Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 35

Sponsored Links

Chapter 35

Ɗaukan ta yayi be direta ko ina ba sai a tsakiyar office ɗin sa yashiga kallon ta daga sama zuwa ƙasa dakyar ya hadiye wani abu daya tokare masa a maƙoshin sa,
Cike da taƙaicin ɗaukarta dayayi kafin yayi magana tariga shi cike dajin haushin sa a tsiwace tace”wai me hadina da kaine daxaka wani kinkimo ni haka saikace
wanda ya dauki matar sa?

Wani abu yaji yana yayo tun daga saman kansa zuwa babban yatsan kafarsa dakyar ya iya daidaita nutsuwar sa fizgo maganar yayi yace”wani irin shigane wannan da kikayi?

Mamakine yacika Aisha a fakaice takalli kanta sai kuma ta maida kanta gefe ba tare data tanka mishi ba,ganin tamasa banza yasake jeho mata da wata tambaya data sata ɗago kanta ba tare data shirya ba,zuba masa idanunta tayi sai ta murguɗa masa baki tana dauke kanta daga kallon sa.

Takowa yayi gareta cikin takun nan nasa na ƙasaita baya baya tasoma yi yana biye da ita saida tajin gina da bango takowa yayi daf da ita tokare bangon yayi da hannuwansa duka biyu ritse idanunta tayi da karfi ganin yanda yatsaya daf da ita har suna iya jin hucin numfashin junan su,

zubama baby face ɗinta ido yayi yana kare mata kallo wani abu yaji yana taso masa tundaga babban yatsan kafan shi har zuwa tsakar kansa.

Wani abu yakeji mai kaman mayen karfe yana jansa zuwa gareta besan sanda yakai hannun sa ɗaya ya dago haɓarta ba,sai jin saukan tattausan leɓenta tayi saman nata.

Waro manyan idanun ta tayi bata sauke ko ina ba sai saman fuskan sa da idanun sa suke kulle,wasu zafafan hawaye na zallah takaici da tsanar sane suka shiga zubo mata daga ƙwarmin idon ta.

Ɗumin hawayenta dasuka zubo masa saman fuskan sa shiya ankarar da shi kuka take saurin saketa yayi yana ja da baya,ganin ya saketa yasata duka awajen tasaki wani kuka maicin rai kaman ranta zebar gangan jikita tanayi tana goge bakita da gyalen dake kanta tana tofar da ƴawu.

Saida ya daidaita kansa sannan ya iya buɗe bakin sa yace,matukar kika sake irin wannan kwalliya kikazo to wannan shine hukunci da zanyi miki,sai na tsotse jan bakin tass…Ɗagowa tayi a zafafe ta banƙa masa harara kaman idonta ze faɗo kasa ta murguɗa masa baki tace”ɗan iska kawai kace kawai iskanci kake neman yi mun.

Wani irin zabura yayi jin abunda tace ɗin ƙwasa tayi da gudu tayi waje kaman zata kife,komawa yayi ya zaune saman kugera haka kawai ya tsinci kansa da sakin murmushi da besan dalilin sa ba,dacewa yarinya bar ganin kun tsira zamu haɗune dake.

Saida tayi nisa da office ɗin nasa taje can ƙarkashin wani bishiyar maina sannan taji wani irin kuka mai karfi yataso mata,saida tayi mai isarta sannan ta tashi jiki baƙwari tanufi hanyan fita dan tafiya gida.

Tana ƙokarin fita wata baƙar mota ta shigo wajen haka kawai zuciyarta ta bata tabi sa komawa tayi da baya ta laɓe bayan wani mota tana kallo wani mutumi yafito daga cikin motar bayan ya faka yanufi ciki wajen direbobi dake lodin kaya suna kaiwa gari gari bayan ɗan shuɗewar minti shida zuwa bakwai sai gashi da wani daya daga cikin direbin sun iso wajen motar tasa a tare shiga ciki sukai sai gashi wannan direban ya fito riƙe da wata baƙar jaka rike a hannun sa sai washe baki yake yana dafe da aljunun sa da alama kudi aka bashi yasa sallama sukai yashiga ciki dan komawa inda yafito shikuma wacan mutumin yaja motar sa yafita da uban gudu.

