Yar Zaman Wanka Book 3
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
2️⃣1️⃣➡️2️⃣2️⃣
Suna zuwa falon Imran ya ja tunga ya tsaya yana ƙoƙarin danne dariyar da take son fitowa ba tare da ya shirya ba, dan yadda ya ga Inna ta wani biyo su kamar wanda suka yi wani gagarumin laifi sai wani muzurai take kamar ta yiwa sarki ƙarya. Sadiya ma sai da suka dangana da falon ta fara jin haushin gudun famfalaƙin da suka yi, dan abin na Inna ya wuce misali.
Inna na fitowa falon ta kasa ta tsare riƙe da makamanta, kallonsu kawai take tana jin haushinsu gabaɗaya, dan kawai gani take shegiyar jaraba ce da rashin haƙuri ya sa suke nema su jiƙawa mutane aiki su ɓallo ruwan da tsayar da shi zai yi wahala, amma fa in ji Inna. Imran ƙarasawa kan kujera ya yi ya zauna tare da wani hakimcewa ya tattaro gabaɗaya jarumtarsa ya dake da ita, kamar ma bai san Inna na hasala tana hatare -harare ba kamar wacce aka yiwa ƙwacen kuɗi.
“Ni dai wallahi zuwa birnin nan da zaman gidan nan ya zame mini masifa da bala’i yo Allah na tuba idan ba masifa ba menene wannan a ce tun da na zo ZAMAN WANKAN nan da raina ban huta ba sai bala’i daga wannan sai wancan kullum da kalar wanda nake hantsilawa a ciki” Ta faɗa tana kallon Sadiya da ta sunkuyar da kai ƙasa.
Babu wanda ya tanka ta dan haka bata yi wata-wata ba ta cigaba da magana cikin hasala.
“Banda rashin mutunci a ce ina cikin gidan nan Imirana kake neman haikewa ƴar nan me ɗanyen jego, kenan ma bani da amfani? Ko dan baka san wahalar ɗaukan ciki da nakuda da kuma reno ba, abin da ka sani kawai ka yi fush ɗan ya faɗo duniya, ai ana barin halal dan kunya” Ta faɗa tana jin kamar ta hau Imran da duka.
“Dan Allah Inna ki yi haƙuri babu wanda ya san kin dawo ma gid…
“Rufe min baki algunguma, irinku ne daga an yi arba’in sai a ji kun fara amaye-amayen jaraba, har kin manta uwar wuyar da kika sha a naƙudar ku ne masu biyewa namiji ya ƙara ɗirka muku wani cikin saboda rashin sanin ciwon kai daga namiji ya fara muku daɗin baki sai ku bada kai bori ya hau a barku da wahala yo ciki da goyo ai wahala ne” Inna ta katse Sadiya cikin harzuƙa.
Shiru Sadiyar ta yi bata ce komai ba amma a zuciyarta sai ta ce
“Inna ke kika ga bala’i a zuwanki ko kuma mu muke ganin bala’i kala-kala, tun da kika zo wa ya huta jarabar yau da ban, ta gobe da ban, in ban da neman magana da hana rai sakat a ce muna cikin ɗaki ma sai kin bimu ko ke zaki yi rainon cikin” Cewar Sadiya a zuciyarta.
“Kai kuma Imirana na lura inda aka raba kunya ma baka bi ta wajen ba, lokacin da ake raba sanin ta ido kai kana bacci ina tsaye a ɗakin amma ka yi getse-getse riƙe da mace wai kai ɗan duniya ” Ta faɗa tana kafe Imran da ido tamkar za ta sakar masa muciyar a kansa.
“Matarki ce?” Cewar Imran cikin izza ya kuwa make kamar ma bashi ya yi maganar ba.
Sakin baki kawai Inna ta yi galala tana kallon Imran cike da mamakin kalamansa, ta ma rasa bakin magana.
“Na ga dai sadaki na biya ko kyauta aka bani ita, in kuma…
“Lallai in da ranka ka sha kallo, duk mai rai ba ya rasa ganin abin mamaki, Imirana ni kake cewa Halima matata ce, ban da dai ka ga makwancina, to bari in tuna maka idan mantawa ka yi, ni nan Azumi ni na haifi uban Sa’adiyya tun kafin ai ɗaran akay kwanɗi, da kai yaushe ma ka san Halimar yarinyar da ka san ta bayan uwarta ta gama cin fitsarinta da kashinta”
“Bari na je masallaci” Cewar Imran yana kallon Sadiya ya nuna ma kamar bai san Inna da shi take magana ba.
“Au ga mahaukaciya tana magana, shi yasa za ka barni ina ɓaɓatu, ni na ma rasa me ya kaini na baro ɗakina, ina cikin rufin asirina a gidan Malam na kawo kaina nan inda ake cire min zane a kasuwa, ban da dai ka gan ni a gidanka Imirana har ka isa ka yi watsi da maganar da nake ka ce wai masallaci za ka tafi, in ban da dai ka raina ni kuma kana so dai ka fice ka barni wato ga karya tana haushi, yo na ga yanzu ma aka fara kiran sallar ko gama kiran ma ba a yi ba amma wai kai ga sallau shi ne za ka yi riga malam masallaci” Ta faɗa tana share ƴar ƙwallar takaicin da ta sirnano mata.
Shi dai ko kallon inda take bai yi ba ya sa kai ya fice abinsa dan Inna ta fara kai shi bango tun baya son magana amma duk zuwanta ta hore masa baki tana sa shi yawan magana. Jan hanci ta shiga yi tana cigaba da share hawayen, Sadiya dai bata ce komai ba ta nemi wuri ta zauna.
“Halima kina jin wannan kurman mijin naki wai shi ma ya waye ya yi baki, wai har ni yake faɗawa magana son ransa”
“Haba Inna shi fa babba shi yake siya wa kansa mutunci, duk da kuna kakata amma ai dole ki ja girmanki yadda Imran zai ke shayinki amma a ce abin da huruminki ba kina shiga duk yadd…
Salatin da Inna ta ɗauka kamar ta ga gawar da aka yiwa kisan gilla shi ya sanya Sadiya jan bakinta ta yi shiru dan sai da ta faɗi maganar ma ta gane katoɓarar da ta yi dan ta san ko sama da ƙada za su haɗe babu za a yi Inna ta fahimci maganarta.
“Halima yanzu kenan kin zaɓi mijinki kin bar Kakarki wacce ta haifi ubanki, to in banda ma na haifi uban naki ta yaya ke za ki zo duniya amma kin zaɓi mutumin da kika haɗu da shi da haƙwaransa talatin da biyu kin ajiye ni, ni da na haifi ubanki har ke ma kika samu dirowa duniyar”
“Ba baka nake nufi ba Inna ke ɗaukan ƙafarki yake sanyawa ki ga laifin mutum…
“Ɗakko… na ce ɗakko, ɗaukan hannu gareni ba ɗaukan ƙafa ba, in banda kin raina ni Sa’adiyya har ma ke faɗi in faɗa, to shikenan ɗan halak ka fasa tun da Imirana kika zaɓa daga yau ko gani na yi ya haike miki kina neman ɗauki ƙur’anin Allah ba zan kai miki ɗaukin ba, tun dai kin ce namiji ubana ne akwai ranar ƙin dillanci ranar da za ki mutu marainiya, tun da duk wannan jihadin da na yi, ki kalli hannuna na dama taɓarya, na hagu muciya duk dan in ceto ki daga ɓarakar ɗinki da kuma ciki da goyo amma saboda ke ƴar ƙundun uba ce baki gani ba” Ta faɗa tana yin jifa da taɓaryar da muciyar ta koma inda ledar kayan marmarinta ta faɗi ta ɗakko da ta ajiye, ta juya tana cewa.
“Gwara ma in je in yi abin da zai fishshe ni, na tsaya ina gwagwarmaya ba magriba gashi har ana kiran ishsha’i, kar ma in je ina nan ina ta alkinta miki mafitar ɗa (HQ) Mala’ikan ɗaukan rai ya zo, tafiya da ni, a je a binne ni in zo amsa tambayar kabari na rasa bakin magana idan an ce Azumi me yasa baki yi sallar magriba a kan lokaci ba, kin ga bani da bakin magana, sai dai in ta jejjefa ido yo ai dai ba na buɗi baki ba in cewa mala’ikan ina can ina gwawarmaya da ƙartin mazan da suka saceni, sannan na dawo gidan na shiga ƙwatoki a hannun wancan jarababben mijin naki ba”
“Sacewa kuma Inna? Ke da kika tafi gidan Hajiya waye ya saceki kuma gwagwarmayar me kika yi sannan ya ka yi Inna kika kuɓuto?”
Wani mugun kallo Inna ta jefawa Sadiya kamar ta hauta da duka, ta juya ta fice daga ɗakin ta ɗauro alwala. Sai da ta jera sallolinta ta idar sannan ta tashi tiƙis-tiƙis ta fita jimawa kaɗan sai gata da plate da wuƙa da roba me ruwa a ciki, zaunawa ta yi ta ɗakko ledar kayan marmarin take sakawa a robar tana wankewa sai da ta ɗauki iya yanda take so sannan ta buɗe frige ta sanya sauran a ciki ta shiga yankawa tana cin abinta.
Kallonta kawai Sadiya take tana mamaki ko ta yi bata mata ba kuma ta ma rasa ina ta samo wannan uban kayan marmarin tili guda.
“Meye kika tsareni da ido sai kace wata tsohuwar mayyar da ta daɗe bata ci jariri ba?” Inna da ke kallon Sadiya ta wutsiyar ido ta faɗa lokacin da take yanko wata ƙatuwar abarba ta sa a baki.
“Haba Inna wace irin magana ce wannan ni ce ma tsohuwar mayya, to idan ma ni mayyar ce ai ke ce kat”
“Yo na sani ko wajen uwarki kika yi gado” Ta faɗa hankali kwance.
“Ni uwata ciki ɗaya ce, wai dan Allah Inna ina kika samo wannan kayan?”
“Halima kenan a tarar aradu da ka mana na samo su, dan ke baki san irin sadaukarwar da na yi ba na san da Malam zai san na damƙi mazaƙutar maza har uku wallahi duk da larura ce ta sa na yi hakan da har ya bar duniya da kishi zai mutu” Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma ta ce.
“Na faɗa miki saceni aka yi”
“Wai wace irin sata Inna, a sace ki kuma ki dawo har da kaya tili haka”
“Wallahi sace ni aka yi”
Kallonta kawai Sadiya take cike da mamaki
“Anya kuwa Inna bata fara shiriftun tsufa ba” Sadiya da ta yi niyyar faɗar maganar a zuciyarta bata san ta fito fili ba sai ji ta yi Inna ta ce.
“Bana son ƙaniyanci Halima, kar fa kaza ta tono wuƙar yankan ta fa, abin da kike min fa ya isheni tura ta kai bango aradu, ni ce nake shiriftun?”
“Allah Inna a raina na yi niyyar faɗa”
“Sai Allah ya toni asirinki ya fito min da ita fili na jita dama ai Allah ba azzalumin bawa bane”
“Yanzu dai ki yi haƙuri ki faɗa mini”
“Humm ke dai bari Halima ai yau na tsallake rijiya da baya, wallahi wani gida na je garin kallon gidan ƴan gayu wasu ɓarayi da suka zo satar wata mata muka yi arangama, aikuwa ji kike ƙiiii kamar sun samu tsohuwar motar da ta daɗe bata ga garejin gyaraba haka muka rinƙa nausawa daji kamar za mun doshi dajin sambisa, ke da na gaji dai na ga ana neman wuce gona da iri, ana neman a je a yi watanda da kaina, na yanke shawarar na fara yunƙurin ƙwatar kaina ta hanyar yin abin da ya dace” Cewar Inna tana gaftarar appale har tana lumshe idanu.
“Inna ba dai wani abin kika kwaɗa musu kika yi kisan kai kika gudo ba?” Cewar Sadiya a fili a zuciyarta kuma ta ce
“Na shiga uku kar dai tsohuwar nan ta sanyamu a uku a zo har gida a kame mu bamu ji ba bamu gani ba”
Ganin Inna tana ta dariya ko tsayawa bata yi sai Sadiya ta zuba mata ido kawai da mamaki.
“Wayyo Sa’adiyya ni na san abin da na yi yau wallahi ko ni na tuna abin da na yi sai na ji dariya da kunya sun kama ni, sai dai ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba, yadda na ringa shaƙe ƴaƴan mutane kamar Allah ne ya aikoni wallahi, daga na damƙi wannan sai na damƙi ta wancan” Cewar Inna a zuciyarta tana ta dariya tana hango yanda samarin suka yi ta zare ido daga zarar ta ƙwamuso al’aurar su.
Nan ta kwashe labari kaf ta faɗawa Sadiya, Sadiya kwa dariya har da riƙe ciki, tana ta mamakin Inna tabbas tsohuwar ta san kan mugunta amma kuma sanin muguntar tata ya mata rana tun da ta ƙwato kanta har da tsarabar kayan marmari. Imran da tun da zai shigo ya ji Inna ta kamo labari ya dakata ya laɓe sai da ya gama ji kaf sannan ya yi sallama ya shigo yana ta danne dariyarsa dan sosai yake hango idanun samarin da Inna ra yiwa wannan ɗanyan aikin da a ce wani zai samu labarin cewar ba aljana bace ya san idan suka haɗa hanya ba lallai su barta da rai ba dan ko shi yanzu ya hasaso irin yadda zai ji jiki da a ce shi aka yiwa haka.
Haka dai aka cigaba da ZAMAN WANKAN ana karawa tsakanin Inna da Imran, har ya zamana saura kwana biyu suna, ranar ta kasance ranar laraba inda suna ya kama za a yi shi ranar juma’a dan haka ranar ana ta yiwa me jego ƙunshi da wanda suka zo daga dangin mahaifiyar Sadiya da da wasu daga cikin ƙawayenta na kusa, sai Ashrof da ƴaƴan ƙanwar Mama, Jan lalle ne ake zana musu sai kuma fulawa da ake zana musu Inna da ke gefe a zauna tana ta kallon budurwar da ta duƙufa wajen zanen fulawa kamar dama can da shi aka halicceta yadda take zanawa, Inna da ta gaji da taɓe baki ta ce.
“Kai wannan yarinya da kudura kike da shegen son kuɗi yo in banda neman kuɗi ke ɗaya da ranki amma kin kama ƙafafu sai zane su kike kamar kin samu bayan ƙwarya, ke bakya ma tsoron aljannu su tasheki tsakiyar dare su ce ki zana musu a hannu da ƙafafunsu, baki ji ba an ce kwalliyar aljannu ce, a ce ki rasa sana’ar yi sai zanen aljannu ban da ɗorawa kai jafa’i” Cewar Inna tana kallon budurwar da tun da Inna ta fara rattabo maganganunta ta dakata ta zuba mata ido cikin mamakin kalamanta.
“Kin ga Inna neman kuɗi halak ne, da a ce sata nake fa ai gwara na nemi halal ɗina, kuma da kika ce kwalliyar aljannu ce ni ban ma taɓa ji ba, kawai idan so kike a zana miki ki shiga layi idan layi ya zo kan ki in miki” Cewar budurwar dan dama da ganinta idonta a tsaitsaye yake kamar ma wata ƴar duniya-duniya.
“Allah kiyashe ni aikin da na sani, ni Azumi dan asara in zauna a zana min wannan abin me kama da jelar saniya, kakar dai wata me budurwar zuciya dan na faɗa miki gaskiya za ki nemi ki faɗa min magana to wallahi kar ki min rashin kunya kin ji na faɗa miki” Cewar Inna tana wani hayayyaƙowa yarinyar kamar ta kai mata duka.
Sadiya da ta shigo falon yanzu ta ga abin da ke faruwa dan dama kitso ake mata ta fita ta yi fitsari, ta dakatar da yarinyar tana baiwa Inna haƙuri dan a zauna lafiya duk da ta san Inna ce bata da gaskiya amma haka ta ɗan yiwa yarinyar signa a kan ta ja bakinta ta yi shiru.
“Faɗa mata dai ku da kuka san darajar mutane, me zan yi da wannan zanen fulawar ban da ma toshewar basira a zana maka ka je ka mutu da shi a kai ka kabari mala’iku su kankare maka da dutsin wuta, gwara in yi da lalle na asali tun na iyaye da kakanni, saboda gudun matsala ma da kayana na taho daga garinmu yana cikin jaka lalle me kamu idan ka ƙunsa ka ga ƙafafunka babu banbanci da ƙafar ba’indiyar da aka yiwa ƙunshi, , sai gobe zan ƙunsa kayana, na san aminiyata Tsahare ma shi za ta ƙunso in ta tashi ziwa suna.Bari ma dai na tashi na je na yi sallar azzahar dan na ga ku wannan abin ma kafin ya kama ku cire sai dai ku harhaɗa sallolin haka kawai ko tsoron Allah bakwa yi” Cewar Inna ta tashi.
Me ƙunshin ce ta raka bayan Inna da wata uwar harara tana murguɗa baki ba tare da kowa ya lura da hakan ba, ji take kamar ta yi ta dukan tsohuwar nan me shegen rangwangwan da shiga shari ba shanu. Ji take da a ce za ta samu dama babu dalilin da zai sa ta rama cin mutuncin da Inna ta yiwa sana’arta.
Kowa dai bai furta komai ba, dan gudun Sadiya da Ashrof kar su ji haushi, a haka aka cigaba da zana musu ƙunshi ja da baƙi.
Inna kuwa tana fita ta nufi bayi ta yi tsarkinta ta fito ta fara ɗaura alwala. Ƴan falo ana ta hira kowa yana tofa albarkacin bakinsa, Hassan da Husaini kuwa Sadiya ta ajiyesu a bedroom saboda bacci suke kuma bata son hayaniya ta tashe su. Lokacin da Sadiya ta fita za ta jefar da gashin danya fita daga kanta da aka mata kitso, kawai ƴan falo sai ganin miciji suka yi ya fito zulululuu daga cikin ɗaki, gabaɗaya aka shiga gudun famfalaƙi kowa yana neman ceton rai haba wa Inna da ke zaune tana alwala lokacin tana wanke fuska sai ganin mutanen falo ta yi suna fitowa kamar ana korosu kowa yana kama gabansa, da mamaki ta dakata da alwalar da take tana so ta gano abin da ya sanya su wannan gudun. Sadiya da ta juyo daga wajen bola ta hango mutane kowa a ruɗe, Ashrof da ta yi wajen bayi ce kaɗai ta iya nuna mata hanyar falo da hannu alamar akwai wani abu tana nuna mata kwa ta yi wuff ta faɗa bayi ji kake gararaf ta banko ƙofa, ta jingina da ƙofar daga cikin bayin.
Inna ta kasa gane dalilin da ya sa ake tseran ta buɗe baki za ta fara sababin nata ba sai hango miciji ta yi ba ya fito daga falo, idanu ta zaro a kiɗime ta tashi daga kujerar da ta zauna take yin alwala, ji kake gwaraf ta bi ta kan butar alwala tana kama zaninta da ke neman faɗuwa, mamaki take duk sawayar da Hassan ke yi ma iyakarsa ya motsa jela ko kansa amma yau ya fito da kansa har tsakar gida, da alama farautar rai ya fito, aikuwa Inna ƙafa me na ci ban baki ba sai ta nufi hanyar kicin ko sauraren Sadiya da ke ta faman mata maganar ta kalli Hassan ya koma miciji ya fito bata yi ba ta faɗa cikin kicin har tana gware da bango sosai goshin ya bugu amma babu damar murzawa haka fa daure tana neman mafaka.
Tana shiga kicin ɗin ta hango ƙafar wata ta leƙo daga cikin lokar kicin ɗin da nan take niyyar shigewa, amma ganin kusan mutum biyar a ciki sun cunkusu wata ma a kan wata take sai Inna ta fara rarraba ido.
“Wannan tashin hankali da me ya yi kama ni Azumi, a ce kai kullum baka da kataɓus baka da kwanciyar hankali” Ta faɗa a ranta hankali tashe, hango yarinyar nan me ƙunshi Inna ta yi a bayan ƙofar kicin ɗin daga ciki sai raba ido take tana ƙifƙiftawa wata harara Inna ta doka mata tana juyawa ta fara waigen mafaka, ganin danƙareriyar freezer wacce suke ajiye kayayyaki, karamin frige ɗin kuma shi ne a falo da hanzari Inna ta buɗe freezer aikuwa ta yi sa’a babu komai a ciki ba ma a kunne take ba.
“Yawwa Allah ya bani mafakar ɓuya, haka kawai Halima ta haifa mana jaraba shi kuma wancan mijin nata me kai tun na haihuwa ya hana a kai yaron bakin ruwa su ɗau kayansu ya bar mana shi kullum mu hankali rabe a biyu” Cewar Inna tana kiciniyar shiga freezer, sai da ta shige ta miƙo hannu za ta rufe murfin sai ganin yarinyar nan me ƙunshi ta yi tana ƙoƙarin shiga ita ma da sauri Inna ta tashi tsaye daga ɗan ɗosana ɗuwawunta da ta yi a ciki ta tsugunna ta galla mata harara ta ce.
“Gidan uwaki za ki shiga, na ce gidan uwaki ne nan ɗin za ki shiga?” Cewar Inna tana yi tana dogon wuya dan kar micijin ya zo kicin ya farmata.
