Hausa NovelsTUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 8

Sponsored Links

 

 

1️8️⃣

AL AZIZ,,,,,,,,,,

 

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI K

ARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

 

 

   Allah ya taimakeni
ba a wani taru sosai ba a makaranta amma haka nake ganin kamar idon kowa na
kaina lokacin suna kallona haka na fito na rufo motana a hankali na tako yadda
na saba tafiya a nutse zuwa department din mu.

    Akwai mutane
saidai ba sosai ba don safiyane sosai lokacin kamar yadda na saba shiga da
siriryar sallama haka na shigo na dan gaisa da na kusa da ida na zauna daga
haka na zaro takarduna na fara karatu.

    Can na tuno da
lecture din da ban samu attendedi ba jiyan da rana lokacin da abin ya sameni
don dolene na koma gida saboda bana cikin hayacina lokacin.

    Dago kai nayi na
kalli ta gefena ina fadin don Allah yar uwa jiya an dauki attendaces ne na rana
wani iri tayi far da idanu tana fadin ke baki ajine lokacin da aka dauka din.

  Kaina girgiza tare
da fadin banda lafiya na tafi gida ban samu daukan darasin rana ba jiya din
kaita jijiga min tana fadin jandi kina da aiki ga wanan malamin da baijin Allah
tana fadan haka ta juya ta barni cikin damuwa.

   Har muka fito daga
lectures din ina tunanen rashin yin attendance da ban samu yiba don nasan halin
lectural din da zafin kai sosai da a hankalina nake ba abinda zaisa na yarda
naje gida a lokacin.

    Tun daga nisa na
hango mutum yana bin motan da kallon mamaki saidai baiyi kama da dan makaranta
ba shi don kayan jikinshi da suke kode duba ga yadda yan makaranta ke shigowa
cikin kure adaka ko wani lokaci ba mazanba ba mata ba.

    A hankali nake
takowa cikin mamakin me yake nema a wurin motan daga bayan shi na tsaya ina mai
sallama ya juyo yana amsa min tare da fadin ashe kin samu shigowa yau din ?

   To yaya jikin naki
banda waya naso na karbi layin mahaifiyar ki naji yadda kika kara ji sai rashin
waya ya hana hakan saidai ki kula tunda kina da lalura koda kinji wani abu zaki
iya nemana ina Science department UG four.

   Sake kallon shi
nayi ina mamaki a raina dan makarantane wai wanan din dama ashe ga yadda yake
nunawa shine wanda ya kaini gida jiya ke nan nan na fara kokarin tuno da abinda
ya faru jiya din tabas shine wanda ya tsaya ya kare min mutuncina a jiyan don
ummah ta danyi min bayani kamar yadda yai mata shima.

  Saida na nunashi da
yatsa nace Kaine kaine dama ka taimaka min jiya nagode gida zaki tafine ya fada
yana kawar da fuska gefe daya kamar baison kallona.

   No mosque zan tafi
nayi sallah daga nan saina tafi wurin malamin mu ya shigo jiya bana nan ya
dauki attendance kuma baida sauki mutumin.

    Wani department
kike ya tambaya wanan karon yana kallona apply chemistry nake karantawa na
bashi amsa kai tsaye.

    Ok department din
mu daya ke nan dake idan kina da matsala zaki iya nemana duk da ba wani sani
nayi sosai ba kan haka.

   Ki dai kula da
addua kafin ki fito gida da kuma lokacin da zaki shiga school din don yanzu
mutane sun baci sosai.

  Saboda haka don
Allah idan kinji alama ciwo zai taso ki samu wuri ki dinga natsuwa don jiya
badon Allah ya gyara ba zaki iya halaka kanki a motan nan.

   Don a yanzu taimako
yayi karanci sai gulma dasa ido ga al,umma ana yadawa a duniya don mutane yanzu
suna tsoron taimako saboda shiga fitinan jami,an tsaro. 

   Ki kula sosai
saboda kasancewar ki mace don mutane basu da gaskiya yanzu yana kaiwa nan ya
dago yace na barki lafiya dama motan nan da na gani nayi mamakin ganin kin
shigo kuma school yau duba ga yadda na kaiki gida jiya a wani yanayi can.

    Duk wanan bayanin
da yakeyi sai kallon fuskanshi nakeyi ina son intuna inda nasan fuskan nasa
saidai na kasa tuna hakan saida ya juya zai tafine na tuno ai shine wanan guy
din na shagon abinci dana ga anaciwa mutunci har naji haushi matar a raina na
taimakeshi.

