TUMFAFIYA 57
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[4/22, 11:47 AM] +234 908 769 2191: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH
,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
5️⃣7️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,
Barkan da wanan lokacin yan uwa musulmai ubangiji Allah ya
karba muna ibadun mu Amin Allah ya bamu ikon jajircewa a wanan watan mu samu
falalan dake cikin sa Allahuma Amin.
Duhune ya mamaye
dakin baka ganin komai a lokacin sai
duhu a hankali ya dago santala talan hanayen shi ya kaisu ga makunin wutan gefen gadon dake dakin
ya kuna.
Hjy Yabice a
gefensa kwance tana kwasab barcin ta a lokacin dan hasken daya kunna bai hanata
barcinta ba a lokacin don asalima ita bata san ya kunna wanan wutan ba a
lokacin.
Bin dakin nasa
yakeyi da kallo zakace bakoneshi a dakin ranan ya fara ganin dakin nasa don
yadda yake bin ko ina na dakin da kallo lokaci guda.
Hankalinshi ne ya
karkata zuwa mafalkin daya tasheshi a lokacin tabbas yasan a yan kwanakin nan
mafalkin wanan matashin na yawan damun shi a cikin barcin shi.
Saidai ya kasa
tuno inda yasan fuskan yaron mai zubi daya da nasu don yasan ba danshi yasir
yake gani a mafalkin nasa ba son wanan yafi yasir din shi tsayi da haske da
mugun kama dashi wurin kamanni .
Mikewa yayi zuwa
bandaki ya dauro alwala yana kokarin tayarda sallah lokacin ne matar nasa ta
dan falka ta sauke kallonta gareshi .
Idan ba gizau idon
take mataba sallah yake kokarin yi a lokacin duk da mamakin sabbin halaiyan shi
a yanzu nauyin barcin dake idon ta bai barta taci gaba da cigaba da mamakin
nashi ba.
Kamar yadda shima a
yanzun yake mamakin kansancewarta matarshi don gani yake komai ya faru dashine
a cikin rashin sani ko a malfaki.
Iya abinda zai iya
tunowa a baya shine irin tsana da tsangwaman da bangarenta suka nuna mashi a
baya kasancewan shi da daya tillo daya fito a wurin mahaifiyar shi kafinta bar
duniya.
Da yadda ya taso a
cikin shi suna nuna mai hasada da bakin ciki irin na yan uba a lokacin wanda
badon shi din ya iya kanshi ba da ba yadda zai taso a gaban ita uwar rikon yabi
din wace kishiyar uwane a gareshi lokacin kuma mahaifin shi ya hana bangaren
uwan shi dasu daukeshi.
Yabi yar kanwar
Attuce data rasu tabarta tana karama a cikin yan uwanta su hudu duk Attu din ta
kwasosu ta rikesu lokacin a hannun ta tana tayar dasu a cikin gidan mahaifin
nasu.
Kasancewanta ita din
matar basarkene a lokacin kuma mai abin hannun shi don yana da dukiyanshi da
abin hannunshi sosai don haka abinci bai masu wuya koya katse masu a gidan yasa
ta dauko yaran ta hada da nata ta rike
Akan yaran tana iya
sabawa da kowa a gidan a wanan lokacin don yadda ta daukesu a ranta amma diyan
mijinta kiri kiri take nuna masu kiyayyanta a fili.
Kowa yayi mamakin
batan habu dan gaske da suke mai lakani da hakan don kasancewan shi da daya
dasha wuyan kishiyoyin uwarshi kuma yana raye a cikin su ya tashi hakana.
Lokacin daya fara
bude ido da kasuwanci mahaifin nasa ya dauki wani kason daya gada a wurin
mahaifiyarshi sai wanan matar abin yai mata bakin ciki sosai a zuciyar ta .
Duk da mijin nasu ya
fahintar da ita cewa kason shine na mahaifiyar shi ya fara juyawa amma sai bata
yarda da hakan ba tayi ta kokarin ganin ta hada kai da sauran iyalan gidan aiwa
mijin nasu banga kan hakan sai sauran basu mai da kai ga hakan ba.
