Bakar Ayah Hausa NovelHausa Novels

Bakar Ayah 32

Sponsored Links

Page 🖤32🖤

 

Hamma Hajiya zeenah tayi tareda kallon muruje wanda yakai karshen labarin dayake basun.
Kuɗi ta ciro daga cikin purse ɗinta ta miƙamasa tareda yimasa godiyah.
“Mun gode da wannan labarin daka bamu,koba komai yanzu munsan mai yake wakana,mu bari mutafi gida,yamma tayi bazamu hau cikin jejin yanzu ba”
Zaro ido muruje yayi tareda cewa.
“Hajiyah wai har yanzu baki haƙura da zuwa wajenta ba,bazan tambayi mai kike nema ba a wajenta,nagode ni bari na tafi”
Fita muruje yayi daga cikin motar yakama gabansa,yabar su Hajiya zeenah cikin nazari.
Iliyah ne yakalli Hajiya zeenah tareda cewa.
“Hajiya gaskiyar wannan ɗan yaron fah,kinaga bazamu hakura dazuwa wajenta ba kuwa,ni aradu bana fatan ma nahaɗa hanya da ita tunda naji labarinta,batayi kama da wacce wani zai haɗa hanya da itah,kinaji fah ko iyayenta ma ba a bakin komai duke ba a wajenta”
“Kai rufemin baki,dama kaine kasakani zuwa wajennan komai,rashin mutuncinta danaji dama shiyasaka nazo nemanta,dan naji labarin hakan bashine zaisa na janye daga kuɗirina ba,saidai idan itace da kanta taƙi amincewa da buƙatata”
Daga haka iliyah bai sake cewa komai ba yaja motar suka bar anguwar su Bombee zuwa gidan su Iyani.
A hanyar sune ta dawowa Hajiya zeenah ta kira Jabeer.
Yana zaune sun gama hayaniya da lubna idonsa a rufe ya jiyo ƙarar wayar.
Da kaman bazai duba ba saikuma yaga an rubuta “Mommah”
Sallama yayi,tun kafin ta amsa sallamar tafara faɗamasa dalilin ƙiran.
“Jabeer shin private plane yana nan kuwa?”
“Ehh yana nan hajiya,ban fita ko ina na ina nigeria”
“Toh karka fita dashi nan da sati,dan zan kiraka a cikin satinnan azo a ɗaukeni a Gembu”
“Gembu kuma,dama can kikaje,wajen wa kenan?”
“Uhmm naje yin wani abune wanda zai taimaki rayuwarka,Aure zan yimaka wanda sandiyyarsa zaka rabu da wannan jarababbiyar matar taka,sannan idan nadawo ma zamuyi magana.
Zaka koma ainihin Side dinka na gidan,zaka barwa su Abdulmaleek wajensu”
“Amma Hajiya naga basu tashi aure ba,sannan kuma wancan side din ya fiye girma dayawa sannan yayi ciki kaɗan,sannan………”
“Sannan me Jabeer bazanyi abinda zai cutar da rayuwarka ba,yarinyar nan baka buƙatar sakata cikin rayuwarka,zatazo ne domin kawar da lubna a rayuwarka.
Bangama tsaida abun ba tukunna,zai iya yiyuwa a fasa,yansu dai jirgin nafi buƙata a ready idan zan dawo,dan bazan sake bin wannan hanyar ba karna mutu.
Komai yafaru zan ƙiraka ko abbanka gobe”
Tana gama faɗin hakan ta kashe wayar.
Ɗan murmushi yayi yana kallon sunanta a gaban wayar tasa,yayinda cikin ransa kuma yacika da matuƙar kaɗuwar jin abinda mahaifiyar tasa take shirin yi.
“Hmmm dama kina tsoron mutuwane Ummah….kai Allah ya kyauta.
Daga nan side ɗinsu yawuce wajen abbansa,saboda ƙarajin labarin a wajen,dan yasan bazai rasa sanin mai yake wakana ba.

