Yankan Karfe 13-14
*💫⛓️⚔️YANKAN ƘARFE⚔️⛓️💫*
~Written By~
*Hanyluv✍🏻*
*Free page*
*Page 13 & 14*
“Yanzu ni sam ban san me zanyi ba Khaleel, idan ban tafi ba Abba zeyi fushi idan kuma na tafi Mami zata yi fushi dani kuma fushin ta se yafi na Abba, sannan fushin ta yafi dafa ni! ya fi tashar mun da hankali! haka kawae ta fara fushi dani nake jin komai na rayuwa ta ya tsaya cak! koh aikin ma bana iyawa! ni sam yanzu ban san ta inda zan fara ba,” se da Khaleel ya nisa sannan ya fara magana,
“Saheel! kasan dae bazan taɓa faɗa maka abun da ze cutar da kai ba koh?,” ɗaga kai Saheel yayi, jinjina kai Khaleel yayi sannan ya cigaba da magana,
“Good! in dae zan faɗa maka gaskiya toh kabi abun da Abba yake so! saboda abun nan da yake so kayi nan gaba ba ƙaramin alfahari zaku yi da haka ba hatta Mami ina me tabbatar maka se tayi alfahari da kai a wannan lokacin yanzun din ma kawae soyayya ne ya rufe mata ido, kuma shawaran da zan ba ka a ƙarshe shi ne muddin zaka tafi kar ka bari kuyi sallama da Mami saboda hakan shi ze karya mata zuciya har ya jawo ranta ya ɓaci tayi fushi da kai sannan kuma da zaran ka dira UK🇬🇧 se ka kira ta ka sanar da ita tafiyan bazata ne ya zo maka amma baza ka daɗe ba, ka rarrashe ta sosai kuna gama wayan se ka canza SIM card ka ajiye tsohon, ni kaɗai zaka dunga kira da shi tunda dama kace Abba har kaje ka gama abun da za kayi bakwayin magana saboda yace tunda ya damƙawa Mami komai, ba se yaji abun da ke going ba…”
“what if ta gane na canza SIM card? ba ka tunanin ranta ze ɓaci fiye da tafiya ta? za ta ga a matsayin ta na mahaifiya ta har zan iya canza SIM ba tare da na sanar da ita b…,” katse shi Khaleel yayi
“wa yace maka zata sani? Koh kai ne zaka gaya mata? Koh kuma ni kake tunanin zanje na sanar da ita ka canza SIM?” girgiza kai Saheel yayi sannan yace “that’s not wat i mean, idan Mami bata jini ba zata shiga damuwa,”
“kar ka damu ni zan dunga zuwa ina kwantar mata da hankali, zance mata wajan SIM din wayan ka ne ya lallace, ka kai gyara ance baze gyaru ba kai kuma baka son canja waya saboda abubuwan ka dake cikin wannan, so yanzu dae Whatsapp kawae kake yi shiyasa ka siya WiFi don yin amfani dashi, dama ka ce mun ita bata iya su Whatsapp, Instagram da dae sauran su ba koh?,” ɗaga mai kai yayi,
“Yawwa toh kaga mun samu hanyan da zamu fake, kuma dae yanda nasan baka shiri dasu Nadiyyah baza tace su amsa numbern ku dunga magana ta wajan su ba,” jinjina kai Saheel yayi alamun gamsuwa sannan yace “Alright no problem, se ayi hakan, Allah dae ya bawa Mami juriya!” ya ƙarashe faɗa tare da lumshe idanun shi, shi dae Khaleel kawae bin shi yake yi da kallo don shi soyayyar dake tsakanin Mami da Saheel mamaki yake bashi, sun jima suna fira daga bisani suka tashi suka rankaya gidan su Saheel dan Khaleel na son gaishe da Abba yayi mai barka da zuwa……
_______________________________
Tunda aka fara shirya Daadah har aka kimtsa ta aka fita da ita Nimrah bata farfaɗo ba, ita kam Ni’imah ta sha kuka har ta godewa Allah, Gidado na rungume jikin ta dan tunda yaga duk suna kuka shima ya fashe da kukan damma dae shi sam be san me ake nufi ba shi dae yaga anata kuka shi ne shima ya biye, suna nan zaune a tsakar gida maza suka fara shigowa alamun an dawo daga kai Daadah Allahu Akbar nan Ni’imah ta ƙara fashewa da wani sabon kukan wanda yasa Mama Lami da wasu daga cikin mutanen dake zaune a gurin hawaye, sosai tausayin yaran ya ɗarsu a cikin ransu, gyaran murya Baba Rabe yayi sannan ya ɗaga hannu ya fara koro addu’o’i gabaki ɗaya mutanen gurin na amsawa da “Ameen,” ya jima yana addu’a daga bisani aka shafa, bayan an shafa a hankali ya fara magana cike da nasiha,
