Hausa NovelsYankan Karfe Hausa Novel

Yankan Karfe 15-16

Sponsored Links

*💫⛓️⚔️YANKAN ƘARFE⚔️⛓️💫*

 

 

 

 

 

~Written By~

 

 

 

*Hanyluv✍🏻*

 

 

 

 

 

*Free page*

 

 

 

 

 

 

*Page 15 & 16*

 

 

 

 

 

“A wanne dangin! kai a wa? Meye haɗin ka dasu da har zaka yanke wannan hukunci! toh wallahi baka isa ba! kayi kaɗan!,” suka ji maganan daga sama, ɗagowa suka yi suna binta da kallo, Gwaggo ce ta shigo fusace tana binsu harara se faman karkaɗa ƙafa take yi, cike da takaici Mallam Buba ya fara magana,

”Haba Asiyah ai be kamata kizo kina gayawa Mallam Rabe irin waɗan nan maganganun ba, don dae yanzu ae ya fi ƙarfin a kira shi bare tamkar ƙanin ki Ballo yake a wajan k..” katse shi tayi,

“yi mun shiru! Ah ah Ubana ne ba ƙani na ba! Wato munafiki harda kai ake kitsawa koh! toh wallahi babu inda yaran nan zasu je daga nan se gidana! se ƴaƴan ƙanina ne!,” girgiza kai Mama Lami tayi cikin ɓacin rai da takaicin munanan hali irin na tace “amma dae Asiyah kinyi asara! ba ƙarama ba ma kuwa! Ace ɗan uwanki ya rasu baki tako gidan sa ba! Matar shi ma ta rasu baki tako ba! Se yanzu kuma saboda ke baki san Allah ba ki wani zo ki fara kumfar baki akan zaki ɗauki ƴaƴan su! Toh wallahi ba jini ba koh hanta kuka haɗa da baban nasu baki isa ki tafi dasu ba! Dan dae nasan muddin kika ɗauki yaran nan se kin kashe su kaman yanda kika kashe babban su!,” katse ta Baba Rabe yayi,

“Subhanallahi! Haba Lami! Ban sanki da irin halin nan ba! ni a sanin da na yi miki nasan kina da haƙuri da kawar da kai!”

“Ah ah ae da ka barta! ta faɗi duk abun da take so yara ne dae baza ki tafi dasu ba!,” girgiza kai Mama Lami tayi tace “hakane Mallam, yanzu ɗin ma raina ne ya ɓaci sannan kuma na fuskanta matar nan bata san mutumci ba! ta ya za’ayi ina ji ina kallo ta dunga faɗawa mijina duk maganan da ya fito bakin ta! toh idan ita bata san darajar miji ba ni na sani!,” girgiza kai yayi yace “Toh shikenan kiyi haƙuri! ae wannan ba komai bane yanda take yaya wajan aminina Ballo nima yaya ta ce don haka duk abun da zata faɗa ta isa ne,” taɓe baki Gwaggo tayi sannan tace “Haram! kar ka ƙara kira na yayar ka! ni ba yayar ka bace kuma bazan taɓa zama yayar ka ba! ku ni ku dakata ma ba wannan surutun banzan ne ya kawo ni ba! ɗaukan yara nazo yi dan haka! kai ku taso mu tafi!!,” ta faɗa tana kallon su Ni’imah, Ni’imah da jikin ta ya fara rawa don dae ita a duniya idan da akwai wanda take tsoro to be wuce Gwaggo ba, baki na rawa tace “Mu dai dan Allah Gwaggo ki barmu wajan Baba Rab..,” wata irin tsawa da ta daka mata se da zabura tare da matsawa jikin Mama Lami,

“Dan Uban ki ni nake magana kina maida mun! Yaushe na fara wasa da ke!,” a fusace Mama Lami ta miƙe,

“kar ki ƙara zagin Uban su! Dan dae a yanzu idan baza ki yi mai addu’a ba toh ki daina aika mai da zagi! har a haka ne ma kike wani ikrarin shi ɗin ɗan uwanki ne? Toh wallahi yaran nan dae baza su bi ki ba! tun a yanzu ma ki nuna idan kin tafi dasu gallaza musu zaki dunga yi!” sosai Ni’imah da Gidado suka ƙwaƙume a bayan Mama Lami, Nimrah kuwa babu abun da take fahimta illa ido da ta zuba musu,

“Haka kika ce? toh shikenan ki jira ki ga abun da ze faru!,” ta faɗa tare da juyawa, rakata Mama Lami tayi da cewa “Insha Allah babu abun da za mu gani se alheri!,” ficewa tayi daga gidan tana bambami, shi dae Baba Rabe shiru yayi don beyi tsammanin halin Yaya Asiyan ya kai haka ba, shi kuwa Mallam Babu babu abun da be sani ba a cikin halin Gwaggo ba dan yasan ma zata yi abun da yafi haka, sannan shi abun da ke damunsa ma yanda duk abun da zata yi baya iya taka mata burki, sam tafi ƙarfin shi har tsoro yake yayi mata magana idan tayi wani abun, komawa Mama Lami tayi ta zauna tare da janyo su Gidado jikin ta tace “ku sha kurumin ku Insha Allah babu inda zaku bi muguwar matar nan!,”

A ranar su Baba Rabe suka tattara suka tafi dasu gidan su…..

