Dabarun Rubutun

[YADDA AKE RUBUTUN WAKOKIN HAUSA. by MSZ]

Sponsored Links

             DABARUN RUBUTUN WAKA  

                   KASHI NA TAKWAS

  Daga

Nasir G Ahmad


       RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA

  Barkan mu da sake kasancewa a cikin wannan topic inda zamu dura da bayani a cikin sa.

Assalamu alaikum.

A makon jiya mun fara magana kan baiti, inda muka bayyana ma’anarsa. To yau za mu dora:


NAU’O’IN BAITI

Ana so tsarin rubutacciyar waka ya zamo dayan wadannan nau’o’i:


1. Gwauruwa

Waka gwauruwa ita ce mai dango daya-daya a kowane baiti nata. Misali:

Alhamdu lillahi mun samo fita hadari,

Wancena jan zamani da ke sa maza wadari,

Jama’a musulmi ku ce amin mu zam shukuri.

(Sa’adu Zungur)

2. ‘Yar Tagwai

Ana kuma ce mata ‘Mai Kwar Biyu.’ Wato wakar da kowanne daga baitocinta ke kunshe da dango biyu-biyu. Misali:

Ko akwai wani wanda ya tambaya,

Mene ne sargartacciya?


Diyar da ta taso ba kula,

Ba zuwa makaranta ko daya.


Babu tarbiyya a wajen uwa,

Da uba sai shashancin tsiya.


Sai tallace-tallace barkatai,

Wai su tara kudi su yi dukiya.

(Baba Maigyada Agege)


3. Mai Kwar Uku

Ita ce waka mai dango uku-uku a kowane baiti nata. Misali:


Rashin hada kai shi ka ba makiya,

Damar su bata zaman lafiya,

Su kawo akida marar ci gaba.

(Wakar Hada kai)


4. Mai Kwar Hudu:

Ita ce wakar da kowanne daga baitocinta ke da dango hudu-hudu a cikinsa. Misali:


Ga abin da hali ya kawo,

An yi dauri yau kuma ya dawo,

Na kudurta buri na sawo,

Rabbana nufe ni da dacewa.

(Wazirin Gwandu, Umaru Nasarawa)


5. Mai Kwar Biyar

Ita ce wakar da ke da dango biyar-biyar a cikin kowane baiti nata. Misali:


Mutum kadan ba shi sani,

Kira shi jaki da zani,

Da tambaya kan yi sani,

Abin da zan zo na sani,

Ba zan ki tambayar sa ba.

(Akilu Aliyu: Wakar Kokon Mabarata)


Mu kwana nan.

Ma’as Salam.


anan zamu diga aya sai muhadu a Kashi na gaba.


Daga 

Tsangayar da ta himmatu wajen kulawa da killacewa da taskace abubuwan da suka shafi adabi da zamantakewar al’ummar hausawa

  Domin Karin bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan za’a cigaba da kasancewa wannan wensite mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauransu, 

Ana iya subscribe ta hanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode.

Leave a Reply

Back to top button