Musabbabi Book 2 Page 2
MUSABBABI BOOK 2
NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM
( mrs Aliyu mayare)
Page 2
Ranar laraba kuwa, Afrah bata bari an tashi islamiyya ba, domin aji daya kawai ta dauƙa, daganan ta nemi izinin tafiya wajen ya sayyadi, yana yi mata izini ta fice zuwa gidansu. Ta tadda mahaufinta a ɗakinsa yana share ɗakin gwanin ban takaici, da sauri ta amshi tsintsiyar ta share ɗakin fes, ta gyara masa kan gadonsa ta gpge komai, nan da nan ɗakin yayi kyau matuƙa, mallam Mahmud ya zuba mata ido, sonta ƙara shiga ransa yake, shin me zaisa wanda ya mallaki ya irin Afrah zai damu da wani abu a rayuwa, Afrah daban take, yana alfahari da kasancewarta yarsa, babu abinda yake yi sai sa mata albarka, a zuci da zahiri.
Ita kuwa Afrah zuciyarta cika ta yi da damuwa, da takaicin yadda ko shara Na’ima ba zata iya yi ma mahaifinta ba, idan Mama Hauwa ta manta da girman kula da miji, ai bai kamatq Na’ima ta manta da martabar da mahaifinta yake da shi a gareta ba, lalle akwai buƙatar su sami masu yi musu nasiha. Sosai ta ji tana jin haushin Mama Hauwa da Na’ima domin ko gaisuwar kirki ba su yi ba tsakaninsu, yadda Mama Hauwa ke dauke kai itama yau Afrah bata bi ta kanta ba, ita kanta Na’ima ba su yi magana da juna bq.
A ƙofar dakinsa ta shimfiɗa masa tabarma, bayan ta kunna masa maganin sauro a ɗakin nasa. Don haka suka fito suka zauna kan tabarmar, daga bisani ma tashi tayi ta ɗauki butar sa ta ciko da ruwa ta kawo gaban tabarmar ta aje, kasancewar an kusa kiran sallah magriba. “Zo ki zauna uwata, ki huta Allah ya yi miki albarka, Allah ya baki masu yi miki kema”. Mama Hauwa da ke aikin ijin wutar tuwo ta juyo ta saki wani dogon tsaki, wanda baisa sun ko kalli inda take ba. Afrah ta dawo kusa da shi ta zauna tace “Amin Baba, bana son magariba ta yi ban koma gida ba, dama yaya musaddik ne ya aiko ni”, nan da nan ya cika da fara’a yace “To Afrah, sai ki hanzarta ki ida saƙon ki tafi”, Mama Hauwa dakatar da komai ta yi ta sa musu ido, zuciyarta ta ta gama gaya mata yauma kuɗi ya aiko masa da shi, cikin gasgata hasashenta Afrah ta ciro kuɗi ta miƙa masa tace “Gashi yace na kawo maka kayi cafane, babu yawa”.
Ya amsa fuskarsa ta ƙara cika da farinciki, ya zubama kuɗin ido, gami da sakin ajiyar zuciya, yace “Yanzu wai musaddik ne yake min irin wannan kyautar, Afrah musaddik ya samu, ya Allah ka duba girman sadaukarwar da ya ta ta yi ka ƙara dawo da musaddik hanya madaidaiciya”, Afrah tace “Amin Baba, ai akwai sauƙi sosai komai ya na tafiya yadda muke addu’a kullum, Alhamdulillah”. Zaiyi magana kenan Mama Hauwa ta taso tana cika tana batsewa tace “To ni dai ka sani, duk abinda ka sayo a matsayin abin buƙata a gidan nan, in dai da wannan kuɗin ne bazan yi amfani da su ba, domin dai ni ban yarda da kuɗin ba………..
Cikin tsantsar fushi da zafin rai yace “ Tir da zuciyar da bata da kamun kai irin ta ki. Zuciyar da bata da zuciya, tun yaushe na gargaɗeki da ki daina shiga duk wani abu da ya shafi Afrah da aurenta, amma saboda tsabar rashin zuciya irin na ki, kin dage dole sai kin wofintar da kanki ta hanyar shiga abinda bai shafe ki ba, ki bari sai na yi maganar Na’ima to ananne ki ke da damar yin duk abinda ki kaga dama”.
