Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 75

Sponsored Links

CHAPTER 75

Harsuna ture ture wajen shiga kitchen ɗin ja sukai suka tsaya ganin ƙofan ɗakin abude,sauri shiga ɗakin sukai zuciyoyin su na bugawa a mugun tsorace baki na rawa Alhaji sunusi dayayi baya yana neman faɗiwa ya dafa bango kansa na mugun sarawa yace”wannan wani irin musiba ne daga wannan sai wannan wannan watan ba watan sa’ar mu bace ba,yana karasa fadin haka juyawa yayi da gudu zuwa waje yana ce kunsa fa idan muka bari wannan matar ta gudu a kwai matsala babba ma kuwa.

Ammin na zaune falo bayan ta haɗawa alhajin ta abinci yaci ta bashi magani yasha yaɗan kishingiɗa kan kugera,Ahmad da shigowan sa kenan gaishe da Abban nasa yayi tare da yimasa yajiki”amsa masa yayi a daƙile kaman wanda a kamasa dole.

Juyawa yayi ya gaida amminsa ita amsa masa tayi da sakin fuska da tambayan ya yakwana”lafiya lau Ammi ina fadwa da meena fadaɗa murmushi dake kwance saman fuskarta tayi tana cewa”kamanta yau akwai makaranta.

Dafa kansa yayi yace”wallahi kinga namance shaff kuma yau inada haɗuwa da wasu baƙi karfe shaɗaya dan ma khalid yana nan ze kula komai kafin naje.

Suna cikin magana sai ga sallamar Anty hajia da farin ciki Ammi ta tari ƙanwarta mafi soyuwa a ranta tace”irin wannan sammako haka ikilima?

Ƴar dariya tayi tana cewa “ai yau cewa nayi ba zanci komai a gida ba dake zanyi kari muna hira kina samun abinci abikina ina ci ina baki labari dariya suka kwashe a tare dan tunawa dasukai da ƙuruciyar su.

Zama tayi saman kugera tana gaida Alhaji badamasi dayayi idon fara tun shigowar anty hajia amsa mata yayi yana miƙewa zaune suna ɗan taɓa hira yace”lalle kunaji da juna keda ƴar uwarnan taki wato dan yau zakizo shine ko abincin ma ƙin tsayawa ci kikayi”wallahi kuwa ta amsa masa.

Ahmad dake zaune saman dining ne ya shigo cikin falon yace”ina kwana Anty”lafiya Ahmad dama baka fita ba ta tambaye shi tana gyara zaman ta”eh wallahi anty yanxu ma fita zanyi ya amsa mata yana kokarin miƙewa.

“Dan dakata koma ka zauna tace dashi komawa yayi yana zama,gyara zaman ta tayi ta fuskance sa sosai ta cigaba da cewa ai gwara da Allah yasa baka fita ba nazo nasame ka a gida gaka kuma ga Alhaji gwara aiyi komai a gaban sa yanzun ma karyace mu mukai.

Shima Alhaji sunusi gyara zama yayi yana kallon su da sauraron kuma dame sukazo masa wannan karon”dama nace ya maganan tarewar ita ɗaya matar taka?

Dif Ahmad yaɗauke wuta ma ɗan wani lokaci ƴawun bakin sa yakafe,ya shiga zazzara ido kaman wanda aka kama yana aikata abu mara kyau.

“Kayi shiru Ahmad Ammi tasake tambaya sa tana son su haɗa ido dashi amma yaƙi ɗagowa ya kalle ta.

“To me kukeson yace?ai bashi da abuncewa kunsako yaro a gaba kun masa auren dole badason ransa ba wannan ba ƙa’ida bace,sannan yanzu kunzo kunason yimasa dole wajen tarewa wai ku waya muku dole kan naku auren ne?eh da zama a gidagen ku….katse sa anty hajia tayi tana cewa

“A’a Alhaji ai sai kace…..kinga ikilima kike ko wace wannan magana ta ahaline..itama katsashi tayi da cewa idan ma ta hanjine ba ahali ba,to dole Ahmad ya tarewa da matar sa tunda addini ya halasta masa igiya uku nasa ya hau kanta kuma dol….miƙewa Alhaji badamasi yayi a fusace yana cewa idan ni na haifi Ahmad dole yasaki wannan yarinyar idan ko besake ta ba wallahi wallahi kundeji na rantse muku ko?saide yanemi wani uban bani ba.

Itama Ammi miƙewa tayi a mugun fusace tace”ni kuma idan nice na haifi Ahmad dole ya tare da matar sa ko kokuma ya fuskanci fushina tana kare fadin haka tayi ɗakin ta tana kulle ƙofan dakin.

miƙewa yayi dafe da kansa dake sara masa yana barazanar rabewa gida biyu ga jijiyoyin kannasa duka sun miƙe ruɗu ruɗu har wani jiri yakeji zuciyarsa kaman zata faso ƙirjinsa ta fito miƙewa yayi yasoma takawa yana haɗa layi kaman ze fadi kasa sabida dishi dishi dayake gani da sauri ya dafa bango yana ambatan sunan Allah.