“Ki bari mana mu shiga tare baki ga na cikin lokar nan ba ma duk cunkusuwa suka yi wani kan wani, zama da ba na daɗi ba yaushe mutum zai ce baya son matsi”
“Ai wallahi ko haɗiyeki micijin nan zai yi sai dai ya haɗiye, ba ke taƙamarki fitsara ba to ma ji ma gani an rufe tsohuwa da ranta” Cewar Inna tana ture hannun yarinyar daga jikin freezer da shige tare da rufe murfin freezer.ƙwafa yarinyar ta yi ta duba mukullin freezer ta ga yana jiki, aikuwa ta kulle, ta ɗauki wayar freezer ta jona a socket ta kunna ta ce .
” Ma ga yadda za ki yi” Ta faɗa tana komawa mafakarta ta ɗazu bayan ƙofa ta raɓe tare da ɗaukan wani buhun shinkafa danya ƙare ta lulluɓa duk gudun kar miciji ya ganta.
A tsakar gida kwa Sadiya ta rasa yadda za ta yi, ta taɓa micijin ya fi sau a irga amma yaƙi komawa mutum kawai sai ta samu wuri ta durƙushe take rasgar kuka abinta da abin ya girmi tunaninta.
A kicin kuwa Inna da ke cikin freezer ta fara jin wani sanyi a ƙafafunta, dan babu takalmi a ƙafarta tun lokacin da ta kwaso fa gudu ta silleshi jin zai hanata wali wajen gudu. Jin wani sanyi yana ratsa ƙafafu da jikinta sai abin ya bata mamaki dan ta san dai da idonta ta ga wayar freezer ma bata jikin socket, amma kuma ya ɗauki sanyi sai hakan ya bata tsoro sosai, jim kaɗan kawai sai ji ta yi gabaɗaga freezer ta ɗauki mugun sanyi, a take ta fara karkarwa jin sanyi na ratsata ta ko ina.
“Habunallahu wa ni’imal wakil, kar dai shegiyar yarinyar nan ce ta rufeni a ciki” Cewar Inna lokacin da take ƙoƙarin buɗe freezer ta ji ta a rufe gam. Jin sanyin ya yi yawa ta fara share hawaye tana cewa.
“Malam ka ga Azuminka dai ko suna ba a yi ba amma ina karɓar uƙuba kala-kala daga wannan sai wannan sai ka ce wacce uwarta ta ce ki je kya gani, ko dai baka yarda da tahowata ba ZAMAN WANKAN nan ba har zuciyarka, a ce ina ganin ƙalubale kamar an min baki” Ta faɗa tana sa hannu ta bugi jikin freezer. Ƴan cikin loka da me ƙunshi da ke lulluɓe da buhu da bata gane daga inda ƙaran ya fito ba duk zatonsu miciji ne ya ƙaraso kicin ɗin, ƴan ckn lokar a take suka cure a wuri ɗaya kamar ƙarago, ta cikin buhu kuma ta tuƙunƙune gefen buhu ta cusa a bakinta gudun kar tsoro ya sa ƙara ya kuɓuce mata micijin ya ga maɓoyarta ya farmata.
09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
2️⃣3️⃣➡️2️⃣4️⃣
“Haba jama’ar annabi ku kawo min ɗauki mana, ni ba tumatur ba ba gwanda ba amma gani a firinji sai ɗaukan sanyi nake” Cewar Inna cikin ɗaga murya tana jin wani kuka na taho mata. Wata atishawa ce ta taho me haɗi da majina saboda sanyin da ya gama ratsa ƙasusuwanta, so take ta yi ihun da kowa zai ji ta, a san cewa tana cikin na’urar bada sanyi dan ta lura duk kwakwazon da take ba wanda ya ji ta.
“Halimatus Sa’adiyya, ki bar micijin nan ki taho ki buɗe firinji kafin in yi ƙanƙara, ko masasssara ta kamani Malam ba zai yafe muku ba, Asharofa, Asharofa, ki fito daga bayin nan ki zo ceton rai ” Cewar Inna da sanyi ya gama ratsa muryarta har ta fara shaƙewa ta faɗa tana sakin kuka. Jin shiru babu alamar ma ana jiyo ta sai ta fara magana a ranta.
“Yau ni Azumi wannan yarinyar akwai ƴar ƙundun buhun uba, yarinya ƙarama cakuru kuci cikon bancin ta garƙame a cikin wurin nan firinji sai aikinsa yake ni kuma ina ɗaukan sanyi, wannan ZAMAN WANKA bai ƙare ni da komai ba” Ta faɗa tana sanya hannunta ta rufe hancinta saboda sanyin da take shaƙa kamar wanda aka jefa ƙanƙara a cikin hancin.
“Ƴan nepa ku taimaka ku ɗauke wuta dan shi firinjin ba hankali ba gareshi bare ya san Azumi ce a ciki, ya san ba fura bace ya dakata da aiki” Cewar Azumi tana ɗaga ido ta kalli ɗan ƙaramin ƙwan da ke cikin freezer ya kawo haske abinsa.Hannu ta kai ta zage ƙarfinta duk da a takura take saboda matsi amma a haka ta jimƙe hannunta ta daki jikin ƙwan tana cewa.
“Wallahi gwara na fasaka firinjin ya lalace gabaɗaya a kan ina ji ina gani in ke zaune cikin ƙanƙarar nan, ni ba me rayuwa a turai ba, in zo in sandare in mutu a banza a ɗakko ni a daskare makara ma bata karɓeni ba dan ba tanƙwasuwa zan yi ba yadda nake a tsugunnan nan a haka zan ta zama, ko kabarin na san sai ko a gina min me zurfi a zura ni a ciki kawai, babu damar a kwantar da ni, ko ƴan gaisuwar mutuwata suka zo, na san sai dai suke cewa ashe azumi sa’i ya yi to Allah sa tsugunno hutu ne, dan babu me cewa kwanciya hutu ce, dan a tsugunne nake ba a kwance nake ba”
Ta faɗa lokacin da ta naushi jikin ƙwan amma ko gezau be yi ba bare ta sa ran zai fashe,ssi wani zafi da hannun ya ɗauka. Hannu ta kai ta shafo goshinta inda ta bugu ɗazu a garin gudun ceton rai, wurin ya yi ƙullutu ga zafi, tana taɓawa wani tausayin kanta ya kamata haushi ne ya sa ta shiga bugun freezer ba ƙaƙƙautawa dan ta san idan bata yi da gaske ba haka za ta mutu babu wanda ya sani.
Ƴan cikin loka ƙaran bugujn freezer da Inna take sai suka ɗauka micijin ne ya ƙaraso jikin lokarsu yake bugawa hakan ya sanya kowacce ta tsure, wata ƴar gidan ƙanwar Mama da yake ƴar siririya ce ita ce daga ƙasa sai wata bazawara ƙatuwa ƴar uwar Imran a kan ta tsabar yadda bazawarar ke da nauyi kuma a kan siririyar budurwar take dakyar take jan numfashi dan gabaɗaya ta danne mata har wajen kanta amma saboda tsoro sai bata ce komai ba, wannnan ƙaran da ya sanya suka firgita sai ƙatuwar ta ɗan muskuta ɗuwawunta aikuwa tsabar tsurewa ta saki wata uwar tusa da ta gama ratsa hancin siririyar ji ta yi kamar an saka hancinta a cikin kashi, tsabar wari har wani ɗaci-ɗaci ta ji a maƙoshinta. Kai ta shiga girgizawa, tsabar. Inna da bata san wainar da ake toyawa ba tana ta ƙoƙarin a zo a ceceta dan ta san har ƙwara na cikin lokar sau dubu a kan ita da ke ciki duk ta fara sandarewa dan da wani zai taɓa jikinta yanzu sai ya ji kamar ƙanƙara ya taɓa. Wani uban zabura ƙatuwar matar ta yi aikuwa kanta da ke dab da saman lokar ta ciki ya bada wani gum, gumewar da ta yi a kanta sai kuwa ta sake sakin tusar, gabaɗaya lokar ta haɗe da wari su duka a takure suke, ba dan micijin nan ba da babu wanda zai iya shaƙar numfashi saboda ɗoyi amma tsoro ya sa ba za su fito ba, siririyar nan jin an ƙara sakar mata tusa haushi da takaici ya sa ta ɗan gota kanta daga saitin ɗuwawun matar dan hancinta ma a wajen maraba biyu yake ta tsagar ɗuwawun matar aikuwa cikin fusata ta buɗe bakinta ta gantsara mata cizo a ɗuwawun wani azababban zafi ne ya ratsa matar da ta manta da cewar a ɓoye suke ta hangame baki ta saki wani uban ƙaran ta ce.
“Wayyo ya gantsara min cizo a ɗuwawu” Duk ta ruɗe da zafin cizo sai ta zata micijin ne ya shigo ya cijeta dan ƙuncin da suke ciki ko ƙasa baka iya kallo duka a wuri ɗaya suke a cure. Yarinyar nan me ƙunshi jin an ce an yi cizo a ɗuwawu sai ta fara karkarwa dan ta san ita ma micijin dole ya ganta tunda ya ga na cikin loka ma bare ita aikuwa ta saki wani kuka, ga buhun da ta tuƙunƙuna ta saka a bakinta sai sautin kukan ya bada wani wuuuuu kamar wata jiniya. Inna da ke cikin freezer jin ihun da kuma ambaton da aka yi na an yi cizo sai ta ce.
“Wallahi gwara ku a kaina duk tsiya ai inda sauran kwananku za a sa muku maganin dafin miciji ku warke, idan kuma kuka mutu ai zaku kwanta a kabarinku a kan ni da sai dai ake Allah sa Azumi tsugunno hutu ne” Ta faɗa tana sakin kuka tana da na sanin zuwa ZAMAN WANKAN ma gabaɗaya.
Sauran ƴan cikin lokar kuwa sai tsoro ya ƙara shigarsu ji micijin har ya shigo lokar ya yi cizo banda wacce ta yi cizon da ta san ita ce ta yi cizon ba miciji ba, hakan ya sanya ɗaya kama jikin ɗaya ta damƙe da hannu biyu aikuwa wacce aka damƙa ta wage baki ta saki ihu ta ce.
“Wayyo an damƙe min nono, wayyo ni Allah na, ni ba a min ƙunshi ba amma za a min lahani” Ta faɗa cikin kuka da azabar da ta ji a jikinta, da yake yarinya ce ba wata babba ba irin ƙirgen dangin nan ne ta fara wanda ko ɗan bigewa ka yi a jiki sai ka ji azaba. Ita kuwa wacce ta damƙi yarinyar bata ma san abin da ta yi ba, jin wai an ce ta damƙi nono da sauri ta saka dan ita bata ma san ina ta kama ba ta dai ji fitsarin yarinyar na gangara a kan ƙafafunta.
“Wayyo Allah wallahi da a taɓa min wurin nonona, ko da kuwa da ɗan yatsa ne gwara in bada kyautar naira dubu saboda azabar ciwo amma kin zo kin damƙa kamar kin samu ƙanzo” Ta faɗa cikin kuka, babu wanda ya ce wani abu dan yanzu ta kai- ta kai ake.
“Gwara ke nono aka damƙa, wayyo ɗuwawuna za a cire min fatar” Ta faɗa jin an ƙara cafka da haƙori dan tana sakin tusa ita kuma ta ƙasanta ke gatsara mata cizo.
Inna da ke cikin freezer ta ƙyalƙyale da dariya duk da halin da take ciki, amma jin ana damƙe-damƙen ɗuwawu da nono sai abin ya bata dariya ta ce a zuciyarta
“Yau dai ana dara ga kuma dare ya yi, Hassan duk ya rabawa kowa aikin wahala”
Me ƙunshi ma kukan da take ne ya haɗe da dariya a ranta ta ce.
“Taɓɗi yau da a ce ba a halin ƙaƙanikayi nake ba dariyar da zan yi sai cikina ya yi ciwo, dan ko ni lokacin da na fara ƙirgen dangi ko wanka na zo sai dai in zuba musu ruwa in ɗauraye su, ba na yarda in sa soso in wanke saboda azaba” Ta faɗa tana dariyar da ta kusa fitowa fili saboda yadda dariyar ke cinta.
“Inna! Inna!! Inna!!!” Inna ta jiyo muryar Sadiya tana ƙwala mata kira tun ƙarfi.
“Inna dan Allah ki fito ki tayani mu dawo da Hassan gashi can ya kama hanyar ƙofar gida zai fice kuma ƙofar ba a rufe take ba, ni kaɗai ba zan iya ba dan ya ƙi tsayawa ko ɗaukansa zanyi zulalewa yake” Cewar Sadiya tana kuka ta rasa yadda za ta yi hankalinta ya kai ƙololuwa wajen tashi, bata so ɗan nata ya fice duk da kasancewarsa a siffar muciji tana ƙaunarsa, Allah sarki uwa!
“Mtssss” Inna ta ja wani dogon tsaki ta ce.
“Banza ta kori wofi ma kenan yo Allah na tuba da ba a cikin firinjin nan nake ba ma babu abin da zai sa na zo wallahi, da kaina zan kaɗashi ya tafi, gwara ma ya je ya fice abinsa wataƙila ma wahalarki ce ta yanke, yo Allah na tuba zama da wannan abu a gida ai jafa’i ne, ya je can daji ya samu ruwa ƴan ruwa su ja abinsu mu huta, ga Husaini nan ya isa” Ta faɗa tana ɗaɗɗaga kai take kallon saman freezer.
“Dan Allah ku taimaka mini” Cewar Sadiya tana ɗaga murya.
Ashrof tausayin ƴar uwarta ya kamata amma ga kuma tsoro tana ganin kamar micijin zai iya cutar da ita, amma ita Sadiyar ba lallai ya cutar da ita ba saboda ita ce mahaifiyarsa.
“Ke dalla ɗaga ni kin wani min ɗirkaka a kaina kamar wani buhun hatsi” Ƴan cikin loka ke faɗa saboda sun ji an ce miciji ya kama hanyar fita waje.
“Kan ku ake ji wai mahaukaci ya faɗa rijiya ya ce ni wankana nake “Cewar Inna.
“Ƴan cikin kicin ga Hassan nan ya nufo kicin” Sadiya da ta shawo gaban Hassan daga hanyar gida ya iyo kwana ya dawo gida ta faɗa cikin ɗaga murya ganin gadan -gadan ya nufi kicin ɗin.
Ashrof da ke ƙoƙarin fitowa ta taimakawa Sadiya ta dakata daga ƙoƙarin fitowa daga bayi jin Sadiya ta ce ya nufi kicin.
“Hahahaa na dawo in ji ɗan yawon duniya, yau akwai gwarama” Cewar Inna tana dariya ido na zubar da ruwan hanci ku sai tsiyaya yake kamar an kunna fanfo tsabar sanyin freezer da take shaƙa.
Gabaɗaya masu faɗa a cikin loka sai suka sha jinin jikin su ko kyakkyawan motsi sun kasa yi, kowa bakinsa sai motsi yake alamar addu’a.
Sai da ya je tsakiyar kicin ɗin ya ja ya tsaya tare da fasa kai alamar sara, Sadiya da ke tsaye a bakin ƙofar sai kallonsa take so take ta koma ɗaki ta ɗauki wayarta ta kira Imran amma bata so ta matsa daga wurin wani abu ya faru kuma ma ta san shi ma Imran tsoron Hassan ɗin yake ji idan ya sawaya.
“Kar wanda ya motsa daga inda yake Hassan yana tsakiyar cikin kicin ɗin” Cewar Sadiya cikin muryar kuka.
Ɗif kowa ya yi, me ƙunshi kwa da ta buɗe idonta guda ɗaya ta ɗan leƙo daga cikin buhun da ta lulluɓa da shi. Ganin micijin danƙarere ya fasa kai da alama sara kawai yake son yi, gashi kuma ta san babu wanda zai fi saurin gani sama da ita, a take ta ji ina ma ita ce a cikin freezer kuma freezer a buɗe a kan wannan tashin hankali da take ciki.
Bum-bum ƙaran bugun freezer da Inna take ya karaɗe wajen, duk bugu ɗaya sai micijin ya zabura, zaburarsa kuma ba ƙaramin ƙara razana me ƙunshi take ba, Inna kuma dama da niyya take bugawa saboda ko banza ta san ta rama kaɗan daga abin da yarinyar ta mata.
“Wayyo wannan tsohuwa masifarta ta yi yawa, yanzu sai ta firgita micijin nan ya shiga neman mutumin da zai sara a cikin kicin ɗin, tsoratar da yake yana wata girgiza yana fasa kai ta ko ina hakan ba ƙaramin tsurewa ya sanya me ƙunshi ta yi dan ita kaɗan ke ganinsa na cikin loka da Inna da ke freezer ra san ba za su gani ba.
Shigowar Imran gidan ɗauke da sallama shi ya sanya Sadiya nufarsa da sauri tana kuka tana faɗa masa, wani yawu ya haɗiye muƙut jin wai micijin har ya fara fitowa ya yi waricinsa a cikin gidan lallai babar magana . Haka dai ya daure tare da majewa ya nufi kicin ɗin, a haka ya sanya Sadiya ɗaukan micijin ta nufi ɗaki da shi har lokacin kuka take yi. Imran ganin matan nan na cikin loka ya ɓata mas rai ganinsu cunkushe kamar alhazai ranar arfa, wata da take leƙo idonta ta tsakanin murfin lokar ita ya dakawa wata uwar hararar da ta sanya ta runtse idanu, ƙafa ya sanya ya daki jikin lokar tare da cewa su fito haka, haka suka turo murfin suka fito simi-simi suna ciccira idanu kamar waɗanda suka yiwa sarki ƙarya.Suna fitowa daga kicin ɗin ya tsaya a bakin ƙofar yana binsu da wani mugun kallo dan daga me zarnin fitsari sai wani wari da ya kasa gane na menene.
Me ƙunshi da ke ƙunshe cikin buhu ta buɗe a hankali ta fito daga ckn buhun, da ta lulluɓa, tana fitowa ta kalli freezer a ranta ta ce
“Ke kuma tsohuwa a nan za ki kwana uwar sababin tsiya” Tana zuwa za ta fito ta ga Imran ya yi bake-bake a bakin ƙofar aikuwa ta yi ƙoƙarin bin ta ƴar sauran ƙofar da ya bari, Imran da bai san da sauran mutum a cikin kicin ba sai ji ya yi an ɗan shafi gefen rigarsa aikuwa dama duk a tsorace yake, jin an ɗan taɓa shi sai ya yi zaton micijin ne dan jin an ce micijin da kansa ya fito abin ya matuƙar bashi tsoro sai dai bai faɗa bane. Da gudu ya ruga a sukwane ya nufi ɗaki, sauran matan da suka fito daga loka suka mara masa baya dan duk tunninsu wani abun ne.
Yadda ya zuro a guje babu birki haka su ma suka daddage ƙarfinsu suke binsa da gudun, har da masu tattare zane gudun samun mushkila. Imran da gabaɗaya a gigice yake sai da ya zo falo ya ga Sadiya da miciji a hannu ya ja ya tsaya a ransa yana ganin jarumta irin ta Sadiya yana kuma jaddada soyayyar uwa da ɗa, ganin Hassan ɗin ne ya dawo dashi daga firgici da tsurewar da ya yi sai a sannna ya tuna cewar ashe ma Sadiya ta taho da yaron kawai tsoro ne ya sanya ya ga kamar micijin ne ya biyo shi. Wani yawu ya haɗiye tare da sauke wani numfashi. Matan nan ma ganin ya tsaya sai kowacce ta dakata a wajen dan sun manta da micijin a ɗaki amma ganin Imran na gudu su ma suka fara suna jejjefa idanu kallonsu kawai yake, daga wacce take jige jagaf da fitsari sai wacce ke da ƙunshi ƙafa ɗaya ba a ƙarasa ɗayar ba, sai wacce baƙin lalle ya gogu a fuskar ta koma kamar wacce ta shafa shuni. Wata harara ya musu tare da jan wani uban tsaki, ya wani maje yana harare-harare amma ya kasa shiga ɗakin, hango me ƙunshi a ƙofar kicin ɗin sai lokacin ya ga rashin azancinsa da bai tsaya ya waiwaya ba bare ya gane ba miciji bane.
Harara ya dakawa matan nan da suka biyo shi, dan sun ma kasa shiga falon shi ma cikin wayancewa sai ya juya ya nufi kicin ɗin me ƙunshin da gudu ta bar wajan ganinsa ya taho. Imra n kuwa na shiga kicin ɗin sai ya tsaya a tsakiyar kicin ɗin yana maida numfashi dan ba ya so a raina shi shi yasa bai tsaya maida numfashi a gabansu ba, su ma suna nan tsaye sun yi carko-carko. Dafa kan freezer ya yi tare da ɗora kansa a kanta, Idanu ya rufe ruf yana jin yadda zuciyarsa ke lugude kamar me tseren gudu, hannayensa duka biyu ya ɗora a kan freezer sai ya kwantar da kansa a kan freezer, idanunsa a rufe yana tunano yadda Sadiya ke ɗauke da miciji a hannunta, Inna da tun daɗewa take ta faman magana a kan a kawo mata ɗauki babu wanda ya jiyo ta, dan haka ta raya a ranta za ta shiga jijjiga freezer da ƙarfi dan a jiyo ta a zo a buɗe ta. Wata jijjiga da ta yiwa freezer da Imran ke riƙe da ita gam, hakan ya sanya ya saki wata tusa ta tsurewa ba tare sa ya shirya ba, jin freezer na girgizashi tamkar ana girgizar ƙasa hakan ya sanya ya ƙanƙameta da ƙarfinsa.
