Hausa NovelsMai Maganin Mata Hausa Novel

Mai Maganin Mata 14

Sponsored Links

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*

*Zahra Surbajo*

Bisimillahirrahmanirrahim.

**
*ME BUƘATAR COMPLETE DOCUMENT ƊIN SHAAWARSHI NAKE 500 NE KITURO KUƊINKI ABAKI*

*HARIJA CE,sabon littafine dazan yishi akan kuɗi 500 kacal,karku bari abaku labari,yazo da salo na musamman shima meso ze iya turo kuɗinshi yanzu ta acct kawai*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*

 

*14*

Tunda gari ya waye yakeso yaje yaga ya fareeda ta kwana,amma fadeela ta kankane komai koya ya motsa akan idonta.

Fareeda dake can ɓangarenta,anci kwalliya ana jiran shigowarshi amma taji shuru,hakanne yasa ta yanke shawarar binshi can ta gaisheshi.

Ƙara gyara fuskarta tayi sannan tasake fesa turare,sannan ta nufi sashin na fadeela cikin takunta me ɗaukar hankali.

Suna zaune a falo,yana matsawa fadeela ƙafafunta datace ciwo suke mata,suka tsikayo sallamar fareeda.

Baki buɗe fadeela take kallon labeeb,dan batasan dalilin zuwan nata ba.

Tun kan ta gama tunanin labeeb ya amsa sallamar gamida bata ixinin shigowa.

Ƙamshinta ne ya mamaye koina na falon,ta shigo fuskarta ɗauke da murmushi.

Kan kujera taje ta zauna,idon labeeb na kanta jikinshi se ɓari yake,

“ranka ya daɗe najika shurune yasa nace bari inbiyo sawu inga ko lafiya?”cewar fareeda tana wasa da idanunta.

Fadeela wacce tsananin mamakin kirsar yasa ta kasa cewa komai raba ido kawai take a tsakanibsu.

“Ayya baby yanzu nake shirin zuwa kuma se gaki kin rigani,to ya kika kwana”?ya bata amsa yana murmushi.

langaɓe kai tayi gefe haɗi da marairaice fuska kamar zatai kuka tace “kewar rashinka kusa dani bata barni na kwana lafiya ba baby”

Satar kallon gefen da fadeela take yayi kamin ya bada amsa,ayko kamin yay maganar ta rigashi inda ta ce”Amarya kinsha ƙamshi,to sannu da ƙoƙari,sede shi be kwana da tunaninki ba,hasalima murna yake da baroki da yayi,yanzu base anjima ba kitashi ki fice daga nan,kuma ina me gargaɗinki wannan ne karo na ƙarshe da zaki ƙara biyomin miji,kijirashi yazo inda kike,ay yasan hanya,inkuma kika kuma shigomin nan wlh sena saleki tass da ruwan zafi,ƙaryar bariki kikeyi”ta faɗi ba tare da damuwar komai ba.

Itako fareeda dubanta takai gun labeeb taga ko zeyi magana setaga bece komaiba,hakanne yasa ta miƙe tsam tace”yi haƙuri aunty bada wata manufa nazo ba”

Kallo ma bata ishi fadeela ba bare tasa ran zata bata amsa,ayko sum sum ta fice daga falon tana waigen labeeb.

Se bayan ta fitane ya dubi fadeela,yace a tausashe”kiyi haƙuri don Allah tabbas bata kyauta ba zuwan datayi,sabida atsawon wata guda da kika bamu baki taɓa bina can ba se ranar dani na gayyaceki,ni kaina banso ta biyoninba,kuma zan mata magana”ya faɗi yana kamo hannunta.

Dubanta takai gunshi tace”abinda na faɗi koda zaa kashenine wallahi zan aykata,dan haka ku kiyaye”tana kaiwa nan ta ƙwace hannunta tabar gurin.

Duk yadda yaso yaje gun fareeda ya kasa sabida wutar balain da yake hangowa a idanunta,besan daliliba amma yana shakkar ƙwayar idanunta.

Miƴewa yayi ya bita abaya,yaje ya dinga ƴan kame kame harde yasamu ta sakar masa fuska.

*********

Wasa wasa saida fadeela ta fita girki sannan yaje ga fareeda.

Tana ganinshi tasa masa kuka ta faɗa jikinshi,rungumeta yayi yajata suka zauna kan kujera,a hankali yace.

“koma fe menene fareeda laifinkine,waya aykeki bina gurinta bayan kinsan ita bata biyoniba,duk fa abinda zamuyi arayuwa mu dinga yiwa kanmu adalci,tunda kinsan dole zanzo baki da right ɗin bina alokacin da kikasan muna tare”

Ɗago kanta tayi ta dubeshi tace murya na rawa”baby kana mijina amma ace zaamin iyaka dakai?”

“Ba iyaka bane fareeda hanyar da zaa zauna lfy nake nuna miki”ya faɗi yana shafa bayanta,

Shuru tai masa bata kulashiba,dan ta rasa abun ce masa,amma ta ƙudiri aniyar zama tauraruwa agun mijinta.

 

Kumude je zuwa.

*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*

*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*

FREE NE HAR ƘARSHE

07044600044

Leave a Reply

Back to top button