    Kayan jikinshi na
kalla duk sun kode saboda tsufa ga takalman kafan shi duk sun kode sunyi wani
baki dasu da ganin shi  zagaka gane shi
din fakirine na gaske tun daga duba ga yanayin shi kuma a haka yake rayuwa
cikin diyan mayan da masu hali bai damu ba.

   Wani irin tausayin
shi naji ya shigeni lokaci guda sai naji matukar sanyin jiki gashi dai da halin
kirki irin wanda ake son samun dan musulmi dashi .

    Amma rashin gata
yasa ya koma kamar mahaukaci a ciki
mutane har wasu na tafiya suna kallo inda muke ganin na tsaya dashi ina
magana ashe sam baya shiga harkan kowane a makarantar.

 Shine da aka ganmu
tare suke mamakin hakan don bai kula kowa shi kadai yake rayuwan shi gashi dai
kamar shiya halittawa kanshi kwakwalwan shi don hakane malamai suke ji dashi
sosai.

   Naje sallah na dade
a masallacin zaune kafin na kalli lokaci na fito saidai na kasa zuwa kai
korafina wurin wanan malamin don ko naje ance baya duban mutane.

   Don hakane na ba
kaina shawaran na kyaleshi kawai zaifi min rufin asiri danaje ya tozartani don
mutum ne shi mai ji da kanshi da zamani yana amfani da daman da Allah ya bashi
yana wullakanta mutane ta hakan.

    Ummah tayi kokarin
buyewa kowa halinda yarta ke ciki a lokacin ba don komai sai don rsshin yarda
da kowa a yanzu tunda ba yan uwane gareta ba a nan sai abokan arziki da dangin
miji.

    Suma din kuma
wasune suke hurdan arziki da ita don sunfi bada karfi a bangaren mama dama haka
yake a al,adan yanzu duk inda miji yafi karfi can mutane ke dosa don neman abin
duniya da gulma.

   Ko wanan maganin da
Tani ta karbo mata saita koma tana tsoron amfani dashi don yanzu mutum ba abin
saurin yarda bane tsakaninka dashi haka kai tsaye.

    Wanan yasa take wasi wasin ko ta mayarwa
Tani din da kayantane ta fallafawa ubangiji lamarin su don Allah shine mai yin
yadda yaso da bawansa haka kuma bawa baya kaucewa kaddaransa tun rangini ranan
zane.

    To amma kuma zaman
ta da Tani na amana ne don hjy tasha kullace tani din yadda tani tabata gaskiya
da amana duk yadda hjy taso taja ra,ayinta.

   Amma Tani din taki
yarda da hakan har saida hjy ta kulafuci tani din taso ta tasa a kori tani din
daga gidan saida ummah ta fahinci me mama ke nufi ta nuna jajircewan ta kan
hakan.

   Tun lokacin sai
gaisuwane da sannu ke hadasu da hjy ddin tana taka tsatsan da lamarin mama din
a gidan harta shigo ta fita da yamma tana part din ummah zaune.

   Wanan gaskiyan da
amana na Tani din yasa ummah kara yarda da lamarinta da har yanzun din ma
hankalin ummah din ya kwanta da maganin data kawo wanda ita tsakani da Allah ta
amsawa ummah din shi.

    Dauka tayi ta kara
dubawa kafin ta mike ta fito zuwa kitchen dashi a hannun ta  Tani din tana tsame shikafan data wanke a ruwa
taji shigowan ummah din yasata juyowa lokaci guda.

   Ummah ce kofa rike
da ledan maganin data kawo mata a hannun ta idon tani ya sauka kan ledan
gabantane ya fadi take fadin  hjy lafiya
dai ko ?

    Lafiya Tani ummah
ta dan sake murmushi tana takowa cikin kitchen din tana fadin kinga Tani ba zan
boye maki ba da farko ban dauki wana
maganin da kika kawo min dazun ba.

   Amma yanzun nayi
tunane na aminta dake Tani duba da yadda mukai sabo da amana kuma a tsakanin mu
dake nasan kinyi wanan ne da niyar taimakona nida diyana.

   Don sanin halin
rayuwan da muke ciki a gidan nan daba kowa yasan da hakan ba sai yan tsiraru
suka sanda hakan a garemu.

