Hausa NovelsYankan Karfe Hausa Novel

Yankan Karfe 7-8

Sponsored Links

💫⛓️⚔️YANKAN ƘARFE⚔️⛓️💫

 

 

 

 

 

~Written By~

 

 

 

 

 

 

*Hanyluv✍🏻*

 

 

 

 

 

*Free page*

 

 

 

 

 

 

 

 

*Page 7 & 8*

 

 

 

 

 

Se da ta ƙare mai kallo sama da ƙasa sanna ta sannan ta juyar da kai tare da tufar da yawu sannan ta dawo da kallon ta kanshi ta fara magana cike da ƙyama,

“kai yanzu fisabilillahi ka ga nayi kama da matar ka? Koh ka taɓa ganin inda aka haɗa gurɓataccen abu da mai kyau? Toh bari kaji ni koh da duka mazan duniya zasu ƙare ya rage daga ni se kai wallahi wallahi bazan taɓa iya auren ka ba! Da in aure ka gwanda na mutu!” nan tayi gaba ta barshi tsaye yana ta faman bambami, ba tayi wani tafiya sosae ba ta isa gidan Laure, tura ƙyauren tayi ta shiga gidan da sallama, Laure na zaune ita da ƴarta Mariya suna ta ɗaɗɗaura kayan miya a leda, ɗagowa Mariya tayi suka yi ido huɗu da Nimrah, aikuwa Nimrah ta watsa mata wani banzan kallo tare da yin ƙwafa,

“zamu haɗu a waje ne ae ban manta da abun da kika yi mun ba!” ta faɗa ƙasan laɓɓen ta, Mariya mai da kanta ƙasa tayi gaban ta na faɗuwa dan kaf ƙauyen nan babu wanda yara ke tsoro irin Nimrah, sam ita bata ɗaukan raini,

“Nimrah me za a baki?” Laure ta tambaye tana miƙewa, miƙa mata kuɗin Nimrah tayi a yatsine tace “tarugu na talatin, tumatirin hamsin, albasa ta ishirin se man gyaɗa kwata,” amsa Laure tayi tare da wucewa, a hankali Mariya ta ƙara ɗago kai karaf suka ƙara haɗa ido da Nimrah, a zafafe ta fara magana tana nuna ta da yatsa,

“Wallahi ki ka ƙara haɗe shegun mici²n idanun nan naki da nawa se na ƙwaƙule miki su! Kuma wallahi kar wae ki yi tunanin gidan ku na shigo kin san dae ba ƙaramin aiki na bane in yi miki ɗan iskan duka koh da kuwa a gaban Lauren ne,”

“Ah ah Nimrah lapia? Meya faru naji kin tasa Mariya a gaba kina zazzaga mata bala’i, ni dae gaskiya kar ki kuskura ki taɓa mun ƴa!,” Laure ta yi maganan yayi da take miƙowa Nimrah siyayyan da tayi da chanjin ta, fizga Nimrah tayi tare da yin gaba abun ta tana cewa “Ae se ki tambaye ta abun da tayi mun! Kuma se dae kar ta bari mu haɗu a hanya dan wallahi muddin mu ka haɗu se na jibge ta!!!”

“Aw harda ma rantsuwar ki! toh Allah ya baki sa’a ae dae nasan hanyar gidan ku!,” taɓe baki tayi tayi ficewar ta daga gidan,

Koh da ta ƙarasa gida ta tadda Ni’imah har ta gama hura wutan ta ɗaura sanwan girkin rana zuwa dare, ƙaraswa tayi ta taya ta suka cigaba da haɗa girkin, Daadah na daga gefe zaune, Gidado kuma yana gidan abokan sa be dawo ba har se da suka kammala girkin, Abboh ma yau tun 3:00pm ya dawo gida sosai suka yi mamaki dawowan na shi dan su dae tun da suka taso sun san muddin Abboh ya fita tun safe se bayan isha’i yake dawowa toh wataran ne ma ze dawo gab da magrib,

