Hijab Garkuwa ne ga yar macce.
Hijabi Garkuwa Ga Matan Kwarai
A sakamakon rubutun da na yi kwanakin baya, sai wata baiwar Allah ta turo min da sako, ta kuma bukaci da na yi bayani filla-filla a kan yadda ya kamata mata su suturce jikinsu, da kuma irin suturun da bai kamaci mata su sanya ba. Dalilin da ya sa a wannan makon zan yi bayani a kan suturar da ya kamata matan kwarai su sanya ke nan.
Wasu matan sukan dauka yin shigar da ta dace ko musulunci ya tanadar hakan ba komai ba ne, face wani kauyanci da rashin wayewa, yayin da wasu kuma suke ganin cewa, wai ya za a ce mata su lullube ko’ina a jikinsu, hakan zai hana ta walaya da kuma sake wa, baya ga haka wai idan suka sanya suturar da ta rufe musu tsaraicinsu, suna ganin sun takura ne. sun manta umarni ne daga Ubangiji cewa a sanya suturur da za ta lullube jikin nasu.
MENE NE HIJAB ? YAU SHE AKA SAUKAR DA UMARNIN SANYA HIJAB
Hijab sutura ce da ake sanyawa domin suturce duk wani waje na jikin mace da ka iya darsa sha’awa a zuciyar namiji. Ana so mata su rufe ko’ina a jikinsu face tafin hannu da idanuwa biyu, da mace za ta iya amfani wajen gani idan tana tafiya. Ana so mata su sanya hijab tun daga sama har kasa.
Ubangiji Ya yi mata umarnin su fara sanya hijabi ne a sheakara ta uku bayan Hijira, a wata ruwayar kuma an ce shekara ta biyar ce bayan Hijra.
A da kafin Ubangiji Ya yi umarnin a rinka sanya hijabi, mata sukan yi irin shigar da suka ga dama, ba ya ga haka kuma sukan fita duk lokacin da suka ga dama. Amma daga baya, sai Ubangiji Ya ce a fada wa matan musulmi su runtsar da gannansu ga kallon abubuwan da suka haramta, su kuma suturce jikinsu, face tafukan hannuwansu da kuma idanuwansu don su gani idan suna tafiya, (hakan zai kubutar da su daga aikata ayyukan alfasha), ka da kuma su kasance masu nuna kawa da ado, face mazajensu ko iyayensu ko surukansu ko ‘ya’yansu, ko ‘ya’yan mazajensu ko ‘yan uwansu maza da matansu ko kuma sauran mata musulmi ko kuma baiwar da suka mallaka ko tsoffi bayi da ba su da sha’awa ko kananan yara da ba su fahimci mece ce sha’awa ba. kada kuma matan musulmi su yi taku mai sauti don ku bayyana adonsu.
Daga nan sai ya zama ba a so mata su rinka fita ba tare da dalili ba, idan kuma ya zama dole to, ana so, su sanya tufafin da zai lullube ko’ina a jikinsu, yadda ba za a iya ganin duk inda yake da tudu ba a jikinsu, ma’ana, su kasance tsulum a cikin hijabin ko suturar da suka sanya.
Tufafin da ya dace mata su sanya idan za su fita:
– Su sanya tufafin da zai rufe ko’ina a jikinsu, face idanuwa don su gani da kuma tafin hannuwa.
– Ka da su sanya tufafi ko hijabin da yake daukar hankalin, wanda ko daga nesa za a iya hango su, a kuma gane mata ne sanye da kaya.
-Ka da mata su sanya tufafi ko hijabi mai shara-shara, watau tufafi ko hijabin da ba a yi shi da gamammiyar saka ba.
– Ka da mata su sanya tufafi ko hijabi mai matse jiki, wanda zai fito miki da dukkan tudu-da-kwarin jikinsu.
– Ka da su sanya tufafin da ya yi kama da na tufafin maza, ba a so ki sanya riga da wando irin na maza.
-Ka da su sanya tufafin da wadanda ba musulmai ba suke sanya wa, domin shigarsu kullum ta tsaraici ce.
-Ba a so mata sun sanya kayan alfarma masu sheki da daukar ido, idan za su fita.
Amma abin mamaki a yanzu sai ka ga matan suna sanya kayan da suka ga dama, ba tare da tunanin mai hakan zai haifar ba, ka da ku manta saboda irin hadarin da shigar tsaraici za ta haifar Manzon Allah (SAW), ya ce da matansa su sanya hijabi ko da a gaban makaho ne. domin Hajarat Ummu Salma (Allah ya yarda da ita) ta rawaito cewa, “Wata rana ni da Hajara Maimuna (Allah Ya yarda da ita), muna tare da Manzon Allah (SAW), sai ga Abdullahi ibn Maktoom, sai Manzon Allah (SAW), ya ce, mu sanya hijabi, sai muka ce makoho ne fa, a nan Manzon Allah (SAW), ya ce, idan shi makaho ne, ba ya ganinku, to, ai ku kuna ganinsa.” (Miskat da Tirmizi da Abu Dawud sun rawaito shi)
Wani hadisi da yake dada tabbatar da wajibcin sanya hijabi da kuma sutarar kwarai shi ne, akwai wata rana da wata mata mai suna Ummu Khalid Kais ibn Shammas, ta zo wajen Manzon Allah (SAW) don ta nemi karin bayani a kan danta bayan an dawo daga wajen wani yaki, ta je tambayar ne, don ganin an dawo daga yakin, amma ba ta ga danta ya dawo ba, kuma yana ta ce wa an kashe shi a wajen yakin. Sai Sahabbai da suke tare da Manzon Allah (SAW) a lokacin da ta zo, suka ce ya aka yi take sanye da hijabi da kuma tufafin da ya lullube mata jiki gaba daya, duk da irin wannan hali da ake ciki na tashin hankali da bakin ciki. Sai Manzo Allah (SAW) ya sanar da ita cewa danta ya yi shahada, sai ta ce musu idan na rasa dana, ai kuma ba zan yi kowace irin shigar da za ta zubar min da mutunci ba.
Don haka ya kamata mata su gane shigar tsaraici na haifar da illoli da yawa wadanda suka hada da: zina-zinace da yawaitar bazuwar cututtukan zamani, kuma bala’o’I iri-iri za su sauka a gari da kuma duniya baki daya. Za a samu yawaitar fyade a cikin al’umma. Za a kuma debe wa al’umma albarka, ya zamanto komai ba shi daraja, har ya zamanto yanzu za ka ci abinci, amma cikin kankani lokaci ka sake jin yunwa, haka duk kudin da ka tara za su zama ba su da kima ko wata daraja, kuma al’umma za ta kasance cikin tsanani da wahala.
To, a yanzu a duka abubuwan da na lissafa, wanne ne bai addabi jama’a ba? Don haka lokaci ya yi da ya kamata, matan da suke shigar tsaraici su fahimci bala’in da hakan yake haifar wa al’umma, ka da fa su manta ko turawan da suke kwaikwayonsu wajen yin shigar tsaraici, an yi hani a littafinsu, ku duba littafin Mateyu Surah ta 5, Aya ta 28.
Allah Ya taimake mu, amin.
Posted by DIDIGI
MASU ALAKA DA WANAN
Domin karin bayani
Domin Karin bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan za’a cigaba da kasancewa wannan wensite mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauransu,
Ana iya subscribe ta hanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode.
written by ceo
Page
musa s zage