“Kullu nafsin za’ikatil maut! wato haka Allah SWA yace, duk mai rai ze zama mamaci! da ni da kai da ke babu wanda ze dauwama a duniya! tun kafin kazo duniya aka rubuta tsawon lokaci da zaka yi, wani idan yazo awa ɗaya ze wani yini ɗaya wani kwana ɗaya wani wata ɗaya wani shekara ɗaya tafi² dae har sama, Allah shi ke ƙa’ide maka tsawon lokacin da zaka yi! Shine me rayawa da kashewa! Kuma ba ya barin wani dan wani! Sau nawa ze ɗauke wanda yake kula da me mara lafiya sannan ya bar mara lafiyan da ranshi! haka zalika ya kan ɗauki uwa yar ɗa! Kuma kar kuyi tunani wae baya son ɗan ne shiyasa ya ɗauki Uwar, A’a koh ɗaya! Kawae dae yana so mutum ya ɗauki hakan a matsayin jarrabawa! muddin ka yi haka toh Insha Allah zaka cinye ta! Dan haka ina so ku ɗauki dangana kusa aranku cewa Allah ya isa shiyasa ya yi muku haka, sannan Insha Allah baza ku tagaiyara ba!,”
“Bi’iznillahi,” Mallam Buba ya faɗa cike da jimami, sosai Ni’imah take kuka kaman zata shiɗe,
“Ya isa haka Nimrah, haquri zaku yi ina ita Ni’imahn?” Mallam Buba ya faɗa dan gabaki ɗaya ƙauyen ba sa gane su, ta in da ake gane su ita Nimrah masifaffiya ce ita kuma Ni’imah babu me haquri ce,
“ai ga Ni’imahn nan Nimrah kam tun da akayi rasuwa ta suma har aka fitar da ita daga gidan nan bata farfaɗo ba!,” Mama Lami ta faɗa a sanyaye,
“subhanallahi! Tana ina ne?,”
“tana ɗakin su,”
Da hazari Baba Rabe da Mallam Buba suka miƙe tare da nufan ɗakin su Nimrah, biyo su a baya Mama Lami tayi,
A kwance suka same ta kaman yanda aka barta, ƙarasawa suka yi tare da zama daga gefen ta,
“Lami samo mun ruwa a kofi!,” Baba Rabe ya faɗa yana kallon Mama Lami,
“Toh” tace tare miƙewa ta fice daga ɗakin, bata jima ba ta dawo hannun ta riƙe da kofi, ta miƙawa Baba Rabe, amsa yayi yace “yawwa toh ɗan ɗago ta ki rungumo ta,”
“Toh Mallam,” tace sannan ta zauna tare da rungumo Nimrah jikin ta, yan addu’o’i Baba Rabe yayi tare da tofawa acikin ruwan sannan ya zuba ruwan a hannun shi a hankali ya shafa a fuskar ta ta,se da ya shafa mata sau uku sannan ta sauke wata doguwar ajiyar zuciya, jim kaɗan ta fara bude idanun ta ahankali² har ta bude su gabaki ɗaya, binsu take yi da ido,
“Sannu Nimrah!” Mallam Buba yace,
“Nimrah! Ya kike jin jikin naki?” Baba Rabe ya tambaye ta, shiru tayi babu wanda ta iya bawa amsa acikin su,
“Nimrah me zaki ci a kawo miki?” Mama Lami tayi tambayan tana shafa kanta, nan ma dae shiru tayi,
“Yanzu dae ki samo mata abin da zata ci, da alama jikin nata babu kwari shiyasa baza ta iya amsa tambayoyin nan ba,” Baba Rabe ya faɗa suna miƙewa shi da Mallam Buba amsa mishi Mama Lami tayi cikin ladabi da biyayya, hannu yasa a aljihu ya ciro dubu biyar ya miƙa mata sannan suka fice daga ɗakin, janyo filo Mama Lami tayi tare da kwantar da Nimrah sannan ta fita dan nemo musu abin da zasu ci, bata jima ba ta dawo hannun ta ɗauke da flask🧂 da kuma bread🍞dasu madara a bakan leda, da soyayyan ƙwai tare da cups ,ajiyewa tayi sannan ta fice daga ɗakin, inda su Ni’imah ke zauna ta je tare da ɗago ta sannan ta riƙo hannun Gidado suka nufo ɗakin, Allah Sarki Gidado jiki duk yayi laushi sosae yake jin yunwa dan shi ba ya iya jurewa yunwa, bayan sun shigo suka zauna kusa da Nimrah dake kwance,
“Ku matso ku karya dan dae nasan yau duk baku ci komai ba!” Mama Lami ta fada tana ƙoƙarin haɗa musu tea☕️, ai kuwa da sauri Gidado ya matso jiki na rawa, bayan Mama Lami ta gama haɗawa ta miƙa mishi ya amsa hannu na ɓari sannan ta yanko biredi da soyayyan ƙwan ta ɗaura a plate🍽️ta ajiye a gaban shi, gani tayi ya tsaya yana kallon ta ba tare da yaci,
“Ci mana Gidado,” jinjina kai yayi sannan ya fara ci, hakan yana daga cikin tarbiyyar da Daadah tayi musu basa taɓa cin abu se an basu dama,