“Abbohn su yau dae lapia ka dawo tun Uku?” Daadah tayi tambayan tana ajiye mai ruwa kusa da abincin shi, shiru taji be amsa ba hankali na can wajan su Nimrah dake zaune daga can gefe Gidado a tsakiyar su suna fira se dariya suke yi, se da tasa hannun ta ta ɗan taɓo shi,

“Abbohn su magana nake yi! hankalin ka na can kana ta kallon yaran ka!,” firgigitt ya jiyo a hankali ya lumshe idanun shi sannan ya buɗe su tare da ɗaurawa akan Daadah, murya a sanyaye ya kira sunan ta,

“Halimatu!!”

“Na’am Gorko am(My husband),”

“Yau kwata² ji nayi bazan iya zama a kasuwan nan ba tare da na dawo gida ba! Ji nake a jiki na kaman daga yau bazan ƙara ganin su ba!,” wani irin murɗawa cikin Daadah yayi da se da taji kaman ɗan dake cikin ta ze fito, nan da nan fuskar ta ta koma karlar tausayi cikin rawar murya tace “Gorko am dan Allah ka daina yi mun irin maganan nan wallahi ta shar mun da hankali kake yi! duk da nasan mutuwar dole ce amma a halin da yanzu muke ciki ka daina kirawa kanka mutuwa! dan tabbas nasan ka rasu ba na jin nima zan ƙara wasu kwanakin!,” girgiza kai Abboh yayi yace “A’a sam ki daina faɗin haka Insha Allah koh bana raye nasan zaki kula ƴaƴamu sannan kuma nasan zaki zame musu uwa kuma zaki zame musu uba! Kuma ina fatan Allah ya sauke ki lapia! duk lokacin da zaki haihu muddin ba na raye ina so ki faɗawa abun da zaki haifah ina matuƙar ƙaunar sa!” ya ƙarasa faɗa yana shafa tsohon cikin nata, zirrr hawayen dake maƙale a idon ta suka samu nasarar zubowa, girgiza kai yayi tare da sa hannu ya share mata hawayen, su Ni’imah na can basu san ma abu da yake faruwa ba, Abboh kuwa haka ya cigaba da ƙafafawa Daadah gwiwa, ganin ta ɗan saki yayi murmushi cike da zolaya yace“Matar so yau dae ɗaya a taimaka a bani abincin nan a baki!” murmushi tayi tare da janyo kwanon abincin, ɗibowa tayi a cokalin zata bashi ya kawar da kai,

“Ni da tattausan hannun ki nake so ki bani!” wani kyakkyawan murmushi ta ƙara yi mai sannan ta ajiye cokalin sannan ta saka hannun ta ta ɗibo abincin tare da kaiwa bakin shi, da sauri ya buɗe baki ta zuba mai yana lumshe idanun shi, haka ta dunga bashi abinci har ya ƙoshi sannan ta bashi ruwan ya sha, haka suka cigaba da firan su se da aka kira Sallahr la’asar ya miƙe tare da cewa Gidado ya taso su tafi, sun juya zasu tafi ya juyo tare da kiran sunan su Nimrah,

“Na’am Abboh,”

“Dan Allah a cigaba da haƙuri da rayuwa! a duk halin da kuka tsinci kanku kada ku taɓa zubar da mutumcin ku na ƴaƴa mata kun ji koh?” jiki a sanyaye Ni’imah ta amsa da “Toh Abboh Insha Allah!” ita kuwa Nimrah bata iya amsawa ba saboda yanda taji Abboh yayi maganar duk se jikin ta yayi sanyi ɗaga kai kawai tayi,

“Allah ya albarkaci rayuwar ku!”

