GIRKE GIRKE

YADDA AKE HADA+ ICE CREAM+ VANILLA DA CHOCOLATE [ GIRKE ~GIRKE….

Sponsored Links

YADDA AKE HADA+ ICE CREAM+ Vanilla da Chocolate 2023…

Assalamu Alaikum Uwargida, barkan mu da wannan lokacin. 

 Yau a filin namu na Girke-girken Azumi, za mu kawo muku yadda ake Hada Ice cream A Taikaice. 


ABUBUWAN DA AKE BUKATA


Ruwan kwai (farin kawai)

Madara ta ruwa ko ta gari

Vanilla Flavour

Pure cocoa

Maltisers chocolate

Sukari ‘Icing’ na yin cake. 


YADDA AKE HADAWA SHINE:


1~ HADIN VANILLA_:🍦

Da farko Uwar gida  sai a fasa kwai kamar biyar sannan a tsane gunduwar (kwaiduwar) da ke cikinta sai a zuba a blender.

 Bayan haka, sai a zuba madara da sukari na yin *cake* (Icing sugar).

 Sannan sai a diga flavour na vanilla a ciki sannan sai a markada su har sai sun yi kumfa sai a zuba a roba sannan a sanya shi a gidan sanyi (fridge) ya yi kankara.


2~ HADIN CHOCOLATE_:🍧

A zuba madara da sukarin yin *cake* a na’urar markade ta gida (blender). Sannan a dauko cokali daya na ‘pure cocoa’ a zuba sannan a zuba *flavour* na kwakwa.

 Sannan sai a markada har sai ya yi kumfa sannan a zuba a roba.

 A dauko *chocolate* na maltisers a jefa a cikin hadin sannan a saka a gidan sanyi (fridge) ya yi kankara._

_Bayan haka za a iya dauko hadin *Vanilla* da wannan na *Chocolate* a hada sai a sha.

Leave a Reply

Back to top button