Hausa NovelsTUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 17

Sponsored Links

 

 

Duk juyawa mukayi muna kallon su don wa yanda ke shigowa da
kayan da muka sayo masu a lokacin wanda munir ne ya bada shawara haka gare mu
aka hada kudin aka sayo.

   Master munji shiru
ne muka biyo bayan ka don mu diba ko lafiya kasan ance ka kula wanda ya kulaka
munir ke wanan maganan daga inda uwargarke take tsaye sai kuka takeyi har
lokacin tana bubuga kafa a kasa.

   Jinin jikina nasha
don haka kawai naji tsikan jikina yana tashi duk lokacin da wana  akuyan tayi kuka, magana yake damu amma
hankalinshi na gun akuyan nan.

    Tabarma tsohuwar
ta dauko muna dakinta mu matan tace mu zauna Dije zasu iya zama kuwa ya fada
mezai hana mu zauna mu da indan mun mutu akasa za a samu hannatu ta fada.

   A gurfane nake a
can karshe kusa da tsohuwar yayin da take zuba muna godiya da fatan alheri
bamuyi aune ba aga wanan akuyar ta balle daurinta ta nufo wajen mu da gudu.

    Muryan malam
tanimu ne ke fadin kai kai kai kada ki soma karki fara wanan ga yayan mutane
kaji mun akuya ke baki son bakine a gidan.

    Amadi din ya mike
ya kamata yana fadin aiko na baku abinci da zan fita dazun mana uwargarke ya
dago yana fadin abinci ta gani yasa harta ballo a madaurin ta.

   Kukan nan nata
takeyi tana turjewa a wuri daya ya samu da kyar yajata yaje ya daure ta tare da
zuba masu abinci saidai takici sai kuka takeyi sosai kamar taga wani abu.

   Amma ba wanda ya
farga da kukan da takeyi sai malam tanimu da akai mai bayanin dalilin zuaan mu
yake sa muna albarka da fatan alheri

  Nikan mikewa nayi
daga inda nake tsugunne a cikin tsawala bayan na dan tabo hannatu nayi mata
alaman da mu tafi.

    Sauran suka mike
sai anjima mukaiwa tsohuwar wani kuka sosai akuyan keyi da kamar guda na fice
gidan ko kafin mazan su fito har na shiga motana ina kokarin tattara natsuwana
waje daya.

    Don harna shiga
motar ina ganin kamar wanan dabban zata biyoni ta yakusheni har cikin motar sai
waigen kofan gidan nakeyi ina kokarin tayar da motar na kasa saka key din motar
da kyau.

   Wai lafiya kike
kuwa Mayana naga kamar a tsorace kike mana hannatu ke fada daga gefena don
yanzu itace babban aminiyata ta kut a school din duk inda nake muna tare duk da
halin mu yasha bambamda ita sosai.

   Na samu na tayar da
motar ban jira su karasa fitowa ba na fara yin kwana don barin wajen duk suka
bini da kallon mamaki a hanya na saukesu nace gida zan tafi nabasu kudin taxis.

   Na isa gida a
firgice dakina na nufa da kyar na samu saita kaina nayi sallah la,asar na koma
saman gado na dunkule wuri daya sai ga zazzabi yana neman kamani lokaci guda.

    Jikin ummah ya
bata cewa na dawo sai ta leka dakin ta hangoni kwance hardasu jan bargo na rufa
kafana yasa ta gane cewa nice a dakin dai kwance.

   A,a ke yaushe kika
dawo har kika shigo banji shigowan ki ba ummah ta fada saida na yaye abin rufan
nace dazun nan na dawo ummah babu kowa a falon lokacin.

  Lafiya kuka dawo
haka da wuri ta tambaya tana kafeni da idanu nace umma sanyi nake ji na dawo
subbahanallahi ta fada to kinsha magani nace bansha ba ummah yanzun ne na fara
jin hakan.

   Waike yaushe zakiyi
wayaune wai maamah ki tashi kici abinci kisha magani ina zuwa tana fadin hakan
ta juya ta fita daga dakin binta nayi da kallo na koma na kwanta.

  A haka ta dawo ta
sameni kwance fada ta fara min dole na tashi nadan tsakuri abincin na hade
magani na koma na dunkule sai barci yaso ya daukeni sai naji kukan akuyan nan a
kunnena in zabura na bude idona.

