Hausa NovelsYankan Karfe Hausa Novel

Yankan Karfe 11-12

Sponsored Links

*💫⛓️⚔️YANKAN ƘARFE⚔️⛓️💫*

 

 

 

 

~Written By~

 

 

 

 

*Hanyluv✍🏻*

 

 

 

 

 

*Free page*

 

 

 

*Page 11 & 12*

 

 

 

 

Da hanzari suka miƙe suka matsa kusa da ita, taɓa ta suka yi suka ji shiru,

“Maman Halifa! Maman Halifa!!” Nimrah ta kwallawa Hannatu kira, da sauri ta shigo tana ƙarasowa ganin Nimrah na nuna mata Daadah, hannu ta kai tare da taɓa jijiyoyin hannun ta, cak ta tsaya zuciyar ta na bugawa dab! dab! dab!

“Maman Halifa lapia! wani abun ne ya same ta?,” Nimrah ta faɗa tana riƙo Hannatu, ji tayi kaman an sa zip an rufe mata bakin ta, sam ta kasa magana idan ma zata yi bata san ta inda zata fara ba, da sauri Mama Lami ta shigo jin maganan da Nimrah tayi, kallo ta bisu da shi daga Daadah ta har su da Hannatu dake tsaye kaman an dasa ta, tuni ta fahimci abun da yake faruwa, ƙarasawa tayi tare da janye Gidado a jikin Daadah sannan ɗauki zanin da ke gefe ta rufe gabaki ɗaya jikin ta dashi, tuni Ni’imah ta fahimci me suke nu da sauri ta fice tare da fashewa da zazzafan kuka, bin bayan ta da ido Nimrah tayi kaman sakarya sannan ta juyo tana kallon Mama Lami murya na rawa tace “Ma.. Mama.. Lami mey.. meyasa kika rufe ta… Bacci take yi ne?,” a hankali Maman Lami ta riƙo hannun ta cikin murya ta rarrashi ta fara magana,

“Nimrah! Allah shi ne Allah! Allah ya kan jarabci bawanshi a da duk sanda ya so haka kuma a duk lokacin da yaso! Sannan Allah ba ya barin wani dan wani! Duk abun da ka ga Allah ya yi maka ka karɓe shi da hannun bibbiyu walau me kyau walau mara kyau! Allah yana son me yarda da ƙara! haka zalika cikakken musulmi shi ne me yadda da ƙaddara! Nimrah ina so ku ɗauki wannan a matsayin ƙaddara! Allah ne ya halicci Hadiza haka zalika shi ya karɓi abarsa a yanzu! A yanzu babu abun da take buƙata daga gare ku illa addu’a!!,” cak komai na Nimrah ya tsaya, tunanin ta! ganin ta! jinta! da numfashin ta duk suka tsaya cak,

“Nimrah! Nimrah! Nimrah!,” Mama Lami ke kiran sunan ta tana jigjiga ta ae ina luuuuuu! Nimrah ta tafi tare da faduwa alamun ta suma…….

__________________________

Be tsaya a koh ina ba se a ƙofar gate din gidan su Khaleel, horn yayi me gadi ya ƙaraso tare da wangale mai gate ni, tura hancin motar shi yayi tare da shiga gidan, parking lot ya ƙarasa yayi parking sannan ya fito koh tsayawa amsa gaisuwan me gadi be yi ba ya wuce part din Khaleel dan yasan iyanzu yana can, a bakin ƙofar yayi knocking, be fi 15sec ba Khaleel ya ƙaraso ya buɗe, da kallon mamaki ya bishi tare da cewa,

“Ah Guy lapia zuwa babu alerting?,” be ce mishi uffan ba ya raɓa ta gefen shi ya shiga cikin parlorn, girgiza kai Khaleel yayi sannan ya maida kofar ya biyo bayan, zama yayi shima Khaleel ya zauna a kusa dashi ya karantar shi,

“Saheel lapia? Me ke damun ka?,” Khaleel ya yi maganan da alamun damuwa, jingina kai Saheel yayi a kan kujera tare da lumshe idanun shi, ya kai tsawon 30mins a haka ba tare da ya buɗe idon ba haka ba tare da yace uffan ba, shima Khaleel shirun yayi tare da zuba mai ido, daga bisani yay ajiyar zuciya tare da buɗe shanyayyun idanun shi ya ɗaura akan Khaleel, shima Khaleel ɗin idanun shi na kan Saheel, ɗaga mai gira yayi alamun yane! sannan ya fara magana a hankali,

“Saheel meke damun ka ne na ganka haka? koh dae wata ciks ce ke buga maka kai?,” wata muguwar harara Saheel ya balla mai sannan yace “Se kuma aka ce maka ni ɗin irin ka ne! Ni sam ba na tunanin akwai yarinyar da ta isa ta juya mun kai!,”

“A Dar bar cika baki dan kar lokaci ya zo na tuna ma mutum yace be faɗa ba,” Khaleel ya faɗa yana dariya,

“Mtwwwss!,” Saheel yaja tsaki sannan ya cigaba da magana,

“Lets keep this a side! koh ka tambaye ni meke damuna ma,” taɓe baki Khaleel yayi yace “Sau nawa kake so nayi maka wannan tambayan? Nan da nake ta faman tambayan ka koh kallo na ma kayi ne?,” girgiza kai Saheel yayi yana ɗagowa,

“Kai banza ne! Wa yace maka ana tambayan mutum idan ya shigo a irin wannan yanayin! ae se ka bari na dawo cikin hayyaci na koh”

“Mtwwss! Toh kar ka dawo cikin hayyacin naka mana dan Ubanka,” murmushi Saheel yayi wanda har se da dimple ɗin shi ya lotsa sannan ya fara magana kaman ba ya so, kab labarin abunda ya faru ya kwashe ya bashi, a ƙarshe ya ƙarasa da cewa,

“Yanzu ni sam ban san me zanyi ba Khaleel, idan ban tafi ba Abba zeyi fushi idan kuma na tafi Mami zata yi fushi dani kuma fushin ta se yafi na Abba sannan fushin ta yafi dafa ni! ya fi tashar mun da hankali! haka kawae ta fara fushi dani nake jin komai na rayuwa ta ya tsaya! koh aikin ma bana iyawa! ni sam yanzu ban san ta inda zan fara ba,” se da Khaleel ya nisa sannan ya fara magana……………….

 

 

 

 

_Dan Allah ayi haquri da wannan wallahi ban jin daɗi ne😰👏🏻👏🏻👏🏻_

 

 

 

*@Hanyluv✍🏻*
*07044454719📲☎️*

Leave a Reply

Back to top button