Cinikin Rai Book 2Hausa Novels

Cinikin Rai Book 2 Page 39

Sponsored Links

39- “Nice Daadi Malik!” Wani irin takaici ne ya kama shi, ya kura mata idanu. “Me yasa Nadrah?” Hawaye ne ya zubo mata. “Saboda Abbana!” Kura mata idanu yayi, yana sauke wata numfashi “Ok muje naji domin Abbanki kika yi, babu me miki kome muje!” Ciro wuka tayi zata yanke shi. “Me yasa..” wani irin ƙara yaji a tsakiyar kanshi. Wanda ya tilasta mishi faduwa babi shi. Domin baki daya ya dauke wuta, wasu matasa ne a tsaye. “Daure min shi, na tsani mutumin nan, ke kuma kin yi abin da ya dace zaki iya tafiya.” “Shi kenan da fatan babu wani matsala ko? Domin ina tsoron kada a kama ni na rasa inda zan saka kai na, ga Abbana ban san inda yake ba!”t faɗa kamar zata yi kuka, tsayawa mutanen suka yi, sannan daya daga cikinsu ya ce mata. “Kije abinki, shi wannan karen zamu kashe shi, ai kin gama mana aiki.”
“Da fatan suna na, ba zai fito ba bana son a kamani!” Kar’ar motar yan sanda ne, ya cika unguwar, babu shi matasan suka tsalleke Malik suka gudu, sai Nadrah da take tsaye ta kasa gudu, a wannan takin ina zata? Gara kawai a kamata abin da take gudu kenan. Kuma gashi ta faɗa hannunsu. Da gudu suka shigo gidan, ganinta tsaye da wuka tana nuna Malik yasa suka dan dakata. “Kin ga ki ajiye, wukar.” Wuyarta ta kai wukar. “Ku kyale ni, ko na yanke wuyata.” Tashi dakyar Malik yayi yana rike kanshi. “me kike so nayi?” “Abbana nake so, ka nimo min!” Kallonta yayi tare da mika mata hannu. “Ba ni zan nima miki, shi i swear!” “Kace kada su kama ni.” “Shima na rantse miki babu me kama ki.” Hawaye ne ya zubo mata ta ce mishi. “Me yasa ka fasa aurena?” Ta saka wukar sosai, a wuyarta. “Daadi Malik me yasa kace ba zaka aure ni ba? Ka je ka auri street girl! Bani da quality na matar da kake so ne? Ko ban isa na aure ka ba ne?”
“Nadrah! Ki bari muje gida!” Wani uban ihu tayi tare da buga kafarta a kasa, tana faɗin. “Me yasa ba zaka bani amsata ba? Ita wancan yarinyar da me ta fini?” “Bani sai na gaya miki abin da baki sani ba!” Kallon cikin idanunta yayi, na wani lokaci kafin ya sunkuyar da kai ya ce mata. “Are taking drug’s?”
“Me yasa ba zan dauka ba? Kaina ya gaza daukar kome, da kai nake kwana da kai nake tashi, me yasa ba zaka gane ina sonka ba.” “Ok na yarda kina so, shi kenan ajiye wukar kada ki cutar da kanki, domin bana son ganin tab’o ko karami ne a jikin matar da zan aura, so nake jikinta ya zama kamar na maciji.” Sake wukar tayi, a hankali ya taka gabanta, zubewa zata yi ya tare ta. Ta kwanta a jikinshi. Tana kuka tare da dukar kirjinshi. Cak yayi sama da ita, suka fita a gidan. Kallonshi Zulfah tayi na wani lokaci, kafin ta kauda kai. Tana taya yar Uwarta kishi. “Ina ga zamu kaita asibiti sai mu saka jami’an tsaro su kula da ita.”
“A’a zan wuce da ita, gida kawai likita zaku turo min, sauran bayanan zuwa jibi sai mu bincike ta.”
“Shi kenan!” Ta fada tana barin wurin. Haushi ne cike a ranta, sai kumbure kumbure take, sai da suka wuce kafin ta tuna ta tura mishi. *AN KAIWA ZEENO HARI AMMA Allah ya tsare babu abin da ya faru ita da yaran suna gida!* Yana tuki ya gani. _Allah ya tsare_ yasan duk rikicin Zeeno akan idanunshi da gabanshi take, yayi imani da Allah, mutuwa ce zata shiga tsakaninsu da Yaranta. Da tana da hali ba zata bari wani abu ya cutar mata da Yara ba, ua yarda da matar da ya aura.” Ya kuma yarda da wacece ita, don haka ya wuce abinshi, har cikin barikin ya shiga da ita, a falon gidan shi ya kwantar da ita. Elbashir ya fito rike da cup. “wace ce?” “Kai makaho ne?” “Ba mamaki!” “Hmmm!” Leka fuskar yayi, sannan ya ce masa. “Yar shatima ce?” “A’a Shatima ne!” “Dadina da kai bakar magana, tow me ya faru?” “Ita ke turo min sakon barazana!”
“Hmmm! Kuma shi ne kake jin haushina? Tare da min sharrin ni nake bibiyarka.”
“Ai inda matsalar take, ba ita ke bibiyar ba, wani ne na daban, wanda ya san ni kwarai da gaske!”
“Tow Allah ya tsayar haka, kada a kuma min sharri domin wallahi ba zan yarda ba.” Ya faɗa in serious tone, tabe baki Malik yayi, kiran wayar Zulfah tare da gaya musu gasu tare da likita, yasa dole suka yi shiru. Har cikin gidan sojoji suka rakota, tare da wasu likitoci sojoji, suka zo ana duba abubuwan da za a mata amfanin dasu kama daga allura drip, da kome sannan suka dibi jininta.