“Ameen,” gabaki ɗayan su suka amsa, ɗagowa yayi suka haɗa ido da Daadah da ta kafe shi da ido, a hankali ya ta ka har gaban ta tare da riƙo hannun ta murya ƙasa² ya furta,

“Me so yiddi ma!!( I love you!),” yana faɗin haka ya saki hannun ta tare da kama hannun Gidado suka fice daga gidan, haka Daadah ta bisu daga kallo har suka fice daga gidan,

Su Abboh bayan sun idar da Sallah wajan aminin shi Baba Rabe suka nufa zama yayi suka sha firan su na tsawon lokaci sannan daga bisani ya riƙo hannun Gidado suka nufo gida, sun shigo soron gidan kenan Juwairiyya ta kwalla mai kira,

“Kawu Ballo!” juyowa yayi,

“Na’am! Ah ah Juwairiyya ce, toh shigo muje cikin gidan mana!,” girgiza kai tayi murya ta mara sa tarbiyya tace “A’a ni ba abun da ya kawo ni ba kenan dama Inna ce tace nazo na kira mata kai!,” tana gama faɗin haka bata ma jira me ze ce ba tayi gaba abunda, shiru Abboh yayi na ƴan sakanni sanna ya shafa kan Gidado yace “Gidado nah je ka gida ka gaya ma Daadahn ku zanje gidan Gwaggo zuwa anjima zan dawo,”

“Toh Abboh,” ya faɗa tare da shigewa gida a guje, juyawa Abboh yayi tare da ficewa daga soron, be tsaya a koh ina ba se a ƙofar gidan Gwaggo, sallama yayi daga cikin gidan mijin Gwaggo (Malam Buba) ya amsa sannan ya fito ya same shi, hannu Abboh ya miƙa mai suka yi musabaha sannan yayi mai jagora zuwa cikin gidan Gwaggo na zaune akan kujera tana jerawa Juwairiyya kayan tallar ta, zama Abboh yayi akan tabarmar dake shimfiɗe a tsakar gidan, cike da girmamawa yace “Yaya ina wuni,” banza tayi da shi tana cigaba da gyagygyar tiren, cikin rashin jin daɗi mijin Gwaggon ya kalle ta yace “Asiyah baki ji yana gaishe ki bane?,” shima banza tayi da shi bata amsa mishi ba har se da ta gama kammala abun da take yi sannan ta taya Juwairiyya ɗaura tiren tallan a kan ta tayi mata a dawo lapia, har se da ta ga ficewar ta a gidan sannan ta maido da kallon ta kan Abboh, wani matsiyacin kallo ta watsa mai tare da kawar da kai,

“Yaya naji kin aika a kira ni, ina fatan ba wani abun mara daɗi bane ya far..!!” katse shi tayi

“dakata mun! Ka rufa mun baki Ballo! Ni zaka turowa ƴaƴan ka su ci wa mutumci
! Ni Ballo! Toh wallahi daga ku har ƴaƴan naka kun yi kaɗan! Daga kai har Halimatun har kuna da bakin da zaku ce baza ku ɗaurawa ƴaƴan ku talla ba! Toh ai ƴan tallan sun fi ƴaƴan na ku! Su da suke feƙaƙƙu! ƴan iska! Karuwai! Duk kun bi kun sake su basu nan basu can! Da yawon da suke yi ae gwara tallan! Wallahi ba ƙaramin kirki ma Sa’idu yayi ba da yace ya ji ya gani ze yi shahada ya auri Nimrah b..,” katse ta Mallam Buba ya yi,

“Haba!! Asiyah ɗan uwan naki kike faɗawa munanan maganganun nan! Yanzu ke zaki ji…,”

“Dakata mun Mallam ba da kai na kasa ba bare ka ɗauka! Se ka bari tukunna idan na juyo kan ka!,” ƙara juyowa tayi kan Abboh da yayi mutuwar zaune da jin zantukan da take gaggaya masa,