Nan da nan ran Mama Hauwa ya kara ɓaci, tace “meye abin tunƙaho, tunda dai har ƙasa ta naɗe ba za’a kiran yarka da matar ɗan iska ba….. “, A fusace jiki na rawa Mallam Mahmud ya tashi ya yo kan Mama Hauwa da alamar duka zai naɗa mata, a gaggauce Afrah ta taso cike da tashin hankali ta shiga tsakaninsu, tana tsuma. Tana faɗin “A’a Baba don Allah ka yi haƙuri, na rantse maka hankalina yana matuƙar tashi ina jin damuwar yadda duk zuwan da zanyi gidan nan, sai kun sami matsala a tsakaninku, ya kuke son na yi don Allah”.
Jikin mallam mahmud ya yi sanyi, ya shiga faɗin innalillahi wa’inna ilaihirrajiun, domin yana son ya mallaki fushinsa. Ayayinda Mama Hauwa ta ƙara fusata, da ƙarfi cikin daka tsawa tace “ke da Allah can munafukar banza da wofi, idan bakya so mu dinga samun matsalar ba sai ki daina zuwa gidan ba da guntun kinibibinki, na nuna cewa kimfi kowa son ubanki, ki je can kiyi zamanki da mashayin mijinki mana” ananne Mallam Mahmud yace “ Babu wanda ya isa ya hana Afrah zuwa gidan ubanta ke ɗin me?”
Ta ƙara watsama Afrah harara tace “ ku kuka sani, idan kana iyawa ma ka basu ɗaki da ita da musaddik ɗin duk su dawo gidan su tare, wama ya sani ko kuɗin sata ne ake kawo maka ka ke washe baki”.
Afrah ta zame ƙasa ta yi zaman dirshan tana dafe da kanta, saboda damuwa.
Mallam Mahmud ya ƙara tunzira yace “Wallahi Hauwa ki ji tsoron Allah, ki sani ke ma kin haifa, kuma duk taƙadarancin musaddik bai taɓa sata ba, ko sanda ya shiga halin talauci balle yanzu da Allah ya azurta shi da aikin yi, wanda na fahimci shi ki ke ma baƙinciki, kuma sai dai ki mutu”.
Tsaki mama Hauwa ta saki ta juya tana ƙunƙuni ita kaɗai tasan abinda take faɗa ta koma wajen tuwonta da ya tasamma ƙonewa.
Tagumi Afrah ta zuba, ta rasa abinda ta yi ma mama Hauwa ba ta ƙaunarta, ko ko laifinta kenan na kasancewa yar kishiya, me yasa ba zata ɗauketa a matsayin ya ba, wannan abu yana ci mata tuwo a ƙwarya, lokaci ɗaya kuma tunanin abinda ya shiga tsakaninta da Haj kilishi ya dawo mata aka, ta ƙara aminta da cewa duk ƙarya ce ta gaya mata, tafi yarda da wata ƙila wani abun take nema agareta ya sata zubda kimarta har tana bata haƙuri, domin dai kusan ta fahimci matsalar su ɗaya da musaddik yadda Mama Hauwa ba ta sonta to hakanan Haj kilishi bata son musaddik, duk don saboda sun kasance yayan kishiya.
Mallam Mahmud ya durkusa a gabanta cike da ƙauna yake tausarta, yana nuna mata muhimmancinta a rayuwarsa, basu gushe a haka ba, har sai da Afrah ta ji damuwarta ta tafi. Ta yi masa sallama ta tafi, ba tare da ta ko kalli inda Mama Hauwa ta ke ba, ko kuma ta kalli cika da batsewar da Na’ima take yi a tsaye a ƙofar ɗakinsu.
Ta so wucewa gidan Inna Halima musamman yadda bayan saƙonta da zata kai mata akwai kuma maganar da take son ta yi da ita.amma kiraye kirayen sallar magriba ya tilasta mata wucewa gida, da zummar gobe ta je gidan inna Halumar tunda basu da islamiyya.
Washegarin kuwa, da wuri Afrah ta shirya zuwa gidan Inna Halima, bayan fitar musaddiƙ wajen aiki. Ta fito kenan ta yi kaciɓis da masu aikin Haj kilishi zasu shiga gidan suna maganar jikin Haj kulishi ya yi zafi jiya ma daƙer ta iya zuwa asibiti. Afrah ta ɗanyi turus, tayi tunanin ta shiga ta gaisheta amma kuma saita gommace ta tafi inda zata idan ta dawo ta leƙata.
Inna Halima ta yi matuƙar farincikin zuwan Afrah. Wacce tunda ta je gidan bata zauna ba sai aikin gyara mata gida da take yi, sai da ta gama gyara mata ko’ina samnan Inna Halima ta janyota cike da ƙauna ta zaunar da ita kusa da ita , ta ƙura mata ido tace “Afrah nayi kewarki, a zahiri a duk lokacin da irin wannan ranar ta zagayo , sai nayi tunaninki, kin sangarta ni , bakya jin wahalar jikin ki a kan aikina, Allah ya saka miki da alheri”.