“Ni’imah ga naki,” Mama tace tana mai miƙa mata, zirrr wasu zafafan hawaye suka zubo daga idanun ta, murya a shaƙe alaman anci kuka tace “Mama bazan iya sha ba, koh kaɗan ba na jin yunwa,” cike da ban tausayi Mama Lami ta matso tare da riƙo hannun ta, ta fara yi mata nasiha mai kashe jiki se da taga nasihan ta shige ta sosai sannan ta miƙa mata tean da bread🍞 da soyayyan ƙwa, amsa tayi jiki a sanyaye ta fara ci, ita dae turawa kawae take yi amma tamkar magani haka take jin su, haɗawa Nimrah ma Mama Lami tayi sannan ta ƙarasa in da take a kwancen,
“Nimrah! Nimrah! Tashi ki karya kema,” a hankali ta buɗe lumsassun idanun ta sannan ta mai dasu ta rufe ruff! ajiyewa a gefe Mama Lami tayi sannan ta zauna tare da rungumo ta jikin ta tana ƙara kiran sunan ta, sam ta kasa buɗe idanun nata tarr, a haka dae Mama Lami ta fara ƙoƙarin bata tean amma sam ta ƙi amsa se da ta tursasa ta sannan tasha tean ɗan kaɗan banda bread da soyayyan ƙwan, Gidado kam yana gama nashi yayi hamdala sannan ya kalli Ni’imah yace “Adda a haɗawa Daadah a kai mata dan nasan yanzu itama tana jin yunwa!” juyawa Ni’imah tayi tare da lumshe ido hawaye na zuba dan ita babu wanda tafi ma tausayi irin Gidado, ya ya zeyi idan ya daina ganin Daadah?,
“Gidadon Daadah kenan! Ae tun ɗazu aka kaiwa Daadah nata, yanzu dae tunda ka gama ci bari azo ayi wanka koh? koh baya son yin wanka?,” Mama Lami tace cikin sigar zolaya da kuma kawar da zancen da ya ɗakko, washe baki yayi sannan yace “Mama ina so mana, ni bana son ƙazanta,”
“Yawwa,” tace sannan ta fice daga ɗakin,
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, sosai Mama Lami da Baba Rabe suke bawa su Ni’imah wata kulawa ta musamman dan tunda akayi rasuwan Mama Lami ta dawo gidan da zama kasancewar dama bata ƴaƴa saboda su Allah be basu haihuwa ba, sam Nimrah har yau bata dawo daidai ba, kwata² ta daina magana koh tambayan ta akayi se dae ta bi mutum da idanu babu ma abunda yake damun Mama da Ni’imah irin har yau Nimrah bata yi kuka ba alamun abun yana nan yana cin ta a ranta, Gidado kuwa koh da yaushe se ya dame su da tambayan ina Daadan shi se dae su basar dashi daga ƙarshe ma Mama tace ai tayi tafiya tace se ya gama karatun shi zata dawo, sam baji dadi ba amma yanda Mama take ta jan shi aji yasa ya ɗan manta, haka koh da yaushe da Mama Lami da Ni’imah suke zama kusa da Nimrah suna kwantar mata da hankali amma se dae kawae ta dunga bin su da ido.
Yau ya kama kwana shida kenan da rasuwan Daadah, Abboh kuma kwana bakwai, anyi addu’a a gidan sannan akayi ma a masallaci, Ni’imah dae ta ɗauki dangana yanzu babu wanda ake shafa se Nimrah, har da addu’o’i Baba Rabe yake haɗa mata.
Da daddare Baba Rabe da Mallam Buba suka tara su a tsakar gida, dukkan su suna zaune jungum kaman yau akayi rasuwan, gyaran murya Baba Rabe yayi sannan ya fara da nasiha, idan ya ajiye se Mallam Buba ya ɗauka, haka sukai tayi har suka kai inda suke so sannan shiru ya ziyarci tsakar gidan, daga bisani a hankali Baba Rabe ya fara magana.
“Toh Allah ya kawo mu lokaci, muna fatan Allah ya jiƙan waƴanda suka riga gaskiya!,” da “Ameen,” suka amsa, ya cigaba da
“yanzu dae babu yanda za ayi nima a amatsayi na na mahaifin ku na barku ku cigaba da zama a gidan nan ku kadai babu wani babba ba, shiyasa ni da Mallam Buba muka yanke shawarar a yau din nan zaku koma gida na da zama sannan zaku kasance a ƙarƙashin kulawa ta Insha Allah…,”
“A wanne dangin! kai a wa? Meye haɗin ka dasu da har zaka yanke wannan hukunci! toh wallahi baka isa ba! kayi kaɗan!,” suka ji maganan daga sama, ɗagowa suka yi suna binta da kallo………….
_Alhamdulillah naji sauqi, Nagode sosai da kulawan ku, Allah ya saka da alheri🙏🏻🥰_
*@Hanyluv✍🏻*
*07044454719📲☎️*
_Chat me through this👇🏻_
*09129251300🤳🏻*