______________________________

 

Zaune yake a kan bed ɗinshi ya tasa laptop💻 a gaba yana dube², ringing wayan shi yayi ya miƙa hannu ya ɗakko, Manager Mahmoud ne ya bayyana a kan screen ɗin, picking yayi tare da karawa a kunne,

Assalamu alaikum! barka da war haka Sir,” a ka ce daga ɗaya ɓangaren, amsawa Saheel yayi tare da tambayan shi

“Lafiya dae! naga kiran ka a irin wannan lokacin,”

“Yes, everything is alright but there’s a little problem!”

“Problem?” Saheel ya faɗa yana janye laptop💻 din dake gaban shi, daga ɗayan ɓangaren yace “Yes Sir, dama akan waƴan nan Companies ne da suke bukatan ayi musu zane! so we meet up amma sunce wae da kai kaɗai suke son suyi magana, kuma gobe ne dateline din da na basu!,” jinjina kai Saheel yayi sannan yace “Okay no problem! I will be there tomorrow Insha Allah, just fix the meeting by 3!” da mamaki Mahmoud ya amsa da “Okay Sir, thank you,” dan be taɓa tunanin baze yi mai faɗa ba saboda sau da yawa idan hakan ta faru se yayi ta faɗa yace ba a faɗa mai da wuri ba shi yayi sallama da Mamin shi wani zubin cewa yake baze zo ba amma yau first in history be musa ba, daga nan suka yi sallama ya katse kiran, a cikin daren nan yayi booking ticket🎫 na 6:30am, bayan ya gama ya kashe laptop💻 din ya ajiye a bedside drower ya kashe bobs din ɗakin sannan ya koma tare da yin addu’a ya shafe jikin ji da shi ya kwanta…

Tunda akayi sallahr asuba ya dawo ya fara shirin tafiya, dama ya rigada yayi wanka tun kafin ya tafi sallah, tsab ya kintsa cikin black suit yasa wani kyakkyawan glass, rass ya fito kaman wani balarabe, ya fitowa daga part ɗin nashi yayi hannunshi riƙe da trolley, ƙarasowa parking lot yayi da sauri Sani Driver dake jiran shi daga gefe ta ƙaraso tare da buɗe mai ƙofan, shiga Saheel yayi Sani ya ɗauki trolleyn ya saka a booth sannan ya dawo da sauri tare da yi wa motar key, wangale musu gate Me Gadi yayi yana ɗagawa Saheel hannu suka fice daga gidan,

Suna ƙarasawa airport Sani ya fara ƙoƙarin fita ya buɗe mai kofa da sauri ya dakatar dashi,

“No thanks! zan buɗe da kaine,” buɗewa yayi ya fice Sani ya ɗaga murya yana cewa “Alhaji Allah ya kiyaye hanya! Allah ya dawo da kai lafiya! Allah yasa maƙiyan ka su zama takalmin ka!,” ba tare da ya juyo ba ya shige,

6:30am dot! Jirgin✈️ su ya ɗaga zuwa UK🇬🇧, 1:10pm suka dira, Mahmoud na nan yana jiran shi a waje, fitowa kowa ya fara yi a hankali², can ya hango Saheel ya fito yana tafiya cikin ƙasaita yanda kasan wani Sarki, shi dae Mahmoud har yau yana mamakin irin na Saheel, koh kwana ɗaya yayi be ganshi ba se yaga ya ƙara mai kyau, sam be ma san ya ƙaraso inda yake ba se da yaji maganan shi yana cewa “Hey! are you Okay? what’re you thinking of?,” daburburcewa Mahmoud yayi ya amsa trolley din shi yana cewa “U’re welcome Sir! how’s the flight?” ya ƙarashe faɗa yana buɗe mai mota, shiga Saheel yayi yana amsawa da “Fine Alhamdulillah,” buɗe booth Mahmoud yayi tare da saka trolleyn sannan ya dawo Driver seat ya zauna tare da yi wa motar key suka bar airport ɗin, gida direct ya wuce da shi, dama already an sa masu aiki sun gyare gidan tass! sannan sunyi abincin da za’a tarbe shi dashi, duk Mahmoud ne ya tsara hakan sosai gidan ya haɗu dan ya ninka wanda suke zaune a Nigeria kasancewar ginin ƙasar waje da nan ba ɗaya bane, koh da suka shiga gidan Saheel be tsaya a koh ina ba se a bedroom ɗinshi, yana shiga ya kwaɓe sannan ya shiga bathroom🚿, ya ɗan jima sannan ya fito ɗaure da towel a ƙugun shi da ɗan ƙarami a hannun shi yana goge suman shi, Mami ce ta faɗo mai ya ƙarasa gaban bedside drowern shi ya ɗauki wayan shi dake kai, zama yayi tare da canza SIM card sannan ya shiga dubo numbern ta, My world❤️ ya binciko sannan ya danna mata kira, ringing wayan yake yi amma ƙirjin shi bugawa yake yi yana tsoron abun da ze faru, ita dae Mami acan da mamaki taga kiran Saheel da numbern shi na Uk amma dae bata kawo komai ba tayi picking, Saheel na jin tayi picking ya lumshe idanun shi sannan a hankali yayi sallama………..

 

 

 

_Toh me karatu koh ya zata kaya tsakanin Saheel da Mami?🤔_

_Allah dae yasa kar Mami ta tursasa shi ya dawo Niger😰_

 

 

*Wannan littafin ₦500 ne*
*Za’a iya fara biya kafin free pages ya qare‼️*
*Send via*
*1467362098*
*Muhammad Hanifa*
*Access bank*

_*evidence of payment through 09129251300 WhatsApp number*_

 

*@Hanyluv✍🏻*
*07044454719📲☎️*

_Chat me through this👇🏻_
*09129251300🤳🏻*

Leave a Reply

Back to top button