   Allah sarki hjy
yadda kika rikeni nida diyana da yan uwana meye ba zan iya maki ba a rayuwa
wallahi Allah jiya na kwana da tunanen uwar dakina a raina don kiri kiri ake
son a illanta maki zurian ki nan a gidan nan.

   Wanan yasa nayi
asubancin zuwa gidan yaron nan na jiya da yai min kwatance shine nayi asubancin
zuwa unguwar na kuma gane gidan nasu.

   Saidai a lokacin
nayi rashin sa, a don shi ya fito zai tafi makaranta a lokacin shine ya hadani
da kakarshi ta kaini wurin wani dattiju a nan unguwar tasu.

    Ni kuma sai ban
boye mai komai na irin matsalan da kuke fuskanta a gidan nan shine yaba da
wanan yace a kawo maku kuyi amfani dashi mugu na fili dana boye saidai aniyar
shi ta koma mai .

   Watau aniya
makomiya ke nan yadaice kuyi amfani dashi kamar yadda yace ayi in sha Allah ya
wadatar daku saida hjy naga kamar baki yarda dani ba kan hakan ?

   Saidai banga laifin
hakan ba tunda ba da sanin ki najeni ba amma idan kina wani shakku ga hakan
kina iya sa uwar dakina ta binciko maki wanan wurin yaron jiya din tunda suna
ganin juna wata kila dashi din a makarantar su.

    Haba Tani ba
zancen rashin yarda bane ko wani abu yanzu tsakanin mu don mun zama daya daku
yanzu ai bake ba ko wani naki bazai cuta min ba a yanzu.

    Zuwa nayi ki kara
min bayanin yadda zamuyi amfani dasu don dazun sam ban fahinceki ba koda kike
min bayanin su a lolacin.

    Karban ledan tayi
ta warwale ta fara yiwa ummah bayanin yadda akace kafinta dago tana fadin
kaidai kada kaiwa wani sheri kadai tsare jikinka yadda ko yayi saidai ya koma
kan maishi don ansan asiri gaskiyace tunda yaci Annabawan Allah.

    Ina shigowa gidan
namu mamace naci karo da ita a waje da alama fita zatayi lokacin mota na fito
na rufe na nufi inda suke suna magana da driver gidan mu koshi zai kaita
unguwar ban sani ba lokacin.

  Fuskana dauke da
fara na nufi inda suke din saidai nayi mamakin ganin yadda mama din ta daure
min fuska tam babu ko yar fara,a a fuskanta gareni.

   Ganin hakan yasa na
rage nawa fara,an dake fuskana na karasa ina fadim mama lafiya dai ko ko fita
zakiyi ne na tambayeta lokacin ta juyo gareni tana fadin.

   Eh zan fitane har
kun dawo tana kokatin shiga mota na bita da kallon mamaki daga hakan bata kara
juyowa inda nake tsaye ba din sukaja mota suka tafi.

    Ajiyan zuciya na
sauke tare da juyawa zuwa cikin gidan namu zuciyana da tunanen wanan sauyin da
nake gani a gun mama din yanzu.

    Da sallama a
bakina na shiga part din mu saidai babu kowa a falon mu lokacin haka yasa na
wuce zuwa bedroom dina na fara kwabe kayan jikina.

    Sauyawa nayi zuwa
wani dogon riga kafin na sake fitowa zuwa dakin ummah don na gaida ita kuma
tasan na dawo a lokacin ban son ta shigo ta same ni a dakina.

    Zan shiga dakin ke
nan naji motsinta a falo na juya zuwa falon na sameta a nan ummah na kira sunan
ta tajuyo tana fadin ashe kin dawo ke nan to yaya kan naki bai tashi ba acan
yau ko ?

    A, a ummah saidai
nan gefe daya danaji ya daure min kamar zai fara min ciwo din lokacin saina
shaka wanan maganin na jiya a masalaci naji ya bari .

   Kikuma dinga yin
addua kina tofawa ai haka wanan yace min yau da muka hadu dashi a school yau
din ma kun hadu ke nan dashi ummah ta tambayeni ?

    Eh yazo wurin
motana yana duba da mamakin har naji sauki nafito yau makaranta shine yake
fadin na kula da jikina da kuma addua don ni mace ce daba don Allah ya kawoshi
jiya ba baisan yadda zamuyi ba a wurin.