Dan gabaɗaya ma sai tunanin guduwa ya kwance masa.
“Allah wannan baƙar wahalar da nake shiga tun ranar da Sadiya ta haihu Allah ka sa kaffara ne” Ya faɗa lokacin da ya saki wani kuka me cin rai Inna kuwa bata daina jijjiga a cikin freezer ba yi take tun ƙarfi.
“Ai wallahi da in mutu a binne ni a tsugunne na gwammace in daddara firinjin nan in bayyana kamar wata ɗan daren goma sha huɗu” Ta faɗa tana lokacin da ta kai hannunt ta ƙwarzani jikin freezer ganin yadda farin ƙanƙarar nan me kamar dusa ta fara baibaiye jikin freezer.
“Oh Allah ni Azumi kamar wanda aka sanyani cikin buhun fulawa ji yadda farin ƙanƙanarar nan ya maida ni kamar furfura ta kar ni, ganin mukullin ya faɗo daga jiki, saboda bugawar da ake, cikin sanyin jiki da tsoro ya ɗau mukullin ya sanya jikin freezer ya buɗe a tsorace tare da ja baya kaɗan bakinsa sai kaiwa da komowa yake wajen addu’a amma baka jin me yake cewa shi kansa be sai me yake karantawa ba.
Yana buɗe freezer sai ya yi baya ya maƙe a bango, yadda ya tsaya kamar ka ce as ya zura a guje, jira yake kawai wani abu ya fito ya arce a na kare, dan ya yi alƙawarin idan ya doshi ƙofar gida sai dai idan ya je ƙofa ya ce kowa ya taho sarkin aljannu a frezer.
Inna ganin an buɗe dan ta ga alama murfin ya ɗan ɗaga da take ɗaga shi sama da kanta, hamdala ta yi a zuciyarta, ta fara kiciniyar miƙewa amma ina, ashe gabaɗaya zanin setin mazaunanta ya haɗu da ɗan sauran ruwan ƙasan freezer ya daskare har zanin. Hannu ta kai ta taɓo sai ji ta yi gabaɗaya ɗuwawunta yana danne da zani da ƙanƙarar.
Bata gama tsurewa ba sai da ta jita gabaɗaya a daskare har ta buɗe baki za ta yi magana sai ta fasa saboda ta san ita tana jiyo maganar mutane amma ita ta ga duk kwakwazon da take ba a jinta.Zunkuɗa kanta ta yi cikin sa’a kuwa sai ƙoƙon kanta ya buɗe murfin ya yi sama. Imran da ke rakuɓe a jikin bango dan tun lokacin da ya buɗe ya koma ya rakuɓe sai karkarwa yake kamar shi ne a freezer, ganin an buɗe ƙofar sai kawai ya saki kuka yana ta matse ƙafafunsa amma tsoro sai da y sa fitsarin da yake ta matsewa tun daga lokacin da freezer ta fara girgiza ya ƙwace masa ya zubo. Tsoro ne marar misali ya baibaiyeshi.
“Ku min rai dan Allah, in gidan ma kuke so mu bari a yau ɗin nan za mu bari a yanzu ma kuma ko tsinke ba za mu ɗauka ba, ku taimaka mana” Ya faɗa yana ta so ya zura a guje amma gani yake kamar ma rafkoshi za a yi a dawo dashi kicin ɗin.
Inna kuwa gyaran murya ta shiga yi dan muryar duk ta shaƙe. Ai gyaran muryar da ta yi sai ya bala’in ƙara sanya Imran cikin tashin hankali da mummunan tsoro, bai ankara ba sai jin bakinsa ya yi yana faɗin
“Ya kusamu ya mu rasa, ya kusamu ya mu rasa” Sai maimaitawa yake kamar wanda aka sa tilawar ƙur’ani, shi kansa bai san me yake faɗa ba. Ya gama jiƙewa da hawaye da fitsari ga majina duk shi kaɗai kawai sai ji ya yi ta cikin freezer an ce.
“Imirana, Imirana, Imirana” Jikinsa ne ya fara karkarwa be ma san ya aka yi ba kawai dai ya ga ya fara zagaye wani kofi da ke tskiyar kicin ɗin, sai zagawa yake kamar yadda ake ɗawafi yana cewa
“Ya ku samu, ya mu rasa” Dan yadda aka kira sunan nasa ya tsorata shi dan yanzu dai ya tabbatar sarkin aljannu ne dan ya ji an kira shi d sunansa da alama suna ganinsa suna kuma sane da motsinsa. Dan yadda muryar Inna ke shaƙe idan ta yi magana kamar an shaƙewa kuturu wuya haka sautin ke fita, gabaɗaya ma ya manta da wata Inna bare kuma ya gane ita ke kiransa Imirana.
“Imirana, yaka buɗe firinjin nan” Cewar Inna dan duk abin nan da ake murfin freezer ɗagawa yake kawai idan Inna ta buga kai a jiki.Imran kuwa ji ya yi tamkar ya zura a guje, amma ba hali.
A hankali ya taka ya ƙarasa wajen hannunsa na karkarwa ya kama murfin freezer yana sakin wani kuka me cin rai marar sauti, haka ya buɗe freezer cikin cika umarninsu amma sai ya rufe idanunsa gam dan gani yake idan suka yi ido huɗu ganinsu zai sa ya haukace.
“Oh ni Azumi matar Malam sai yanzu kuka kawo min ɗauki” Imran da ke riƙe da murfin freezer ido a rufe hawaye na kwaranyowa sai karkarwa jikinsa ke yi ya tsinkayi muryar Inna daga cikin freezer da sauri ya buɗe idon aikuwa idanunsa ya sauka a kan Inna da ke cikin freezer ita ba a zaune ba ita ba a tsugunne ba, ga wani ɗankwalinta ya yi gefe ɗaya ya mata wani zungurgur kamar hular ibro.Ta yi wani yamutsatsa kamar an tsamo ɓera daga ruwa, Gabaɗaya sai Imran ya manta halin da yake ciki na damuwa, a take ya saki wata dariya dan har ya hango dalilin shigar Inna freezer.
“Hassan” Ya faɗa a zuciyarsa, wato dai saboda miciji ta shiga freezer ya baiwa kansa amsa.
“Ko wa ya kulleta kuma?” Ya faɗa a ransa.
“Tabbas a kwai ayar tambaya da…
“Imirana tsamoni dan Allah”Cewar Inna murya a shaƙe.
“Me kika ce ” Ya faɗa dariya na fitowa daga bakinsa irin dariyar ƙetar nan, Wani haushi ne ya turnuƙe Inna dan ita babu yadda za a yi ta fito dan ɗuwawunta daskare yake a jikin zani”
“Ni yau na ga abin mamaki ɓatan nono a ƙirjin budurwa” Cewar Inna cikin shaƙewar murya
Lura da Imran ya yi cewar Inna a daskare take sai ya miƙa hannu zai fiddota, aikuwa ya finciko ta da ƙeta.
“Wayyo mafitar kashina, wayyo Allah na haba Imirana ƙanƙara fa na yi” Cewar Inna cikin shaƙeƙƙiyar murya.
Dariya Imran ya ƙyalƙyale da ita, dan daga yadda ya finciko hannun Inna ya jita a manne da freezer, amma a haka yake ƙoƙarin fiddota amma ta ƙi ɓanɓaruwa.
“Haba Imirana ka kashe firinjin mana mazaunan nan nawa su ɗan saka mana, amma kake janyoni baka ji yadda muka yi tif da taya ni da firinjin ba kamar an manne tangaran da sufagilu” Cewar Inna cikin fuskar tausayi, haka dai ya kashe soket ɗin sai da ta ɗan saka ya taimaka mata ta fito, amma dariya na cinsa, haka ta fara takwa dakyar saboda yadda jikinta duk ya yi tsami ga karkarwa da atishawa da take yi a kai- a kai. Haka ta dudduƙo ta fito daga kicin ɗin tana dudduƙawa, tana ta kwashewa yarinyar nan me ƙunshi albarka, a haka ta fito ta kwa yi ido huɗu da sauran matan nan tsaye cirko-cirko har Ashrof lokacin ita ma ta fito sai maida yanda aka yi suke. Ganin Inna a yanayin da take sai kowa ya zura mata ido. Banda yarinyar da aka riƙewa mamanta, ta daddage sai masifa take a kan an riƙe mata nono a loka har sai da ta yi fitsarin wuya.Ita kuma ɗayar sai bata haƙuri take ta ce ba da niyya ta yi ba amma sai masifa take. Inna na ƙarasowa ta kalli yarinyar a shelaƙe ta ce
“Ni ina dalili kin damu mutane tun ina cikin firinji nake jin kina an damƙe miki nono, wai a nan ina nonon yake? Ba dan fuskarki ba ma babu yadda za a yi a banbance gabanki da bayanki, abu kamar an sawa muciya zani ba gaba ba baya, amma a haka kike cewa an damƙi nono, yo an damƙi nono ko dai an damƙi fata da fatar ma kika ce da daɗi, dan ban ga nono a nan ba wannan ƙirji naki kamar ƙirjin babe”
09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
2️⃣7️⃣➡️2️⃣8️⃣
Tsit gidan ya yi baka jin motsin kowa, sai sautin kuka Sadiya da ke tashi, dan kowa yana mafakarsa ya ɓuya. Inna duk da sanyin da ake amm sai jabga uban gumi take saboda tsabar tsoro da kuma yanayin da take ciki, uban buhhunan da ta libgawa kanta kaɗai sun ishe ta da zafi sai zufa ke ta faman kwaranyo mata tana sanya hannu tana gogewa.
“Oh Allah mutubi am, in ji fulani wai yau ni Azumi ce cikin buhhuna rufe sai kace masara, da a ce wani zao yiwa Tasalla video na ya tura mata da na san sai na gaggara komawa gida saboda tsoron abin da zan je in tarar, yo ni da nake ƙafafa da birni kullum ina mata gorin bata ƴan uwa a birni amma a tura mata videona ina ƙunshe a buhu ni ba tafasa ba sai ka ce wata kukar kaɗi”
Cewar Inna ta haɗa hawayen da gumin ta goge, tana tuna duka -duka ba a ɗauke wasu lokuta masu yawa ba da ta baro cikin freezer yanzu kumangata ƙasan benci rufe da buhu.
“Allah ka yafe mana idan saɓo muka yi amma lallai muna haɗuwa da jarabawa musamman ni Azumi” Cewar Inna tana hararo abubuwan da suka faru da ita daga barowarta ƙauye zuwa birni.
Dariya ta ƙyalƙyake da ita marar sauti sai da ta yi dariyarta son ranta har sai da dariyar ta tsagaita dan kanta sannan ta ce.
“Kai Allahu akbar Imirana Baban miciji ana can garƙame a cikin tukunya, yau dai ƙarshen tsafta da karkaɗar jiki sun ƙare tun da ana cikin sauran ruwan wankan jego luntsum” Ta faɗa tana ƙara dariyar ƙeta.
Jim kaɗan ta yi shiru kamar ruwa ya cita, can kuma da ta tuna kicin ɗin a kulle babu hanyar da micijin zai shigo ko da ya ji motsi ko magana sai ta dage ƙarfinta ta ce
“An ɓuya? An ɓuya?? An ɓuya???” Ta faɗa tana dakatawa dan jin abin da zai wakana, aikuwa kafin laɓɓanta su gama haɗuwa wuri ɗaya sai ta ji ƴan cikin loka suna ta surkune surkune alamar sun, a gyara zama dan jin abin da Innar ke faɗa sai suka ɗauka wani abu ne na da ban.
Jin babu wanda ya kulata sai ta yi shiru ta shiga addu’a a kan Allah ya kawo musu ɗauki dan bata fatan su kwana a halin da suke ciki yanzu.
Ƙaran bugun ƙofa ne da ake wanda aka kasa dainawa ya sanya Sadiya tashi tana goge hawayenta ta tafi domin ta buɗe, dan har lokacin Hassan na a yadda yake. Gabaɗaya mutanen da ke maɓoya sai suka shiga ƙara gyara zama saboda duk a tunaninsu miciji ne ke ta aikin buga jikin ƙofar gidan.
“Mamar Sadiya a ina kika samu mafaka ne, dan Allah, faɗa min ko cikin raɗa ne idan gurin da kike ya fi nan wasaci sai in lallaɓo in fito dawo wurin naki, dan ban ga alamar za mu fito a ƙanƙanin lokaci ba, kuma ƙasan gadon nan yadda kika san matsin kabari da ake bada labari haka nake ji ba na iya ko da kataɓus a danƙare nake a wuri guda” Cewar Hajiya tana nishi kamar an ɗorawa raƙumi kayan da suka fi ƙarfinsa.
Hannu Mama da ke cikin wardrobe ta sanya ta ɗan bugi jikin wardrobe ɗin, dan ita bata ma ƙaunar ta buɗe bakinta saboda gudun tsautsayi.
“Haba Mamar Sadiya kin fini son ranki ne da ba zaki buɗe baki ki ce min kina cikin sif ba, kuma da alama ma a ta Imran kike inda yake ajiye kayansa ko nauyi da kunya bakya ji ki shiga lokar kayan sirikinki?” Hajiya ta faɗa cikin ƙarfin halin matsin katakwayen da suka mata ƙawanya a ƙasan gadon.
“Wai Hajiya Amina menene haka, dan Allah sai kin jawo micijin nan ya shigo ɗakin nan, tun da kika ji na yi shiru ai sai ki kama bakinki ki yi shiru, da na miki alamar da inda nake ta hanyar buga katakon lokar ai idan za ki dawo nan ɗin sai ki fito ki dawo mu kwatsu, amma kina ta maganar siriki, sirikin da ya damƙeni a gudun famfalaƙin da miciji ke zagaya mu, menene saura kuma ya rage ai babu shi wa ya san a inda yake yanzu, ko ke kika samu lokar Sadiya tuni zaki manta da surukantaka ki afka ciki babu shiri”
Wani bugu da aka yiwa ƙofar gidan ne ya sanya suka yi shiru, me ƙunshi da ke ƙunshe cikin loka sai kuka take hawaye ne ke ta kwaranya dan zuwa yanzu babu abin da ta fi buƙata sama da ta samu ruwa ta wanke fuskarta zuwa wuyanta, dan gabaɗaya sai yanzu ta gama jin lallan fulawar ya gama baibaye fatarta da uban raɗaɗi.
“Wayyo Allah na shiga uku na, tsohuwar nan ta taƙaitani ta cuceni ya fi cikin carbi, lallan da ko a farce aka sa maka shi sai ka gwammace kiɗa da karatu amma ta min wannan ɗanyen aiki dashi, irin zafin da yake min a fata wallahi gwara ta rufeni a cikin freezer ta rama a kan wannan abin, ta min asarar bilicin ɗina, da na kwaile fuskata duk tattalin arziƙina da nake samu a ƙunshi a siyen man gyaran fata yake ƙarewa amma a ce yanzu ta maidani baƙaƙirin kamar tukunya da wane ido ma zan fita waje” Ta faɗa tana sanya hannu ta janyo wata farar shaddar Imran ta gogo fuskar tare da sakin wani kuka marar sauti
Imran kuwa da ke cikin tukunya duk ruwa ya gama jiƙa masa jiki gashi a ringishe yake shi ba a kwance ba shi ba a karkace ba, hannu kawai yake sanyawa yana kore ruwan da ke barazanar shigar masa hanci dan ruwan da ɗan damarsa. Idanu ya ɗaga ya sauke a jikin murfin tukunyar ta ciki, cikin tausayawa kansa ya ce.
“Haihuwa me jaye -jaye Allah ka sanya mu haifo alkairi, kar mu haifi abin da zai zama sharri garemu da wasu ma baki ɗaya, ni Imran babban yaro wanda ko giftawa na yi sai ƙamshin jikina ya gama buɗaɗe hancin mutane amma yau ni ne a cikin tukunya a rufe ina tsilla idanu kamar kwarton da aka kama, ni ba naman kai ba amma ina cikin tukunya da ruwa a rufe wuta kawai ta rage a kunna na zama naman da za a kai baki” Ya faɗa yana jin saukar ruwan hawayensa.
Sadiya kuwa cikin sanyin jiki ta sanya hannu a hankali ta buɗe jamlock ɗin, tana addu’a da fatan ba wani bane hallaw zai kawo kansa, dan ita ko kaɗan bata ƙaunar mutane suna zuwa suna ganin Hassan a suffar miciji, wani in ya gane baiwace wani in ya tafi ya rinƙa yawo da zancen kenan gashi baka san bakin wani ba. Idanu ta sauke a kan Lawal maƙocinsu na can gaba da su, ustaz ne dan shi ne ke jan sallah a masallacin ahlis sunna na unguwar, sanye yake cikin farar jallabiya, da farin dogon wando, sai hula irin tashi da ƙwawar nan a kansa , da jan hirami rataye a wuyansa, sai carbinsa irin counter ɗin nan wanda ake dannawa.
“Assthalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu, ya Sthadiyya” Ya faɗa lokacin da ya ga Sadiya ce ta buɗe ƙofar, gashi dama maganarsa ma irin ta ustazai ce ana yi ana saka gunna da ƙalƙala.
Ya yi sallamar yana ɗan kauda kai gefe irin baya son nan ma ya kalleta saboda shi ustazu ne.
Sallamar ta amsa masa cikin sanyin murya, da shaƙewar muryarta kana ji ka san ta aha kuka babu lefi. Jin muryarta sai da shek Lawal ya saci kallonta ta gefen ido, ganin yanayinta sai ya ce a ransa.
“Iko sai Allah, Sthadiya kuma fuska da alamar kuka, wataƙila ba a kawo haƙiƙa ba ne(Ragon suna) Kuma suna har ya rage saura kwana biyu, ashe kowa yana jin yanayin garin”
“Sannu da zuwa ya shek bismillah” Ta faɗa tana juyawa cikin sanyin jiki ganin sai satar kallonta yake ita kuma bata son kallo shi kuma duk da ana kiransa uztaz amma kallon mata ne da shi sai dai yana yin kallo saisa -saisa ne dan kar a gane shi. Ganin ta juya sai ya shigo tare da sakin ƙofar yana sakawa kuwa iska ta maida ta rufe.
“Ya subhanallah! Iska a yi haka kuma ki rufe liman, kuma shek a cikin gidan matan aure daga zuwa barka” Ya faɗa cikin muryar ustazai, ita dai Sadiya bata ce masa komai ba, haka ya shigo gidan ma bakinsa da sallama, sake amsawa ta yi, tana cewa ya shigo falon.
“Toh, toh” Ya faɗa yana tsegumin ƙarewa tsakar gidan kallo, dan sau ɗaya ya taɓa shigowa lokacin da aka kwantar da Imran a asibiti da aka taso shi ya zo ya masa sannu. Kallon da yake kuwa tsegumi ne da gulma dan yana so ya ga a kan abin da Sadiyar ta yi kuka, da ya ga bai hango ragon suna ba sai zarginsa ya zama gaskiya na cewa kukan rashin ragon suna ne da ba a kawo ba.
“Amma kuwa Imran ka yi wawta, kuma ba Sthadiya kawai ka yiwa baƙinciki ba har da mu dan na san dai za ta aikawa Barira naman suna kuma ni ma ai Barira ta ajiye min ko da tsoka ɗaya ne” Ya faɗa a ransa yana me kutsa kai cikin ɗakin. Zaunawa ya yi yana ƙarewa falon kallo yana yaba kyau da kuma tsaruwa na falon.
“A masu ƙaramin ƙarfi dai iyayenta sun yi ƙoƙari” Ya faɗa yana danna carbinsa tare da yin mismis da baki alamar ko yaushe dai basa yin sake da yin hailala da salatin annabi S A W. Gaisawa suka yi ya mata barka, da fatan Allah ya raya, ganin tun da ta ce amin bata sake magana ba sai wasa da yatsunta wanda suka sha ƙunshi take, yatsun ya kalla yana jinjina ƙoƙarin wacce ta zana ƙunshi, ya ce.
“Imran ɗin baya nan ne?”
Shiru Sadiya ta yi da ta tuna inda Abban twins ɗin yake, dan ta ji lokacin da Inna ta ce ya yi hanyar wajen murhu wataƙila ma yana cikin tukunyar kamar yadda Innar ta faɗa.
“Eh baya nan” Ta faɗa dan ta san dai har ya bar gidan Imran ba zai fito ba, bare ya gane ƙarya ta masa.
“Allah sarki, ko zaki samo mini ruwa in ɗan sha maƙoshina ya bushe, ba daga gida nake ba daga masallacin la’asar nake” Ya faɗa yana ɗan shafa gemu.
“To ” Ta ce ta tashi ta nufi frige.
“Wato ainifin ba mai sanyi ba sabo mura ta mun kamu me ƙarfi” Ya faɗa cikin yiwa maganar tasa kwaskwarima irin ta ustazai.