Kalaman iyayen nasa biyu su suke masa amsakuwa a kunne kaman yanzu suke maganan”inde ni na haifi sa dole yasaki wannan yarinya,idan nice na haifi Ahmad dole yatare da matar sa ko kuma ya fuskanci fushina”innalillahi ya’ilahil alamina kakawo mun ɗauki cikin lamurana dakyar ya iya lallaɓawa yafita daga cikin falon yanufi ɗakin sa ya faɗa saman gado notinan kansa duka sun kunce yarasa wani irin tunani zeyi yama rasa a wani irin ma’auni ze ajiye maganan iyayen nasa biyu shin maganan Ammi ze dauka yabar na Abban sa ko nasa ze dauka yabar nata rintse idonsa yayi da karfi yana rasa abunyi jikin sa na daukan zafi kaman zazzaɓe ze kamasa yanda jikinsa ya dauki zafi hakama zuciyar sa ke daukan zafi.

Alhaji sunusi duk ya rude ya ɗimauce yana neman zarewa gun maigadi yanufa buguzum buguzum dasauri kaman ze tashi sama mai gadin na hangosa yanufo sa da sauri yana zubewa ƙasa dan gaidash…katsesa yayi yana cewa”baka ga wata mata yanxu tafita waje ba?cikin inda inda mai gadin yasoma cewa”ranka yadade wato kasan yau ai ranar sune masu shige da ficen suna da yawa bazan gane ba,wani irin mahaukacin kallo Alhaji sunusi ya watsa masa ya juya yana cewa”bansan amfanin zamanka a nan ɗin ba,tunda baka gane masu shige da fice,daidai nan suka bangaji juna da wani matashin saurayi a fusace Alhaji sunusi ya ɗago da rinan nun idanun sa cikin faɗa yake cewa”baka ganine kai mahaukacin inane kawani zo kana bangaje mutane kaman wanda yasamu sa’an sa”yi hakuri Alhaji ba danufu nayi ba yana cewa haka yafice zuwa baki get da sauri,bayan ya fitane Alhaji sunusi yaji kaman abu a hannun sa yana dubawa kuwa sai yaga ashe takarda wannan matashin yasaka masa hannu yana dubawa yaga anyi rubutu kaman haka.

 

Kada kabawa kanka wahala wajen neman ta ni kaman guguwa nake matukar nayi niyar bayyana a waje zan bayyana kainane ta yanda mutum baiyi zato ko tsammani ba kaduba wayan ka zakaga sako Alhaji sunusi ruwa yakusa karewa ɗan kada boom.

Ai Alhaji sunusi besan sanda yasaki wayan hannun sa ƙasa ba tsaban rikicewa.

Da yamma Ahmad ya lallaɓa yafito daga ɗakin sa dan sallan azaha data la’asar duka a ɗakin sa yayi yana fita wajen motan sa yanufa kai tsaye yashiga motan yamata key horn yake ba kakkautawa da gudu gudu mai gadi yabude kofan yasan yau ba lafiya ba irin wannan horn din da Ahmad ke masa dan ze iya cewa tun zaman sa a gidan be taɓa yimasa irin haka ba,yana budewa ya ɗaga masa hannun dayimasa fatan Allah yatsare kaman yanda yasa ba amma ko kallon inda yake Ahmad din beyi ba.

Saida ya hau kan titi sosai yakira wayan faisal yana dagawa be bari ko sallama sunyi ba yashiga cewa ina hanyata ta zuwa gidan ku yau ɗinnan zankawo karshen matsalan nan,kafin faisal yasamu zarafin cewa wani abu tuni ya katse wayan yana tafiya gidan ba kowa sai Aisha kaɗai dake kwance saman kugera a falo yana shiga falon ko sallama babu kansa tsaye yanufi dakin ta saide ganin ta falo ya nufota ita ma sauri miƙewa tayi sanda ta shaƙo kamshin turaren sa tamiƙe zumbur daidai yana juyowa basuyi aune ba ƙirjinsu ya haɗu dana junan su sauri yin baya tayi amma kafin tayi baya tuni taji anyi sama da ita.

 

Wani iri shock suka shiga dukkan su su biyun ta dalilin haɗuwar gangan jikinsu dakyar ta samu daidaita nutsuwar ta tace”me haka malam saukeni wani hancky yaciro daga aljuhunsa ya daura mata a fuska daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba.

Bayan barin Ammi falon kallan sa a wulakance Anty hajia tayi tana taɓe bakin ta tace”idan wani abu yasami yaran nan tasanadin ka bakar zuciyar ka zanyi shara’a dakai daganan har sai inda karfina yakare hakama ƴar uwata kafin yayi yunkurin yin magana tuni tabar masa falon tanufi kofan ɗankin ammi dayake a garƙame tana buga ƙofar tabude amma taƙi saurarota.

Wayanta ne yayi ringin tana ddubawa gani mai kiran yasata dauka tana karawa a kunnenta ta kk sallama beyi mata ba yashiga cewa”anty hajia fatan kina gida?”a rude ta amsa masa da bana gida amma lafiya?jin muryansa kaɗai yanuna ba lafiya ba.

“Ahmad yamun waya ina tsoron karyama yar mutane wani abun dan najisa kaman yana cikin fushi kuma kinsa idan yana fushin nan ze iya yin koma ai bata bari yakare maganan nasa ba tace”innalillahi nashiga uku ni ikilima wannan wani irin ………sai

[9/16, 7:47 PM] Ummahani: 💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

Leave a Reply

Back to top button