Yadda zaka san, ana girmama Malik, a tare aka tafi da shi lab na sojajin aka gwada, na tsawon awa hudu, kafin aka dawo da shi. Amsa Dr Abdulwahab yayi yana dubawa, soja ne. “Taya yarinyar nan ta samu, sinadarin Cocaine a cikin jininta? Wanda karfinshi ya kai ya kashe mutum.” Duba hannunta suka yi, suka ja rigarta saman hannu. Fatar wuyar hannunta, ta sama har wani irin ja da kore yayi. “Me ta faru ne?” “Babu wanda ya san asalin abin da ya faru, sai dai ta ce min mahaifinta take nima! Duk wanda ya santa, tow yayi amfani da kalmar mahaifinta ko abin da yake tsakanin mu ya yaudareta ne, amma na yarda da nagarta Yarinyar.”

“Gaskiya tana da nagarta shi yasa, ni har kwnaan gobe ka ke min fatar na zama Ni ke cin amanarka!” Inji Elbashir da yaji haushi. “Bashir wannan ba abin wasa ba ne!” “Abin wasa ka dauki magana ta? Ko ka ga na maka kama da me wasa? Kasan yadda nake ji kuwa idan kace bakan yarda da ni ba? Is killing me insane. Karfin hali nake domin wata rana zaka gane, haka ka daina zargina. Bana kaunar ko ciwon kai ya same ka. Amma kai dake dan ku…”
“Jama’a kun ga zagina Elbashir yake, har na kai ka zage ni?” “Eh na zage ka, wallahi ka kuma zargina tafiya zan yi ba Barka, sannan ka mikawa hukuma yarinyar nan, domin bata da wani amfani a wurinka. Idan na kuma ganinta sai na kira Zeenobia na gaya mata ka fara kwashe-kwashen mata.”
Abin dariya ya bawa su Zulfah, saboda rigimar kamar ta yara, “Yanzu Zulfah me ake ciki!”
“Hey! A fitar min da yarinyar nan, a gida domin bata kuma zama ayi maza waje da ita.”
“Heey hey!! Babu inda zata, na gaya maka zama zatayi domin aurenta zan yi?”
“Kutumar uba?” Elbashir ya fada. “Billahi Azim baka isa ba, aurenka da Zainab mutu karaba, duk shegen da ya gaya maka zaka kuma aure ya gaya maka karya ne, don ubanshi, kuma na gaya maka Zainab ta cinye kome naka, yara uku ai baka da kome a cikin dukiyarka ita da Yaranta suke da iko da shi.”
“Tow kuyi fatan na mutu mana, sai ku raba dukiyar da hujja!” Ai kuwa rigimar gaske , aka yi kafin kuma aka ajiye Maganar a gefe. “Elbashir zaka tafi Nigeria, kai da matarka. Kayiwa Yaran huduba, macen ka saka mata sunan Maidah, mazan ka saka sunan mahaifina da na Zainab!”
“Na me zaa saka sunan Maidah, kana nufin.” “Kayi yadda nace, ina sane nace haka!” “Shi kenan Malik!”
“Ita wannan yar kwayar fa?”
“Aurenta zan yi!” Malik ya fada babu wasa a kalamanshi. “Me yasa to?” “Saboda idan na barta tana watangaririya a gari, wani zai kuma amfani da ita, idan na aureta babu me sauya mata tunani!”
“Amma Yallabai Zainab ba zata ji dadin haka, zata ga kamar mun boye mata ne. Gaskiya ba zan iya daukar wannan rigimar ba.”
“Hmmm! Nima haka nake ji, haka nake ji amma for sake of my family, har da ita Zeeno saboda ita, da Yaranta. Ba don rayiwata ba. Idan na bar Nadrah ta fita a hannuna ban san waye zai kuma sakata a cikin yanayin fansa ba. Kin san kaifin Fansa kuwa? Yafi wuka kaifi don Allah ku fahimce ni.”. “Idan matarka kake bukata, ba sai mu tafi Nijeriyar da kai ba!” Murmushi yayi yana kallonshi. “a duk inda haka ya taso, dole cikin biyu ayi daya. Imma ka hakura da kome ka rungume ƙaddara imma ka amshi kome a zauna lafiya, a halin da muke ciki da Zeeno bata gaya min matsayina na mijinta tana son zama da ni bata son zama da ni. Zainab ta ajiye ni ne, domin na jira kiranta. A wannan lokacin matukar ba ita ba ce, ta nemi ni ba zan tab’a kai kaina gare ba, kun san yadda zaman jira yaƙe? Koda kuka gaya mata na mutu, ya kamata ace ta kira layina taji da gaske ina raye? Amma dake mace ce, ba zata kira ni ba. Sai lokacin da wani abu me karfi ya tab’a ta, a nan ne zata nime ni, a lokacin ni ma zan tafi da kwarin gwiwata.