Afrah ta yi murmushi tace “inna kenan, nifa yau wata maganace ta kawo ni gunki,Inna Halima ta gyara zama tace “To ya akayi Afrah, wace magana ce ta kawo ki, Allah yasa lafiya”.
Tayi murmushi tace “lafiya lau Inna ba wata matsala, kafin dai mu fara magana ga saƙon ki yaya musaddiƙ yace na kawo miki”, ta janyo leda ta miƙama Inna Halima, da hanzari ta amsa tana buɗewa . Ganin tsaleliyar atamfa yasa Inna Halima ta cika da fara’a, abubuwa dai sai gyaruwa su ke, tana mamakin yadda musaddiƙ ke tunanin faranta ransu a duk lokacin da ya samu wata dama.
“ Alhamdulillahi, Afrah Allah ya yi muku albarka Allah ya ƙara cika mana burin mu akan musaddiƙ”,
Afrah ta ƙara murmusawa tana jindaɗin yadda ake yabon musaddiƙ, tace “Amin Inna,ai haƙiƙa wannan samun aikin na yaya musaddiƙ ya janyo mana farinciki, domin a kullum natsuwa aikin yake ƙara sama masa,”.
Inna Halima tace “ƙwarai da gaske Afrah, don haka babu abinda zamu ce da wannan mata sai addu’a don a gaskiya ta taimake mu wajen dawo da musaddiƙ turbar arziƙi”. Afrah ta saki murmushi tace “ Ni kaina Haj Hudah banda wata kalma da zanyi ma ta godiya , ko na saka mata da irin alherin da tayi min sai dai nayi ta yi mata addu’a, domin tana ɗaya daga cikin mutanen da bazan taɓa mantawa da su ba a cikin rayuwata”, inna Halima tace “ Hakane,Allah dai ya cigaba da taimakonsa”.
Inna Halima ta ƙara matsowa kusa da Afrah sosai tace” To me zaki gaya min bayan wannan?”.
Afrah ta juyo tana kallonta sannan ta numfasa tace “Inna wani tunani nake yawan yi a kwanakin nan”, tace “Tunanin me kuma?”. Ta ɗan yi jim kamar tana tunanin abinda zata faɗa sannan tace “Al’amuran yaya mysaddiƙ ne nake tunanin tamkar akwai wata a ƙasa”, Inna Halima ta ƙara kallonta tace “kamar ya ya kenan?”.
Afrah tace “Abubuwan da yake yi, na tabbatar ba yin kansa ba ne,akwai alamomi da suke tabbatar min da hakan , sannan zuciyata tana cike da zargin Haj kilishi akan lalacewar yaya musaddiƙ”. Inna Halima ta yi jugum ta kafe Afrah da ido, zuwa ɗan wani lokaci sannan tace “ke Afrah idan baka iya kama ɓarawo ba sai ɓarawo ya kamaka, nasan Haj kilishi bata da kirki, kuma ba wani son musaddiƙ take yi ba, ni ma kuma akwai lokacin da nayi irin wannan tunanin naki, amma ban gayawa kowa ba na bar abin acikin ziciyata, kin san dalili?”, Afrah ta girgiza kai tace “A’a Inna”, tace “saboda ba ni da wata hujja ko shaidar da idan na faɗa zan gamsar da wanda na gayama ɗin, to kamar ke ce yanzu, wannan zargi ne yau idan kina da shaida na rantse miki sai inda ƙarfin mu ya ƙare”.
Afrah ta yi shuru, tana nazarin maganganun Inna Halima wanda tasan gaskiya ne, ya zama dole idan zaka zargi mutum ace kana da wata ƙwaƙƙwarar hujja, amma tabbas ta gama ji a jikinta akwai sa hannun Haj kilishi a cikin lalacewar musaddiƙ, sai dai kamar yadda Inna Halima ta faɗa ne zata bar komai a ranta har zuwa lokacin da zata sami wata shaida, da zata tabbatar ma da duniya zargin da take yi gaskiya ne akan Haj kilishi.Inna Halima tace cikin lallashi, “ki kwantar da hankalinki, kada kisa wannan tunanin a ranki har ya zo ya zamar miki illa, ki sani Allah baya zalunci ya kuma sanya zalunci abin haramtawa a tsakanin mu saboda haka duk wanda ya zalunce ka komai daren daɗewa Allah sai ya yi maka sakayya, don haka idan ma har tunaninki gaskiya ne to masifa ta na kan Haj kilishi kuma komai daren daɗewa Allah sai ya tona asirinta”.