    Yanzun kai Amadi
banda abinka ai kowa yasan mu tallakawane a garin nan ko meye abin jin haushi
don sun kawo maka wanan kayan haka har gida.

   Haba Dije ai wanan
ya zama zubar da mutunci a gareni yaushe don ina koya masu karatu kawai zasu
kwaso wana  uban kayan haka su kawo min
har gida watau gani mabukaci ko suke ganina .

    Amma dai akwaika
da wani zance Amadi ina kayan nan na dubiya suka kawoma don sun dauka kaine
bakaji dadin jikin kaba yasa sukai haka a matsayinsu na aminan ka ?

   Shiru yayi ya barta
tana magana kafin ya mike zuwa ban daki saida ya kewaya ya fitone idon shi ya
sauka kan dan tsiron daya fito a wurin katangan nasu.

  Takawa yayi zuwa
wajen tsiron ya kura mai ido na dan lokaci kafin ya juya yana fadin Dije
tumfafiyace ta fito a wurin nan haka ?

    Tumfafiya uwar
kwankwanmai baki fita a wurin banza, sirinki sai Allah,  mai madaran sihiri, icce kadan da aiki
dubu,  dama iccen tumfafiyace ya fito a
wurin ta fada cikin mamaki.

    Gaskiya kamar
shine nan din ya fada yana kai hannu ga dan tsiron dake tsaye Allah ya kafeshi
a wurin cikin hikima irin na ubangiji.

    Ruwan butan daya
rage a ciki ya juyewa tsiron yana gyara mashi tsayuwa kafin ya mike ya nufo
wurin Dije din tsaye take tana mai kallon mamaki kafin ta saci kallon inda
uwargarke take tsaye.

   Gani tayi ta kura
mai ido zakace mutumce ita ganin ya dago ya bar wurin sai tayi  wani girgiza tare da mika ta dona kanta cikin
ruwan shansu.

   Kai Dije ta gyada
alaman naganeki wanan tafi karfin dabba shike nan yanzu tabbas akwai wani
lamarin boye a gidan su dake shirin faruwa.

   Zama ya kara yi
saman dan dutsen da Dije ke zama tayi sallah yana kurawa kayan dake saman
rabarma ido a cikin tunane yaji muryan Dije na fadin ka dibi kayan nan akaiwa
malam Tanimu tunda ya shigo ya gansu dazun gidan nan.

   Hannu ya mika wurin
kayan yana mata nuni dasu tare da fadin a diban mai mana Dije abinda kaba wani
shine rabon ka ai muma bamu taba zaton samun hakan ai.

  Allah dai yaima
albarka dadina dakai saukin fahintar mutum balle malam Tanimu ai abokim zamane
na gaske duk wanda ya damu da damuwanka ai kaima ka damu da tasa.

   Tana fadin haka ta
dago kai tana kallon jikan nata tare da fadin koba hakana ba Amadi shiru taji
ta kura mai ido kafin tace wai me kake tunane hakane ko har yanzu akan zancen
kake wanan tunane.

   Ajiyan zuciya ya
sauke don shi ba zancen kayan nan bane a gaban shi sai tunowa da sauyin yanayjn
da yaga yar mayana a cikin sa wace ta sauke ajinta da daraja ta tako zuwa gidan
su yau.

    Duk da ta zauna
kamar yadda yan uwanta suka zauna din saidai alama ya nuna a takure take da
irin zamam ko a kyamace da yanayin gidan nasu.

  Wanan yasa yake
gudun yin mu,amula da kowa don gudun irin hakan yayi mamakin yadda suka iya
gano gidan har sukazo gaskiya da ake fadan an daina kiwon dabba yanzu sai
mutane.

   Wai ashe dama har
wasu a school sun sanda da gidansu shibai sanda hakan ba don yana ganin bai
mu,amula da kowa cikin school din ya tsaya matsayinshi da Allah ya ajeshi na
dan tallaka.

   Dije dake kallonshi
cikin rashin fahintarshi ya kurawa ido kafin ya sauke ajiyan zuciya a hankali
dazun da malam Tanimu zai fita yake magana akan rumfar da zakayi akwai kara da
ice ka fara dashi ya baka inyaso alabashin daga baya in Allah ya tarfawa abin
nono sai kayi kokarin gina na kasa kona kwano yace saboda damina kasan dai
yadda ruwa ke muna unguwar nan ai.

