Hausa NovelsYankan Karfe Hausa Novel

Yankan Karfe 9-10

Sponsored Links

*💫⛓️⚔️YANKAN ƘARFE⚔️⛓️💫*

 

 

 

 

 

 

 

~Written By~

 

 

 

 

 

 

 

*Hanyluv✍🏻*

 

 

 

*Free page*

 

 

 

 

 

*Page 9 & 10*

 

 

 

 

 

Da sauri Ni’imah ta miƙe dama duk akwai hijab a jikin su, cewa Daadah suka yi bari suje su dubo koh yana can sam bata ma iya amsa musu ba suka juya zasu fice aka rabko sallama, kallon juna suka yi na ƴan sakanni sannan Nimrah ta amsa sallaman a hankali tare da cewa “Bismillah shigo,” Baba Rabe da Mallam Buba ne suka shigo suna ɗan ƙirƙirar murmushi amma duk wanda ya ƙare musu kallo ze ga alamun jan da idanun su yay, alama anci kuka an ƙoshi, da sauri Daadah dake zaune kan tabarma ta miƙe tana cewa “Ahh sannun ku da zuwa ku shigo,”

“yawwa sannun ku da gida,” suka faɗa suna ƙarasawa tare da zama, dawowa su Ni’imah suka yi tare da tsugunawa suka gaishe su suka amsa ba wani karsashi, cikin sanyi murya Daadah ta gaishe su Baba Rabe ne ya amsa amma Malam Buba ya gagara amsawa, a sanyaye Daadah tace “Hala Malam kuka zo nema kuma gashi baya nan,” shiru gabaki ɗayan su suka yi, kowannen su ya rasa ta inda ze fara, ita sam Daadah haka kawae shirun da taji sunyi yasa gaban ta faɗuwa, miƙewa Nimrah tayi tana cewa “Bari mu duba shi koh yana gidan Gwaggon,”

“A’a kunga ku dawo nan ku zauna magana zamu yi daku,” Mallam Buba ya faɗa, dawowa suka yi suka zauna a daga gefe, gyaran murya Baba Rabe yayi sannan ya kira sunan Daadah amsawa tayi sannan a hankali ya fara magana,

“waye ya halicce mu?,”

“Allah!,” ta bashi amsa,

“lokacin da ya halicce mu yayi shawara da wani?,” ya ƙara tambayan ta,

“Be yi shawara da kowa ba,” jinjina kai yayi sannan yace “Alhamdulillah! Duk kannin mu nan musulmai ne kuma mun yarda da Allah, haka zalika mun yarda Allah shi ne me rayawa kuma shi ne me kashewa!,” atake Daadah ta lumshe ido, zirrrrrr! Wasu zafafan Hawaye suka zubo mata dan ta riga da tasan me aukuwa ta auku, haka Baba Rabe ya cigaba da magana,

“kuma Allah be barin wani dan wani! Yau ina iyayen mu! ae ba da son ran mu mutuwa ta raba mu ba! Amma Allahn da ya fi mu son su shi ya ɗauki abin sa! Dan haka ina son gabaki ɗayanku ku sa haƙuri da dangana a zuciyar sannan ku ɗauki abun da zan faɗa muku a matsayin ƙaddara!,” izuwa lokacin harta su Ni’imah jikin su ya basu amma dae suna son su tabbatar da abun da zuciyar su ke faɗa musu,

“Mallam Ballo dae wanda ya fimu san sa ya ɗauki abun sa!!,” kamar saukar aradu suka ji zancen, Nimrah da ba ta gama yarda da abun da kunnuwan ta suka jiye mata ba a daburburce tace “ Ba..Baba Rabe! Me.. me kace?,” ƙasa yayi da kai yace “Nimrah hakuri zaku yi, shi kuma Mallam Ballo Allah yayi mishi rahama!!” cak!! Nimrah taji komai ya tsaya mata, fashewa da kuka Ni’imah tayi Gidado ma ganin Adda na kuka shima se ya taya ta, Daadah kuwa juriya ta aro ta ɗaurawa kanta murya na rawa tace “Allah yasa gafarta mai kuma yasa can ta fi mai nan!” da sauri Mallam Buba ya amsa da,