Afrah ta gamsu ƙwarai da maganar Inna Halima, don haka ta samu sauƙin damuwar da ke zuciyarta.
Afrah ta ƙara duban Inna Halima tace “shikenan Inna mu bar wannan maganar mu yi ɗaya maganar”, ta yi murmushi sosai tace “To ina jinki”.
Afrah ta gyara zamanta tace “ Inna na ga kamar kun manta da burina na son yin karatu, tun bayan aurena da yaya musaddiƙ kullum ina tsumayin ranar da ke ko Baba zaku tuna da burina ku kuma taimakeni na cika shi, duk da a da nayi tunanin haƙura da komai, don kawai na kula da yaya musaddiƙ, yanzu kuwa ganin abubuwa duk sun yi sauƙi yasa na yi tunanin me zai hana na cigaba da karatuna”.
Inna Halima ta sauke a jiyar zuciya tace “Allah sarki Afrah, al’amuran musaddiƙ yasa muka manta da komai, amma ina tabbatar miki in sha Allah zaki cigaba da karatunki, da kaina zan samu yaya Mahmud mu yi magana, ke kuma sai ki zauna da mijinki ku yi magana idan ya amince to idan bai amince ba, ki kira ni ki gaya min”.
Gaba ɗaya Afrah sai ta kwanta a jikin Inna Halima cike da farinciki da jindaɗi. Afrah ta daɗe a gidan Inna Halima domin hatta abincin dare ita ta girka mata, tana gamawa gaf da magariba ta ɗauki hanyar gida.
Ko da ta koma gidan, daƙer ta lallashi zuciyarta ta shiga cikin gidan domin ta gaida Haj kilishi. Duk da duhun da ya fara Haj Rakiya ce zaune gefen Haj kilishi da alama itace ke jinyar, ta sami waje ta zauna tana yi mata sannu, gami da kallon tarin maganin da ke gabanta, ta jinjina kai tace “ciwon meye haka ke damunta irin waɗannan magunguna haka”, idon Haj Rakiya na kafe a kanta tace “ciwon ƙirji da kai ke damunta, amma ai ta ji sauƙi ma a haka”, Afrah ta jinjina kai tana ƙara mata sannu, daƙer take ansawa saboda ba ƙaramar wahala ta yi ba, amma duk da haka baƙar zuciyarta tana nan tana jifan Afrah da mugun alkaba’i, gami da tunanin yadda har yanzu bata ga alamar maganin da ta ci a cikin abinci ya yi tasiri ba, ko dai maganar mai Rakwacam gaskiya ne cewar Afrah ta fi ƙarfinta, da sauri ta kori wannan tunanin da ƙarfafa ma kanta guiwar cewa Afrah bata fi ƙarfinta ba, tasan wannan ciwon ne kawai da ya kwantar da ita ya hana mata komawa wajen me Rakwacam da Tsiduhu da zaran kuma ta sami lafiya zata tafi.
Kallon kallo kawai ake tsakanin Haj kilishi da Afrah, ita kuma Haj Rakiya tana kafema da Haj kilishi ido, tana karantar abinda ke kwance a cikin zuciyarta, ta yi murmushi a ranta tace na fiki son ki warke, domin ina buƙatar kuɗi, duk wannan bin da nake miki da zaman jinyar ki da nake yi duk sai na fanshe. Afrah na shirin tashi ta tafi domin tasan musaddiƙ duk inda yake ya kusa dawowa gida. Amma ga rashin tsammaninta kawai sai ta ji sallamar musaddiƙ a cikin falon, tayi saurin kallonsa tana amsawa.
Cike da damuwa ya ƙaraso kusa da Haj kilishi ya zube a gabanta, fuskarsa na nuna tsantsar tausayi da kulawa yace “Sannu Haj, ashe baki da lafiya ban sani ba sai yanzu da na dawo baba maigadi yake gaya min Afrah tana ciki ta zo duba ki ba ki da lafiya”, ta motsa a hankali ta ƙara langaɓewa tace “ya za’ayi ka sani musaddiƙ tunda ka manta da nauyi na da ke kanka, ban taɓa tsammanin zaka iya juya min baya ba”, nan da nan musaddiƙ ya ji damuwarsa ta ƙara ƙaruwa ya zauna sosai kusa da ita cikin ƙoƙarin kare kansa yace “Don Allah Haj ki daina faɗin haka, babu yadda za’ayi na juya miki baya, abubuwa ne kawai su ka canja,” Cikin wata irin galabaitacciyar murya tace “ Na sani,komai ya canja musaddiƙ”.
