Dabarun Rubutun Waka

DABARUN RUBUTUN WAKA KASHI NA TARA

Sponsored Links

   

             DABARUN RUBUTUN WAKA  

                      KASHI NA TARA


            MATAKAN DA AKE BI WAJE

             RUBUTA  KARBABBIYAR

                   WAKA (POEM).


Barka da zuwa wanan shafin namu mai albaraka .


    Gabatarwa 

         Daga 

Tsangayar da ta himmatu wajen kulawa da killacewa da taskace abubuwan da suka shafi adabi da zamantakewar al’ummar hausawa.

  by

 msz

Ba tun yau ba, na lura da irin kura-kuran da suke ta faruwa a wakokin mawakanmu. Da na yi bincike da nazari ne, na gane hakan yana faruwa ne, a ta dalilin yawancin mawakan haye suke yi wa waka, ma’ana ba sa tsayawa don fahimtar yaya zubi-da-tsarin waka yake (Peotics), ya  dokoki da kuma hanyoyin da suka jibanci waka suke (Lyricism).


Wasunsu ba su san mene ne yake sanya waka ta zama karbabbiya ba, a lokaci guda ba su san mene ne ke rusa waka ba. Shi ya sa wani lokaci za a ji wakoki sakakaka, marasa kan gado, ba tare da an fahimci ina suka dosa ba. Da na kara nazari ne, sai na fahimci cewa wasu mawakan damuwarsu abin da za su samu, wanda hakan ne ya rufe musu ido, wajen neman ilmi a kan waka. Na kuma sake fahimtar cewa mawakan suna da lalaci wajen yin bincike da kuma nazarin ya za su inganta wakokinsu.


    Rubutun da zan yi a yanzu, yana dauke da matakan da ake bi ne wajen gina ko rubuta ko kuma shirya karbabbiyar waka. Ga matakan kamar haka:


(1) KARIN WAKA (Mood and Tone)

  Ana so mawaki ya kasance ya samu karin waka na musamman, wanda ya tabbatar zai gamsar da masu saurare ko karantawa. Ya kuma tabbatar da karin wakar ya dace da wakarsa. Bayan mawaki ya samu karin wakarsa, to ana so wakar ta ci gaba da shi ba canzawa  har zuwa karshenta.

  Idan mawaki ya yi waka ba karin waka, to ba ta da maraba da tadin baka ko abin da ake kira zube (prose). Wanda yanzu mawakanmu suna cikin waka da karin waka, sai ka ji kuma sun canza, sun ci gaba da wani kuma. Wani ma sai ka ji an yi amfani da karin waka uku ko fin haka a cikin waka daya. To a nan, ina shaida wa masu yin hakan cewa, yin hakan kuskure ne, wato sun karya dokar waka, walau rubutacciya ko kuma wakar baka.


             MASU ALAKA DA WANAN

Reading more….Asali-hausa-da-ginuwar-daidaitaciyar Hausa.

Reading more….ko-kasan-yadda-harshen-hausa-yake-bun kasa

Anan zamu diga aya sai kashi nagaba sai mu dora inda Aka tsaya.


                       Domin Karin

 Domin Karin bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan za’a cigaba da kasancewa wannan wensite mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauransu, 


Ana iya subscribe ta hanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode.

One Comment

Leave a Reply

Back to top button