Dabarun Rubutun Waka

[YADDA AKE RUBUTUN WAKOKIN HAUSA. by MSZ]

Sponsored Links

      DABARUN RUBUTUN WAKOKIN HAUSA

                                 KASHI NA 

                                   SHIDA 

Daga

Nasir G Ahmad

         RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA 

Assalamu alaikum.

 A makon jiya mun fara magana a kan ma’aunin waka, wato karin da akan gina waka kansa, inda muka duba tarihin samuwar ma’aunan rubutattun wakokin Hausa. To yau za mu karasa tare da misali.

 Duk da kasancewar har zuwa yau akan samu rubutattun wakoki da akan shirya bisa ma’aunan Larabci, mafi yawan mawakan wannan zamani ba su ma san da zamansu ba, duk kuwa da kasancewar wasu wakokin nasu za su iya hawa ma’aunan Larabcin, wadanda galibi da su akan fara auna waka yayin nazarin ta.

 Kada wannan dogon labarin ya dami mai sha’awar fara rubuta waka. Babban abin da ake bukata shi ne, duk karin da ka zabi ka rubuta waka da shi, ya zamo ka bi hawa da saukar muryarsa sau-da-kafa. Wato kalmomin da za ka zaba su zamo dai dai yawan gabobin wancan kari, ba tare da sun gaza ko sun zarta ba. Ga misalin wani baiti na wata wakar Abubakar Imam:

Maraba da kai muhammadu dan Amina,

Maraba da shugaban duka Annabawa.

Ga yadda za a bi sawun karin:

maraabadakai/Muhammadudan/amiinaa,

maraabadashuu/gabandukaan/nabaaawaa.

Sai mu ce:

idankaasoo/kazaabikarii/nawaakaa,

kaluuradashii/dakyausannan/kabiishii

Wato:

idan ka so ka zabi kari na waka,

Ka lura da shi da kyau sannan ka bi shi.

Mu lura da cewa, yayin auna waka ana nuna dogon wasali ta hanyar rubanya wasalin sau biyu.

Ma’asSalam.

Daga

Tsangayar da ta himmatu wajen kulawa da killacewa da taskace abubuwan da suka shafi adabi da zamantakewar al’ummar hausawa.

   Domin Karin bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan za’a cigaba da kasancewa wannan wensite mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauransu, ana iya subscribe ta hanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode.

Leave a Reply

Back to top button