Ɗan jim ta yi tana jinjina ƙoƙarin mutumin, shi da ya zo barka, barkar ma daga maƙota amma har yake neman ruwa, haka dai ta kama hanya ta fita tsakar gidan tana addu’ar Allah sa dai shek ya tafi ba tare da matsalar da suke ciki ba ta bayyana kanta.
Ƙoƙarin sanya takalminta take amma kuma ganin Hassan na warware jelarsa sai ta dakata, tana ɗan kallon Ustaz ɗin da fatan Allah sa kar ya lura.
“Ɗan kula Sthadiya kin san daga nan wajen wani wa’azi zan je da ake gabatarwa a can masallacin sama damu duk laraba da yamma” Ya faɗa yana ɗan satar kallonta, tana shirin bashi amsa sai ganin micijin ta yi ya taso kamar wanda yake tafiya a kan iska, bai yi masauki ba aai a tsakiyar gidan, ya ɗaga kai sama ya fasa kansa alamar sara tare da sakin wani ƙara me kamar hamimiya.
Ya yi sallamar yana ɗan kauda kai gefe irin baya son nan ma ya kalleta saboda shi ustazu ne.
Sallamar ta amsa masa cikin sanyin murya, da shaƙewar muryarta kana ji ka san ta aha kuka babu lefi. Jin muryarta sai da shek Lawal ya saci kallonta ta gefen ido, ganin yanayinta sai ya ce a ransa.
“Iko sai Allah, Sthadiya kuma fuska da alamar kuka, wataƙila ba a kawo haƙiƙa ba ne(Ragon suna) Kuma suna har ya rage saura kwana biyu, ashe kowa yana jin yanayin garin”
“Sannu da zuwa ya shek bismillah” Ta faɗa tana juyawa cikin sanyin jiki ganin sai satar kallonta yake ita kuma bata son kallo shi kuma duk da ana kiransa uztaz amma kallon mata ne da shi sai dai yana yin kallo saisa -saisa ne dan kar a gane shi. Ganin ta juya sai ya shigo tare da sakin ƙofar yana sakawa kuwa iska ta maida ta rufe.
“Ya subhanallah! Iska a yi haka kuma ki rufe liman, kuma shek a cikin gidan matan aure daga zuwa barka” Ya faɗa cikin muryar ustazai, ita dai Sadiya bata ce masa komai ba, haka ya shigo gidan ma bakinsa da sallama, sake amsawa ta yi, tana cewa ya shigo falon.
“Toh, toh” Ya faɗa yana tsegumin ƙarewa tsakar gidan kallo, dan sau ɗaya ya taɓa shigowa lokacin da aka kwantar da Imran a asibiti da aka taso shi ya zo ya masa sannu. Kallon da yake kuwa tsegumi ne da gulma dan yana so ya ga a kan abin da Sadiyar ta yi kuka, da ya ga bai hango ragon suna ba sai zarginsa ya zama gaskiya na cewa kukan rashin ragon suna ne da ba a kawo ba.
“Amma kuwa Imran ka yi wawta, kuma ba Sthadiya kawai ka yiwa baƙinciki ba har da mu dan na san dai za ta aikawa Barira naman suna kuma ni ma ai Barira ta ajiye min ko da tsoka ɗaya ne” Ya faɗa a ransa yana me kutsa kai cikin ɗakin. Zaunawa ya yi yana ƙarewa falon kallo yana yaba kyau da kuma tsaruwa na falon.
“A masu ƙaramin ƙarfi dai iyayenta sun yi ƙoƙari” Ya faɗa yana danna carbinsa tare da yin mismis da baki alamar ko yaushe dai basa yin sake da yin hailala da salatin annabi S A W. Gaisawa suka yi ya mata barka, da fatan Allah ya raya, ganin tun da ta ce amin bata sake magana ba sai wasa da yatsunta wanda suka sha ƙunshi take, yatsun ya kalla yana jinjina ƙoƙarin wacce ta zana ƙunshi, ya ce.
“Imran ɗin baya nan ne?”
Shiru Sadiya ta yi da ta tuna inda Abban twins ɗin yake, dan ta ji lokacin da Inna ta ce ya yi hanyar wajen murhu wataƙila ma yana cikin tukunyar kamar yadda Innar ta faɗa.
“Eh baya nan” Ta faɗa dan ta san dai har ya bar gidan Imran ba zai fito ba, bare ya gane ƙarya ta masa.
“Allah sarki, ko zaki samo mini ruwa in ɗan sha maƙoshina ya bushe, ba daga gida nake ba daga masallacin la’asar nake” Ya faɗa yana ɗan shafa gemu.
“To ” Ta ce ta tashi ta nufi frige.
“Wato ainifin ba mai sanyi ba sabo mura ta mun kamu me ƙarfi” Ya faɗa cikin yiwa maganar tasa kwaskwarima irin ta ustazai.
Ɗan jim ta yi tana jinjina ƙoƙarin mutumin, shi da ya zo barka, barkar ma daga maƙota amma har yake neman ruwa, haka dai ta kama hanya ta fita tsakar gidan tana addu’ar Allah sa dai shek ya tafi ba tare da matsalar da suke ciki ba ta bayyana kanta.
Ƙoƙarin sanya takalminta take amma kuma ganin Hassan na warware jelarsa sai ta dakata, tana ɗan kallon Ustaz ɗin da fatan Allah sa kar ya lura.
“Ɗan kula Sthadiya kin san daga nan wajen wani wa’azi zan je da ake gabatarwa a can masallacin sama damu duk laraba da yamma” Ya faɗa yana ɗan satar kallonta, tana shirin bashi amsa sai ganin micijin ta yi ya taso kamar wanda yake tafiya a kan iska, bai yi masauki ba aai a tsakiyar gidan, ya ɗaga kai sama ya fasa kansa alamar sara tare da sakin wani ƙara me kamar hamimiya.
“Allahu akbar! Sthadiya wato ainihin ki bar ruwan nan kawai, na yi ɗoren azumin nafila” Ya faɗa a ɗan gigice yana miƙewa tsaye daga zaunen da yake, a ransa ya ce.
“Ashe dai Barira da gaskiyarta da take bani labarin an ce yaran ɗayan miciji yake zama, da na aan gaske ne da sai dai na yiwa Imran barka a waya ko a hanya in mun haɗu amma babu abin da zan shigo yi gidan nan saida rai”
“Azumi kuma yau fa laraba” Sadiya ta faɗa dan ita kawai ƙoƙarinta ta ɗauke nasa hankali kar ya ga micijin bata san ya gani ba, bare kuma ƙaran da micijin ke yi ma tuni ya sanya hantar cikin Shek ɗin ta kaɗa.
“Bari kawai dai kowace rana ma ai mutum na iya azumin nafila” Ya faɗa da magana kamar yadda kowa ke magana ya manta cewa sai ya yiwa maganarsa kwaskwarima irin ta Ustazai.Ganin rikicewar da ya yi sai Sadiya ta fahimci ya ha micijin, a hankali cikin sanɗa ya nufo ƙofar falon, Sadiya ta koma gefe ɗaya ta takure a jikin bango dan ta bashi hanyar. Idanunsa a kan micijin ya tsugunna yana lalumen ƙasa takalmansa yake so ya ɗauka amma ruɗewa ta hanashi nutsuwa bare ya fahimci ko inda takalmin yake hannunsa bai kai ba.
“Ɗaya mafarin ƙirge, biyu idanun dabba, uku duwatsun murhu, huɗu ƙafafun tebur, biyar na yatsun hannu” Cewar Shek hankali tashe ganin micijin ya iyo tsalle ya sauka a gabansa.
A hankali ya ɗaga kai sama ya fasa a lamar sara.
“Shida ranakun aiki, bakwai kwanakin mako, takwas goma ba biyu kenan, tara daga ke sai goma, goma biyar biyu kenan” Ustaz ya faɗa yana sakin kuka kamar ƙaramin yaro dan tun da yake bai taɓa ganin miciji me girman wannan ba, kuma a gabansa haka yana neman saran sa, in ba tsautsayi ba zagin mahaifi me zai kawo sa barkar mutum ɗaya miciji ɗaya.
“Dan Allah Shek ka yi addu’a wallahi tun wajen ƙarfe ɗaya yake a haka so nake ma ya koma mutum amma har yanzu shiru, gidan nan kusan mutum goma ne amma duk sun ɓuya sai ni kaɗai, kai da yake malami ne ko ka masa addu’a” Cewar Sadiya tana kuka.
Shiru Shek ya yi sai lokacin ma ƙwalƙwalwarsa ta fara taryo masa cewa ashe karatun hausa ne na irge da aka koya musu tun suna primary yake faɗa ba addu’a bace, so yake ya tuno wata addu’a ko da ɗaya ce amma ya kasa sai danna carbinsa yake kamar zai maida madannin ciki, ga bakinsa har kumfar yawu yake kan magana amma bai san me yake cewa ba.
“Labbaika lahumma labbaik, labbaika lashari kala labbaik, innalhamda, wanni’imata laka wal mulk laaaaaaaasharikalak” Cewar Shek da mugun ƙarfi dan har la ɗin lasharikalak ya ja duk ya karaɗe gidan ganin miciji zai bi ta tsakanin ƙafafunsa dan tun lokacin da micijin ya tunkarosa ya tashi tsaye daga durƙuson ɗaukan takakalmansa.
Sulululuuuu micijin ya bi ta tsakanin ƙafar, Shek ai kafin micijin ya fito ta tsakanin ƙafafun Shek fitari ya rigasa fitowa, fitsari ne kawai yake kwaranyowa kamar an buɗe famfo, duk ya zuba a jikin micijin amma Shek bai ma san ya yi fitsarin nan ba kawai tashin hankalinsa micijin a tsakiyar ƙafafunsa. Haka micijin ya bi ya fito ta baya, ya ƙara gewayowa zai shige ta tsakiyar ƙafafun nasa
“Innal halala baiyyinun, wa innal harama bayyinun, A ƙarama A babba Ba ƙarama Ba babba, ca ƙamara ca babba, an, in, un, ban, bin, bun, tan, tin, tun” Ustaz fa sai bitar karatu yake a matsayin addu’a ko gaga baya yi. Amma micijin nan sai da ya bi tsakiyar ƙafarsa sau uku sannan ya dawo gabansa, ya juya masa baya ai da ya ɗaga jelarsa bai sauke a ko ina ba sai a kan ƙafar Shek, Shej yadda ka san wuta aka ɗora masa haka ya ji.
Ai da ya wani buɗe murya ya dage ƙarfinsa ya ce.
“Assalatu kairum minannaum, Allahu akbar la’ilaha illalllaaaaaaaaaah” Ya faɗa yana kuka har da dariya.
Inna da tun karatun Shek na farko ta jiyo daga maɓoyarta, hakan ya bata tabbacin akwai wanda ya kawo kansa gidan dan haka bata yi sanya ba ta taka bencin ta leƙo ta window dan haka duk abin da ake a kan idonta, dariya kwa ta yi ya fi cikin carbi, babu abin da ya bata dariya sama da yadda zilaikar Shek ta yi sharkaf da fitsari, sai kwaranyowa yake.
“Jama’ar unguwar nan ku zo ga limaminku na fitsari a tsaye, da a ce wani ya gani yana fitsari a tsaye wataƙila sai ya masa wa’azi” Cewar Inna a ranta tana dariya har da ƙwallarta.
“Allah, Allah, sayyadina Muhammadu, wa ala alih sayyidina Muhammadu” Ya faɗa likacin da ya daddage yana bugun ƙirji irin yadda maulidi ke yi.
“Bari na biya maka karatuna ni ma sanda na samu kaina a wannan halin har Imirana ya tuna min wani wajen, zan ji ko kai za ka karɓa” Cewar Inna tana dariyar ƙeta.
“Alif, anbaki, wawzal” Cewar Inna da ta leƙo kanta daga windown ta sako bakinta. Ai hakan sau ya tunawa Shek da makarantar allo lokacin yana ƙarami, a take ya karɓe har yana neman yin gaga.
“Baaaa, aliiiiif, baƙiiiii, lallaaaaaan, hakuriiiii” Ya faɗa yana jan kowane ɗaya daga ciki. Dariya sosai Inna ke yi har ta kasa magana jan dariya, yana gama faɗar wancan sai ya fara.
“Book littafi kenan, chair kujera kenan” Yana ta jero sunayen abubuwa da turanci tana fassarawa da hausa, dan har lokacin jelar tana kan ƙafarsa. A guje micijin ya yi hanyar zaure be tsaya ba sai da ya dangana da ƙofar, ai Shek na ganin haka sai ya ɗakko hiramin wuyansa ya durƙusa cikin sauri ya ɗauki takakmansa ya naɗe takalman a cikin hiramin ya ci uban tumuri da shi a tsantsa, sai da ya ɗaure hiramin sosai a tsantsarsa sannan, ya zura da gudu, wurin Sadiya, yana zuwa ta yi saurin natsawa ganinsa dab da ita, ƙara matsawa ya yi, ta kuwa sake matsawa ta bar jikin bangon ai Shek sai ya koma yake ƙoƙarin laɓewa a bayanta.
“Haba Shek ya za kake matsowa kusa da ni, baka ganin matar aure ce ni”
“Haba Sadiya wato ainihin babu banbanci tsakanin jinsi da jinsi idan a halin ceton rai ake ” Ya faɗa yana neman kai hannunsa jikinta, dan shi gani yake tun da uwar micijin ce ita to ba zai masa komai ba in ya gansa a wurinta.
“Me ye hakan wai?” Ta faɗa tana mata rai.
“Ki ceci limamin masallacin unguwarku mana Sadiya, kin san dai in micijinnya ganni tare da ke zai ƙyaleni” Ya faɗa dan zuwa lokacin duk ya daina maƙale-maƙaken murya Sadiya ma yake faɗa sak, ba kamar zuwansa ba da yake cewa Sthadiya.
“To dan gwafar ubanka Imirana da ya haifi micijin yana tukunya a ɓoye, ka ga kuwa ai bai bar ubansa ba ma bare kai” Cewar Inna da ke window. Ganin micijin ya dawo daga zauren sai kuwa Shek yake neman damƙo Sadiya cikin ficewar hayyaci da tsoro.
“Ihuuuu kwarto, jama’a ku kawo ɗauki kwarto a gidan nan zan yi fyaɗe” Cewar Inna gabaɗaya kowa ya ji maganar duk sai suka ƙara tsorata da maganar kwarto dan haka, Hajiya sai ta ƙara totsuwa cikin ƙatakwaye, har tana buga kanta a jikin fikankin gado.dan kar kwarto ya ritsa da ita da girmanta, Mama da ke cikin drower sai ta ƙara totsuwa duk da matsin da take ciki, can ƙarshe ta matsa ta miƙa hannu ta kwaso kayan Imran wanda duk siglet ne da gajerunan wanduna, a inda ta sanya hannun nata, ta kwaso ta jibga a kanta, duk da tana jin nauyin ɗora gajerunan wandunan da singiletin amma haka ta daure dan kar a mata fyaɗe a gidan siriki.
“Wayyo Allah, ga raɗaɗin lalle a fuska da wuya, ga miciji, hallaw ga fargabar shigowar kwarto, wayyo ɗan budurcina da nake tattalawa zan kai gidan miji, haka kawai ina ganin ƙawayena suna bin maza amma na ƙi san in kai mutucina gidan aure amma gashi a neman halal wani ƙaton zai karɓe min” Cewar me ƙunshi da ke cikin kayan wanki.
Ƴan cikin loka kuwa kuka suka fara haiƙan jin wata ƙaddarar ta shigo gidan. Ashrof da ke bayi ita kaɗai tuni gumi da hawaye sun daɗe da mata sallama.
Imran kuwa jin abin da Inna ta ce sai ya koma ya ƙara lumewa a cikin ruwan, har yana shiga hancinsa amma gani yake da ace ya fito wurin micijin nan gwara kowa ta yi ta kanta dan ya san dai ba Sadiya ce kaɗai a gidan ba.
Inna sakkowa ta yi daga saman bencin, ta ɗakko ashana tare da buhun shinkafa marar komai, ta ɗaga ƙafa ta doki jikin lokar da matan nan je ciki, aikuwa suka ƙara sakin wani kukan, tsaki ta yi, ta juyawarta ta buɗe ƙofar kicin ɗin ta fito, ganin Hassan daga gefe ɗaya, ga kuma Shek tsaye bayan Sadiya dan tana motsawa yake take mata baya. Hanyar murhu ta nufa tana zuwa ta ce .
“Ihuuuu kwarto” Sai da ta tabbatar Imran ya ji da gangan ya ƙi fitowa, aikuwa ta sanya buhu a murhun dama cike yake da ita ce ta kunna ashana ta sanya nan sa nan wuta ta kama ci galgalgal, dariyar ƙeta ta yi tana jijjiga kai ta koma gefe ta tsaya ta ce.
“Kamar yadda na fara jin sanyi lokaci guda ya baibaye firinji, haka kaima za ka ju zafi lokaci guda ya baibaye tukunya”
Imran da ke cikin tukunya, ya ji wani zafi ya fara ratsa tukunyar, gyara rungisan sa ya yi amma sai ya ji abin na ƙaruwa, amma aai ya daure, jim kaɗan sai ya gabaɗaya kamar an sanyashi a ovin.
A mugun firgice ya bugi murfin tukunyar ba shiri, ji kake gwagwaraf, ya yi jifa da murfin, sai gashi yana fitowa jargaf da ruwa a jikinsa ga kuma uban gumi kamar an masa wanka …
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
2️⃣5️⃣➡️2️⃣6️⃣
Wani ƙululun baƙinciki ne ya zo ya tokarewa yarinyar maƙoshi, jin abin da Inna ta faɗa, gabaɗaya sauran matan suka fara bin ƙirjinta da kallo suna so su gano asalin gaskiyar abin da Innar ta faɗa, aikuwa kowa ya shiga danne dariyar da ke cin sa ganin gaskiya Inna ta faɗa in ma akwai gyara a maganar to kuwa kaɗan ne. Ganin kowa ya zubawa ƙirjinta ido sai ita ma ta shiga kallon ƙirjin nata har da sanya hannu ta ɗan ɗame jikin rigar wai dan ta ga girmansa.
“Duba da kyau dai ɗiyar nan ƙarya zan miki, ai yanzu kya yarda da kika ɗame rigar ai kin ga girmansa bai fi ƙwayar ƙarago ɗan nera biyar ba idan ma ya kai kenan”
Magana yarinyar ke yi ƙasa-ƙasa da baka jin me take faɗa sai yafda bakinta kawai ke motsawa kake gani da alama rashin kunya take yiwa Inna.
“Wa ya ga banza ta kori wofi ai maganar ciki ba magana bace a fito fili a faɗa mana” Cewar Inna ta juya ta nufi ɗaki tana ɗan dudduƙawa dan har zuwa sannan hancinta bai daina zuba ba sosai mira ta mata kamun kazar kuku. Sai kuma wacce ta yi tusa aka cijeta ita ma ta fara magana.
“Aikin banza da wofi duk kin bi kin cije ni, haba wannan wane irin abu ne” Harara kawai ɗayar ta bita da ita ba tare da ta yi magana ba dan idan ta buɗe baki komai ma za ta iya faɗa, saboda yadda ta yi ta ƙwararta da warin tusa sannan ganin Imran ma a wajen ya sa ta ɗaga mata ƙafa.
Inna tana zuwa falo sai ganin Sadiya ta yi kamar an dasa ta a wajen tana tsaye a tsakiyar falon hannunta riƙe da Hassan a siffar miciji har lokacin bai dawo siffar mutum ba. Wani yawu Inna ta haɗiye ba tare da ta cewa Sadiya uffan ba ta nufi inda suka ajiye lalle, kowanne a leda aka kwaɓashi sai mai ƙunshi take ɗauka tana zubawa a cikin kwarkwaron da take ƙunshin. Lalle ne ɗan kwali sajen ne ja da kuma baƙi na fulawa. Da ɗan yawansa a cikin ledar, saboda gabaɗaya ta kwaɓe yadda zai ishe su. Inna baƙin ta ɗauka na fulawar ta ɗauki baƙar leda ta sanya a hannunta ta ƙulle sannan ta juye wannna lallen a kan baƙar leda Sadiya da ke cikin wani haki ko kallon Inna bata yi ba tun shigowar Innar da ta kalleta bata ce komai ba. Dan kawai gabaɗayansu mamaki suke bata na gudun da suke yi, duk da ita ma ta san da a ce Hassan ba ɗanta bane dole ta gudu dan tsoro amma yanzu babu yadda za ta yi ko da tana jin tsoron saboda ya zame mata dole.
Inna sai da ta juye baƙin lallan nan duka sannan ta juyo a dudduƙe ta fito daga ɗakin har lokacin dai kowa na tsaye carko-carko, me ƙunshi ta ɗan juya kenan kafin ta juyo sai ji ta yi an damƙeta an shiga lafta mata wani abu a fuska da ta kasa tantance menene.
