TUNATARWA

{Raƙumi da abinda ya kunsa}

Sponsored Links
Daga msz 
Sunana Mal.nagudu
 Na kasance ina kiwon RAKUMA na tsawon shekaru, Wata rana na fito na kora rakuma na zuwa kiwo saiga wani bawan Allah saurayi yazo ya same ni muka gaisa na bashi suna na Mal, Nagudu.. Sai yace dani mal, Nagudu nazo da wasu “yan tambayoyi ne in bazaka damu ba !
Ni kuwa nace ina sauraron ka…
sai wannan saurayi yace dani : in bazaka damu ba ina so ka bani takaitaccen abundaka sani dangane da rakumi, ‘Dabi’unsa,Halayya da sauran.
 Sai na tambayeshi da cewa hala zaka fara kiwon rakuma ne ?
sai kuwa yace: a‘a ni ‘dan makarantane,
sai na fara da cewa: wato shi rakumi Allah ya halicce shi kuma ya ban-bantashi da sauran dabbobi, ta fiskoki da dama, misali
1-rakumi ne kadai-dayan dabbanda zai iya rayuwa acikin sahara duk yawansa ba tare daya samu wani damuwa ba, sabanin sauran dabbobi.
2-rakumi yana iya shan ruwanda zai kai masa sama da wata 2 (bisaga yananin da kai me shi ka sabar masa kake bashi) kuma in lokacin shan ruwansa yayi to kuwa sai ya nema ya sha. sannan ya ajiye saura a Reserve.
3-rakumi zai iya tafiya acikin ko wani irin sahara ba tare da kafafunsa sun lume a ciki ba.
4-Allah yayi wa rakumi wani murfi a gaban idanunsa, (wato idonsa duk tashin kuran sahara bazai ta6o idonsa ba) kuma ba tare da ya rufe ba,
5-rakumi ne dabban da yake iya gane cewa gabansa akwai ruwa kafin ya isa da kusan meter 100,
6-rakumi dabba ne da baya yin bar-bara wa jininsa ( Qanwa ko yayarsa)
7-rakumi ne dabbanda yake canza hanya in akwai kunawa a hanyar, domin yana ganewa kafin ya isa kuma duk girmansa nan yana tsoron kunama,
8-kuma inka cuci rakumi ko ka zalunce shi saiya rama, duk daren dad’ewa.
(wata rana wani me kiwon rakuma, rakumi daya aciki yayi laifi, sai kuwa ya hukunta wani daban ba me laifin ba, yayin hakanne cikin rashin sani, daga baya sai ya gane wanda yayi laifin to saiya fara kaffa-kaffa da rakumin don yasan zai rama, rannan sunje rafi ashe rakumin na kullace da abun a ran shi wanan mutum saiya shiga rafin wanka, nan da nan rakumin nan ya bishi ruwa ya danne shi, dakyar ya kwace, rakumin yayi niyyar kashe shi, karshe dai sayar da rakumin nan yayi)
9-rakumi ne dabbanda yake barin aiki in ranshi ya 6aci, duk kuwa yanda kakai da zafin ka hada zaka hakura.
10-sannan aduk dabbobi ba wanda yafi rakumi hakuri da kawaici,
da mal, madu ya kawo wannan gaba sai yace ina cikin fada ma wannan saurayi wannan sai na fahimci kuka yake ta shar6a!, sai nace dashi me yakefaruwa ?
Anan ne saurayin yace dani wato ni ‘dalibi ne akullum malamin mu yazo karanta mana wata aya sai ya zubda hawaye!,
-mal, madu yace sai kuwa mamaki ya kama ni nace kai kuwa wata ayace acikin al-Qur‘ani haka ? Kuma don me ?
sai saurayin nan ya kada baki kuwa yace ayan tana cikin sura ta 88 aya ta 17 inda Allah yace SHIN BAZA KUYI DUBI IZUWA GA RAKUMI BA TA YADDA AKA HALICCE SHI ?
 ni kuwa sai nasha alwashin sanin me yake sa mal, kuka !,
Kuma sai naga abun harya wuce tunani na !
-sai ya tashi ya tapi yabarni ina cike da mamaki !,.
copy righting 
   By msz

Leave a Reply

Back to top button