______*****______

Biron dayake hannunsa ya ajiye,ganin yayi kusan minti talatin amma yagagara yin signing ɗin da bazai daukeshi sakanni ba,saboda yawan tunani dayake fama dashi a kodayaushe.
Ƙarar bugun kofar da akayi ne yasashi jefar da biron akan paper tareda jan ɗan ƙaramin tsaki.
“Banda kaima kasake ɗoramin wani tension din,a tunanina dai baka buƙatar saina cemaka ka shigo koh?”
Cikin kasala yayi maganar kamar shima buɗe bakin aikine a gareshi.
Khaleel ne ya buɗe ƙofar ya shigo yana murmushi,akan kujerar datake kallon table ɗin Jabeer ya zauna.
“Mai ya farune mutumina,yanzu kullum haka ake ganinka,yakamata fah kaga likita idan wani abune yake damunka,An tafi wata uku da mutuwar Hafsa amma kaƙi barin lamarin a cikin ranka”
Ya mutsa sumar kansa yayi tareda fesar ɗa iska,dan jijjiga kai yayi alamar shima kannasa ciwo yake yi masa.
“Hmmm Khaleel ba iya wannan ne matsalata ba,inaga Hajiya so take takasheni tun kwanana bai ƙara ba,nifah inaga bata kallona mutum,tafi tunanin ni robot ne”
Ƴar dariyah Khaleel yayi jin furucin abokinnasa,wanda bazai ga laifinsa ba akan maganar kam,dan ko mahaukaci ya kalli Jabeer yasan yana cikin yanayi na buƙatar hutu ba kaɗan ba,sannam kuma yanada buƙatar wanda zai kwantar masa da hankali.
“Menene yafaru kake wannan furucin Jabeer,komai zai faru kasan Hajiya mahaifiyar kace,sannan kuma kasan bata nufin ka mutu ta kowacce siga”
“Hmm baxaka gane bane,kasan yanzu zancen danake maka kwananta uku kenan bata gida,wai tatafi yimin aure a can gembu,ka duba yanayin danake ciki ban gama warwarewa da mutuwar matata ba,ga ita wancar har yanzu nagagara jin daɗinta dama,yanzu kuma ta tafi can uwa duniyah zata auromin wata,wadda ni bansan ma ita mai zan tarar a gareta ba.
Kuma wani abin tashin hankali ma Khaleel,auro waccar ɗin fah dan na auri Jawaheer ne fah?”
Zaro ido Khaleel yayi jin abinda Jabeer yafaɗamasa.
“Jawaheer kuma,ehh nasan yarinyar tana sonka kam,amma banyi zaton dagaske abin yake ba”
Ƴar dariyar takaici yayi kafin yaƙara da cewar.
“Khaleel kenan,to tunda aka haifi Jawaheer Hajiya rabi tabani ita,rashin aurenta da banyi ba saboda suna tsoron kar lubna tayi mata illah ne,yanzu kuma idan suka auramin wata anan zasu samu hanyar yanda zasu saka Jawaheer a gidana”
“Tohh gaskiya abinkan ba ƙarami bane,toh amma kai taya kasan hakan dukka”
“Jiya ta ƙirani take faɗamin wai na shirya jirgi za’aje dakko ta a gembu.
Abin yabani mamaki,akan mai takeyi a gembu,nan take faɗamin wai aure taje yimin,kaji fah irin wannan zancen Khaleel,dan ta sameni mai yimata biyayya akan buƙatarta,bai kamata kuma ta dunga yin biriss da abinda zuciyata keso ba”
“Eh to hakane,amma kuma kacigaba da haƙuri,inshaaallah biyayyar dakake mata ma bazai bari ka dawwama a cikin wannan halin ba,inshaaallah allah zai kawo maka mafita”
“Ba wannan ba ma Khaleel,karka manta bafah iya anan abin zai kareba idan ta kawo wannan. Duk neman mafita ne na yanda Jawaheer zata zauna a gidana,nakasa cire tunaninnan a raina tun daren jiyah”
“To a ina duk kaji wannan ne,zai iya yiyuwa ita Hajiya kawai Lubnah ce bataso a cikin rayuwarka,ka rabu da itamana kawai,ni inaga Jawaheer ɗin ma tafi maka lubanan”
“Inda zan iyah sakin Lubnah da tuni na rabata da rayuwata kodan saboda sabanin danake samu da dangina akanta,amma abin ya ci tura duk iya koƙarin danayi. Hmmm Jawaheer din ma dakake gani ba kanwar lasa bace wajen rashin daɗin zama,tsawon rayuwarta ba’a cemata tayi tayi,taya kake gani zan sakata abu tayi,ko kuma zatayi wani abun amatsayinta na matar gida. Sai uwa uba ita wacce ake shirin mannamin banma santa ba kwata kwata”
“Uhmm kaman kace Hajiya tafaɗamaka zaka koma Ainihin side ɗinka,meyasa kenan”
“Baka san meyasa ba,saboda yana babbane yana ɗauke da Side guda huɗu,tana shirin yimin tanadin zama da mata uku,shiyasa ta buƙaci nakoma can”
“Mashaallah nabaka wata shawara mana?”
“Hmmm wacce shawara ce zatayi maganin wannan abin dayake shirin tunkaroni a yanzu”
“Mezai hana tunda kace side ɗin na ɗauke da bangare huɗu,kuma mata uku take son saka zama dasu. Kaikuma saika auro kamilar yarinyar mai addini da nutsuwa wacce tasamu tarbiyya ka aura,kaga idan sun kunna maka wuta zaka samu wajen zuwa a kwantar maka da hankali”
“Hhhhhhh amma Khaleel yau na yarda kai mungune,ina koƙarin janye jikina daga wanann matan kaikuma kana shirin ƙaromin wani bala’in,kajanye wannan shawarar tun batayi nisa bama”
“Nizan tafi Jabeer Allah yakawo maka sauki akan lamarin nan,amma dai kayi tunani akan abinda na faɗamaka,inaga idan kasamu wata yarinya a rayuwarka kaman hafsa abin zaizo da sauƙi,koda wancan din suna nan”
“Hmmm naji abinda kace,yi sauri ka fita ka bani wajen Khaleel,nakula bazaka gane yanakeji ba”
Jijjiga kai Khaleel yayi ya fita a office din,cikeda tausayin abokinnasa wanda yagamu da Jarabawar mata a rayuwarsa.
“Nakaro aure bayan waɗannan……….kai wannan ba shawara bace ma,gwanda nacireta cikin raina kawai”
Daga haka shima ya tattara shirginsa ya bar companyn ma gabaɗaya,bai koma gidaba wata hanyar yakama zuwa wani wajen daban,wanda yake ɗaya daga cikin sirrinsa da yabarshi a iya saninsa kaɗai sai mahaliccinsa.