“kuma daga yau ka sani babu ni babu kai kuma babu zuri’a ta babu ta ka! kuma ƴaƴan ka a bin ɗakunan kwartaye zasu ƙare haka zalika a wulaƙance zasu ƙare!!,” tana kaiwa nan ta miƙe tare da jan mayafin ta dake sagale a igiya gab da magrib din nan ta fice daga gidan ta bar Abboh zaune dafe da saitin zuciyar shi, tsawon minti 15 yana nan zaune shi kuma shi da Mallam Buba da ya rasa ta ina ma ze fara bashi baki, a hankali ya fara magana cikin sassanyar murya,

“Mallam Ballo dan Allah kayi haƙuri, Asiyah dae ƴar uwarka ce, kuma ka fi kowa sanin halin ta, duk wannan maganganun da take yi ita kanta ta san ba gaskiya take faɗi ba, duk garin nan an san yaran ka hankali da kuma kamun kai, dan haka maganan da tayi kar ka wani bari ta samu matsuguni a zucyar ka, kuma da take wani cewa babu ita babu kai kuma babu iyalanta babu naka rabu da ita kawae zafin zuciya ne, Insha Allah babu abun da ze faru mara kyau daga ɓangaren ka da nata,” duk maganan nan da yayi be ga alamun Mallam Ballo ya motsa koh da da ɗan yatsan sa ba, a hankali ya kai hannun shi tare da dafa shi, luuuuu!! ya faɗo jikin shi, gaban Mallam Buba ne ya faɗi dammmm!

“Mallam Ballo! Mallam Ballo!!,” sosai yake jijjiga shi yana kiran sunan shi amma shiru alamun rai yayi halin sa…..

 

___________________________________

A hankali yake driving cikin kwanciyar hankali, shirye yake cikin T-shirt navy blue da jeans black yasa P-cap navy blue sosai yayi kyau, babu abun da ke ta shi a cikin motar se karatun Alkur’ani ƙira’ar Sudias, a hankali yake bin karatun ƙarar da wayan shi yayi ne shi ɗan dakatawa tare da sa hannu ya janyo wayar, sunan Khaleel ne ya bayyana a screen din wayar, rage sautin yayi tare da picking call din ya kara wayan a kunne,

“Saheel kana ina ne ka ajiye ni se faman jiran ka nake!,” Khaleel ya faɗa, yatsine fuska Saheel yayi murya can ƙasa yace “Malam ya zaka kira ni koh sallama babu ka fara mun wasu maganganu! wallahi zaka sa na juya abu na,” da sauri Khaleel ya tare shi da “Allah ya baka haƙuri dama kawai kira nayi naji koh holdup ne ya tare ka, Allah ya ƙaraso da kai lapia,” ba tare da ya amsa ba ka katse kiran, be ƙara 30min ba ya isa mamakeken gate din gidan su Khaleel, horn ya danna da sauri me gadi ya ƙaraso ya wangale masa gate din, tura hancin motar tashi yayi cikin gidan, Masha Allah shi ma gidan me kyau ne, parking lot ya ƙarasa yayi parking, a hankali ya fito daga motar da sauri me gadi ya ƙaraso ya zube yana gaishe shi, alama yayi mai da ya miƙe, se da miƙe sannan ya miƙa mai hannu suka gaisa, hannun shi ya sa a pocket ɗin shi ya zaro 10k ya bashi be jira jin me ze ce ba yayi gaba abun shi, nan me gadi ya ya shiga zubaba mai addu’o’i kala²,

Hajiya Mama na zaune ita da ƴar autar ta Aneesah, kyakkyawa yarinya, fara ce, tana da ɗan tsayi, baza ta wuce 18 years ba, atamafa ce a jikin ta anyi mata ɗinkin A shape, jin ƙarar door bell yasa me aikin su Laraba dake kitchen fitowa da sauri za ta je ta duba Hajiya Mama ta dakatar da ita,

“A’a Laraba koma ki cigaba da aikin ki Aneesah zata duba,”

“Toh Hajiya Nagode,” Laraba ta faɗa cike da yabawa da halin kirki na su Hajiya Mama da iyalan ta, komawa kitchen tayi ta cigaba da aikin ta,

“Aneesha je ki duba,”

