GIRKE GIRKE

Yadda Ake Alalen Doya….. [ Girke Girke.

Sponsored Links

     


               Yadda Ake Alalen Doya….. 

Assalamu Alaikum Uwargida, barkan mu da wannan lokacin. 

 Yau a filin namu na Girke-girken Azumi, za mu kawo muku yadda ake girka Alalen Doya A Taikaice. 

Da farko dai ga kayayyakin da uwargida ke bukata don yin alalen:

  ABUBUWAN DA AKE HA Dawa SUNE :

Kwai

Doya

Curry

Hanta

Maggi

Attaruhu

Manja 

Laida /gwangwani

Kayan kanshi

Yadda ake yi:

Uwargida za ki wanke doyar sai a yanka ta daidai yadda hannu zai iya rikewa, sannan a goge ta a jikin greater, sai a yi blanding dinta da attaruhu da albasa! yayi kauri kamar yanda ake kullun wake. 

To sannan akawo maggi asaka, da curry kadan ba’aso yafito, se’akawo yan kakkiyar dafaffen hanta asaka aciki, akawo yankakken dafaffen kwai asaka aciki! Amma kananan yanka za’ayi musu, idan ba’a bukatar dafaffen kwai da’a iya saka danye bayan ankadashi, da’a kulla kamar yanda akeyin Alalen wake, sai adafashi,  ana iya cinshi haka nan, kuma da’a za’a iya cinsa da miya.

Shi ke nan alalen doya ya kammala.

A ci dadi lafiya.

Leave a Reply

Back to top button