Inna kuwa tun da ta damƙi wuyan me ƙunshi ta baya, bata saki ba ta dage sai lafta mata lallen take a fuska kamar wacce take fenti a bango, sai da ta lafce mata shi gabaɗaya a fuska har wuyanta sannan ta sake ta tana ta ihu dan ma dai ta rufe ido da har idanun zai shiga. Imran tun da ya kallesu sau ɗaya ya ɗauke kai dan shi baya son hayaniya kuma ya san da alama yarinyar wani abu ta yiwa Inna dan ba ya raba ɗayan biyu ita ce ta rufeta a freezer.
“Wayyo Allah na Allah sa dai ba kashi bane kika lafce min shi a fuska” Cewar me ƙunshin tana ƙololon amai lokacin da Inna ta sake ta.
“Shigiya kudurarriya ni da kashin ma na samu ai da wallahi har haɗiya sai na sa kin yi, har ni zaki garƙame a cikin firinji, sanyin duniyar nan na cikinsa ya ƙare a kaina, hancina banda yoyo babu abin da yake in ba ruwan zafi na yi ba ma masassara ce za ta kama ni, saboda rashin tsoron Allah duk sanyin nan da ake baki tausaya min ba kika rufeni kika kunna firinjin” Cewar Inna tana face hanci tare da sakin wani kuka na tausayin kanta irin yadda ta sha artabu a cikin freezer.
Gabaɗaya dariya suka kwashe dashi Inna da ke shirin magana ta dakata ganin Sadiya ta fito riƙe da micijin a hannunta ba Inna ba su duka ma masu dariyar dakatawa suka yi, Imran da ya fara wani ɗan kakkauda kai yana sosa ƙeya dan ba ya son Sadiya ta zo ta bashi micijin ta kunyata shi a gaban matan nan. Dan haka sai ya shiga muzurai yana ɗan babbasarwa shi a dole ba komai bane. Inna kuwa tun da Sadiya ta fito ta fara tunanin inda za ta garzaya dan ta tsorata da yaron yanzu dan bai taɓa kaiwa kamar haka bai dawo mutum ba amma yau ya yi dogon zango.
Sadiya da take shirin buɗe baki ta yi magana Inna ta katse ta da cewa.
“Ke kuwa Halima baka tausayin yaron nan kika fito dashi da sanyin nan, ko dan kinnga ba a siffar mutum yake ba kike gani kamar baya jin sanyi” Ta faɗa tana wani karya kai gefe dan gabaɗaya ta matsu Sadiyar ta kuya ta koma inda ta fito dan kana kallon micijin duk jarumtarka sai ka ji tsoro saboda yanayin girmansa ma.
“Inna wallahi hannu na ya gaji da riƙonsa kinsan akwai nauyi fa kuma ina son na shiga bayi ne shi ne zan baiwa Abbansa ya riƙe min shi” Cewar Sadiya tana kallon Inna. Imran kuwa jin fitowar Sadiya saboda shi ta fito ta baiwa Hassan sai ya ji wani dammm ƙirjinsa ya buga dan shi yanzu har ga Allah ya tsorata da yanayin yaron.Wani yawu ya haɗiye da bai san lokacin da ya taru ba ya kalli Sadiyar yana shirin magana sai Hajiya da Mama da suka haɗu a ƙofar gidan yanzu suka shigo da sallama.
Ƴan matan nan duk sun sha jinin jikinsu, me ɗinki kuwa da fitowar Sadiya ta mantar da ita abin da Inna ta lafta mata a fuska da wuyanta tsabar tsoro, gabaɗaya ya mata baƙiƙƙirin a fuska kamar ta shafa baƙin gawayi dama ga ta sha uban bilicin sai ta koma kamar wata jimina.
“Yauwa ga kakanninsa nan” Imra n ya yi saurin faɗa ganin su Mama sun shigo. Idanun Mama da na Hajiya ne suka sauka a hannun Sadiya da ke riƙe da miciji, gabaɗaya wani tsoro ne ya rufe su dan su bai taɓa sawaya a gabansu ba, sai dai a basu labari ita kuma Hajiya dama ita ce me cewa ko ya zama miciji babu abin da zai yiwa mutane, sai dai ganinsa yau muraran ya kaɗa mata hantar cikinta, Mama kuwa cikin ficewar hayyacin ganin ƙaton miciji riƙe a hannun ɗiyarta ta buɗe baki ta ce.
“Sadiya me zan gani haka? Hassan ɗin ne ya zama wannan ƙatoton micijin kamar wata mesa? Kuma kika kama shi kika riƙe a hannu, me ye amfanin ubansa da yake tsaye?” Mama da soyayyar ƴa da uwa tasa ta manta cewar Hajiya na wurin ta faɗa tana kallon micijin.
“Haba Mamar Sadiya ai ana barin halak ma dan kunya, kuma uwa ai ita ce tushen ɗa, kuma da ita da Imran ai duk ɗaya ne ma in ta riƙe babu komai” Hajiya ma da son ɗanta ya rufe mata ido ta faɗa ita ma idanunta a kan Hassan ɗin.
“Wai ni kam me yasa kuke haka, ta yaya ma za a ce uwa ce rushen ɗa haba Amina wannan ma ai ba maganar ɗauka bace, uba ai shi ne tushen ɗa, lokacin da ya ɗirkawa ƴar mutane ciki take riƙitu da tsohon ciki baki ce haka ba sai yanzu da take riƙe da miciji aka ce a bashi ya riƙe?” Cewar Inna tana hararar Hajiya Amina da sai yanzu ta ga wautar ta amma ai da gaskiyarta ya za a yi a riƙe miciji da bbau tabbas a kansa.
Hajiya da ke shirin maida martani ta rufe bakinta ruf, ganin wani uban ƙwacewa da micijin ya yi daga hannun Sadiya ya wani zabura ya yi sama kamar wata iska ya bar hannun Sadiya. A tsakiyar mutanen nan ya tsaya tare da fasa kai yana wani wawwaiga idanu. Kowa ya matuƙar razana da yanayin yadda micijin ya yi, Mama kallon ƙofar gidan ta yi amma cikin rashin da’a sai ta ga a kulle dan dama Imran na shigowa sai ya manta bai rufe ba su kuma suna shigowa sai suka maida ƙofar suke rufe jamlock ɗin ya shiga.
Dan haka babu hanyar fita dan yadda jikin kowa ke karkarwa babu inda za su iya buɗewa saboda a tsorace suke gabaɗaya sun gama tsurewa.
Inna kuwa tana ganin hakan sai bakinta ya fara motsi leɓanta na sama ya fara gwaruwa da na ƙasa alamar dai tana rattabo du’ai.
Kowa karkarwa yake kamar sun haɗiyi mazari.
“Wai shin Imirana duk wurin nan fa kai ne namiji, ka yi wani abu mana ” Cewar Inna cikin sarƙewar murya.
” Haba Inna in shi ne namiji ma sai ya kai kansa ga halaka, kar ki manta ni fa shi kaɗai gareni, ga uwar yaro kya ke cewa wai shi namiji ne ai Sadiya ma mace ce me kamar maza kwari ne kawai babu” Hajiya ta faɗa har rana yin in’inna tsabar a ruɗe take.
“Oh ni Azumi na ga abin da ya turewa buzu naɗi wallahi yanzu Amina ƙin gaskiya ƙiri-ƙiri to wallahi ki ji tsoron Allah dan faga ƙin gaskiya sai ɓa…
Wani uban zillo da micijin ya sake yi tare da maida kansa ya kwantar a ƙasan sai kuma ya ɗaga jelar sama, shi ya dakatar da Inna daga maganar da take son ƙarasawa. Kowa ɗif ya yi babu me cewa uffan amma da ka gansu ka san a matuƙar tsorace suke. Imran kuwa sunkuyawa ya yi ya ajiye wayarsa a ƙasa ya ɗago tsaye ya sanya hannunsa na dama a haɓarsa ya shiga shafa haɓar da shi kansa bai san dalili ba, shafawa yake ba ƙaƙƙautawa daga gefe zuwa gefe, bakinsa kuwa sai mismismis yake shi kaɗai ya san me yake faɗa. Inna kuwa hannu ta sanya ta toshe hancinta da ke zubar majina, idanunta a kan me ƙunshi nan da take karkarwa fitsari na biyowa ƙafafunta sai buɗe baki take tana kuka amma marar sauti zuwa lokacin lallan ya gama haɗa mata fuska da baƙi ta yi baƙiƙƙirin da ita.
“Shegiyar yarinya ji yadda ta koma kamar bunsurun ɗan akuya, gabaɗaya ta yi baƙi kamar ta shafa baƙin bula, sai ta zama kamar irin baƙin bunsurun nan gemu ne kawai babu” Cewar Inna a zuciyarta tana dariyar ƙeta duk da halin da ake ciki amma fa ka kalli me ƙunshin nan sai ka kai zuciya nesa ne dariya ba za ta ƙwace maka ba. Gurbin idonta kawai ake iya hangowa ita kuwa sai ɓare baki take tana da na sanin zuwa gidan ƙunshin ma gabaɗaya.
Sadiya kwa gaban micijin ta je ta durƙusa tana kallonsa hawaye na zubowa daga idanunta. Mama kuwa so take ta ce Sadiya ta tashi faga gaban micijin sai dai tsoro da fargaba ya hanata magana tana ganin kar ta yi magana micijin ya iyo kanta ya sare ta a banza ta bar duniyar a wufi, dan haka sai ta ja bakinta ta yi shiru tana ta lazimi a zuciyarta lazimin da ita kanta da za a sanya mata wuƙa a wuya a ce ta faɗa ko kalma ɗaya ba za ta iya faɗa ba, dan ta kasa banbance ma addu’a take ko karatun qur’ani ko kuwa ƙasida, wani lokacin ma sai ta ji kamar waƙa-waƙa take amma Allah ne kaɗai ya san karatun kurma.
Da baya da baya micijin ya shiga tafiya aikuwa aka dare aka bashi hanya, kowa cikinsa na ɗurar ruwa ga miciji da shegen gudun tsiya idan ka ce za ka gudu idan ya biyoka ba lallai ka tsere masa ba saboda gudun da yake dashi. Dan haka sai kowa ya shiga taitayinsa aka shiga jiran ganin abin da zai yi. Sauran matan kuwa sai kuka suke marar sauti wata ta kama tsantsa wata ta ɗora hannu a ka har da wacce ta ɗaga hannaye sama irin yadda ake addu’a ta baza tafukan hannaye sai wani karkata kai take tana kai kukanta wurin Allah.
Ashrof kuwa ta sanya hannu a fuskarta ta rufe fuskar da tafukan hannayenta tana kallon micijin ta tsakanin yatsada yatsa dan kar ta rufe idanun duka micijin ya iyo wurinta dan ita ganinsa kaɗai ma razana ta yake. Hajiya yadda micijin ya fara ja baya haka ita ma ta shiga ja baya, a hankali har sai da ta ga babu wurin gudu sannan tana tsoron ta zuba da gudu micijin ya tsallakr kowa ya biyo ta haka ta jure tana cewa a zuciyarta.
“Allah ka dubemu ka kawo mana mafita”
“Allah ka kawo me cetonmu, a wannan gida da muke ciki a rufe ga kuma ajalinmu a tare da mu” Cewar Inna a ɗan hankali kamar tana tsoron faɗa.
A hankali micijin ya shiga kanannaɗewa har sai da ya kanannaɗe duka jikinsa, sai kuma cikin hanzari da zafin nama ya zura da gudu, ya shiga zagaye gefen da mutanen ke tsaye kowa kallonsa kawai yake sai da ya zagaya kusan sau uku, sannan cikin tafiya ɗaya biyu ya yi sai gashi a gaban Imran yana zuwa ya fasa kai ya dakata a wurin ba tare da ya matsa ba.
“Ka min daidai Hassan, gwara da ka je gun ubanka da kan ka yau za mu ga ƙarshn ƙarya” Cewar Inna a zuciyarta tana ƙwafa.
“Wayyo Allah ɗana, ɗana guda ɗaya da nake da shi duk duniya yau ya haifi abin da zai zama ajalinmu” Cewar Hajiya a zuciyarta tana tana share hawaye.
“Gwara da ka je wurinsa tun da ba ita kaɗai ta haifeka ba da za take jigilarka ita kaɗai” Cewar Mama a zuciyarta a fili kuma sai ta dakata da motsin bakinta ta danne gefen keɓenta da haƙori, irin ka min daidai ɗin nan.
Imran kuwa wasu hawaye ne masu kamar an musu dole su fito suka shiga surnano masa a fuska, sai na ido ɗaya ya gama gangarowa sannan na ɗaya idon ma ya gangaro.
“Alwudu’u, alwala, kaifa tatawadda’u, yaya za ka yi alwala” Cewar Imran yana sakin kuka dan yau ya sadaƙar sai dai gawarsa tun da har kicijin ya je gabansa da kansa.
“Ɗan karan uwa ɗan gwafar uba da baka karanci yadda ake alwalar ba sai yau, to duk sallaolinka na baya aradu ka yi su a wofi tun da sanda ka yi baka iya ba alwala, sai yau da ka ji uwar bari, ka fara tuna karatun alwala ai bari ba shegiya bace da ubanta” Cewar Inna a zuciyarta.
Sauke kai micijin ya yi daga fasa kan da ya yi, ya wani kaiwa ƙasa sara sau biyu da mugun ƙarfi.
Imran idanu ya ƙwalalo tare da ɗauke numfashinsa ganin micijin ya sari ƙasa kusa da ƙafarsa, duk tunaninsa ma shi ya sara sai da ya zare idanu da kyau sannan ya gane ƙasa ya sara, sai dai yana rayawa a ransa shi ma ana daf da saransa. Ƙafafu ya ƙame a wuri ɗaya yadda sojoji ke ƙamewa, ya ɗaga hannu biyun duka ya ka gefen kansa yadda sojoji ko ƴan sanda ke yi idan za su sarawa oganninsu, amma shi da hannu biyu ya yi, a wannan ƙamen ya shiga jero taken Nigeri’a ba ƙaƙƙautawa, shi kansa ya tsinci kansa ne yana faɗa ba tare da niyyar hakan ba saboda gabaɗaya ya rasa me zai ce ma.
“Kai jama’a yau ake yinta, lallai gulma yau ya ƙare tun da uwar gulma ta yi cikin shege, wato saboda ɗaurewa Nigeri’a da harshen nasara tsantsa kaima yadsa abokinka sojojo ya yiwa Nigeri’a baitika kaima hakan take” Cewar Inna a ranta tana tuno yadda aka kwashe da soja da Hassan ranar nan.
Kamar wanda aka faɗawa micijin sau saurin barin wurin Imran ya yi ya tafi wurin Hajiya yana zuwa ya tsaya a gabanta. Ai da sauri ta gyara tsayuwarta tana ɗaga hannaye yadda Imran ya yi ra sanya su a gefen kanta yadda sojoji ke yi ta buɗe baki kuka na neman ƙwace mata sai dai tana tsoron sakin kukan dan kar micijin ya sareta ta ɗan ɗaga murya amma kuma ƙasa-ƙasa ta ce.
“Imran karanto min taken Nigeri’ar sai in ke faɗa idan ka faɗa ka san ni ba iyawa na yi ba, amma idan kana karantowa sai in ke bita, tun da gashi a gabana layi ya zo kaina” Hajiya ta faɗa idanunta a kan Imran da har lokacin bai saki hannayensa ba haka zalika ƙafafunsa na nan yadsa suke a haɗe, bakinsa kuwa sai jerawa Nigeri’a kirari yake, kamar wanda aka ce Nigeri’ar za ta watse idan ya dakata da yi.Sara ya fara a gabanta ko ƙaƙƙautawa babu, kuma babu alamar zai dakata, dan haka Hajiya sai ta fara kuka, kuka kawai take wiwi dan ta rasa ma yadda za ta yi. Cikin ikon Allah sai ya bar gabanta amma bata bar yin kukan ba, gaban Inna ya nufa yana zuwa ya tsaya. Kallon kallo suka fara da Inna wacce majina ta taru cikin tafukan hannayenta da ta rufe bakin da su, ganin micijin a gabanta sai ta ce a zuciyarta.
“Yau na tabbatar kai ba mutum bane, ɗan ruwa ne, in ba ɗan ruwa ba a ce jariri da kai amma har ka aan ka je gaban wannan ka je gaban wancan”
Ganin yana shirin kaiwa ƙasa sara sai Inna ta yi karaf ta fara masa waƙa.
“Haba Hasanunu, ɗan aljanna, haba hasanunu ƙaton kirki, haba Hasanuna ɗan Imirana, haba Hasanunu me sauya kala” Ta faɗa tana wani rausaya kai ita a dole ya bar gabanta, ai sai gani ta yi ya kai wani sara me ƙarfi.
“Lanjeriya ƙasar ƴan baiwa, lanjeriya ƙasar talakawa, lanjeriya ƙasar Bahari ɗan daura” Ta faɗa tana kuka hawaye shaɓe-shaɓe.
Wani saran ya kai wanda ya kusa samun ƙafarta ta janye da sauri, cikin kuka ta ce.
“Wallahi tallahi, ƙur’ani ban iya yaren nasaraba (Turanci) Dan Allah tun da dai Nigeri’a ƙasar hausawa ce ka barni hakan dan wallahi ban iya irin wanda Imirana da sojojo ke yi ba” Kamar wanda aka tsikara ya fara tahowa, gabaɗaya matan nan suka sha jinin jikinsu.
Kowacce ta shiga addu’a tana fatan kar ya zo wajenta, zagayasu ya yi sau ɗaya Mama da Hajiya da ke gefe, suka ƙara matsawa kusa da sauran kowa yana jin matsanancin tsoro.Gafe ɗaya ya koma ya tsaya yana ƙare musu kallo har Sadiya da ke tsugunne a wajen, Ashrof kwa hawaye sam basa tsayawa ga tausayin kanta da na ƴar uwarta da ma mahaifiyarta.
“Sahuuuu” Cewar Inna cikin tsoro, kowa da ido ya bita alamar tambaya.
“Yo jama’a ba dole na ce sahu ba tun da haka Allah ya ƙaddara mana yau, zama inuwa ɗaya da miciji, kuma miciji me son taken Nigeri’a to tun da Imirana ne ya fi iyawa sai mu bi ayari mu yi sahu, mu bi bayansa idan ya faɗa sai mu ke masa amshi da dai mu tsaya micijin nan ya mana ɗauki ɗai ɗai, dan ni kuma ban shirya mutuwa yanzu ba in barwa Tasalla Malam” Cewar Inna tana kuka abin tausayi abin dariya.
Gabaɗaya kowa sai ya fahimci maganar Inna haka take dan suna ganin kamar micijin ya fi son national anthem dan haka sai suka fara yin lafi a bayan Imran banda Sadiya da ke tsugunne a tsakiyar wurin, Imran da har lokacin yake a ƙame bakinsa bao huta ba da taken Nigeri’a yana kaiwa ƙarshe sai ya dawo farko. Yana faɗa su ma suna faɗa duk da ba kowa ke faɗa daidai ba irin su Inna da su Mama su ma sauran matan tsoro ya mantar da su cewa sun iya national anthem sai suka dawo kamar wasu ƴan koyo dan suna ganin kamar Imran ne ya fi iya wanda micijin ke so.
Suna cikin yi sai micijin ganin sun tattaru a waje ɗaya sai kawai ya shiga zagaye su, a mugun guje yake zagaye su har wani tsalle-tsalle yake, ganin hakan ya sanya suka ƙara tsorata, cikin tsoro da ruɗewa suka dunƙule a waje ɗaya, kowa ƙoƙarinsa ya samu mafaka a jikin ɗan uwansa, dan gani suke kamar in kana kusa da wani micijin ba zai zo wurinka ba. Imran da Mama sun ƙanƙame juna cikin rashin sani dan ita bata san shi bane shi ma bai san ita bace an haka kowa ya ƙwamusu baka jin komai sai sautin koke -koke.
Sai da ya gaji dan kansa ya koma waje ɗaya ya tsaya, kowa ya ɗan fara sakin ajiyar zuciya, Mama da Imran sai lokacin suka ankare sa sauri suka saki juna Mama na saurin juyawa ta dafe haɓa tana zabga salati a ranta, idan ba larura ba ya za a yi a ce sun rungume juna ita da Imran mijin ƴarta Sadiya. Kafin kowa ya gama tantancewa micijin ya buga wani uban tsalle ya hau kan bishiyar da ke tsakar gidan gabaɗaya kallo ne ya koma sama, kowa na kallon micijin da mamaki har da Sadiya ma da ta rasa bakin magana sai kuka, jelar ya kanannaɗe a jikin reshien bishiyar ya zaro kan sa yana kallon kowa da kowa, ganin haka sai kowa ya fara neman inda zai fake idan an sakko micijin ya dawo mutum sa fito.
Imran da gudu ya nufi wajen tukunyar dafa ruwan wankan jego da ke ɗore a kan murhun sai dai ba a kunna wutar ba, a ka Inna ke barinta saboda wahalar ɗorawa sai dai wani lokacin ta kan bar ruwa kaɗan a ciki. Yana zuwa bai yi wata-wata ba ya gotar da murfin tukunyar da yake babbace sai ya samu ya shiga ba tare da ya cire murfin duka ba, yana shiga ya ringisa a ciki, ya miƙo hannu ɗaya ya ja murfin ya rufe kamar me rufe ƙofa.