“Toh Hajiya Mama,” Aneesah ta faɗa tana miƙewa ta nufi ƙofar, a hankali ta buɗe ƙofar ta same shi tsaye hannun shi zube a cikin pocket ɗin shi, washe baki tayi,

“Laaa Ya Saheel! sannu da zuwa shigo mana, ranar nan kazo bamu haɗu ba” ta faɗa ta na matsawa gefe, shigowa yayi yana sakin murmushi,

“Autan Hajiya Mama haka ki ka ƙara girma,” ya faɗa yana ƙarasawa cikin parlorn tare da zama kusa da Hajiya Mama yana gaishe ta, tana murmushin ta ta amsa tare da tambayan shi yasu Mamin shi ya amsa da suna nan lapia qalau,

“Saheel bari na sa Labara ta dafa maka favorite ɗin ka,” Hajiya Mama ta faɗa yayin da take yunƙurin miƙewa, da sauri ya dakatar da ita,

“A’a Hajiya Mama dawo kiyi zaman ki dan ni dae kam a ƙoshe nake,” dawowa Hajiya Mama tayi ta zauna suka fara ƴar firar su Aneesah se sakalci take yi shi kuma yana biye mata, sosai yake son yarinyar saboda tana da hankali da kuma sanin na gaba, ga ta akwai shiga rai,

Suna nan zaune Khaleel ya shigo cikin shirin shi na manyan kaya ash colour, shi ma yayi kyau kaman su ɗaya da Aneesah,

“Ya Khaleel anguwa zaka?” Aneesah tayi magana tana kallon yanda yaci ado, hararar ta yayi yace “Toh ina ruwan ki da inda zanje,”

“haba Ya Khaleel daga tambaya!,”

“Rabu dashi Aneesah idan be faɗa miki ba toh ni meye amfanin in raka shi! Ba in da zan bi shi in dae be faɗa miki ba,” Saheel ya faɗa yana gimtse fuska, juyowa Khaleel yayi yana yi mai kallon meyasa kake haka, ɗaga mai gira Saheel yayi, a marairaice Khaleel ya ya zauna yana kallon Hajiya Mama,

“Hajiya Mama dan Allah kisa baki mana,”

“A’a ni babu ruwana a ciki, tsakanin ku ne,” Hajiya Mama ta faɗa tana dariya don dae dama ita ta saba koh da yaushe suka haɗu se anyi, haka Khaleel ya dunga yi mi shi magiya da kyar ya tashi suka fito, gidan wata sabuwar budurwa da suka haɗu a social media ya raka shi, kasancewar yau zasu fara haɗuwa yasa se mazallaƙo Khaleel ke yi shi dae ban da girgiza babu abun da Saheel ke yi, a bakin wani gida haɗaɗe suka tsaya me gate brown colour, a nan waje suka yi parking motar su Khaleel ya danna mata kira ya sanar da ita gasu sun ƙaraso, me gadi ta sa ya shiga dasu gidan yayi musu iso har zuwa parlorn baƙi, ba su jima da zama ba ma su aiki suka cika musu gaba da kayan ciye², babu wanda ya taɓa komai a cikin su barin ma Khaleel da ya ƙagu ya ga sahibar ta shi, juyowa yayi ya kalli Saheel,

“Saheel dan Allah idan ta shigo ka ɗan yi snapping ɗin mu ba tare da ta sani ba,” wani kallo Saheel ya watsa mai ya buɗe baki kenan ze yi magana aka turo ƙofar ɗakin, a tare suka juya, wata irin dariya ce taso suɓucewa Saheel sakamakon gamon da idanun shi yayi, dammmm! gaban Khaleel ya faɗi ganin suffar da ya gani, gajera ce sosae, ga baƙi kaman gawayi, mummuna ce dae ta ajin ƙarshe,