   Binta yayi da kallo
kawai wanda ke nuna alaman ba zaiyi ba ke nan kaiko wataran hutsune Amadi ina
laifi da yazo ma da wanan sharan kuma.

   Dije bana son hada
abina dana kowa kin sani dama yace na sayane zan saya din in gwada in gani amma
ni kan ba zan dau kayan shi haka kawai na saka a cikin nemana ba gaskiya.

   Yanzu halinka
yaimun kama dana ubanka sak wurin rashin yarda da mutane kana wanan girman kana
kara kamanni dashi sosai.

   Abinda ta fada yasa
ya mike tsaye yana fadin sai ana magana ki dauko wani zance kisa aciki na fada
maki ki bar hadani da mutumin da baisan nibama.

  Amadi dole in hadaka
dashi don saukin mu ke nan kowa garin nan yasan kai ba shege bane da ubanka
tafiya yayi ya barka ya koma kasan su da har yau bao juyo inda muke ba.

    Ranshine ya kara
baci sosai kan wanan zancen da Dije ta dauko a yanzu don shi sam baison a dauko
mashi zancen mahaifin shi dukko yadda yake da mutum yanzune zai bata ranshi.

   Wanan yasa Dije ta
daina mai irin zancen nan a gabanshi ko yanzu ma subul da baka tayi ta fada don
kamanin mahaifinshi data hango a tare dashi lokaci.

   Ganin ya doshi hanyar
waje Dijen tace ina kuma zaka ba zaka tsaya kaci abinci ba zaka fita da yunwa
dadina dakai zuciya kaman kuturu idan kaso.

    Ko kaki ko kasa
kowa yasan mahaifinkane shi garin nan da wayauka ya sa kafa ya wuce ya barmu da
sunan zai je duban gida har yau bamu kara jin labarin shi ba kuma.

   Wajen gidan nasu ya
tsaya yana kalle kalle kamar yana neman wani abu aikin dole ya tsiruwa kanshi
na gyaran kofan gidan nasu yana tarawa yasala wuta kafin ya koma daga ciki yaci
gaba da gyara don yaga gidan ya yamutse kwana biyun da bai samun zama ya
gyarashi.

   Ranan kan a tsorace
na kwana don saida hankalin ummah ya tashi don ganin yadda nake firgita da
zaran barci ya dan daukeni zan zabura na kadu in bude idona a firgice karshema
dakin ummah na dawo na kwanta.

   Sai washegari bayan na shirya na fito daga
daki zan tafi school har lokacin yanayina ya nuna ba daidai nake ba sosai hakan
yasa hankalin ummah ya koma kaina.

   Nafito nake fadin
zantafi ummah ta dago ta kalleni tare da fadin kin karyane sai na bata rai ina
fadin banjin yunwa sai take tambayana wai meke damun kine haka ?

   Ko ciwom kanne ya
kara dawowa kuma jin haka yasa na dan kai zaune saman hannun kujeran dake kusa
dani ina fadin ummah kaina bai ciwo saidai idan na rufe idone sai na dinga jin
tsoro.

   Koda barcin ya dan daukeni sai naji kukan
dabba a kusa dani shine kawai damuwana yanzu ina maganin da kike shakawa yake
ta tambayeni yana daki cikin jakkana na bata amsa.

   Dauko shi ki shaka
kafin ki fita kuma ki fito nan gabana ki shakashi yanzun nan ta fada a tsigar
umurni a gareni wanda hakan ke nuna ba wasa ga zancen nata.

   Juyawa nayi na
dauko a gabanta na shaka a take na fara atishawa tasa Tani ta kawo garwashin
wuta nayi hayaki hakan dana tsaya yi ya bata min lokaci saidai na gode Allah
malamin bai shigo ba ya aiko motarshi ta lalace a hanya .

    Don haka na samu
kowa na harkan gabanshi a cikin ajin hannatu na zaune da wayanta tana charting
nayi mata sallama na zauna yau kinso makara ta fada daga gefena.

   Wallahi ummahce ta
tsayar dani nasha magani kafin na fito ko tun jiya da kika sauke mu kina nufin
baki da lafiya nace eh to ba dai wani sosai din nan ba.

   Amma kuma ai lafiya
mukaje gidan nan ni har na tuna jiya kun tafi kun barni da mamaki da tausayi a
raina zarah kinga gidan da mutanen nan ke rayuwa a ciki zarah ?