Ita kam Afrah ido kawai ta kafama Haj kilishi tana mamakin yadda ta ƙara langaɓewa tare da ƙoƙarin dasama musaddiƙ damuwa don kawai ya ji da gaske baya kyauta ma ta, ta girgiza kai wai shin Haj kilishi wace irin mutum ce?
Afrah ta fahimci musaddiƙ ya damu sosai da ciwon nata, har yana ƙoƙarin a koma asibiti, Haj Rakiya tace ai an riga anje asibiti tana kan shan magunguna ne. Lokaci ɗaya kuma ta na cike da mamakin, irin natsuwar da take gani a tare da musaddiƙ, gaba ɗaya ya kusa komawa musaddiƙ ɗinsa na da, lalle sai yanzu ta ƙara fahimtar daliln damuwar da Haj kilishi ta ke ciki.
Tabbas komai ya canja, shi yasa Haj kilishi ta ƙara haukacewa.
Musaddiƙ da Afrah sun daɗe tare da Haj kilishi, kafin ya tasa matarsa a gaba cike da so da kulawa suka tafi ɓangarensu. Suna fita Haj kilishi ta ja jiki ta zauna tana maida numfashin ciwo da tashin hankali, Haj Rakiya ta taso ta dawo gefenta ta zauna tana kallonta, Haj kilishi itama ta ɗago tana kallonta tace “kinga musaddiƙ ko Haj, maimakon warin taba da wiw-wiw da tsamin giya da yake yi kullum yau kina jin irin ƙamshin turare da yake yi”, Haj Rakiya tace “Na ji fa “, ta ƙara kallonta tace “ kinga kayan jikinsa, duk da nasan tun safe ya sa su, to amma har zuwa daren nan kina ganin har yanzu karin gugar su bata bar jikin kayan ba, ki duba irin hular da ya murza a kansa yadda ya yi kyau matuƙa, a haka waye zai dube shi a matsayin mutumin banza”, Haj Rakiya tace “Babu, gaskiya duk wata kamala ta kusa cika ga musaddiƙ”, Haj Kilishi ta dafe ƙirjinta da yake dakan uku uku , zafin ƙirjinta ya ƙaru, lokaci ɗaya kuma mugun ciwon kan da take yi ya dawo ji take kamar ana tsige gashin kanta saboda azaba, bakinta na rawa tace “Na shiga uku, ta yaya ina saƙa amma zare na warwarewa, ina zansa kaina idan musaddiƙ ya dawo mutumin kirki, bana son yaron nan har cikin zuciyata, bana son ganinsa cikin farinciki, bana son a kira shi da mutumin kirki”.
Haj Rakiya tace “Nasan abinda ki ke ji, ai kawai kuɗi zaki ƙara saki tunda Allah ya azurtaki, ranar biyan buƙata ai rai ba bakin komai yake ba”.
Cikin azabar ciwon ƙirji Haj Kilishi tace “kuɗi ba matsalata bace, wajen da zan samu biyan ɓuƙata ne damuwata”.
Haj Rakiya ta yi ƙasa da murya sosai tace “ kada ki damu, Allah kaɗai yasan inda za’a dace, shi yasa raba ƙafar yake da amfani, idan ba’a samu a can ba za’a samu anan”, Haj Kilishi tace “Allah ya ba ni lafiya mu koma wajen Tsiduhu da mai Rakwacam, kamar yadda muka tsara, idan kuma ban ji dama ba ina ganin kece zaki tafi min kiyi mu su bayanin komai”.
Haj Rakiya tace “Babu damuwa, babu abinda ba zanyi miki ba matuƙar zaki jidaɗi, don haka a shirye nake”, ta lumshe ido ta buɗe cike da tashin hankali tace “ madallah da samun ƙawa irin ki, Allah yabar mu tare”. Ta yi ɗan murmushi tace “Amin”. Yadda jikin Haj kilishi ke rawa yasa Haj Rakiya ta kwantar da ita, sannan ta bata maganinta na dare sai da ta tabbatar ta sha sannan ta yi mata sallama ta kama hanyar gida goman dare ya wuce.
Bata san dalilin da yasa sam bata jin tausayin Haj kilishi ba, don a yanzu tana nazari sosai tana kuma iya hango tsantsar rashin adalcin da take yi ma musaddiƙ gami da ɗimbin zaluncin da bata ga dalili ba.
Yar gidan Imam ✍️