kallon mamaki
nayiwa mahaifiyar tawa don ban fahinci wani yaro take zance ba lokacin sai naji
tace wanan yaron da dai kina nacewa tunda an rabaku kin ki rabuwa dashi.

    Ummah wake nan
kike nufi wai Ahmed ko wa ni yaushe rabon dana ga Ahmed a idona mutumin da
yanzu bai ma garin nan sosai yana karatu a zaria tun bayan gama school din mu
marabina dashi haka.

   Kada kimun karya
maamah don Alh yace ko kwanakin baya an fada mashi anganku a wani layi dashi
kuna magana don haka yanzun dai yace ki turoshi yana son ganin shi.

    Kasa na zube na
fara rantsuwa ga ummah ta daka min tsawa tana fadin kimun shiru ki saurareni
kiji mezan fada maki.

  Ko kusa bana son
inga kin nuna wani abu cikin zancen nan ki natsu kiyi yadda kikaga nayi din
idan anyi don aga bayan mu na roki Allah ya mayar muna da hakan alheri a
garemu.

   Nasan bana nufi dan
kowa da mugun nufi a zuciyata don haka Allah yasan dalilin haka garemu duk
abinda za,ayi ko Alh ko wani zaice dake kan haka  kiyi hakkuri ki shanye hakan a zuciyar ki.

   Nasan anyi hakane
don an dade ana neman hanyar da za a tozartani cikin garin nan Allah bai basu
dama  yin hakan gareni ba sai yanzu suka
biyo gareki suga sun tozartani nidake.

  Don haka duk ritsi
da wuya kada ki yarda ki nuna hakan ya bata maki rai ni zan biki da addua ako
yaushe Allah ya bashi yaton ikon rikeki amana ya hore masa abinda zai kula dake
a rayuwa.

    Kuka sosai na
fashe dashi don hawayen da naga ummah din nayi a lokacin da take wanan maganan
gareni ta mike kawai ta fita har takai kofa ta juyo tana fadin kada ki manta da
kiran nasa na fada maki.

  Komawa nayi na zauna
na bude babin kuka mai tsuma zuciya ta yaya haka har ya faru har Abba ya yadda
da sherin da ake bina dashi a yanzu kala kala komai a fada masa cewa nayi kuma
ya dauka haka din ne.

    Wayana ya dauki
kara na duba hannatu ce nasan bataga na shigo school bane zata tambayeni ko
lafiya bata ganni ba.

   Ban dauki wayan ba
har ya katse ba a jima ba ta sake kirana naki dagawa don banda courage din
daukan waya sam a lokacin yadda nake jin kaina kamar bani bace.

   Layin ummah ta kira
don tayi serving a wayanta takan kirata su gaisa tana tambayan ummah din ko
lafiya bata ganni ba kuma ta kira ban dauki waya ba ?

   Ummah din tace da
ita bana jin dadine yau tayi Allah ya sauwaka ta kashe wayan shine ummah din ta
shigo dakin ta sameni tana fadin hannatu ta bugo dazun.

   Ganin yadda na koma
yasaka ummah din tsayawa tayi min fada sosai ta kara da fadin hakan dana fara
nunawa zaisa suji dadi sugane abinda suke nema garemu ya fara samuwa a garesu.

   Ko shi Ahmed din
yaji ina bore a kanshi ya dauka ko bansonshi ne sai lokacin na dago kai na
kalli ummah dakyar na bude bakina nace ummah ba soyyaya a tsakanina dashi sai
mutunci.

   Da sannu zaku saba
na kalleta ina mamakin saukin kai irin nata haka tace eh idan makiyin ka yana
jifan ka da sheri nuna masa baka damu da hakan ba sai abin ya koma ma taki
karshe suji kunyan hakan.

   Kedai abinda nake
so daje har in Allah yayi shine mijin naki son Allah maamah ki zauna dakin ki
lafiya kiyi biyayya ga mijin ki ba wanda yasan abinda gobe zai haifa ga bawa.

    Lokacin dana auri
mahaifin ku kusan hakane baida komai banda takardun shi sai lokacin da akaga ya
fara samu ya samu wanan aikin lokacin ne dangi sukai ta kawo mashi yayan su ya
aura.

   Sai ita mamaku
dayake itace uwar yayan nasa duk da a lokacin kowa yasan tayi girma a cikin mu
amma haka akayi aurensu har take yadda taga dama yanzu a gidan nan.

   Don haka ki natsu
ki bi mijin ki ku zauna lafiya kada naji wani abu ya fito daga bangarenki nima
yin auren naki a yanzu shine saukina don hankalina zaifi kwanciya da hakan.

  In sunga su  kai inda suke tsamanin zaki cutu nasan zasu
fita zancen ki kuma su kama wani don dama abinda ake so ke nan a gareki aga
rayuwan mu a lalace kawai ba karuwa.

   Niko na yarda da
arziki na Allahne shike ba wanda yaso a lokacin da yaga daman hakan ga bawansa
don haka ki dauka dama wanan na cikin kadaran ki.

    Nayi kuka kamar
raina zai fita bayan fitan ummah dakin gashi ta kara fada min lalai in kira
Ahmed din in fada mai sakon Abba yazo don an kasa kunnuwa aji kome zai faru.

   Idan kuma ban kira
ba din za a iya cewa shima Ahmed din ya gama danine ya gujeni kai jama,a uwa
mai kishiya ko yarta bata huta ba wani lokacin.