Wanan yasa taje
wani dutse wurin wani boka yai mata aiki suka turashi uwar duniya daga tafiya
ba a kara jin duriyan shi ba kuma har tsawon wani lokaci.
Fahintar hakan da
amin nasa sukayi sune suka shiga suka fita sukai masa aikin dayafi nata har
Allah ya dawo masu dashi gida kwatsam aka ganshi ya dawo a jirgice babu wani
abinda ya dawo dashi lokacin.
A binciken
mahaifinsa ne ya gano cewa yayi aure acan inda yake harda karuwa amma ba hausa
ya aura wanda su kuma basu son hada jinin su da hausa don sunyi yakinin cewa
hausawa ba abin yarda bane.
Wanan yana cikin
shawaran tsohuwa mallam a lokacin ita ta shiga ta fita data gano cewa dole fa
sai tabi ta wani hanya sanan bukatanta akan habu din zai biya.
Don hakane ta dauki
yarta datake gabanta a lokacin ta mika masa da sunan irin hadin su na fulani
wanda mutane da yawa a lokacin basu so hakan ba.
Saidai zaman ta mai
fada aji a gidan yasa kowa yaja bakin shi yai shiru ya zura ido suga manufanta
duk da sun san me hakan da tayi ke nufi amma babu halin magana akai.
Shima din uban
gayyan bai cikin hankalinshi don gaba daya juyashi akeyi akan komai har zuwa
lokacin nan da abu ke shirin faruwa dashi din.
Sallah ya tayar don
neman sauki a wurin ubangiji bai daga ba har dan gyangyadi ya fara daukan shi
wurin kuma anan ya sakeafalkin daya daga mashi hankali sosai.
Ina zaune muna fuskantar
juna da ita mamakine a fuskanta karara wanda take mamakin abinda nake fada mata
din a lokacin kafin ta nisa tana fadin.
Ni abinda nagani
shine kifita zancen kowa zahra ki kama mijin ki tunda bashi ke maki hakan ba
kuma shi har yana nuna rashin son hakan a fili kanki.
Don me zan fita
zancen hakan yanzu ina yake ina tare dasu ya tafi ya barni a nan zaune kinga ke
nan ya zama dole in gyara zama tsakanina dasu tako wani hanya.
Kaita girgiza tana
fadin Zahra ke nan ki rabu da irin matan nan masu kishi da matan diyan su duk
abinda zakiyi ba zataga hakan ba don idonta ya rufe ga son danta a yanzu.
Tana ganin komai ya
samu akanki yake karewa duk abinda yake masu bata ganin hakan ita gani take
keyske kashewa ke kadai a yanzu.
Kada ki rage ki
kara ita irin matan nan ne masu adawa da hassada tana ganin kin fito gida akwai
kin fisu kina daga masu kai ko tana ganjn kedin baki cancanci hakan ba garesu ai.
Ta manta Allah ke
bayarwa a inda yaga dama shike zaba yaba wanda yaso a rayuwa har ma ke wani
hali itin na diyan masu kudi kike dashi zahra tunda abinki bai rufe maki ido ba
ga kowa.
Ita bata tunanen
arzikin kine master ya shafa har ya dago yakai haka a yanzu idan ita bata san
wanan ba kowa ya sani a gari don da yaya dan nata yake cikin garin nan yana
yawo a kafa a talauce zabar tausayi.
Murmushi nayi ina
fadin hannatu ke nan wanan kuma wani hukuncine na Allah ya nuna hakan amma ai
ban isa in masa arziki bani.
Nasan da hakan
amma mutane sun camfa hakan kuma hakan maganan yake don ko last week saida su
munir sukai zancen ku irin wanan .
Don haka ni in nice
wallahi zan bita a yadda take son mu zauna don nasan ba zata iya sa master ya
sakeki ba saidai abinda ya fito daga Allah.
Hannatu bawai akan
hakane na nemi shawaran kiba a yanzu na nemi sharankine naji hanyar da zan fito
mata mu zauna lafiya shine dalilin dana nemeki shawara yanzu .
Akan hali irin
nakiba zahra na sanyin hali amma inda nice wallahi daidai zamuyi da wanan matar
amma tunda kince haka yanzu ai shikenan .