“Ameen Halimatu! Allah ya yi muku albarka ke da abun da ya bari kuma ya duba ku,” miƙewa su Baba Rabe suka yi tare da ficewa, tuni maƙota mata suka fara shigowa suna jimamin rasuwan mutumin kirki irin Mallam Ballo, koh 15min su Baba Rabe basu ƙara ba suka dawo cikin gidan su da wasu matasa ɗauke da makara da Abboh a ciki, tsaf an ma gama kintsa shi, har gaban su suka ƙaraso tare da dire makarar, juyawa Mallam Buba yayi dan zuciyar shi ta gama karyewa, Baba Rabe ne yayi jarumtar cewa “Halimatu! duk ku matso kuyi mai addu’a sannan kuyi bankwana dashi,” a lokacin cin ne zuciyar Nimrah ta karye ta fashe da wani kuka me karya zuciyar mai sauraro, itama Daadah kasa danne nata kukan tayi, matan da suka shigo ne suka dunga lallashin su da kyar suka iya ƙarasowa gabaki ɗayan su, Daadah sosai ta daure tayi mai addu’a, bayan sun gama ne a ɗauki makarar sannan aka tafi kai Mallam Ballo gidan shi na gaskiya, har aka tafi dashi Gwaggo bata ma sani ba, dama tun ya rasu Mallam Buba ya kira Baba Rabe suka kai shi gidan Baba Raben, a nan aka shirya shi sannan aka kawo shi gidan nashi daga nan kuma aka yi mai Sallah aka kai shi, koh da ta ji daga baya nunawa ma tayi koh a jikin ta sam bata damu ba, su kam ranar babu wanda ya runtsa a cikin su,

Washegari da safe Daadah ta tashi da zazzafar naƙuda, hankali a tashe Nimrah ta tafi kiran maƙobciyar su Hannatu da ke aiki a asibitin ƙauyen….

___________________________

 

11:30am

Wasu zafafan motoci ne ke shigowa gidan su guda biyar, me gadi se ɗaga hannu yake yi yana musu barka da durowa, parking suka yi a parking lot, da sauriya bodyguard ya fito tare da buɗe bayan wata haɗaɗɗiyar mota, ƙafar shi ya sako waje tare da fotowa gabaki ɗaya, wani babban mutum ne kyakkyawa dashi gemun fuskar shi duk yayi fari, sanye yake da milk din shadda malum² sosai suke ɗiban kama da Saheel,

Da sauri me gadi ya ƙaraso tare da durƙusawa yana gaishe, murmushi yayi yace “A’a Mallam Idi taso kasan dae bana son irin gaisuwa nan koh,” miƙewa yayi sannan ya miƙa mai hannu suka yi masaba, sannan a hankali ya juya yayi ma muƙarraban nashi magana kana ya juya ya nufi Entrance door,

Mami na zaune kan three sitter tana bawa Anam abinci a baki ta ji ƙarar door bell, da sauri Lanti ta fito daga kitchen ta nufi ƙofar, buɗewa tayi nan idon ta suka tozali da Abba ae da saurin ta zube tana cewa,

“Alhaji barka da dawowa, sannu da zuwa! an zo lapia!,”

“Ahhh Lanti miƙe²! sannun ku da gida,” ya faɗa fuska sake yayin da yake shigowa cikin parlorn, cike da mamaki Mami ta juyo tana kallon shi dan dae ita be faɗa mata ze dawo ba kuma sam bata ji ƙarar shigowar mota ba, ƙarasowa yayi fuskar da kwantaccen murmushi da gudu Anam ta faɗa jikin shi tana ihun,

“Oyoyo Abba! Oyoyo Abba,” zuwa Lanti tayi ta gaishe shi sannan tayi mai sannu da dawowa ya amsa a mutumce sannan ta koma kitchen ta cigaba da aikace²n ta, da mamaki Mami tace “Abban su dama yau zaka dawo amma sam baka sanar dani ba?,”

“Yau ina so nayi surprising Mata ta ne!,” ya faɗa yana sakin mata murmushi, ita ma murmushin ta mai da mai sannan ta ce “amma da ka faɗa ae da mun shirya maka tarba ta musamman,”

“kar ki damu ni dae tarba ɗaya zaki yi mun ita ce kuma ta dare!” ya ƙarashe maganan yana kashe mata ido ɗaya, kawar da fuska tayi tana murmusawa,

“ina su Nadeeyah!,”

“Suna School!,” ta bashi amsa a taƙaice, jinjina kai yayi sannan yace,

“Uhmm hmmm wae kuwa kina samun layin Saheel? Ni dae kwana biyu idan na kira shi ba na samu! kuma dama nasan layin shi na nan ƙasar ba shiga zeyi a can ba!,” buɗe baki tayi zata fara magana karab suka ji buɗewar ƙofa, shigowa yayi cikin dae irin shigar da ya saba idan yana gida, sosae yayi kyau, yana tafiya cikin ƙasaita se kace wani Sarki se faman danna wayan shi yake yi, baki buɗe Abba yake kallon shi,

“Dama ya dawo ƙasar nan!” Abba ya faɗa a ƙasan ranshi, shi kam Saheel sam be ma kula da Abba ba ya ƙaraso ya zauna a 1 sitter sanna ya ɗago da shirin gaishe da Mami karab idonshi ya sauka akan Abba!

“Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un!,” Saheel ya faɗa a cikin zuciyar shi, kallom kaɗai da Abba yake jifan shi dashi se da ya bashi tsoro, baki na rawa yace “Ab.. Abba sannu da dawowa!,” miƙewa Abba yayi a fusace ya wuce sama koh kallon inda yake be yi ba, juyowa yayi ya kalli Mami a marairaice yace “Mami na shiga uku dama Abba ze dawo shi ne baki sanar dani ba?” girgiza kai itama tayi cike da damuwa tace “wallahi nima ban san ze dawo ba kawai ganin shi nayi koh ƙarar motar shi banji ba!,” hannu yasa tare da dafe kanshi cike da tashin hankali, cike da rarrashi Mami ta fara magana,

“Son kar ka wani tashar da hankalin ka, yanzu zanje na rarrashe Abban ku zuwa anjima idan ya sakko se kaje ka bashi haƙuri sannan kace mai kai dae baka son Companyn dake UK🇬🇧 ya barka a nan ƙasar!,” ɗagowa yayi cikin rashin gamsuwa da batun nata yace “A’a Mami bazan iya ce mai bana son komawa UK🇬🇧ba tunda nasan bashi da burin da ya wuce naje can na kula da Companyn dake can din! In na faɗa masa haka ze ga a matsayina na ɗanshi bazan iya bin abinda yake so ba kenan!,”

Haɗe rai Mami tayi “Toh shikenan tunda shawarar da na baka bata yi maka ba se kaje kayi abun da kake!,” ta faɗa tana ƙoƙarin tashi ta bar gurin da sauri ya riƙo ta yana cewa,

“Mami Please am sorry, ban faɗi haka dan na ɓata miki rai ba, ba kuma wae bazan ɗauki abun da kika ce bane, ina son ki fahimci abun da nake nufi ne! Abba sam baya son zama na a ƙasar nan sannan Companyn ƙasar nan da Companyn dake UK🇬🇧 ba ɗaya bane, na can shi ne tsani! da shi Abba ya dogara muddin ya lalace wannan ma ya lalace kuma babu wanda ze kula da shi kaman yadda ni jinin sa zan kula dashi kuma ma ba zama zanyi din³ ba, it’s only for 6 months, da zaran na gama zan dawo,” zare hannun ta tayi daga cikin nashi ba tare da tace komai ba ta wuce sama, komawa yayi ya zauna tare da lumshe idanun shi sannan ya dafe kanshi da hannayen guda biyu, shi sam yanzu kuma be san meye abun da ze yi ba, shin yabi abinda Mami ke so ne koh koh umarnin Abba ze bi, yana cikin tunanin nan ne ya ji Anam a kusa da tana cewa,

“Ya Saheel! Ya Saheel! ba ka da lapia ne?” a hankali ya buɗe idanun shi tare da ƙaƙaro murmushi yace “A’a Lapia na qalau Autan Mami,” leƙa fuskar shi ta ƙara yi tana son gaanowa, ware mata idanu yayi sannan yace “Ga Baba Lanti can na yin aiki a kitchen je ki taya ta,” washe baki tayi tace “in ce ta bani inyi girki,” ɗaga mata kai yayi yana murmushi, aikuwa cike da farin ciki ta juya ta nufi kitchen ɗin a guje, ajiyar zuciya yayi tare da miƙewa ya fice daga parlorn,

Part din shi ya wuce, yana shiga be tsaya a parlorn ba ya wuce bedroom ɗin shi, ƙarasawa bedside drower yayi ya ɗauki keyn🗝️motar sannan ya fito daga part din nashi ya ƙarasa parking lot tare da shiga mota yayi mata key ya bar gidan…..

