Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 3

Sponsored Links

Chapter 3

__”Anna bani kuɗin naje nayo mana cafene muma yau ɗaya muci mai daɗi,yanda nakare maganan da ɗan ihun murna yasa suma ƙannena tayani ihun murnan jin nace zamuci mai daɗi wato khadiza da mubaraq ita de Anna sake baki tayi tana kallon irin taɓarar da nake kaman wata yarinya karama.

Muna cikin yin ihu wani yaro yashigo gidan namu da sallama amsa masa mukai kasancewar zaune muke a tsakar gida”wai ana sallama da Aisha zuciyana ne yafara dukan uku²da jin abunda yaron.

Cikin rawar baki nace”kai kaje kace banan bane gidan,har yaron ya juya zeyi ficewarsa yasa Anna cewa”kai jekace gata nan zuwa,yaron yafita rau rau nayi da ido kaman zanyi kuka kauda kai Anna tayi daga kallona tace”zama tashi kije kiga ko waye?amma de kinsan ba kyau wulakanta mutum dan ɗan adam darajane dashi”amma Anna aini ba wanda mukai dashi ze…katsane ni tayi da cewa haba Aisha yanzu sai wanda kika kasani ko yasanki shine kawai zai iya turowa amiki sallama yau naga ikon Allah kinga maza tashi kije kigani sai kizo kuwuce islamiya kinga lokacin tafiyanku yayi.

Badan naso ba,haka namiki na saka hijabina nariko hannun mubaraq muka doshi kofa,tunkan na karaso ya tsareni da mayun idanun sa yana mai sakin murmushi,haɗa giran sama da ƙasa nayi danma karya kawomun wargi.

Ahmad
Wanka yayi yafito ɗaure da towel a ƙugunsa yana goge jikinsa da ɗan karami wayansa dake burari yakai hannusan ya ɗauka ganin mai kiran nasa yasashi sakin guntun murmushi yana kai wayan kunnen sa”kaifa ɗan iskane wallahi in kasan bazaka tafi ba ai saika sanar dani dawuri dan bazaka ɓatamun lokaci ba ehem.

Suƙe fuska yayi cikin hocky voice ɗinsa yace”to ai sai mutum yakama gabansa idan na son gulma ba ai nima nasan hanya mtsss yakare magana yana jan guntun tsuka”dariya akai daga ɗaya ɓangaren ana cewa”eh son gulmar dama shiya tsaidamu oya kai maxa kafito gamu a falo muna tare da mama”khalid ya ambaci sunan cikin sanyi’na’am yason ranka malam kayi mamakine to karkayi kasan lamarin tuzurun abokina dole nabashi mahimmanci idan ma wankan naka beyi ba sai nasa kacanzo dan karmuje babin daddy taga tsofanka tace bata sonka,dole yayi ɗan dariya dan yasan halin khalid”meyasa baza shigo nan ɗin ba dot?”ina tare da mamata tana bani abinci ya amsa masa agajarce.

Shaf shaf yashirya yana fitowa daga ɗakinsa khalid nasa kai tsaye khalid yayi yana karewa ɗakin kallo yanda ya hargitsa komai”mutumina gaskiya kana bukatar aure da wuri kodan kasami mai gyarama daki dan Allah kalli yanda ɗakinka yake ka kuma kalli kanka ta madubi idan kafita wajene kawai kake guy amma gaskiya wannan ɗakinaka um um.

“Kai ɗan sa idone khalid ina ruwanka da makwancina in banda rainin wayo,kasan Allah har yanzu har yanzu banga macen da tayi daidai da rayuwata ba,kaga kowannan ɗin zan jenine saboda banaso mama tasami matsala da Alhajinta idan ba haka ba wallahi ba inda zani.

Raƙe haɓa khalid yayi yana kare masa kallo danson tabbatar masa kai ya jinjina masa,hmm”kai ko wacce irin mace kakeson ka aure?nagade ƴan mata zuƙa zuƙa kaman su sukai kansu kawo maka tallan kansu sannan ga waƴanda ake kawo makasu daga waje ma bambanta kade tsaya ruwan idon kazaɓo mana wata bagidajiya.

Murmushin gefen baki yayi sannan yafara takawa a hankali yace”inason takasance bazata ji shakku ko tsoron wani ba matukar akan gaskiyarta ne,sannan takasance mai hakuri dakuma ɓoye sirrin gidan su wacce abun duniya be tsone mata ido ba,mara ƙiwa wacce ko karfe ɗayan darene idan nace coffe zata tashi ta dafomun kafin natashi daga bacci an haɗamun break fast ɗina sannan ta haɗamun ruwan wanka na.

Tafi kawai khalid yasoma yimasa dan yaga yanda abokin nasa yazage yana ta karonta masa halin macen da yake so kaman a littafi”karon farko a rayuwata naji kayi maganan halin mace saide baka faɗamun yanda tsarin ta ze kasance ba,saboda tsaro ba tsoro ba kaga sai na riƙe matukar gana mai irin hali dakuma yanayinda ka zaiyano sai… Duka Ahmad yakai masa yayi saurin gaucewa yana masa dariya.

 

Wannan littafin mai suna a sama na kuɗine dazaran mun gama free page zamu sanar daku yanda zamu biya kuɗinku #300 kacal zaki biya ƴar uwa dan kikaranta.

ALLAH YASA MUDACE
[5/2, 8:34 AM] Xeenat: 💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

Na
Zahra Ali Abdullahi

Bismillahir rahmanir rahim.

 

Leave a Reply

Back to top button