Matan nan sai gasu suna tseren shiga kicin da Inna, Inna ce a kan gaba, tana shiga ra sauke idanunta a kan freezer da sauri ta ɗauke idanunta dan ko ƙaunar ganin freezer bata yi.
Wasu lokarsu ta ɗazu suka ƙara komawa bayan sun garƙamawa ƙofar kicin ɗin sakata. Me fulawa da Hajiya da Mama suka shige ɗaki Hajiya ta shiga ƙasan gado dakyar tana kukkujewa amma ba damuwarra bace hakan mafaka kawai take nema. Mama cikin wardrobe ɗin Imran ta shige ta rufe, tana kallon yadda ta zaune kayan sirikinta har da gajerunan wandunansa. Me ƙunshi kuwa kayan wankin da ta gani a ƙulle a zanen gado masu yawa su ta sunce cikin sauri ta kwasa ta libgawa kanta.Sai wani zarnin fitsari take ji a hancinta ashe wandon Imran ne da ya jabgawa fitsari ranar da Inna ta rufe shi a ɗaki a ranar farko da Hassan ya zama miciji. Amma bata damu da warinnba tun da ta samu mafaka.
Ashrof kuwa bayi ta koma, ta banke ta aka bar Sadiya kawai a tsakar gidan tana kallon Hassan rataye a sama.
Inna da ke ƙasan wani dogon benci da da ake ɗora kayan abinci a kai ta rufa buhhuna kusan goma a kanta ta daddage ƙarfinta ta ce.
“Halima in ce dai kin samu mafaka, dan na ga Imirana tuni ya yi hanyar murhu, in kuwa tukunyar da nake dafa ruwa ya shiga dan na ji ƙaran murfin ina samun kaina wuta zan galgala masa sai na dafashi luguf ya dahu…
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
2️⃣9️⃣➡️3️⃣0️⃣
Yadda Imran ya fito a firgice cikin kiɗemewa ko lura bai yi ba da Inna da ke tsaye, ƙaran dariyar da ta saki ne ya sanya ya dakata daga ƙoƙarin gudun da yake wanda shi kansa bai san ina ya nufa ba. Ganin Inna tana dariya har da nuna shi da yatsa sai ya dakata tare da haɗe rai kamar ba shi ne ya iyo gudun ceton rai ba daga cikin tukunya, sanadin zafin da ya ziyarceshi.
Kallon murhun ya yi ya ga yadda wuta ta kama take ci kamar wanda aka sanya fetur, ga sauran buhun nan wanda Inna ta saka bai gama ƙonewa ba.
“Lallai tsohuwar nan ta ga makwancina da yawa, yanzu ni ta balbalawa wuta? Dan na san dai ai ba za ta ce bata san ina cikin tukunyar ba, ” Ya faɗa a zuciyarsa sai muzurai yake kamar zai hau Inna da duka.
“Imirana wai dama kai ne a cikin tukunyar wankan jegon matarka, soyayya ce ta sanya kakeso a dafa ka ta yi wankan da kai a memekon a dafa mata ruwa?” Cewar Inna tana ƙoƙarin danne dariyarta har da ƙwalla. Gefen leɓensa na ƙasa ya danne da haƙori ji yake kamar ya saki kuka dan takaici. Juyowa ya yi yana ƙoƙarin barin wurin dan dama wurin da murhun yake a ɗan lungu ne ba a sararin tsakar gidan yake ba.Sai da ya fito idanunsa suka sauka a kan Shek da ke ƙoƙarin raɓewa a bayan Sadiya ita kuma tana gocewa tana matsawa yana ƙara bin ta. A take maganar Inna da take cewa kwarto zai yi fyaɗe ta faɗo masa, ai ganin Shek kusa da matarsa ba ƙaramin fusata shi ya yi ba, in ba iskanci ba ya za a yi yake ɓuya a bayan matar aure, shin uban me ma zai shigo da shi cikin gidansa. Cikin jin haushi da fusata ya nufo wurin su dan gabaɗaya kishi ya rufe masa idanu har wani diri-diri yake gani, hakan ya mantar da shi ƙalubalen da yasa ya shiga cikin tukunya, dan gabaɗaya ya manta da batun miciji bare har ya yi tunanin shi ne dalilin da yasa Shek ɗin ɓuya a bayan matarsa. Idanunsa sun rufe ko lura da micijin da ke gaban su Sadiyar bai yi ba,a fusace ya nufo su, dan nufinsa yana zuwa wajen zai manta da mutunci da abokantakar da ke tsakaninsa da Shek ya shaƙe masa wuya sai an ƙwaceshi dakyar a hannunsa tun da shi ma bai ga mutunci da haƙƙin makotaka ba son zuciya ya rufe masa ido har ya zo yake neman yiwa matar aure fyaɗe.
Yadda ya taho a fusace kamar kumurcin miciji za ka ɗauka yana zuwa zai ɗauki hukuncin da ba zai yiwa kowa daɗi ba, amma me sai da ya zo dab da su idanunsa suka sauka a kan Hassan da ya yi wata alkafira, kansa ya cake a ƙasa sai jelar ta zama a sama sai wani wulwula ta yake kamar fanka. Wani uban birki Imran ya ja, tare da haɗiye wani yawu muƙuuut, ajiyar zuciyar ya fara saki a jere- a jere kamar wanda ya ƙwaci kansa daga hannun ƴan fashi. Cikin sauri ya fara kalle-kalle yana so ya ga ta inda zai tsere, yana waiwayawa bayansa sai suka haɗa ido da Inna da ke dariya marar sauti, ganin abin da ke faruwa dan dama ta gama karantar cewa Imran kishi ne ya rufe masa ido ya tafi ba tare da ya lura da micijin da ke juya jekarsa kamar an ƙurewa fanka gudu ba. Ita ma Inna a tsoracen take dan abubuwan da Hassan ke yi yau sun girmi tunaninsu, amma kuma ganin Imran ya taka birki ƙiiii kamar wanda ya kusa faɗawa kwalbati ya lura da ramin gabansa, hakan ya yi lolacin da ya yi ido huɗu da micijin.
“Dole ka nemi mafaka Shek ba lefinka bane, tabbas na daina ganin lefinka ko ni na na shiga gidan matar aure tuni zan manta da igiyar aurenta, in har a irin wannan bala’in ne ko a cikin ɗan kamfai (Pant) Ɗinta sai mutum ya totsu ya yi mafaka” Cewar Imran a ransa, fuskarsa kamar ya saki kuka, ga ruwan tukunyar da ya jiƙa masa jiki sai tsiyaya yake daga jikinsa, kallon Shek ya yi da gabaɗaya gumi ya gama wanke masa fuska sai tsiyayowa gumin ke yi ta jikin gemunsa yana ɗisa a ƙasa, ga yadda ya jiƙe da fitsari da alama ya yi fitsarin sama da kifi uku.
“Wayyo maƙocina, ashe kana cikin gidan nan, wallahi Sadiya ta ce min baka nan da tuni kai zan nema amma ganin baka nan ya sa nake nema ya rungumi wuta da hannu na, yo wuta mana duk inda na rafki matar aure da hannu na ai na san na kama wutar jahannama” Shek ya faɗa yana kallon Imran da ke kalle-kalle dan shi gabaɗaya ya kasa tantance a raye yake ko a mace ko mafarki yake da yake ta haɗuwa da wannan iftila’in.
“Imirana wai ya ka toge abokinka yana maka magana, amma ka ƙeƙashe ƙasa ka tsaya kamar wani gini, kar fa Allah ya kama ka a kan haƙƙin maƙotaka maƙocinka na cikin wani hali amma ka kasa kai masa taimakon gaggawa” Cewar Inna tana kallon Imran tare da danne dariyarta dan wata uwar harara ya aika mata kamar dai ta ce ya damƙi wuta.
“Allah dai ya miki albarka tsohuwa, nagode ƙwarai da gaske da kika ƙara fahimtar da shi” Cewar Shek yana kallon Inna da ke tsaye can hanyar murhu, so yake ya gudu bayan Imran amma yana tsoron abin da zai je ya zo domun kuwa ya ga micijin zai iya wartoshi lokaci guda , a gefe ɗaya kuma ga Imran ɗin ma kamar a tsorace yake, duk da kasancewarsa uba ga micijin.
A hankali Shek ya fara lallaɓawa sai da ya tsugunna daga tsayen da yake, cikin sanɗa ya fara rarrafawa ya nufi wajen da Imran yake, sai dai a matuƙar tsorace yake dan kar micijin ya biyo shi. Imran kuwa kafe Shek ya yi da ido ganin ya tunkaroshi zai je ya goga masa kashin kaji, dan idan da micijin zai masa kara saboda kasancewarsa uab a gareshi amma yanzu ganin Shek zai sa ya canja shawara, wani kallo ya yiwa Shek ɗin, yana kallon wannan hiramin da ya ci tumuri da shi a tsantsarsa. Shek kuwa ya raba hankalinsa biyu, ɗaya yana ƙoƙarin ya kai wajen Imran ɗayan kuma a kan micijin da ya ga duk wulwula jelar da yake amma kuma idanunsa a kan Shek ɗin suke. Har ya yi kamar zai dakata sai dai ya cigaba da rarrafen, sai da ya je daf da Imran micijin ya sauke jelarsa ƙasa, cikin kiɗima Shek ya dakata da rarrafe, bai san lokacin da ya tashi ba sai ganin kansa ya yi a tsaye cankarkar sai dai ya kasa tsayuwa dai dai sakamakon karkarwar da ƙafafunsa ke yi.
Inna kallonsu kawai take tana so ta ga ta yadda wasan zai fara dan ta san babu yadda za a yi a kwashe lafiya. Tun da Hassan ya ajiye jelarsa a ƙasa sai ya juyo ya maida hankalinsa ka su ya fasa kansa yana kallonsu, Shek ganin ya ƙura musu idanu sai ya sha jinin jikinsa cikin sauri ya buɗe baki ya ce.
“Ka masa magana mana Imran kai da ɗanka, ka yi saurin bashi umarni ya koma ɗaki ni in samu in bar gidan ma dan na rasa wane tsautsayi ne ya kawo ni” Ya faɗa yana kallon Imran da ke jifansa da wata muguwar harara.
“Da yana jin umarnin ai da baka zo ka tarar da abin da ka tarar ba hatta uwata tana cikin gidan nan ban san ma a ina ta ɓoye ba, kuma da ya san cewa ni ubansa ne ai ba sai na bashi umarni ba zai yi abu, ɗazu a gabana ya tsaya yana kai sara” Ya faɗa kamar zai saki kuka.
“Ka manta baka faɗa masa cewa har ƙwaƙumar Rakiya ka yi ba cikin rashin sani” Cewar Inna tana dariya tare da tuno lokacin da ta hangi Imran da Mama sun rungume juna kamar za su koma cikin juna saboda tsoro. Banza Imran ya mata dan shi yanzu kawai so yake ya fice daga gidan dan ya gaji da wannan wasan kwaikwayon. Yana tunanin mafita sai ganin micijin suka yi ya fara zulalowa a hankali kamar baya so, sai da ya zo tsakaninsu inda suke tsaye Imran da Shek ya ja ya tsaya, Shek na ƙoƙarin matsawa ya ɓuya a bayan Imran sai Imran ya ce.
“Kar ka kuskura ka motsa dan wallahi idan ya sareka ba ruwana”
Wani yawu Shek ya haɗiye yana kallon micijin kamar ya fasa ihu saboda yadda ya ganshi dab dashi abin ya matuƙar ƙara firgita shi amma ba yadda ya iya haka ya daure ya tsaya a inda yake. Zagayesu ya fara yi amma bai yi yinƙurin yin komai ba, ganin hakan ba ƙaramin ruɗewa Shek ya yi ba, amma kuma Imran ya hanashi motsi kamar yadda shi ma Imran ɗin bai motsa ba.
Wani tsalle da micijin ya yi shi yasa Shek da Imran rungume juna, yana komawa can gefe sai suka saki juna suna maida numfashi, kowa neman hanyar gudu yake, fara zagaya su ya fara yi cikin kuskure sai Imran ya ɗan motsa aikuwa Shek ma ya matsa wurinsa, miciji kwa ya ce da wa Allah ya haɗa shi in ba da su ba, haka suka shiga tsere, Imran a gaba Shek a bayansa, sai miciji a bayan Shek suna cikin zagaye Shek da ya ga micijin a bayansa yake kuma yana neman kai masa cafka sai kawai ya yi tsalle sai gashi ya ɗane bayan Imran, da yake jallabiyar ce a cikinsa kuma da zai haye bayan Imran be tattare ta ba sai ya zamana ya kasa ware ƙafafunsa ya zamana kamar goyo ya yi, sai ya zama kamar ƙadangare a jikin bango. Ƙafafunsa a sake amma kuma sai ya maƙalƙalo wuyan Imran, Imran kuwa tsabar ruɗewa ma bai san Shek ya ɗane bayansa ba shi dai kawai ya ji wuyansa a maƙalƙale sai ya yi tunanin micijin ne, aikuwa ƙafa me na ci ban baki ba, a haka yake ta sheƙa uban gudu a tsakar gidan.
Inna da ke can jikin bango tana hango su dariya kuwa cikinta kamar ya yi ciwo. Suna cikin gudun Imran ya kalli bayansa da wutsiyar ido, aikuwa ya hango Hassan na binsu hakan ne ya ankarar da shi cewar ba Hassan bane a wuyansa hannu ya kai bayansa aikuwa ya taɓo Shek da ke manne da shi kamar cingam haushi ne ya turnuƙe shi, yana mamakin ya aka yi ma bai ji nauyi ba sai ya danganta hakan da ruɗanin da yake ciki.
Wata mugunta ya yiwa Shek wani uban wujijjiga Shek Imran ɗin ya yi sai kuwa ga Shek yashe a ƙasa ya je da reran, miciji da je binsu da gudu yana zuwa sai ya bi ta kan ruwan cikin Shek, gabaɗaya Shek numfashinsa ya ɗauke lokacin da micijin ya bi ta kansa, bai ankara ba ya ji saukar wani fitsarin daga jikinsa. Imran kuwa wani tsalle ya yi ya koma gefe, micijin kamar an ce bi Inna kawai sai ya yi hanyar lungun murhu a mugun guje yana haɗawa da tsalle.
“Inna ce a nan lungun me maka ZAMAN WANKA” Cewar Inna cikin ruɗewa dan bata taɓa zaton zai zo inda take ba, ganin ya kusa ƙarasowa sai kawai ya saddaƙar ta yi wani uban tsalle ta faɗa cikin tukunyar da Imran ya fito.
Azaba da raɗaɗin ruwan ne da ya ɗau zafi ya ziyarce ta, kuka ta saki a zuciyarta tana cewa.
“Gwara na silsilge in yaso daga nan a kai ni maƙera su bani maganin wuta in ke shafawa a kan in bari ka sareni in mutu in barwa Tasalla Malam” Tana daga cikin tukunyar ta hangi micijin ya bar wajen, a sukwane ta fito ta ɗauki wani ruwa da ke cikin bukiti ta sheƙa tun daga kanta ta jiƙe jargaf.
“Kai Allah ka rabamu da wuta, ka haramtawa wuta cin naman mu duniya da lahira, yo ni da nake cewa sai na yiwa jikina ruwan zafi, saboda sanyin da na shaƙa a firinji ai yanzu na huta duk da sai cewa ruwan zafinsa ya wuce misali, oh duniya shi yasa ake cewa idan za ka gina ramin mugunta ginashi gajere gudun kar ka afka wata rana, gashi dai Imirana bai dahu ba ni na kusa dafewa lugugu ma ba luguf ba” Ta faɗa idanunta kafe a tsakar gisdan tana leƙawa dan ganin ƙwaƙwaf.
Shek da ganin miciji ya nufi lungun nan bai san lokacin da wani ƙarfi ya zo masa ba, da mugun gudu ya nufi bishi wani tsalle ya yi sai gashi ya ɗane bishiyar lokaci guda kamar wani biri, wani reshe ya samu ya hau ya zauna ya kama ya riƙe ƙam. Yana a saman nan, Sadiya da zuwa lokacin kawai ta daina kuka tana daga inda take tana ganin iko da ƙudurar da ta sauka a gidanta, micijin kuma yana dawo wa daga lungun sai ya daina gudu yake tafiya a hankali a hankali yana zuwa tsakiyar gidan sai kawai ya yi lifet kamar ya mutu, idanunsa ma a rufe ruf. A hankali Sadiya ta nufi wurinsa cikin sanyin jiki ta sanya hannu ta ɗan taɓa shi amma ko motsi bai yi ba.
“Shikenan ke ma Allah ya yanke miki wahala ɗiyar nan Hassan ya mutu kowa ya huta Husainin kaɗai ma ya isheki” Cewar Inna cikin sanyin murya tana tahowa wajen.
“Inna da ransa fa bai mutu ba da alama gajiya ya yi ko kuma bacci ne ya ɗauke shi.
” Cewar Sadiya tana kallon micijin da tausayawa a gefe ɗaya kuma tana haushi da zafin maganar da Inna ta faɗa na cewar Hassan ya mutu.Taɓe baki Inna ta yi tana wani kallon Hassan ɗin da ke kwance kamar babu rai a tare da shi.
Shek da ke maƙale saman bishiya ya musu ƙuri da ido, duk abin da suje a kan idonsa, ganin dai micijin kwance magashiyan sai ya fara tunanin durƙowa daga sama domin ya gudu. Ƙasa ya kalla daga saman bishiyar wani uban zurfi ya gani daga saman zuwa ƙasa.
“Allah da iko ashe dai wurin haka yake da zurfi amma lokaci guda na haye saman nan ko dan a tsorace nake” Ya faɗa yana jinjina irin namijin ƙoƙarin da ya yi wajen hawa bishiyar.
“Duk da haka dai sai na durƙo na gudu ya faɗa yana seta inda zai faɗo, aikuwa wara Bismillah da ya yi sai ji kake tik ya faɗo, a tsugunne ya faɗo, dan haka ko kallon su Inna da ke wajen micijin bai yi ba da Imran da shi ma yake tsaye ya kama tsantsa a wajen. A 360 Shek ya busawa rigarsa iska.
“Yaka liman zo karɓi yajin gayyata ka kaiwa matarka” Cewar Inna tana dariyar ganin yadda ya sanya gabansa hanyar ƙofar gida a guje ko waiwaye ba ya yi.
“La shakka laisal mushkila ku riƙe abinku” Cewar Shek lokacin da ya je ga ganshi ya buɗe ƙofar gida, shi ne ya ɓuga amsar da ya baiwa Inna.
Ƙo ƙofar bai rufe musu ba yana fita ya rinƙa zabga gudu kamar an biyo shi, mutane a hanya wanda basu san shi ba sai kallon mahaukaci suke masa waɗanda suka san shi kuwa sai kallon ba lafiya ba suke masa, a haka dai ya ƙaraso ƙofar gidansa yana haki. Wani uban bugu ya yiwa ƙofar gidan sai da ƙofar ta bugu da jikin bango, Barira da ke zaune tana tankaɗe garin tuwo jin buga ƙofar da aka yi a bango sai ta tsorata, bata tantance ba sai ganin Shek ta yi ya shigo jallabiya tattare a hannunsa ga hiraminsa ɗaure a ƙugunsa ko takalmi babu a ƙafarsa.
Ta san ba abu bane ƙarami kuma ba wani abu ne me sauƙi zai sa Shek wannan gudun famfalaƙin, tunaninta sai ya bata ko dai wani aka harba ko kuma bomb aka saka a wani wurin, ai tana ganin ya nufi ɗaki da gudu ita ma ta suri robar da take tankaɗe da kuma rariya a ciki dan ta san garin nan shi kaɗai garesu idan ya salwanta sai dai su kwana da yunwa. Tana shigowa falon nasu ta garƙame ƙofa ganin Shek ba ya falon sai ta bishi bedroom ɗin, a can ma sai sa ta sanya mukulli ta kulle ƙofar sannan ta ajiye garin da ke cikin roba ta kalli Shek da ya yi zaman ƴan bori a tsakar ɗaki, wata dariya ce ta ƙwace mata gani yadda farar jallabiyarsa ta jiƙe ga kuma ƙasa a jiki sannan kuma ga tumurin hirami a ƙugunsa sannan bakinsa sai mismis yake. Sai da ta yi dariyarta son ranta sannan ta kalleshi ganin ko kulata bai yi ba ta ce.
“Ya Shak wai duk wannan gudun bomb ɗin ne kamar wanda ke gudu ranar ƙiyama, ashe dai ku ma Malamai kuna tsoron mutuwa?”
Saurin wayancewa ya yi tare da ƙoƙarin seta kansa ya ce.
“Ba haka bane Barira, wato ainihin komai muƙaddari ne amma mutuwa ai dole ce in kin ga ana irin wannan wahala ake gudu bi ma’ana ceton rai kena” Ya faɗa cikin maganar Ustazai.
“Allahu akbar Kabiran, ni wallahi na ɗauka ma wani ne ya ɗora maka bakin bindiga a kan ka” Ta faɗa tana kallonsa.
“To kusan hakan ne, ko ma fiye da haka, wallahi arangama muka yi da zulƙululu”
“Me ye kuma zulƙululu?” Ta tambaya cikin rashin fahimta.