Amma a halin yanzu ba zan tab’a kai kaina gare ta ba, domin ina iya zuwa ta min wulakanci, na san wace ce ita a banza zata min wulakanci a gaban uban kowa. Tow ban da mace wacece zata maka haka? Musamman aka yi katari kana sonta kamar yadda kake son kanka, ai magana ya kare. Sai ayi ta juya ka kamar dan duros.”
Me zasu yi ban da dariya, domin maganar Malik akwai abin tausayi, amma kuma abin dubawa ne, tunda ya tona damuwar da take ranshi, haka yana nufin yana matukar azabtuwa da matsalar shi da Zeeno, sannnan gefe guda yana jiran ta kira shi, kiranta kawai yake jira, da kira daya zata gyara wasu abubuwan. Amma har yau bata kira ba, shi kuma bai ji a ranshi ya nime ta, tunda yana jin labarin halin da take ciki.

Da wannan bayanin aka rufe kome, sai dai akwai binciken da za ayi wa Nadrah, wanda dole yana bukatar sai ta nutsu, idan bata nutsu ba, dole haka zata kaita ofishin yanda, su kuma su turata ga kotu . Yarda da tayi da Malik yasa baki daya, take jin zai aureta, kuma zai kare ta daga duk wani abu. A bangaren Malik kuwa, shirya Elbashir da Matarshi yayi suka tafi zuwa ganin Zainab, wani abin mamaki kuwa yadda yayi ta sayayyar da za a kai musu, kome ya saya sai ya raba biyu. Ya ajiye rabi, “su kuma rabin na meye?” Elbashir ya tambaye shi, yana kallon. “Na matarka!”
“Ce maka nayi tana da ciki?” Lumshe idanunshi yayi ya mai da shi kan Elbashir ya ce masa. “Ni dai naga al’amarin nan gaba, sai na ci dan banza duka a hannu ka.” Dauke kai Elbashir yayi yana faɗin. ” Ka ga ni bana son sharri, babu dukan da zan maka, kawai dai nasan bata da wani ciki. Idan kuma akwai tow daren jiya aka same shi!”
“Koma meye na dai saya, idan bai maka ba. Sai ka watsar da shi.” Ya faɗa tare da ɗaukar wani takalmin Yara, musamman na jarirai. Ya jida kaya kamar bai san ciwon kudi ba, sannan suka je aka biya kuɗin suka nufi gida. Lokacin da suka isa sun samu Nadrah a wurin wanka, dauke kai suka yi, domin baki daya yarinyar tana masifar attempting ɗinsu. Musamman yadda take sexy dress. Jiya sai da aka kai ruwa rana da Hafcy da Elbashir, wasu irin karuwan kaya ta saka sannan ta zo ta tsaya mishi a kai.
Wai ya duba mata, meye ya samu wayarshi. Dauke wuta yayi, suna tsaye sai ga Hafcy tana ganinta shine na mata ya motsa, ta ture ta waje, tana faɗin. “kin kasa auruwa ne kika zo zaki lalata min mijina, mayya mara kunya kada na kusa da miji.”.
“Hafsat me haka?”
“Meye kuwa bayan abinda idanunka ya gani, kai kuma ka tsaya kana kallonta, tsirara ne bana yawo a cikin gidan nan, tun dare kafara surta har tsakiyar dare, ba barina kake ba, shine har akwai wata karuwar da zata burge ka wallahi sai na kashe ta….!”.
*Arewabooks iya book 2 da three*
*Assalamu alaikum……! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A’ishah. +227 84 50 64 76 500*
[9/27, 10:26 PM] Yan Mata:

 

 

Leave a Reply

Back to top button