   Gaskiya ya fada
addua ya dace bawa ya tsare a kullun don ita kariyace ga mumuni don haka ki
kara tsare addua sosai ya fada maki gaskiyan da nima iya nan zan iya fada maki
ai.

   Ummah wai meya samu
mamane naga zata fita ranta a bace ina gaida ita bata tsaya ta amsa min ba tana
dauke kai gareni kamar nayi mata wani laifi.

   Yanzun nan zata
fita da yamman nan haka ban jin nisa zata tafi don bata faye fita haka da yamma
ba saidai in wani wuri mai muhinmancin zata tafi hakan yanzu a wanan lokacin.

    Amma ai mama bata
daure min fuska haka irin yadda tamin yau din nan idan ta dawo anjima zan
sameta a part din ta ai na gani.. 

   Kice mata me idan
kinje ki barta kawai idan wanan zaikaiki wurinta  saidai idan wani abin zai kaiki gunta ban
hana ba amma kada ki mata zancen hakan koda wasa.

  Kaina gyada mata
alaman amsawa kafin na gyara zama ina tunanen abinda ummah ta fada daga haka
mikewa tayi zuwa dakin ta a lokacin kannena suka shigo sun dawo daga islamiya.

  Nan nake tar dasu
har akai kiran magariba muka watse zuwa sallah ban fito ba sai bayan salllah
isha,i da muka fito na samu ummah na waya da Abban mu lokacin naji tana fadin
da sauki sosai don yau din ma har taje schoon din ai kuma ba abinda ya faru.

   Banji meyace ba
tadai miko min wayan na karba a hannunta muryan Abbane ke kiran sunana na karba
mashi yake tambayana ya jiki ya karatu na amsa da naji sauki.

    Muka dan taba hira
yace in ba ummah din waya a lokacin na mike zuwa part din mama da naji
dawowanta ana bude mata get ina sallah isha,i a lokacin.

    Dukkan su basuyi
zaton shigowa na part din ba a wanan lokacin sai ganina kwatsam da sukayi na
shigo hakan yasa da sauri naga Aisha tana kokarin boye wani jarka karami dake
dauke da wani ruwan rubutu   a bayan .

  Nayi kamar banga
haka ba lokacin wurin mama na nufa a sake ina fadjn mama ashe kin dawa andawo
lafiya ya gajiya ta amsa a cikin dan darare da fadin lafiya tana kawar da kai
gareni.

  Nan ta barni zaune
tankar ba mama ba a ranan yadda ta nuna min din tankar bata san dani ba zaune a
wurin ta kama harkan gabanta ta fita batuna ga baki daya.

    Saida na gaji da
zama na mike nake fadin mama zan tafi dama na shigo na gaida kene don dazun
bamu gaisa sosai ba zaki fita.

  Ta dan juyo gareni
tana fadin OK zaki tafi zarah saida safe ke nan wani irin ba dadi naji a rain
haka naja kafana na fice daga part din mama ba tare da kowa ya kulani ba
lokacin.

   Ina shiga part din
duk suna falon a lokacin ummah tana basu wani abu da bansan ko meye ba na daiga
yaran na bata fuskansu alama  abin da ake
basu baida dadi ke nan a baki.

   Kokarin shiga
dakina nakeyi a lokacin naji muryan ummah tana fadin maamah oya zo nan ki karbi
naki kisha .

   Fuska na bata daga
inda nake tsaye din ina fadin ummah bana sha a koshe nake na juya zanci gaba da
tafiya wanan din ba wani abu bane maganine na ciwon zazzabi kawai.

   Ummah oya zoki
karba ban son korafi Anty zarah sai kinsha dole ummah tace don maganin ba dadi
kuma kanina ya fadi daga gefen ummah inda yake zaune.

   Dole nazo na zauna
a gaban ummah ta debo maganin a wani silver ta miko min tare da fadin oya yi
bissimillah kisha.

   Karba nayi ina
bissimillah nakai bakina ba dadi abin amma haka na daure nasha maganin kafin
ummah ta umurce ni da naci abinci.

  Na tsakwara na tashi
zuwa lokacin duk jikina ya mutu tashi nayi zuwa dakina ummah ta dubeni tana
fadin saida kika je gun maman taku din ke nan ko ?

  Kallon ummah nayi a
dan shagwabe kafin na gyada kai alaman naje amma ban yi zancen komai da ita ba
ai itama din kuma ko kulani batayi har yaranta

 

Leave a Reply

Back to top button