“Miciji” Ya faɗa yana kwashe komai ya faɗa mata. Dariya take tun ƙarfinta har da hawaye.
“Yo Ya Shek ai dama na faɗa maka amma ka ca wai zancenmu ne na mata wai mu mata mun saba gutsuri tsoma da yaɗa jita-jita, yanzu kuma ai idanunka sun gani”
“Ki bari kawai Barira ai yau na yi mugun gamon da zai daɗe yana zaune daram a ƙwalƙwalwata, ni dai ko hanyar gidan Imran na daina bi”
“Kai da abokin ka”
“An bar abotar, ko fitsarin da na yiwa jallabiyar nan ya fi a ƙirga, ita kanta na san sai ta ce Shek da fitsari a jikina kuma, carbina ma a can na barshi, ko dan wa ma yake ta carbi ana ta kai wa yake ta kaya” Ya faɗa yana since ƙullin hiramin ya fitar da takalmansa na dai suka sha dariyarsu, ya yi wanka ya canja kayansa.
A can gidan Imran kuwa Imran yana ganin Sadiya ta ɗauki micijin da sauri ya yi ɗaki dan shi abin ya wuce tunaninsa. Yana shiga bedroom ua nufi wardrobe ɗinsa zai canja kaya, yana buɗewa Mama da ke can ciki ta tsorata tare da maƙurewa a can ciki, Imran da bai lura da ita ba ya miƙa hannu zai ɗakko riga sai ya ɗora hannunsa a kan ƙafar Mama da sauri ta janye ƙafar tana zazzare ido, jin ya taɓa mutum ya miƙa kansa ya leƙo ciki aikuwa suka yi ido biyu da Mama, tuna abin da ya faru tsakaninsu ɗazunya sanya ya ji kunya, Mama ma kunyar ce ta rufe ta, cikin ƴar murya ta ce .
“Ashe Imran ne” Ta faɗa tana jin kunyarsa bayan abin da ya faru ɗazu yanzu kuma ya kamata a cikin lokarsa.
“Mama micijin nan fa ya yi bacci” Ya faɗa, jin hakan sai Mama ta ce.
“To, to, to” Ta faɗa tana zuro ƙafarta ta fito daga drower wata muguwar kunyar Imran na kama ta.
Hajiya da ke ƙasan gado jin Imran ya ce miciji ya yi bacci sai ta ɗan yunƙura za ta tashi amma ta ji ba hali.
“Imran, Imran, Imran” Ta shiga kiran ɗan nata.
Imran jin muryar Hajiya a ƙasan gado cikin sauri ya durƙusa ya kamo hannunta, jin ta maƙale a take ya, ya ɗage katifar ya fito da ita yana mata sannu.
“Kai yau mun ga ta kan mu, ko ma in ce na ga ta kaina, wallahi cinnaku ne a ƙasan gadon nan haka suka rinƙa safa da marwa a jikina babu yadda na iya, cizo kamar wani ƙudan cizo haka nake ji idan suka manne a jikin fatata” Ta faɗa kamar za ta yi kuka, sannun dai Imran ya cigaba da mata, ana haka sai ga Inna ta shigo, ganin Hajiya na karkaɗe jiki tana faɗar zaman uƙubar da ta yi a ƙasan gado sai ta shiga dariya, kowa kallonta yake da mamaki ta ce.
“Yo ni dama kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha kuma sata a gidan ɓarawo wallahi rance ce, ba ni ka yi ta yiwa dariya ba ranar da na ƙarasa kwana a ƙasan gado ba yau na rama a kan uwaka dama ai ɗan kuka shi ke jawa uwarsa jifa” Cewar Inna tana dariya.
“Yau dai an yi kwaɗo, sirika a lokar siriki, hallaw sirika a ƙasan gadon sirika kuma duk jika ne ya haddasa hakan, sannu Amina, sannu Rakiya” Inna ta faɗa tana dariya. Babu wanda ya tanka ta dan su burinsu ma su bar gidan kawai.Haka suka fito suka bar Imran da ke shirin canja kaya, sai da ya canja ya fito daga ɗakin, sannan me ƙunshi ta buɗe kayan wankin da ke jibge a kanta ta fito. Tana fitowa ta zo za ta fita daga ɗakin kamar an ce ta duba mudubi ta hango wani baƙin aljani baƙiƙƙirin da shi ƙirji ta dafe tana ambaton Allah sai da ta yi gaba za ta fice daga ɗakin sai ta gane ashe ita ce, kawai baƙin lallan ya mayar da ita haka. Fuskarta ta tsaya ta ƙarewa kallo sai kawai ta rushe da kuka, a haka ta fito lokacin ƴan matan nan har sun fito daga maɓoyarsu sun tafi, sai Ashrof kaɗai, da kuka ta fito falon kowa yana kallonta Imran takaici ne yasa ya ɗauke kai Inna kuwa dariya kawai take tana cewa.
“Gobe ma ki ƙara yiwa tsoffi haka, ita ma yarinyar nan me ƙananun nono ta tafi wai ita nan mace ce ƙirji babu komai yo irinsu ne idan suka tarki saka rigar nono za ki ga rigar nonon da ban ƙirjin da ban”
Ba abin da ta ce a haka ta sanya mayafinta ta naɗe kamar niƙaf duk da haka ana iya ganinta amma hakan ya ɗan suturta ta dan idan bata rufe ba ta san duk inda ta fita gudunta za a ke.
Imran ɗaki ya koma ya ɗakko kayansa cikin jaka, ya fito. Mama da Ashrof sun tafi dan yau babu damar yin girki ko wani abu da gabaɗaya Ashrof a ruɗe take har lokacin tana zabura. Hajiya da ke yiwa Sadiya sallama ta kalli Imran da ya fito riƙi-riƙi da jaka. Kowa da mamaki yake kallonsa Hajiya ce ta yi ƙarfin halin cewa.
“Ina zaka da kaya haka Imran?”
“Tare za mu tafi”
“Tare za ku tafi da wa?”
“Da ke”
“Ina?”
“Gida mana , kawai tafiya zan yi can in zauna a tsohon ɗakina tun da ga Inna nan ta zo ZAMAN WANKA in ya so ta zauna ma har Sadiya ta yaye yaran” Ya faɗa yana sunkuyar da kai, dan kunyar Sadiya yake ji sun haifi ɗan amma yana so ya gudu, shi kuma har ga Allah so yake ya tafi dan ya gaji da darun gidan kuma dai ya ga alama Hassan ya ƙi dawo wa mutum.
” Ikon Allah wai na kwance ya faɗi, Taɓɗiiii, ashe kuwa za a yita a gidan nan, wane shegen ne zai zauna bayan kai ma uban micijin gudunsa kake, wato ga Inna kuka me daɗin hawa, wacce take so ta bar duniya a kwana kusa sai in zauna in maka ZAMAN WANKA, yo ai abin ma ya wuce ZAMAN WANKA ya koma reno wai har a yaye su in ya so idan micijin ma ya sareni baka da asara iyakarta idan na mutu a ZAMAN MAKOKI ka ce Allah jiƙan Inna, ana karɓar sadaka kana afa shinkafa kana kora lemo, haɗe da kunun zaƙi, to wallahi baka isa ba ko tsinke naka ba zai fita daga gidan nan ba” Cewar Inna da ta tashi ta kama tsantsa ta wani haƙiƙice ta rufe ido tana sababi..
09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
3️🅰️➡️🅱️
Kowa da kallo ya bi Inna ganin yadda ta haƙiƙice tana sababi kamar dai za ta hau Imran da duka.
“To kai Imran ban da abinka ya za a yi kana namiji kuma me gida ka ce za ka fice ka bar gida, ina ka taɓa ji an yi wannan sha’ani?” Hajiya ta faɗa tana kallonsa.
“Dan Allah Inna ki yi haƙuri kin san sha’anin yara sai a hankali amma babu inda zai je ma in sha Allah yana nan” Cewar Hajiya tana kallon Imran da ya tamke fuska ita dai Sadiya bata ce komai ba sannan ko a cikin ranta bata ji haushin Imran ba dan tana ganin kowa ma zai iya yin haka duk da kasancewarsa mahaifi a wajen Hassan bai kamata ya yi hakan ba amma dama ta san Hajiya ba za ta barshi ya bita ba ko ya bar gidan.
“Haba Amina ai duk da ba zan haɗa kaina da Imirana a wajen shekaru ba, to kuwa tabbas ba ƙaramin yaro bane, mutumin da yake da aure garsamemen ƙato da shi har da ƙaruwar ƴaƴa biyu duka maza duk da dai ɗayan miciji mutum ne, wato rabi da rabi, kuma ma ai yana saka ƙafa ya bar gidan nan ni ma jikata zan ɗauka da Husaini na aika miki Hassan ɗin in tafi da ita can wajena, ya za a yi ma ya mata ciki ta haife masa amma saboda yaro na da baiwar da yake sanya kowa a taitayinsa ya ce wani zai bar gidan” Ta faɗa tana galla masa wata hararar.
“Ki yi haƙuri Inna” Cewar Hajiya tana mamakin halin Inna da bata iya sakaya abu ita babu ruwanta da kowa duk abin da ta yi niyyar faɗa, to faɗa take ba ruwanta d me zai je ya zo ko kuma ya wanda aka faɗawa zai ji.
“Kar ma ki kai kan ki da nisa na haƙura ma ba dai ba zai tafi ba ai ni bani da ɓacin rai indai zai zauna ɓacin raina a ce ya tafi ya bar Sadiya da ni da Hassan shi ne kawai” Ta faɗa fuskarta fes da alamun dariya, tana ɗan yi tana kallon Imran da zuwa lokacin ya cika fam babu masakar tsinke, ji yake kamar ya hau Inna da duka amma babu hali, nasiha sosai Hajiya ta musu shi da Sadiya a kansu rungumi ƙaddara Inna tana gefe tana tattaɓe baki haka dai Hajiya ta musu sallama ta kama hanyarta ta tafi.
Inna da ke ƙunshe dariyarta ta kalli Imran da ya tashi ɗauke da jakarsa yana wani harare- harare ya yi cikin ɗaki. Dariya Inna ta kyalkyale da ita ta ce.
“Oh ni Azumi Imirana manyan ƙasa ina ga nan gaba duka za ka fara hawan mutane da shi yo Allah na tuba, wannan haloƙoƙon da kake na menene zama dai daram a gidan nan, kuma kai ma muna nan tare da kai”
Shi dai bai ce mata komai ba ya shige ɗaki wata ƴar dariyar ta yi ta ce
“Ni dai ban san ba harara sai ido ya faɗo” Ta faɗa tana kallon Sadiya da ke zaune kawai tana binta da ido.
“Sannu ƴar jikallena, Halimatus Sadiya, yo dole a miki sannu irin wannan ruwan hawaye, ke baki da aiki sai kuka daga kin ga Hassan ya zama miciji ko kuma ana ta tseran gudun famfalaƙi memakon ke ma ki rattaba naki gudun sai ki zauna kina kuka, ai har idanunki sa ke miki ciwo” Ta faɗa idanunta a kan Sadiya da bata ce komai ba.
“To ai shikenan, tun da ba za ki yi magana ba na lura kin gama ɗauke halayen wancan kurman mijin naki Imirana, duk da dai na kula zuwana gidan nan ya sa ya yi baki amma dai da sauran rina a kaba, bari in tashi in je in sake alwala, yo ɗazu ina alwalar na zo wankin fuska na ga yaran nan sun fito a guje, da faɗa zan fara musu amma ganin Hassan ya fito ya sa ni ma na ce ƙafa me na ci ban baki ba, wallahi haka nan na bar yin alwalar na gudu na samu mafaka a firinji amma yarinyar nan me ƙunshi wacce na yiwa yaɓe da lalle ta garƙameni a firinjin ta kunna shi a haka na daskare kamar ƙanƙara” Ta faɗa kamar ta saki kuka da ta tuno da wahalar da ta sha lokacin da ta tsinci kanta a freezer.
Ganin dai Sadiyar bata sake cewa komai ba sai binta da ido take ya sa ta ce.
“Ni fa wallahi Sa’adiyya da a ce ba ni na haifi ubanki ba da babu dalilin da zai sa in kasa yarda ke mayya bace, ko da kuwa baki ci mutum ba, yo ina dalili ki yi ta kallon mutane ba ƙaƙƙautawa ina ga ma ko ƙiftawa bakya yi” Ta ce tana hararar Sadiya da ta ɗauke kanta daga kallon Innar jin abin da ta ce.
“Oh to bari na tashi da wannan in je in yi abin da zai fishsheni, ana zaune ana darun gudu ba azahar ba la’asar” Ta faɗa tana tashi ta fita waje dan yin alwala. Tana zuwa wurin alwala ta ƙyalƙyale da dariya ganin butar da ta bi ta kanta lokacin da za ta gudu da ta ga Hassan ya fito daga ɗaki.
“Allahu akbar kabiran, Allah sarki ni Azumi na haɗu da gararin rayuwa, kalli yadda na yi ƙwallo da butar nan a gudun ceton rai, garin gudu kaɗan zani na ya faɗi in je in yi tsirara a gaban jama’a a shiga uku, dan ma dai lokacin kowa ta kai ta kai yake kamar a filin ƙiyama, ba lallai su gani ba” Ta faɗa tana ɗaukan murfin butar tare da butar ta zuba wani ruwan ta sake shiga bayi ta fito ta zauna tana yin alwalar.
Imran tun da ya shiga ɗaki yake jin wani ƙululun baƙinciki ya tokare masa ya ƙi gaba ya ƙi baya, takaicin abubuwan da Inna take masa kaɗai ya ishe sa musamman yau da ta balbala masa wuta har da sanya buhu kamar ta samu ganda ko naman kai. Baki ya cije a ransa yana raya sai ya rama abin da ta masa in bata gaji ba shi ma ba zai fasa ba an ringa yi kenan, sai dai ramuwar gayya ta fi ta gayya zafi.Tasowa ya yi domin ya fito ya je ya yi alwala dan bai yi sallar ka’asar ba, dama daga masallacin azahar ya shigo gidan ya tarar da abin da ke faruwa.
Yana zuwa falo ya kalli Sadiya cikin jin tausayinta ya ƙarasa kusa da ita ya kama hannunta cikin taushin murya ya ce.
“Ki yi haƙuri Sadiya komai ya yi farko yana da ƙarshe, duk abubuwan nan da kike gani jarabawa ce akwai ranar da za ta wuce komai ya zama tarihi kamar ba a yi ba” Ya faɗa yana rausayar da kai idanunsa cikin nata.
Hannunta da ya riƙe ta sanya ɗayan hannun da bai riƙe ba ta ɗora a kan hannun nasa da ke riƴe da hannunta, ta ɗan damƙe hannun tana kallon cikin ƙwayar idanunsa, tana jin yadda soyayyarsa ke huda kowane kungu da saƙo na zuciyarta a gefe ɗaya kuma wani tausayinsa ne ya mata dirar mikiyar da har sai da idanunta suka kawo ƙwalla, Allah sarki so, so hana ganin laifi in ji masoya.
“Babu komai masoyina na san komai dama muƙaddari ne amma kai ma ka daina sanya damuwar hakan a ranka kamar yadda ka umarce ni na daina, sheɗan ne ke maka jagora har yake neman nisanta ka da iyalinka”
“Allah sarki Sadiya nagode ƙwarai kuma ina ƙara yiwa Allah godiya ya azurtani da mace ta gari wacce ta san damuwata da kuma farincikina wacce ta san samu na da kuma rashina in sha Allah zan kiyaye tare da ƙoƙarin yaƙi da shaiɗan waje ganin bai cimma burinsa a kaina ba ya samu nasara” Ya faɗa yana sanya hannu ya shafo gefen fuskarta suka sakarwa juna murmushi a lokaci guda kowa ya ji zuciyarsa fes damuwarsa ta wanke, domin kowacce zuciya tana son lallashi da kuma samun jin ƙai daga abokin tarayyarta.
“Ni ma nagode kuma ina alfahri da samunka matsayin mijina kuma uban ƴaƴana” Ta faɗa ita ma tana ɗauke hannun da ta ɗora a kan hannunsa ta shafo fuskarsa kamar yadda ya mata.
“I luv u” Ya faɗa yana mata wani kallo da ita kaɗai ta san ma’anarsa.
“I luv u too” Ta faɗa ita ma tana sakar masa murmushi mai ratsa zuciya.
Haka ya tashi domin zuwa ya yi alwala har ya kai ƙofa ya dawo ya buɗe frige ɗin falon ayaba ya ɗakko guda ɗaya. Ɓarewa ya yi ya cinye Sadiya dai tana kallonsa sai da ya cinye ya fira riƙe da ɓawon a hannunsa yana zuwa kan barandar ƙofar falon ya faki idon Inna ya jefar da ɓawon. Zuwa ya yi zai shige bayin ta kallesa tana ɓoye dariyarta ta ce.
“Imirana na cikin tukunyar wankan jego, an sha zafin wuta” Banza ya mata ya shige bayi, har ta kammla alwalarta ta bar wajen, tana tafiya tana kallon tsakar gidan abubuwan da suka faru yau a tsakar gidan na faɗo mata tana ɗan murmushi, aikuwa tana cire takalmanta ta taka barandar ta sauke ƙafarta a kan ɓawon ayabar da Imran ya jefar, gabaɗaya ta tafi luuuu tana rafka uban salati ƙafar ɗaya ta yi gabas ɗayar ta yi yamma ji kake timmm ta rafku da ƙasa, Imran da ke laɓe yana leƙe ta bayi ta koma cikin yana shan dariya abinsa. Sadiya da gudu ta fito domin ganin me ke faruwa.
“Taimaka min Halima wallahi kamar wanda na yi hatsarin mota, motar ta yi sama da ni haka na ji”
Cikin tausayawa Sadiya ta shiga ƙoƙarin ɗaga Inna, hammatarta ta kama tana ƙoƙarin ɗaga ta.
“Sannu Inna da na ga ba da hammatar kika faɗi ba shi yasa ma na kama nan ɗin sa…
“Haba Sa’adiyya yo a yi zancen ma ba da hammata na faɗi ba, to billahil lazi ko ina na jikina ciwo yake, bakya ganin jikin tsufa ne dama kamar jira jikin yake in faɗi ko ina na jikina sai da ya amsa hatta gashin kaina ban ɗauke ba, har tsakar kaina amsawa yake” Inna ta katse Sadiya daga maganar da take son faɗa.
“Yanzu ina zan kama?”
“Kama ƙuguna daga gefen dama ki ɗaga ni”
“Haba Inna ta ya zan iya ɗaga ki kuma ta ƙugu, ni fa dama taimaka miki zan yi ki tashi amma ai kinsan dai ba zan iya ɗaga ki ba”
“Wato ga buhun gero, ai da uwaki Rakiya ce da tuni kin sunkuce ta kamar kin ɗauki auduga, amma da yake ni ce cewa kike nauyi gareni” Ta faɗa tana sakin kuka.
Imran da ke laɓe daga bayi yana leƙensu sai dariya yake ƙasa-ƙasa ko banza ya rama abin da ta masa.
Haka Sadiya ta yi dibara ta taimaka mata ta shiga da ita falon tana ta sababin wane shegen ne ya jefar da ɓawon ayaba a kan hanya. Sai da Sadiya ta zaunar da ita a kan kujera sannan ta ce.
“Inna ba fa cikin sani aka jefar da ɓawon nan ba, Abban twins ne fa yanzu ya ci ayaba shi ne da zai fita yin alwala ya fita da shi a hannunsa to ina jin bai san ya jefar ba ma, kin san shi dai da tsafta babu abin da zai sa ya jefar da abu a ƙofar falo dan…
“Ni kwa na san shi da tsafta, kuma na san shi da mugunta” Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma ta ce.
“Guda nawa ya ci ayabar?” Inna da tun da Sadiya ta fara magana take kallonta da baki sake tana son gano wani abu ta jefa mata tambayar.
“Kamar ya guda nawa ya ci kuma Inna sai ka ce ayabar ajiya ko ta haram sai an tamabayi mutum nawa ya ci”
“Ke ba na son iskancin wofi ki bani amsar tambayata”
“Guda ɗaya ce fa ya ɗakko ya ci”
“Ɗaya tak?”
“Eh”
“Tabbas Imirana da gangan ya jefar da ɓawon nan dan in taka in faɗi amma kuma da Azumi yake magana indai ni ce mu zuba ɗan halak ka fasa”Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma sai ta ce.
“Allah sarki Imirana kam akwai tsabta, bai san ya jefar ba” Ta faɗa tana sanya hannu ta dafe bayanta tare da yatsina fuska ta ce.
“Bayan nan nawa yadda kika san an yi yaƙi a kansa haka nake ji yana sara min wallahi ko ina ma ciwo yake”
“Bari in ɗakko miki aboniki ki shafa” Cewar Sadiya ta shige bedroom sai gata ta dawo riƙe da abonikin. Haka ta shiga shafawa Inna a ƙafafunta hatta kafaɗunta da wuyanta sai da aka lafta abonikin, tana ta rakin ciwo-ciwo.
“Bani in shafa a kwankwasona da haƙarƙarina” Ta faɗa tana karɓa ta shiga shafawa tana yatsina fuska.
“Sannu Inna”
“Yawwa Halima, ni wallahi wannan ba mini zai yi ba, ku nan ba a siyar da wasai?”
