Hausa NovelsInda Rai Hausa Novel

Inda rai 26-27

Sponsored Links

*INDA RAI…..*

*By*

*MARYAM ABDULLAHI*

( Oum Shaheed )

*Daga ƙungiyar, koda ƙuɗinka….*

*MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION✊*

*Page 26 – 27*

ƘORAFI YA KARƁU SISTER’S, ZAN ƘARA YAWAN IN SHAA ALLAH

 

Daddy bai zarce ko’ina ba sai bangaran Mommy, bai samu damar sallama ba yasa ƙafa ya buga ƙofar ta buɗe ya shiga kamar wanda ya zare. Mommy dake zaune ta rafka uban tagumi gaba ɗaya abun duniya ya dame ta, a rikice ta ta ɗago domin taga waye mai wannan aikin, karaf idanunta suka sauƙa cikin nasa, yau ya bar suffar Daddy ya kuma Alhajin yara sak babu alamar tausayi ko ɗigon imani a fuskar, wanda alamu ya nuna dafin da zuciyarsa tayi ne ta dafa masa fuska ta nuna luguf. “Lafiya kuwa Alhaji.?

“Zan aurar da Imran rana ita yau, akwai mai son shiga rayuwata, sai dai da’alamu bai san waye Auwalu Ocu Kalala ba, amma zan nuna masa kalata.

Tunda ya ambaci kalmar zai wa Imran aure Mommy ta gama firgicewa, ita duk a tunaninta zuwa yanzu baya duniya, toma wai, anya likita ya masa allurar da yace,? shiyasa tun farko ta so ace ayi komi a asibitin a huta amma yace mata akwai matsala a yin hakan, zai dai masa allurar da zata dinga kassara shi a hankali. “Ina miki magana amma kin mai dani banza, tsawar da ya daka mata ne yayi silar dawowarta daga tunanin da ta’tafi, “Alhaji taya zaka masa aure a halin yanzu,? bayan kasan bayi da wani cikekken hankali, ga matsalar shayeshaye, a gaskiya ban goyi bayan wannan auran ba. “Kuma ya zama dole ki yadda, na faɗa miki ne saboda ina so ki shiryamini kayan lefe na gani a faɗa, zuwa jibi kibawa ƴan uwanki su kai, kafunnan zan gyara masa gidansa, idamma ba’acan zai zauna ba sai ya faɗamin na saya masa a’inda duk yake so, dan bazai zauna mini a gida ba, yana gama faɗin haka yasa kai dan komawa asibiti yaga sanyin idaniyarsa, kuma yana fatan idan yaje ya samu komi yaza ma normal.

Baki a sake Mommy ta bisa da kallo, akwai gagarumin aiki a gabanta tabbas, taya zata bari Imran yayi aure? hakan na nufin matar ta haihu kenan sun mallake gidan gaba ɗaya, ita da ɗanta sun tashi a tutar babu, waya ta ɗaga ta kira Ammin Sahla ta faɗa mata komi, nan suka tattauna ta yadda zasu hana faruwar hakan.

Yau tun safe Imran ya ka sa aika ta komi, kwance yake babu abun da ke ɗagasa sai sallah, lokaci lokaci yakan tashi ya ɗan sha fura kaɗan, yanzu ma yana zaune rumgume da pic ɗinta a ƙirjinsa yaji wayarsa dake yashe a gefa ta ɗauki sunwa, kamar bazai ɗauka ba amma jin kiran babu gaggautawa yasa shi ɗaga wayar ba tare daya duba ba, daga can ɓangaren yaji muryar Daddy cike da kulawa yana shaida masa yazo farlou yanzu yana son ganinsa, “okay Dad” ya katse kiran ya tashi jiki a sabule ya nufi cikin gidan.

Zaune ya same su shida Mommy suna magana kamar kuma ran kowa a ɓa ce yake, samun waje yayi kusa da ƙafafun Mommy ya zauna ya ɗaura kansa akan kafarta, gaidasu yayi murya a shaƙe kamar ammasa dole, Mommy jin yadda ya kwanta mata a ƙafafu sai da taji kamar ruwan dalma aka zuba mata a ƙirji har sai da ta rumtse idanu.

Gyaran murya Daddy yayi kafun ya ɗaura da cewa. “wato Imran abun da yasa kaji na kiraka magana ce mai mahimmanci, a jiya na yanke shawarar haɗa ka aure da ƴar wajan abokina, kuma banaso a ɗauki dogon lokaci, shiyasa na yanke ɗaurin auran nanda sati mai zuwa, idan kana da wani tsari naka da abokanka sai ku je ku tattauna, sannan wajan zama, idan a can gidanka zaka zauna ka faɗamin, idamma wani wajan kakeso duk inajin ka yanzu, saboda banida lokaci.

Tunda ya fara maganar Imran yaji zuciyarsa ta tsaya cak, kalmar aure ta daki zuciyarsa sosai, jin kalaman sa na ƙarshe da yadda yaga Mommy ba ta saka baki a zan can ba yasa shi tabbatar da batason wannan haɗin,maida idanunsa yayi kan Dad ɗinsu, a hankali kamar mai ciwon baki ya buɗe baki yace. Daddy banason aurannan, idan ganina babu aure yasa ka yanke wannan hukuncin to kabani lokaci zan nai m… “dakata! Daddy ya katse sa, bawai ba nakira ka bane domin jin wata magana ko ƙorafi ba, sannan ba shawara nake baka ba, umar ni ne, dan haka tashi kaje, kuma ina jiran amsarka ta gurin zama, zan kiraka nan da minti talatin naji, “bama sai ka kirani ba Dad, zan zauna a gidannan a part ɗina, da wani irin kuzari Daddy ya miƙe har sai da abun ya basu mamaki, “ba zaka zauna a nan ba, akamme, ba zaka takurani ba, Allah ya horemin dan haka ba zaka zauna kana samin ido ba, fuuuuuu yaja gare ya wuce patr ɗinsu.

Da kallo duk suka bisa kowa da kalar tunaninsa, a ɓan garan Momy tasan lalle akwai wani gagarumin abun da ke faruwa, shi anasa tunanin dan yaɗau lokaci babu aure ne, da mamaki ya maida kallonsa kan Mommy, a dan dole ta masa murmushin yaƙe ta wuce ta barsa tsaye zuciyarsa fal zargi.

Abee ya kamata ka sanar mata wannan maganar, a ganina babu amfanin ɓoyewa tunda ba fasawa za’ayi, gani idan har masu kayanan suka iso ba tare da sanin ta ba mun mata adalci cewar Mimi da kwance a ƙirjin Aminu. Dogon numfashinya sauƙe tare ƙara shigar da ita jikinsa na shaƙar dadda ɗan kamshin dake fita a kanta, maimakon ya bata amsa sai jita yi ya mirgino suna fuskantar juna, ƙuruuu yake kallonta kamar yau ya fara, gani bazai jure ba yasa shi saka hannu ya tallafo kanta ya fara bata wani zazzafan kiss, daganan suka faɗa wata duniya mai fiffike sai fatan Allah ya fito dasu lafiya, lol.

Farin ciki ne sosai ya bayya na a fuskar Daddy jin cewar cikin ya fita, wato anyi nasarar fitar dashi ta ƙarfi, rumgume likitan yayi yana mai nuna farin cikinsa a fili, wanda hakan ya fara sakawa doctor ɗin shakku da tunani, kuma yaji kamar ance matar ɗansa ne, toma ina ruwansa shikan,? tunda an biyasa haƙƙinsa, sai dai ya tausayawa yarinyar da mijinta gaskiya.

Leave a Reply

Back to top button