   To meye shi Allah
ya nufa su mallaka a nan duniya wata kila rabonsu yana nan tafe nan gaba
tunda  dansu yana karatu yana kuma
sana,an shi .

   Hakane abinne da
ban tausayi wallahi ni tsohuwar ma tafi ban tausyi jifa daki kamar zai fadi har
ya duka don tsufa an tangaleshi da wasu manyan itace da duwatsu.

  Kai sannu dai
hannatu duk kin kallace masu gida ashe da kallon kwan niko banji komai ba illa
wana  akuyar mai kuka itace ta firgitani
har mafalkinta na dingayi jiya a dakin ummah na kwana.

   Keko kan akuya zaki
firgice haka duk wanan tsoron haka inaga kinga zaki  a gabanki ko biri ido na lumshe nace ba zaki
gane abinda nagani ba.

   Sai da malamin da
yai muna lecture karshe ya fita munir yayi saurin samuna don har mun daga zamu
tafi yace Mayana yaufa akwai matsala don master yayi fushi sosai damu yadda
mukai mai jiya wai mun raina da arzikinshi yasa muka hada mai kudi mukai mai
sayayya ko ?

   Kai haba dai
hannatu ta fada a cikin mamaki nace nayi wanan tunanen kuma na fada maku zaiga
mu  raina mashi ai.

  Wallahi kin fada
kuwa aina fada mai komai na kuma bashi hakkuri saida naga kamar ba zai kara
koya muna ba yadda ya nuna don yace shi badon mu biyashi yake koya muna ba
saboda Allah yake taimakon mu.

    Yanzu yaya za ayi
hannatu ta tambaya manir din yace ai shine na fadawa mayana ko zata bashi
hakkuri tunda dama don ita yake koyar damu din don mu albarkacinta muke ci kowa
ya sani.

    Gaskiya ba zan iya
mai magana ba don ina jin kunyar hakan yanzu yaya za ayi don gaskiya ni namafi
fahintar shi akan malaman nan wallahi.

   Hakkuri zatayi ta
sameshi da sauri nace dasu but not now don na fada maki bana jin dadi yau gida
nake son naje na dan kwanta.

  Manya ke nan yadda
kikeso haka za ayi indai har zaki roka muna shi din nace naji na kalli hannatu
nace muje don tare muke fita daga makaranta wani lokaci yanzu tunda muka dan
saba da ita.

    Ban samu ganin shi
a rana  ba sai bayan kwana biyu ga matsin
da yanzu nake gani a wurin mama yafi nako wani lokaci.

   Don yanzun yakai
mama ta rufe damu har ummah ta dauki gaba tanayi damu wanda mu bamu san dalilin
hakan ba garemu .

   Tundai dawowan ta
lagos hakan ya fara don sun dade a can sai su Rukkaiya da yan aiki ke part din
ta ita Aisha daga baya tazo tabi mama da suka dawone ta fara daure muna gaba
daya.

    Sai kuma da Abban
mu yazo shine har yakai ko muna gaida ita zata nuna muna bata jiba kawai ta
kyale ganin haka ummah tace mu kyale ta ida
mun ganta dai mu dinga gaida ita koda bata karbawa.

    Sai hakan ya dinga
damuna tunda ba,a saba hakan ba a gidan namu don akwai lokacin dana sameta
falon Abba suna tare na shigo bansan tana ciki ba na gaida Abba kafin na juyi
na gaida ita.

  Ta kyaleni Abba yace
mata bakiji bane ana gaida ke tace konaji me zance da ita badai diyana suna
gaidani ba to ai Alhamdullahi.

    Wani irin zance ne
wanam kikeyi haka maimuna tace zancen gaskiya yanzun ne a gabanka zatace zata
gaidani yarinyar da gani gata take wucewanta yanzu kamar bata ganni ba.

    Da sauri na dago
kai na kalleta kafin na daga ido na kalli Abba din yai min alama da hannu na
kyaleta nace mama kiyi hakkuri son Allah.

    A, a wanan ya rage
gareku fa keda uwarki ni dai nasan ba zaku tsunci komai a gareni ba in kuma
karyane mu zuba nidaku a gidan nan a gani murmushi naji Abban yayi ya dago yana
fadin maamah ya akayine kuma , ?