“Bismillah mana Amaryar mu zo ki zauna kusa da Angon naki,” Saheel yayi maganan cike da tsokana, washe baki tayi sannan ta ƙaraso tare da zama kusa da Khaleel se faman fari take yi, zumbur Khaleel ya miƙe yana cewa “Atoh Masha Allah bari mu wuce dama akan hanya muke ina nan dawowa na musamman,” ya ƙarashe faɗa yana ƙoƙarin wucewa dakatar dashi Saheel yayi ta hanyar cewa “A’a bari na ɗan yi muku pictures mana,” aiku da sauri ta miƙe da ƙaruwar muryar ta tana cewa “Yawwa ai kuwa ayi mana kafin na ranar aure,” duk ƙoƙarin da Khaleel yayi na ƙin yin hoton amma ina se da Saheel ya ɗauke su, koh da suka fito har bakin mota ta roko su se washe mai baki koh sallama me kyau be yi mata ba ya shige motar Saheel ya ja suka bar ƙofar gidan, tunda suka fara tafiya Saheel yake tuntsira mai dariya, tun yana share shi har ya gaji ya juyo a fusace,

“Mallam ni kawae sauke ni a nan na nemi Napep ta ƙarasar dani gida,” dariya ya ƙara yi sannan yace “Wallahi baka isa ba! yawo zamu je ma,” haka ya dunga yawo dashi yana tsokanan shi, bashi ya maida shi gida ba se bayan Sallahr isha’i, aikuwa yin parking ya buɗe ya fita tare da bugo mai ƙofar motar, tuntsirewa da dariya Saheel ya ƙara yi sannan ya ɗaga murya yace “Se da safe Ango!,” banza yayi da shi yayi shigewar sa, dariya ya ƙara yi sannan yayi wa motar key ya bar gurin…

 

______________________________________

 

Daadah tunda Gidado ya shigo ya shaida mata sakon da Abboh ya bashi ta ji gaban ta yana ta faɗuwa, suma su Nimrah jin abin da ya faɗa yasa duk dae suka ji ba daɗi dan sun san alkhairi baze taɓa sa Gwaggo kiran shi ba dama dae Mallam Buba ne tunda sun san shi babu ruwan shi mutumin kirki ne, suna nan zaune aka kira magrib su kayi alwala Daadah ta sa Gidado shima yayi sannan tace ya tafi masallaci idan sun haɗu da Abbohn su sa dawo tare aikuwa da saurin shi ya fita su ma suka shige ɗaki,

Bayan sun idar da Sallah suka fito tsakar gidan babu dae me cewa uffan a cikin su har aka kira isha’i suka je suka gabatar, bayan sun idar suka dawo tsakar gida ta suna jiran dawowar Abbohn, shigowa Gidado yayi da sallaman shi suka amsa ya ƙaraso ya zauna kusa da Daadah a shagwaɓe yace “Daadah yunwa nake ji,” da kallon mamaki Daadah ta bishi tace “Ah ah Gidado ina Abbohn ku koh ka baro shi a waje ne?,” girgiza kai yayi cikin hali na yara yace “Ban gan shi ba,” cike da mamaki Ni’imah tace “Baka ganshi a ina ba?,”

Cike da ƙosawa shi ta yunwar shi yake yace “Ni Adda Ni’imah muku ban gashi ba, ba ya masallacin, ni ku bani abinci na,” tuni zuciyar Daadah ta yanke, kwata² taji komai na ta ya kulle, miƙewa Nimrah tayi cikin hazari ta kalli Ni’imah tace “Daddah(senior sister) tashi muje gidan Gwaggo mu ga koh yana can,” da sauri Ni’imah ta miƙe dama duk akwai hijab a jikin su, cewa Daadah suka yi bari suje su dubo koh yana can sam bata ma iya amsa musu ba suka juya zasu fice aka rabko sallama……….

 

 

_😍Comments din ku shine ze ƙara mun ƙarfin gwiwa💯, masoya na idan babu ku babu Hanyluv😇🥰_

 

*@Hanyluv✍🏻*
*07044454719📲☎️*

Leave a Reply

Back to top button