Shawaran da zan baki
shine ki kara harkuri ki bita da halinta sai kuma yaran nan kiyi kokarin jansu
a jiki kina masu dan alheri kinga insunga hakan ba zasu biye mata wurin
shirmenta ba.
A karshe kuma kila
ita din ayi sa,a ta sauko don ance idan kana son kama uwa kaso danta fiye da
ita zaka kama zuciyarta a dan kankanin lokaci.
Shiru nayi ina
nazarin zancen ta wanda ba komai nake tunane ba a hakan ta ina zan farane yanzu
don iya bi da kyautatawa ai naga ina masu amma duk bata ganin hakan ita.
Kamar tasan me nake
tunane sai naji tace irin kayan ki dake aje baki amfani dasu din nan ki dan
rika basu shi idan sunyi kwaliya da bai maki ba kikirasu ki gyara masu da hakan
har dai ki jawosu zuwa jikin ki kubarta can tana haukan ta ita.
Wallahi wanan
shawaran yayi kamar kin shiga zuciyana dama kingani hannatu don ina son masu
hakan ina tsoron matan nan don sam bata boye kiyayyarta gareni kada tace nabawa
diyan ta kwance sha tusa don naji ranan tana zagin kanwarta da hakan data aiko
mata da wasu kayan jikinta.
Haba dai zahra wasu
kayan ba amma ba dai irin nakiba da wasu sakawa daya ko biyu kikai masu a jikin
ki ina za,a hada da wanan da nasu kilama yasha wanki ashirin albarkahakan
Kai kajiki da wani
zance yanzu dai zan gwada wanan shawara naki in gani idan anyi nasara zanfi
kowa farin ciki da hakan.
Don wallahi
hannatu wanan matar ta daga min hankali sosai niba auren da tace zataiwa master
bane yadameni kamar yadda take fita tana aibantani wurin mutanen ta.
Kada hakan ya
dameki da baki da alhakinta ai gashi har dakin ki akazo aka fada maki komai
kunya kuma ya rage a gareta ranan da zata gane gaskiyan hakan.
To amin na bata
amsa ina mikewa na fita na debo mata abincin dana girka don zuwanta don nasan
halinta bata wasa da cikinta.
Na samu takai
kwance lokacin tana duban wayanta dake hannunta na dire abincin a gabanta
kamshin yasata dagowa tana fadin kai don haka nake sonki mutumiyar.
Kamar kinsan
wallahi a matse nake nan ina shirin tambayan ki ko akwai abin tabawa na taba
sai gashi kin kawo min tana mikewa zaune take fadin haka .
Fita nayi na dauko
muna drinks da cups na kawo muna na zauna muna ci a lokacin ne Aisha ta leko
part din tana fadin .
Matar yaya kina
cikine kin kwanta tana lekowa ta ganmu zaune a falo muna cin abinci hannun ta
rugume da kayanta sai kuma ta dan dare daga kofa tana fadin ashe kina da
bakuwane.
Ina wuni hannuta ta
amsa mata ba wani sakewa nayi saurin kawar da hakan da fadin ashe baku tafi ba
aina dauka kun fita tun dazunne wallahi naji gidan shiru.
Muna nan wallahi innace
dai tun safe take can yanzun ma Asma,u ta dawo take fadin wai inna tace maza mu
shirya mu zo za,a fara Dj .
Dj kuma hannatu ta
fadi hakan cikin mamaki koni naji wani iri yadda tai maganan nayi saurin fadin
ba bukin gidan su akeyi ba keko taso ace nata sunje mana koni don Master baya
garine aida tare zamu dasu.
Nace don Allah ko
iron dinki na kusa in dan goge tufafina kafin nepa su dauke wuta nace eh yana
nan dama ke baki gogeba tun jiya bayan kinsan yau akwai buki ?
Nifa ba wani damuwa
da wanan bukin nayi ba dama mutanen da sukewa mutane kallon banza balle kaje
sha,aninsu yaya ke nan kuma idan mun kai kanmu cikinsu.
Haba dai keko har
zaki yarda su raina maki ai shiga ta kamala zaki dinga yi idan zaki shiga wurin
wanda kikasan akwai makiyan ki.