Wallahi tunda take bata taɓa taƙaicin rashin riƙe waya ba sai yau”yama zama dole nafara riƙe waya a hannuna tace dafata taji anyi da sauri ta juyo cikin tsoro.

Wannan direban ne ashe tunda suka zo da wacan mai motan yalura da ita a wajen shiyasa yace sushiga cikin mota shine yanzu ma yazago yazo”me kikeyi anan?

Ya jeho mata da tambaya,fuskarsa ba rahma yake kare mata kallo ta tsorata da irin yanda yake binta da kallon dukda ta tsorata da irin kallo daya binta dashi amma bata bari tsoron yayi tasiri a ranta ba ta aro jarumta tace”gudowa nayi ta bashi amsa tana barin wajen.

Tsaidata yayi ta cewa”in ma leƙen asiri aka aikoki kiyi rayuwarki zaki saka cikin hatsari dan haka shawara tarage naki kiyi shiru ko ki fallasa abunda kika gani.

“Barazana kakemun da rayuwata kenan?

“Yaro man kaza bazaki san rayuwarki tana da mahimmanci ba sai randa kikayi gigin shiga hurumin da be shafeki ba.

Kafin nayi magana natsin kayi muryan khalid yana cewa”wai ina kika shiga tundazu sai nemanki nake suhail ya addabeni da kiran waya in bashi ke.

Saida yakaraso wajen namu sosai tukunna ya kula da bani kaɗai bace,da mamaki yake kallon mu yace”malam balarabe lafiya de ko?
Me kefaru anan naganku tsaye koda wani abunne.

Sauri cewa nayi”guduwan aiki nayi shine fa dan ya ganni zaune anan yake tambayata ko wani abu nake nema.

“Da eh eh ya amsa a ɗan rude,murmushi khalid yayi yana cewa”ai tana daya daga cikin telolin da mukeji da ita anan masana’antar ina ga gudun fadan oga yasata gudowa nan taɓuye kasan ogan nan naku idan yafara faɗan nan nasa musamman ga wanda yayi fashin zuwa aiki.

Ajiyar zuciya nasauke a ɓoye ina markin fuskan mutumin kuma araina ina da yaƙinin tanan zan samo bakin zaren.

Tare da khalid muka juya dan barin wajen saida nayi gaba harna juya ina kare masa kallo ganin sa kaman ya tsorata dani hannu nasaka a wuya masa alama da zan yankaka murmushin dan bansan ma’anarsa ba ya suɓuce masa yana kaɗa kansa.

“Basma yanzu kina ganin zuwa musami wannan mutumin shine mafita kinfa sanni da rashin hakuri bazan juri wulakaci daga miskilin mutumin nan naki ba.

“Allah kuwa daya daga cikin ƙawayen nata ta amshe kinsan Allah salaha ni har mamaki basma kebani akan wannan dan rainin hankalin saurayin nan nata.

Duk yanda take gwara kan maza amma namiji ɗaya yake wanata kaman sitarin mota.

“Kanku akeji wai an tsikari kakkausa ni ahaka naga abuna kuma nakeson sa,kinga irin miskilan mutanen nan miskilanci baze barshi yadaga kai ya kalli wata macen bama balle ta burgesa dagani yarufe ƙofa.

Dariya suka kwashe dashi hardasu shewa nan suka shirya ita dasu dan suje office ɗinsa suyi magana akan tsare tsaren da tayima bikin da kuma irin party da dakuma mawaƙa da zasu gaiyato dan katawa abun armashi.

Wanka ta dauka iya wanka tayi shigar wata material ɗinki ya bala’in tsuketa kaman idan tayi ƙwaƙkwaran motsi ze yage.

Motar ta suka shiga ita ke driven abinta salaha na zaune kusa da ita raihana na bayan mota suna hira sunƙure sauti cikin wakar justine biba duk inda motar ta gilma sai anbita da kallo yanda take gudu dakuma yanda sautin kiɗi ketashi.

A harabar ma’aikatar sukai parkin motar suka fito suna takun katsaita cikin son nuna isa dakuma izzar tata data saba,saida suka kai bakin office ɗin sa harta kama handle ɗin ƙofan zata buɗe raihana tayi saurin dakatar da ita akan suyi nockin tukunna.