    Don haka fitanta
dakin na dan wani lokaci na lalubo wayana ina neman layin Ahmed djn zuciya cike
da zargin abinda zan fada mashi din ko yaya shima a bangareshi zai dauki
maganan nawa don nasan baida zarahin aure haka gagauce gaskiya.

   Kira daya biyu gana
uku ya daga yana dan zolayana ta fadin yan makaranta ba lectura ne a ajin kika
samu lokacin kirana yanzu ?

    Ahmed kazo inji
Abban mu yana son ganin ka yau din nan da yamma ina ji yai wani kara yana fadin
what ni Abba keson gani kuma zahra mekikayi ko ince me akace mashi kuma munyi.

    Da kyat na iya
tattaro karfin hali na bude baki ina fadin saidai kazo din kaji don nima dai
bansani ba dazun maganan yazo min haka .

  Innalillahi naji ya
ambata tare da fadin Allah yasa dai ba wani kake bane kuma akai muna a wurin
shi yake son daukan mataki a kan mu saidai idan kazo din na fada na kashe
wayan.

    Kai ya dafe lokaci
guda don dama a tsaye yake suna lissafi na kirashi lafiya wanda yake tare dashi
ke tambayan shi yake fadin bari wani zance naji daya tayar min da hankali .

   Allah yasa alherine
yace amin amma gaskiya da wuya hakan ya kasance sai dai addua kawai sukaci gaba
da lissafin da suke saidai shi zuciyan shi cike yake da maganganu lokacin.

     Don har in ba
matsala bace me zaisa Alh yace yana nemansa kuma a yadda yaji muryana yasan ba
lafiya don ya fahinci nayi kuka sosai a lokacin har muryana ya dakushe alaman
kuka.

    A gagauce ya gama
komai ya nufo gida ba abinda yake tunane sai zancen su da su Dije da mahaifiyar
shi lokacin gaban shi yaji yana faduwa.

   Yana anyana wanan
karon zai iya kyale Abba ya sake ci masa fuska irin wancan karon nasa dashi kuwa
kada kuma yasa ai masa wullakanci jami,an tsaro su kamashi kamar yadda Alh ya
fada a baya.

  Shi yaba  akanshi amsa akan me yarsa ce yace in rabu da
ita na barta sai dan zumuncin da mukeyi yanzu sama sama dashi kawai.

   Ya goge yan
kaya  da zai saka wasu yadi farare an
mashi dinkin daidai gwiwa ya saka hula a saman kanshi ya tunkari gidan namu.

    Yayi sa,a Abban
baida wasu mutane sosai don haka bai dade ba ya samu ganawa da Abba din daya
dade tsungune bai juyo gareshi ba har tsawon wani lokaci.

  Sai can ya dago yana
fadin kaine kwanaki nanemi kazo gidan nan akan zancen zahra ko Ahmed din ya
gyara yana fadin nine Abba OK Abba din ya fada kafin yace wani mataki kake
dashi ga karatu ?

   Ya dan kara dukawa
a ladabce yake fadin yanzu na jona A,B,U zaria ne ina hada masters dina kan
kimiya sai Abba din yai mashi wani kallo kafin yace.

   Hakan na da kyau
Allah taimaka saidai ina fatan kana da inda zaka aje ta a yanzu don zan hada
bukin kune dana yan uwanta taje can gurin ka ta hada karatun ta a can din.

    Wani irjn zufane
ya karyowa Ahmed din don ba hakan ya zaci ji daga bakin Abban ba lokacin sai da
yayi ta maza ya iya ffadin eh to ba za a rasa ba daidai iya karfina Abba.

   Koma meye wanan
matsalan kace daga baya yanzu ina son ka turo min magabatan ka in gana dasu zan
fada masu lokaci idan sunzo daga haka Abba ya mike ya barshi nan sai dai muryan
shi da Abban yaji cikin dan sanya yana fadin.

   Abba nahode Allah
ya kara girma da daukaka bai jiyo ba don haka baisan ko ya amsa mashi ba
lokacin yasa kai ya shige ciki shi kuma ya tashi ya fita gwiwa a sanyaye.

    Yana fita yaji
kamar jiri zai daukeshi saida ya dafa bango ya saka takalmin shi a kafanshi ya
nufi hanyar fita get din yana ji kamar mafalkin komai yakeyi ba da gaske bane
lokacin.

   Gida ya nufa kai
tsaya saidai bai iya shiga gidan nasu ba nan ya tsaya a kofan gidan yana faman
tunanen ta inda zai farawa zancen ke nan ?

    Yana zaune saman
mashin dinshi wayanshi ya dauko daga cikin aljihun shi ya fara neman layin
zahra don yaji meke faruwa daga bakinta har hakan ya faru ?

    Ya kira har kiran
ya kusa katsewa kafin na daga har lokacin muryana a dakushe yake bai fita sosai
Zahra meya farune naje wurin Abba naji zancen da ban taba zato ba daga bakin
shi yau.

    Nima yadda kaji
haka naji yau din nan nan na kwashe yadda mukayi da umma na fada mashi amma ba
duka ba naji ya nisa yana fadin ikon Allah yafi gaban mamaki.

    Zahra bansan me
zance dake a rayuwana ba sai dai godiya da addunan fatan zaman lafiya mai
daurowa a tsakanjn mu nida ke.

   Zan kiraki an soma
kiran sallah yanzu zan kiraki zuwa anjima mu karasa maganan mu insha Allahu
nagode kwarai ya fada ya kashe wayan.

 

 

Leave a Reply

Back to top button