Murmushi tayi tana
fadin inna dai tayi ita don ta saje dasu amma mukan ai wanda suka san mu dashi
zamu sa mu fito kinga kuwa dole su raina muna wayau.
Ina zuwa na fada na
shiga daki na barsu a nan ina ciki naji
muryan Asma,u tana fadin kizo muci abincin mama Aisha.
Ke haba mana keba
kanwarta bace daba zaki kirata da Anty ba ko yaya ai an daina irin haka ku kuwa
sai a daukeki bakauya ko wata bagidajiya can.
Baki yarinyar ta
turo tana shirin mata rashin kunya lokacin na fito daga dakin da kaya a hannuna
naganta a tsaye daga kofa.
A,a Asmau kema
baki tafi bane eh ban tafi dazun dai na leka da Dije ta aikeni shine inna ta
bani abincin in kawo muci kuma abincin ba yawa dan kadan ne tazo muci yunwa
nake ji sosai tana ja min rai.
A,a baga abinci a
nan ba ku diba na dauka aikun tafine ba kowa a gidan shiga kitchen ki dibi mai
isan ku kuci tayi dan jim kamar tana tunane sai kuma ta juya ta tafi .
A nan na zube kayan
dana dauko ina fadin Aisha ki duba wanda zai maki a cikin wanan sai kiba Asmau
sauran kala bibiyu ne na zabo masu lokaci guda.
Don ina da kaya
birjit a dakin daba amfani nake dasu ba yanzu a cikine na debo masu wa yan nan
din yanzu.
Da sauri ta washe
baki tana fadin wai da gaske matar yaya nace da gaske mana gwada ki gani ko
zasuyi maki idan kun dawo saiki goge wanan din kada inna tayi fushi dake bakuzo
wurin sha,anin da wuri ba.
Takai hannunta
saman kayan ta fara dubawa tana nuna farin cikin ta a fili tare da fadin ke
Asmau taho kigani an bamu kayan da zamu saka mu fita.
Saiga Asmau ta bude
labulen kofa tana fadin kizo kiga abincin ko zai muna nikan bancin wancan da
anka bamu don wanga mai dadine sosai harda ganyen salad cikinai hwa.
Sai idon ta ya
sauka akan kayan da yar uwan nata take duba tace kayan waye taho nice kigani
matar yayane tabamu su mu saka.
Da sauri ta sake
labulen ta shigo tana fadin mu ankabasu walle har naji dadi kasan raina muma
zamu hito kamar kowa a bukin nan ashe ?
Ai dama daidai da
kowa kuke idan kuna gyara Zahra kan bata da matsala in kuna hurda da ita fiye
da hakan ma sai ku samu a wurin ta don wanan ba komai bane wurin zahra kowa
yasani .
Ai walle innata
taka hanamu hurda da ita dama wai sai ta mayar damu bayinta Asmau ta fada tana
bude kayan kafinta washe baki tana fadin wayyo ji irin dinkinga da nai maitanai
a baya don Allah.
Ke walle nika
daukane bake ba wanga ina zai maki adaidai lokacin naji hanne tace bayi kuma
don kana shiri da matan yayan ka shine wani abu kuma ?
Ai shina gani daka
zowa muna dan hira halan ta mayar dani boyantana to nidai haka niji inna tana
hwadi ko wani lokaci.
Yanzun dai ku
shirya nayi maku kwalliya sai ku tafi hannatu ta fada sai sunci abinci aiko na
fada daga inda na zauna.
Abinci walle saina
dawo nikan saina dawo nikacinai kedai aje muna har mu dawo daga wurin bukin
Aisha ta fada a cikin zumudi sai hannatu tace ai gara kuci kada kuje can baku
samu wani abincin ba.
Hakan tayi masu
kwalliyan tana jansu da hira nima ina dan saka baki wanda na kula da hakan yasa
sun dan sake jiki sosai a wanan ranan dani har muna wasa da dari a fiye da
kullun a cikin wata takwas din da nayi a gidan tare dasu.
Wanda hakan ba
karamin dadi nima naji ba don har akalma da jakka da gyale suka saka mukai masu
rakiya hannatu nata zugasu Dijema saida ta fito don jin yawan hayaniyar mu da
takeyi daga sashen su.