Badan tasoba dan ita neman izini kafin kashiga guri badamuwar ta bace,saida tayi nockin sau uku sannan akayi magana daga ciki hakan yasa cikin zumuɗi ta tura ƙofar tashiga saide tun daga kallon da Ahmad ɗin ya jefeta dashi taji gwiwarta naneman tsagewa,zama sukai inda yamusu nuni da hannu salaha da raihana suka gaisheshi a gajarce ya amsa musu ita ko gimbiyar jira take shi ya gaisheta dan haka be sake bi takan su ba aikin sa yake cikin systerm ɗinsa saida sauka dauki kimanin minti hudu a haka sannan ya ɗago yadube su”me zakawo muku?

Saurin amsa masa tayi da nothing”ok and?
Saikuma yayi shiru cike da yanga dakuma yauƙi ta ɗago ta zuba masa ido irin na riƙaƙƙun ƴan duniyar nan tace”gami da party da muka tsare na shagalin bikin mu”hmmm yace kawai ba tare da ya kalle taba.

Nan tashiga zayyano masa kusan party aƙalla sunkai kala goma kuma wai duka so ake ya hallarta,saida yagama sauraron ta sannan ya sauke ajiyar zuciya yabude baki dakyar yake motsa lips dinta cike da jan aji yace”all this for what?

A mamakince suke kallon sa dukkan su kana ya daura da cewa duk abinda zakiyi kije kiyi amma karkiyi tsammanin zuwana dan bani da time a mean ina nufin wannan lokacin bana kasar zamuyi tafiya sai ana jibi biki zan dawo so idan tanine walima kaɗai ya wadatar mukirayo malamai suyi wa’azi da faɗakarwa sabida neman albarkar auren koya kika gani tawajena yakare magana cike da zolaya.

Miƙewa tayi tace”wallahi my kai baka isa karusa mana shiri da tuntuni mukeyi akan wannan auren ba,kuma ba wani walima da za’ayi kuma wallahi dole ka halarci dukkan event ɗin da zamuyi kai da ƴan gidan ku,tsaye take sai zazzaga masifa take sabida rufewar ido tama mance da wanda take duk yanda ƙawayen nata sukai ta jan hannun ta kan tayi shiru ta zauna taƙi saida ta sauke duka abunda yake kanta sannan ta zauna tana fashe masa da wani sabon kuka.

Shigowar Aisha daya aika khalid yamasa kiranta ne yasashi bude idanunsa da suke kulle tun sanda basma ta soma masa masifarta yasauke su akanta”ɗauko mun ruwa mai sanyi ya umurceta tunkafi ta ida shigowa ruwan ta ɗauko tana miƙa masa nuna mata inda zata ajiye ruwan yayi gaban basma dake kuka.

“Ɗauki ruwan kisha sai muyi magana yamata magana kaman bashine yayi ba ya maida kallon sa kan Aisha data gama shan jinin jikinta tsoronta karyace ze sake yimata iskancin da yamata ɗazu amma wani ɓari na zuciyarta ta ɗan yimata sanyi tunda taga da mutane cikin office ɗin ai duk iskancin sa baze yimata gaban su ba.

“Meya hanaki zuwa aiki harna tsawon mako guda batare da kinsanar ba.

Wani irin ashariya basma dake kuka ta lailayo ta yaɓa ma wacce yake ma tambaya tunkafin ma taga ko wacece,tayi cilli da goran ruwa tana miƙewa sauke idonta tayi saman fuska Aisha wani irin bugawa zuciyarta tayi”uban me kikeyi anan mai wanki.

Murmushi dauke saman fuskarta duk da taji ciwon zagin uban da tayi mata amma ta dake tana”anty basma ashede kece wani kallon mai cike da tsana da kaskanci take binta dashi”faɗamun abunda kikeyi anan zakiyi bawai iskancinku na ƴaƴan talakawa nace kimun ba.

Ƴar dariya Aisha tayi tace”aiki nake kinsan nafi kwarewa wajen iya wanki to nan din ma aikin shara dakuma bama oga abinci nake kinsan saboda kuɗi ba abunda mutum ba zeyi ba,na gaji da wankin ɗan kanfen mace ƴar uwata shisa naga gwara nayi nabuje ko ba komai wataran zan samu…..ji kake tasss .

Leave a Reply

Back to top button