_____*****______****_____

A bangaren su hajiyah zeenah bayan sun karya suka fito daga cikin gidan su iyani.
Ƙaryah sukayiwa mahaifiyar iyani,dan idan tagane Daji zasu shiga inda gidan Bombee yake,koda wasa bazata barsu su shigaba.
Key iliyah yayi wa motar,amma kuma baisan ina zai dosaba daga haka.
“Hajiya ina zamu nufah daga nan”
“Meyasa kake tambaya ta,nima nasani,nansan kuma da wuyah a samu wanda zai rakamu wajen cikin garinnan”
“Ahh Hajiya ranar da muka shigo Toro yabamu number sa akan ko zamu koma zai maidamu”
“Mezamuyi da wannan yaron kuma yanzu,ko karen hauka ne yacijeni ai bazan yarda nasake gangarawa ta wanann hanyar ba”
“Ahah ba zancen komawar ba,gani nayi kaman fah yana daya daga cikim yaran Bombee,kin manta mai gace mana,cewar a jeji gidanta yake,kuma itace shugabar kungiyar su ta BB. Kaman yayi kama da labarin kungiyarta da Muruje ya bamu jiya”
“Ehh kuma fah hakane,iyani tayi gaskiya Hajiya”
“To danna ki ƙiraman shi,yafaɗamana inda take”
Fita iyani tayi daga motar tashiga gida dakko inda tarubuta number tasa.
Sakawa tayi tareda miƙawa iliya ya ƙirashi.
“Salam ina magana da toro ne?” mune mutanen da ka shigo dasu rannan,dan Allah muna tambaya ne akan inda shugabar ku take,muna son zuwane”
Bayan ɗan wani lokaci iliyah ya sauke wayar a kunnesa yana kallon hajiyar.
“Mai yace bazai faɗamana ba?””
“Ahah yace wai gashinna zuwa yana kusa danan wajen,amma fah da alama yanace wani abu zamuyi mata,bakya ganin bazaiyi shunen mu ba a wajenta”
“Haba dai wane irin shune kuma,tun kafin Hajiya zeenah tayi magana taji bakin bindiga yana zungurar ƙeyarta ta window mota……..

Tohhh fahh🤣🤣🤣🤣

 

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

 

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

 

 

Leave a Reply

Back to top button