Bayan tafiyan sune
Hannatu ta gama yiwa Dije dan bayanin karya tana fadin ai kaka yan mata yanzu
saida sa,oin su a gida suke gyaruwa amma a zauna ga zahra tare dasu muma na
nisa muna cin muriyanta balle wa yanan dake zaman kannenta ai zaman lafiya yafi
komai a rayuwa.
To shina gani yar
nan uwarsu taki gane hakan gashi yau yar nan da take rainawa itace tayi tsaye
ta gyara mata diya haka tsab zasu shiga tsaran su don wanan sha,anin ba lamarin
wasa bane don kowa na wurin a cikin danginsu kinga ko aga naka cikin shiga ta
alfarma ai abin a yabane hakan.
Tagama zuban ta ta
dawo ta sameni ina gyaran part din ta kalleni tace to uwar tsabta koda zaki
hakan ki dinga bari dai sai sun tafi don idan kina nuna wanan shagen tsabatan
naki a gaban su haka zasu dauka kina kyaman tararyanki dasune.
Banyi magana ba
don nasan gaskiya ta fada min saidai ba zan iya ganin wuri haka komai a yamutse ba dole sai na gyara
zanji dadi amma dai zan kiyayye din gaba.
Mun dan taba hira
ta wuce ina mata godiya na rakata zuwa waje a nan mukaga yadda jama,a suka cika
unguwar don halartan wanan bukin mukai sallama ta tafi na dawo ciki nayi sallah
na fito wurin Dije na zauna muna hira.
A nan ta jefo min
tambaya da fadin yaushene mijin ki zai dawo daga tafiyan shi dan murmushi nayi
kafin nace ina ganin sai karshe wani mako kamar yadda yace.
Saidai zuciya yana
ban kamar zai dawo kafin lokacin yadda nake gani yar nan har ganin dawowan
mijin naki kikeyi a yanzu sai nayi murmushi ina dan kame kame tare da fadin .
A,ahaa kawai dai ina
jin cewa zai dawo a yan kwanakin nan ne don haka jikina ke bani ta kara
tuntsurewa da dariya irin na tsofi lokaci guda.
Shigowan wasu mata
wurinta ya dakatar muna da maganan suka tsaya gausawa da ita saidai ina zaune
wurin har lokacin da suka fita bayan sun dan taba hira.
Fitan su take fada
min irin alakansu dasu akwai zumuci sosai a rsakani su na iyayye wanda a yanzu mutane basu daukan
hakan da muhinmanci sosai shi tallaka yana gudun wulakancin da uwa mai kudi don
wullakanci.
Haka dan uwa mai
kudi kuma yana gudun mamuwan dan uwa tallaka don bani bani don wasun su haka
suke zubar da kiman su da roko a yadda Dijen ke min bayani kuma hakan gaskiyane
a yanzu.
Muka dauko hiran
zaman mu da uwar mijina tana kara ban hakkuri kan halayen da take nuna min na
dai nuna mata ai uwace a gareni don haka ba komai.
Muna wurin misalin
karfe biyar na yamma kawai Ahmed ya fado muna gidan kwatsam muka ganshi kamar
an jefoshi a lokacin.
Daga inda nake
zaune ina hango bacin rai a fuskan shi ganin part din mu a rufe don ya dauka na
tafi wurin bukin nasu daya hanani zuwa kenan tunda ga part din namu a rufe don
yasan bana shiga cikin gida in zauna haka.
Yana nufo part
dinsu Dije din yai arba damu zaune tare da Dije din saman tabarma ya dan saki
wani shu,umin murmushi a fuskan shi
lokaci guda.
Mukai mashi sannu
da zuwa a nan ya zauna na mike karbi dan jakar nasa da yake rataye a kafadan
shi na nufi part din mu dashi a nan naji Dije din na fadin.
Allah ya horema mata
mai halin kirki yarinyar akwaita da dattako da sanin yakama ka kara rike yar
nan da hannu bibiyu don ba inda ta kasa da kai haka
Yayi murmushi tare
da fadin kai Dije ai nima ina da wanan halin irin nata kaidin shu,umine wani
lokaci don wanda baisan kaba ya hauka katkace sai ya zame.