   A, a dama na dawo
naga motarka kana gida na shigo in gaida kai yace to nagode ai ina nan zan kwan
biyu tare daku nasan dai shikikewa karna wuce bamu haduba nayi murmushi na mike
nace mu wuni lafiya na barsu tare tana jan tsuki.

  Irin wanan abubuwan
suke damuna yanzu har nake dan rama zuwan Abban namu yasama na mace da zancen
neman shi muyi maganan sai gashi mun hade dashi ya fito sallah mu kuma muna
zaune su hannatu na hira ina duban wayata hannatu ce ta zungureni take nuna min
shi tana fadin.

   Ga Master namu can
fa sarkin ka,ida waifashi da gaske guy din nan keyi yayi fushi damu ke nan ba
zai koya muna ba daga abin arziki saiya zama muna dan kari kuma ?

    Hannatu ku dinga
yiwa mutane adalci mana don kowa akaiwa haka zaiga an raina mashi wayaune fa na
fada ina mikewa zuwa wajen shi.

   Da alama sauri
yakeyi lokacin amma yana ganin na nufoshi ya dan rage saurin da yakeyi da ganin
shi kaga irin daliban nan yan ba ruwan mu karatu ya kawomu .

   Kayan jikinshi da
nake ganin irin wanda basu shiga din nan bane a cikin kayan da yake sayawa ya
saka abinshi hakana kodai kodai dasu ya saka abinshi a jiki.

   Na karaso tare da
fadin brother ina wuni yaja ya tsaya tare da dab gyara tsayuwan shi kayi wuyan
gani fa na fada.

    Ya dubeni da
kyawawan idanun shi yace abubuwane sukai min yawa kwanan nan kisan tallaka baya
zama wuri daya ai ina nan ina can ko yaushe.

    Kodai fushi kayi
kan zuwan ba zata da mukai maka don Allah in hakane kayi hakkuri munyi kuskure
hakan ba zai sake faruwa ba  in sha
Allahu.

  Suma din abin ya
damesu a yanzu tun days ago sukace na baka hakkuri dan Allah ban samu ganin ka
bane sai yau din nan don Allah kayi hakkuri.

  Yace babu komai ni
zuwan ku don baku ganni ba kwana biyu yayi min dadi saidai dawainiyar da kukasa
kanku shine ya dan sosa min rai don zakuzo wurina shine sai kunyi wani
dawainiya irin haka ?

  Nace haba ba don
wani abu bane mukai hakan niya alheri kawai sukayi ma don sun rasa me zasuyi
mane su dan rama alherin ka garemu.

   Yace toh nagode
amma next time don Allah karku sake irin hakan nayi murmushi tare da kallkn shi
nace su dai amma ni ai dan uwana nayiwa koka manta kai yayanane kuma ?

    Yace ta nan zaki
fito min kuma zarah to ai nine yayan ni yakamata nayi maki bake ba nace a yanzu
nice din dai zan tallafawa yayan nawa ko zai daina shiga rana haka cikin
wahala.

   Kai wanan ashe kina
magana irin haka nace ai dole master yayi fushi da daliban shi su kuma sun
sakani gaba na roka masu kai ?

   Su hannatune daga
bayan mu suke fadin master muna gaisuwa baka jimu ba wanan uwar kwarkwasan ta
dauke maka hankali da surutu.

    Shima murmushi
yayi tare da fadin kanwar tawace kuma kuka radawa wanan sunan mai kama data
wata babban mace can ?

   Suka kwashe da
dariya tare da fadin afuwan master ita dince ta faye jiji da kai da wuya kaga
ta tsaya irin haka tana magana sai taga dama irin wurin ku manya.

  Haka muka dan taka
dashi har zuwa inda zamu shiga building din mu shi kuma zai shiga nasa lokacin
ne na dan juyo ina fadin a gayar muna da kaka ya danyi murmushin gefen fuska
yana fadin zataji itama tana tambayana ku .

   A haka muka kara
shakuwa sosai dashi har yakai nice yanzu nake aje mai kudi idan ya tara
shakuwan mu har ya zama mutane sun fahinci da muna tare dashi sosai.

   Sai dai basu
fahinci meye a tsakanin mu ba saidai sunfi daukan abinda irin shakuwar dalibai
din nan ne na karatu nake karuwa dashi shu kuma yana dan samu daga gareni don
ganin canjin da sukayi a garseshi yanzu.

Leave a Reply

Back to top button