__________________________________

 

Tun 7am Daadah take yin naƙuda har ƙarfe 2pm amma shiru don har yanzu bata wuce 2 cm ba, tun da ƙarfin ta har ya zamana jikin nata koh iya ɗaga shi bata yi, sosae hankaln su Ni’imah yake a tashe sunyi kukan har sun godewa Allah, Gidado kam Hannatu ta sa a kaishi gidan ta suyi wasa da yaranta don shima da ya ga haka se ya fara kuka yana matsawa kusa da Daadahn, matar Baba Rabe ma tana gidan dan tunda Daadah ta fara naƙudan Nimrah taje ta faɗa musu, tare suka zo daga baya Baba Rabe ya tafi dan zuwa wajan sana’ar sa amma yace duk lokacin da aka buƙata wani abu a aiko a faɗa mai, sosai Matar Baba Rabe Mama Lami take ƙoƙarin kwantar musu da hankali amma itama amma daga ƙarshe abun ya ci tura itama hankali nata tashi yayi,

Mama Lami tana cikin yi musu nasiha Hannatu ta turo ƙofar fuska ba walwala da sauri sauri suka tashi suka ƙarasa inda take tare da tambayan ta a tare,

“Maman Halifa ta haihu!,” girgiza kai tayi a sanyaye tace “A’a har yanzu dae da saura amma tace in ce ku kira mata Gidado sannan ku ma ku shigo, tana son magana daku,”

“ku shiga ni bari naje na kira Gidadon,” Mama Lami ta faɗa tana ficewa daga gidan, juyawa suka yi tare da shiga ɗakin ita kuma Hannatu zauna a nan hankali tashe,

Kwance suka samu Daadah tana fitar da numfashi da kyar, da sauri suka ƙarasa kusa da ita tare da durƙusawa,

“Daadah!!” Ni’imah ta faɗa tana hawaye, Daadah buɗe kumburarrun idanun ta tayi ta ɗaura a kansu, a hankali ta ɗaga hannun ta tare da miƙo musu, hannun su suka ɗaura akan nata, rumtse hannun nata tayi a cikin nasu, murya bata fita sosai tace “ina Gidado nah!,”

“Mama Lami taje taho dashi,” Nimrah da tafi Ni’imah juriya da dakewa ta faɗa, lumshe ido Daadah tayi sannan ta buɗe ta fara magana a hankali,

“Ni’imah! Nimrah! Ga Gidado nan na bar muku amanar shi!, dan bana jin zan iya tashi dan!, Allah ku kula mun dashi!, kar ku bari yayi kukan maraici! ku zame mai Uwa sannan ku zame mai Uba! kuma ina so dan Allah duk yanda rayuwa zata je ta dawo kar ku taɓa zubar da mutumcin ku na ƴaƴa mata! duk rintsi koh da kuwa ya kama bara zaku yi ci toh hakan shi ya fi muku! sannan ku riƙe junan ku a na ƴan uwa kar ku bari koh da wasa wani yayi ƙoƙarin shiga tsakaninku! Baba Rabe da Mallam Buba kuma kuma iyayen ku ne ku riƙe su gam sannan a ƙarshe ina umartar ku da koh me Gwaggo zata yi muku a duniyan kar ku taɓa ɗaga ido ku kalle ta balle ku musa mata ita ɗin uwa ce a gare ku! Allah yayi muku albarka!!!,” a dae² aka kai stage ɗin da Ni’imah ta fashe da kuka me ban tausayi ga me sauraro, ita dae Nimrah hawaye ne ke tsiyaya, buɗe baki Daadah tayi zata ƙara yin magana Gidado ya buɗo labulan ɗaki ɗaga ya shigo tare da ƙarasowa inda take da sauri ya faɗa cikin ta yana cewa “Daadah nah kin tashi! Ya jikin naki?,” ɗan murmushi ta ƙaƙaro sannan ta buɗe baki a hankali tace “Gidado nah Daadah ta kusa warkewa gabaki ɗaya!,” murmushi shima yayi ganin itama tana yi mishi, janyo shi tayi ta ƙara rungume shi sosai a jikinta tana ajiyar zuciya, sun jima a haka daga su kuwa su da Nimrah kowacce da tunanin da take yi, jiyo muryar Gidado suka yi yana cewa “Daadah nah! Daadah nah! ya naji kin shiru! Bacci kika yi ne?,” da hanzari suka miƙe suka matsa kusa da ita, taɓa ta suka yi suka ji shiru,

“Maman Halifa! Maman Halifa!!” Nimrah ta kwallawa Hannatu kira, da sauri ta shigo tana ƙarasowa ganin Nimrah na nuna mata Daadah, hannu ta kai tare da taɓa jijiyoyin hannun ta……………………………

 

 

 

 

 

 

_Ni fah ban ganewa shin littafin *💫⛓️⚔️YANKAN ƘARFE⚔️⛓️💫* yana yi mu ku daɗi? Koh kuwa na huta abuna😎_

 

 

 

*@Hanyluv✍🏻*
*07044454719📲☎️*

Leave a Reply

Back to top button