“Inna meye wasai kuma?”
“Ke dalla rufe min baki, yanzu wasan ne baki sani ba, mu a can akwai wani me siyar da maganin hausa, me suna wasai, za ki ji yana talla yana cewa, sai na ji wasai in baka wasai, to da wannan maganin na samu da tuni na ji wasai”
“Gaskiya ni ban ma taɓa jin sunan ba”
Shiru Inna ta yi ita kaɗai ta san me take ji a jikinta.
“Inna ki yi sallar mana”
“Haba Sa’adiyya ke ma tun da kika ga bam tashi ba ai kin san akwai magana ya za a yi ma in ƙi yin sallah da gangan bayan dama na san salloli biyu ne , a kaina ai sai dai Allah gafarta mana” Ta faɗa tana yin dibara ta sakko ƙasa ta dafe hannunta a ƙasa tana durƙushe. Imran kuwa dama tun da ya yi alwala ya fice daga gidan ya tafi masallaci duk da ba jam’i zai samu ba tun da an daɗe da idar da sallar, ransa fari ƙal ya rama abin da Inna ta masa.
“Tsohuwa sai dai ki yi haƙuri kin haɗu da mijin jika ɗan zamani, dan dai dama ke ma ba a barki a baya ba” Ya faɗa yana tafiya ya ƙyalƙyale da dariya.
“Inna ya kika durƙusa kuma?” Sadiya ta tambaya da mamaki.
“Bari ke dai Sa’adiyya kwankwason nan nawa ne nake ji kamar ba a jikina yake ba, wallahi yadda kika san mace tana naƙuda take jin mararta kamar ba tata ba, tsantsarta kamar za ta ɓalle to haka nake ji”
“Me naƙuda kuma Inna?”
“Yo me naƙuda mana, ai wai na miki misali ne da yadda za ki gane, tun da baki daɗe da haihuwa ba na san baki manta yanayin da kika ji ba”
“Allah sarki sannu Inna zai daina in sha Allahu”
“Kayya Sa’adiyya baki ga na tashi daga zaune ba yo mazaunan nawa ne nake jin suna wani mamar-mamar sun ƙi zaunuwa dai dai ko za ki samu abu ki bubbuga mini su ɗan lafa in yi sallar ko da a zaune ne” Ta faɗa cikin murya kamar ta yi kuka.
” Buga mazaune kuma Inna?”
“Ke in ba za ki buga mini ba ƙyale ni, sai ka ce wani abu yo Allah ma tuba ma in ba larura ba mai zai sa in ce ki bubbuga min mazaunai,ai tun da na haifa miki ubanki na gama miki komai” Ta faɗa tana sababi. Ita dai Sadiya bata ce komai ba kuma bata buga mata ba, haka ta gaji da durƙuson da ya lafa mata ta yi sallar a zaune, tana idar wa ganin ta ji dama-dama kuma ta gama shirya abin da za ta yiwa Imran dan gabaɗaya ta gama gano da gangan ya jefar da ɓawon, dan ko bayan da ya dawo daga masallacin da Sadiya ke faɗa masa Innar ta faɗi lokacin yana bayi, dakyar ya iya danne dariyarsa kuma ya mata sannu kuma bai san cewa duk abin da yake Innar tana ankare da shi ba. Yana shigewa ɗaki ta ce.
“Halima tun da na ji dama-dama bari in je in kwalfe ruwan can da muka sha tsunduma ni da mijinki a ciki, in ɗauraye tukunyar in ɗora miki na wankan yamma wuri ma ya ƙure ki yi wankan a wanki Hussaini shi kuma wancan lokacin da ya sawaya ya dawo mutum sai a wankeshi dan wallahi ban iya wankan miciji da hannun nan nawa”
“To Inna”
“Kai ai yau dai an sha bidiri a gidan nan, yo wuta na babbakawa Imirana, ai yana jin ba kanta sai gashi ya fito a guje har yana gwara kansa a murfin tukunyar, ashe dara za ta ci gida, ni ma miciji an biyo ni sai gani ina iyo a cikin ruwan zafi” Ta faɗa tana dariya.
“Allah kyauta” Cewar Sadiya tana danne dariyarta.
“Amin dai wallahi ai na ji zafin ruwan nan, na ɗauka ma wutar za ta tashi, sai Allah ya dube ni bata tashi ba”
“Inna ki bar ɗora ruwan tun da bakya jin daɗi”
“A’a wallahi sai an ɗora so kike jikin ki ya yi tsami kike ciwon jiki, ai wankan jego shi ne zai sa kike jin daɗin jikin ki.
09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
3️
*E* ➡️ *F*
~DARE~
Bayan kowa ya kwanta a makwancinsa kamar kullum, Hassan dai a haka yake bai dawo mutum ba dan haka, kwantar da shi kawai aka yi a gadonsa. Inna da ke ta jiran dare ya tsala ta aikata abin da ta shirya, dan haka bakam ta yi babu wani bacci da take. Bayan ta ga dare ya tsala ta tashi zaune ganin Sadiya tana ta bacci abinta ta taɓe baki ta ce.
“Oh ni Azumi yarinyar nan shegen nauyin bacci gareta kullum bacci kamar wata kasa, ni dai ba ni kika biyo ba, dan ni ina cikin mutane wanda basu da nauyin bacci” Ta faɗa a zuciyarta tana sako ƙafafunta ta sakko daga gadon, a hankali ta nufi falon tana zuwa ta kunna fitilar falon ganin Imran lulluɓe a cikin bargo yana ta zabgar bacci ta taɓe baki tare da jijjiga kai ta yi dariyar ƙeta a ranta ta ce.
“Imirana ba dai ni ka jefarwa ɓawon ayaba ya niƙa ni da ƙasa ba dan mugunta, to zan nuna maka kowa ya ci tuwo d Azumi miya ya sha, in dai Azumi ce an buga an ba mu. KoTasalla ta yi iya yinta ta gaji ta bari, a hankali ta shiga janye bargon da Imran ya rufa da shi sai da ta cire gabaɗaya ta ga har lokacin baccinsa yake bai ma san abin da take yi ba. Ƙwafa ta yi a ranta ta wuce bedroom cikin sanɗa saboda tsabar ƙarfin hali Hassan ta kinkimo a siffar miciji, falon ta dawo, Imran ta kalla da ke sanye da singlet sai dogon wando na bacci, cikin sanɗa ta nufi wurin Imran, ajiye micijin ta yi duk da faɗuwar da gabanta yake amma saboda ƙarfin hali ɓarawo da sallama ta daure tare da danne tsoron da take ji, dan ta yi alƙawarin sai ta aikata abin da ta shirya. Singlet ɗin ta ɗan ɗaga daga ƙasa sai da ta tabbatar ta buɗu ta ɗakko Hassan da ta ajiye a gefe guda ta sanya shi daga ƙasan singlet ɗin Hassan da ke ta bacci ya ɗan motsa sakamakon ɗan jijjigashi da Inna ta yi, tana saka shi cikin singlet ɗin sai ya fara tafiya a hankali sai da ya sanyo kansa ta wuyan singlet ɗin Imran, sai ya kwanta a jikin Imran ɗin.
Inna kuwa ganin komai ya mata yadda take so sai ta yi dariya a ranta ta ce.
“Mu zuba mu gani”
Imran da ke bacci jin sanyi na shigarsa sai ya ɗan motsa kaɗan, ya ɗan takure jikinsa, jin abu manne a ƙirjinsa cikin giyar bacci sai ya miƙa hannayensa ya ƙara rungume abun tare da sakin ajiyar zuciya kallonsa Inna ta yi a ranta ta ce.
“Kudurarre me shegiyar jarabar tsiya duk tunaninsa Sa’adiyya ce ya runguma, da ni kake zancen” Ta faɗa tana ɗaukan bargonsa ta rufesu shi da micijin, a hankali ta kashe fitilar ta lallaɓa ta koma makwancinta.
*IMRAN*
Baccinsa yake cikin kwanciyar hankali, dan da ya ji ɗumi ma lokacin da Inna ta maida masa bargon ta rufa masa sai ya ƙara ƙanƙame micijin ya cigaba da yin baccinsa abinsa. Da yake wajen sha biyu da wani abu ne Inna ta yi masa wannan aiki, wajen ƙarfe haɗu da wani abu na asuba sai ya ɗan yi juyi kaɗan ya miƙa hannu idanunsa a rufe ya ja bargo ya rufe ƙafarsa da ta buɗe. Gefen kan micijin ne a wajen hancinsa dan haka da kan micijin ya dan dunguri hancinsa sai ya ɗauka Sadiyarsa ce a cikin baccin aikuwa ya ƙara ƙaƙumeta tare da ƙara gyarawa hancinsa zama a saitin kan micijin yana cigaba da baccinsa. Ƙaran wayarsa na alerm ɗin da ya sanya shi ne abu na farko da ya farkar da shi daga bacci, dafe micijin ya yi da hannu ɗaya duk zatonsa Sadiya ce dan a bacci -bacci yake ya ma manta cewa Sadiya ta haihu kuma Inna tana ZAMAN WANKA babu ma dalilin da zai sa su kasance shi da Sadiya a katifa ɗaya har ma a bargo ɗaya indai Inna tana nan.
Ɗayan hannun ya miƙa ya lalumo wayarsa da ke neman ɗauki, har lokacin idanunsa a rufe ruf, sai da ya ɗakko wayar ne ya ɗan buɗe idanunsa cikin yatsina fuska ya kalli screen ɗin wayar, alerm ɗin ya kashe yana shirin maida wayar ya ajiye ya tashi sai kawai hasken fuskar wayar ya sauka a kan micijin, da mamaki ya ji hannunsa ɗaya rungume da abu, ƙwaƙwalwarsa ce ta fara kai masa tunanin me Sadiya take yi a jikinsa bayan Inna tana gidan, dan son ta addabi mutane da sababi, idanu ya ware fesss a kan micijin wani uban ihu ya ƙwala ya buɗe bargon yana ƙoƙarin tashi zaune dan gabaɗaya jikinsa ya ɗauki rawa, gabansa sai faɗuwa yake, hannu ya kai yana son yakice micijin daga jikinsa amma me sai ya ji a manne suke da juna a cikin singlet ɗaya wacce dama ta ɗan masa faɗi kuma sai micijin ya ƙara taɓata tare da buɗata duk da hakan dai a ɗame take a jikinsu sun zama kamar tif da taya.
“Hasbunallahu wa ni’imal wakil” Wace ƙarar kwana ce ta sanya wannan tsautsayin kasancewa da ni” Ya faɗa a zuciyarsa wasu hawaye da bai san da su ba suka fara yiwa fuskarsa tsinke. Dakyar ya samu ya tashi zaune yana jin jelar micijin a kan cinyarsa, haka ya tashi yana kiciniyar ɓanɓaresa daga jikinsa amma sanyin da jikinsa ya yi ga kuma karkarwa da kuma tsabar fargabar da yake ciki ya kasa yin haka. Tsaye yake so ya miƙe amma ina hakan ya gagareshi, dan haka kawai sai ya yanke hukuncin ta tafi bedroom neman ɗauki dan bashi da ƙwarin gwiwar da zai iya yin ihu a jiyo shi har a taimaka masa, gashi kuma ya ga da alama ma micijin bacci yake dan haka ba ya so ya tashe shi a samu matsala dan haka sai ya yanke hukuncin tafiya ɗakin ko da, da rarrafe ne. Hannayensa duk biyun ya ajiye a ƙasa yana ɗan lallaɓawa ya saukar da gwiwoyinsa daga kan katifar a haka ya fara rarrafawa micijin na cikin singlet ɗin kamar dama a nan aka halicce shi.
“Yiiiii, wayyo Allah, yau kuma haka na tashi ni Imran” Yake kukan cikin ɗan ƙasa da murya yana tsoron kar kukan nasa ya tashi micijin.
A haka har ya je tsakiyar bedroom ɗin yana ɗan rarrafawa kamar wanda aka cirewa laka, dan ko kaɗan bashi da ƙarfi gwiwar tasa ma idan ya ɗaga ji yake kamar wanda aka mata dabaibayi da igiya.
“Sadiya, Sadiya,Sadiya” Cewar Imran cikin raɗa-raɗa, kamar wanda aka shaƙewa wuyansa. Inna da tun falkawar Imran tana jin yadda yake ta tutumurtu da miciji a cikin singlet, dan hatta shashshekar kukan da yake duk tana jin sa. Bare kuma yanzu da ya zo tsakar ɗakin da suke ji take kamar ta tashi ta taka rawa dan murna saboda kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
Tun yana kiran da bakinsa har ya dawo yana ɗan buga jikin gadon a hankali dan shi ba ya so ko kaɗan ya tashi micijin ya je ya sare shi a samu matsala, hakan ne ma yasa yake lallaɓawa ya tashi Sadiya domin ta kawo masa ɗauki dan ya san ita kaɗai ce za ta taimakeshi. Ganin dai Sadiya da shegen nauyin baccinta ba za ta tashi ba dan har ƙafarta yake ɗan ja amma shiru sai ka ce wata matacciya. A hankali ya lallaɓa ya koma wajen setin da Inna take kwance, dan ya tashe ta, ta taimaka masa duk da ya san karon su da Inna ba daɗi amma yaya ya iya dole ce uwar naƙi za ta sa ya nemi agaji a wurin Inna dan ko kusa bai kawo cewa ita ce ummul aba isin shigar da micijin cikin jikin nasa ba.
“Inna! Inna!! Inna!!!” Ya faɗa yana ɗan ɗaga murya kaɗan dan ji yake tsabar tsoro fitsari na neman kuɓuce masa dan har cikinsa ma murɗawa yake ba ya so kuma a yi abi kunya dan ya san dai matasawar aka ɗauki wani lokaci ba a rabashi da micijin ba to ba kallon fitsari da kashi ba da a ce maza na haihuwa to ya tabbata har haihuwa sai ya yi ko da kuwa hanji ne zai haifa.
Inna kuwa da dariya ke neman kunya tata ta ƙara danne dariyar ta shiga sakin wani munshari kamar wata jakin dawa, ita a dole bacci take, amma kawai Imran lura ne bai yi ba da ace ya lura har cikin Inna zai ga yana loɓawa irin na ƙyaƙyata dariyar nan.
“Innarmu, Innata, Innar Malam, ɗaya tamkar miliyan a wajen Malam ki tashi ki taimake ni kar in mutu in bar iyalina, dan ko micijin bai sare ni na mutu ba to tsabar fargaba za ta sanya zuciyata ta buga in mutu” Ya faɗa cikin kuka yana jijjiga ƙafar Inna.
“Kai duniya , wato wuya in ji tsula, wa ya faɗa maka barno gabas take, yaro ya ga uwar bari, to da wa ya ce maka karo da Azumi abu ne mai kyau, wai Imirana ne ke cewa Innarmu, kai har da Innata ma, wai ni Azumi da ya rainawa hankali da wayo ni ce Innarsa” Ta faɗa a zuciyarta tana dariyar mugunta.
“Wayyo zan yi gawa” Ya faɗa yana sakin kuka a hankali. Wani juya Inna ta ɗan yi ta koma ɗaya ɓangaren tana sakin munshari, so take sai ta gama wana shi sannan za ta tashin, a haka ya cigaba da magiya har dai ta ɗan tashi tana murtsuka ido duk da ba haske a ɗakin amma kuma kana iya hango hasken farin wata ya ɗan shigo ɗakin ga kuma asuba ma da ta kawo ki masallatai sao kiran assalatu ake.
“Waye wai ya dameni da shegen kira kamar wanda na ci bashi ban biya ba” Cewar Inna cikin muryar bacci wai ita ala dole yanzu ta falka daga bacci”
“,Inna jikan ki ne Imran” Ya faɗa cikin sanyin murya yana addu’a da fatan Allah ya ɗora shi a kan Inna ta taimaka masa kar ta ja masa rai.
“Wa ka ce sunan naka, ba Imirana bane?” Ta faɗa dariya na son fito mata.
“Eh Imirana ne” Ya faɗa kamar yadda take faɗa masa dan shi gabaɗaya fatansa kawai su rabu lafiya dan ba zai iya da sabgar Inna ba gwara ya lallaɓata su rabu lafiya.
“Wai menene halan, ciwon ciki ne ya koro ka gabannin assalatun nan?”
“Dan Allah Inna kunna fitila ki ga, wallahi Hassan ne a cikin rigar jikina”
Murmushi Inna ta yi tare da tashi ta sakko ta kunna fitalar aikuwa haske ya gauraye ɗakin.
“Meye wai ka wani surƙusa kamar mai naƙudar da ke yinƙurin haihuwa?” Cewar Inna tana danne dariyarta ganin yadda Imran yake kallonta idanu a gwagwgwale.
“Inna kalli ki ga cikin rigata” Ya faɗa yana daga durƙusan hannayensa a ƙasa haka gwiwoyinsa ma.
Ɗan yatsina fuska ta yi, sannan ta ɗan ranƙafa ta leƙa wai ita a dole bata ga micijin ba daga yadda take a tsaye. Ganin micijin da ta yi sai ta wani taɓe baki tare da sakin wani tsaki da ya matuƙar ɓatawa Imran rai, ta ce.
“Wai dama a kan ɗanka kake ta ƙwala min kira ka katse min baccina na gabannin asuba mai daɗi tsiya? Kana ta rafka kuka kamar an aiko maka cewar Amina ta mutu, wai me yasa kake da ɗan karan raki ne kamar mace”
Wani haushi ne ya turnuƙe Imran amma haka da daure ya ce.
“Wallahi Inna kawai ina tashi daga bacci na ganshi a jikina ban san yadda aka yi ba, ki taimaka ki fitar min shi ko ki taya ni tashin Sadiya ta fitar min da shi dan na tashe ta bata tashi ba”
“To sai me dan ya je wurinka, ina ce dai ita kaɗai Sadiya ke riƙitu da shi kuma dan ya je ya shiga rigarka shi wani abu wataƙila so yake ka karɓeta ma’ana nono yake so ka bashi…
“Nono kuma Inna?” Ya katse Inna da tambaya cikin tsoro
“Nono mana baka ga inda ya shiga ba kawai ka bashi ya tsotsa ka bani shi in kwantar da shi”
“Haba Inna wace magana kike haka wai? Nono kuma sai ka ce wata mace, baki ga ba yau d bai dawo mutum ba ko ita ma uwar tasa bata shayar da shi ba sai ni da ba nono nake da shi ba za ki ce wai na bashi”
“Ya baka da nono ɗin nan, kuma wanda Allah ya halitta maka fa?”
“Inna!!! Wai me yasa kike haka dan Allah ki bar faɗa ma kar ki sa ya kafa min haƙora a ƙirji yana neman nono in bai samu ba ya cije ni in shiga uku”
Wata dariya Inna ta fashe da ita ta ce
“Imirana ni ka sanya wa ɓawon ayaba?”
Wani irin zare ido Imran ya yi jin furucin Inna.
“Ba dai matar nan bace ta sanya min micijin nan ba saboda ƙarfin hali…
“Na ce ba ni ka sanya wa ɓawon ayaba ya kada ni ba??? ” Muryar Inna ta katse masa zancen zucin da yake.
“Inna ni ba da niyya na ajiye ba ban san ma na jefar ba kuma tsautsayi ne ya kawo kika faɗi”
“Ni ban san miciji ma ya je wurinka ba, kawai dai na ga kana buƙatar taimakona shi ne nake faɗa maka ta yaya zan taimaka maka bayan kai ma ka sa na faɗi”
“Dan Allah Inna ki taimaka min”
“To zan taimaka maka amma sai ka yi abin da nake so dan ka san ko a nan Kano ba a aikin banza, idan kuma ka ƙi to dan wannan matar taka mai kamar mesa ba tashi za ta yi ba gwara ma ka min abin da nake so”
“To Inna faɗi” Cewar Imran cikin ƙosawa da maganganunta da ya matsu a raba shi da micijin nan da ya masa ƙabe-ƙabe.
“So nake ka min rawa”
“Rawa kuma Inna?”
“Rawa mana in ba haka ba, ba zan cire maka ba”
“Ni da bani da ƙafa da me zan taka rawar”
“Gurguncewa ka yi ne?”
“A’a amma ba zan iya tsayuwa da ƙafafuna ba saboda gudun matsala” Inna ta fahimci me yake son faɗa dan haka sai ta ƙudurta ko ta ina ya biyo tana da hanyar ɓullewa.
“Ka min rawar a durƙushen nan da kake”
Shiru ya yi sai kuma ya ga mafita yake nema dan haka sai ya shiga rawa daga tsugunnen da yake yana ta rausaya kai. Kallonsa kawai Inna take dariya na cin ta.
“Haba Imirana rawa haka salam -salam babu ko kiɗa”
“Haba Inna da gabannin asubar nan wane irin kiɗa kuma ni da nake so na je na tafi masallaci”
“To jeka masallacin da micijinka ma gani ina ƴan masallacin basu dare sun barka ba, kowa gudu zai ke kamar ya ga fatalwa”
“To ai ban san ya zan yi kiɗan ba”
“Waƙa zan ke maka kana yin rawar”
“To” Ya faɗa kamar ya fashe da kuka
In na faɗa sai kana min amshi, kana dawa kana cewa maliyo”
“To”
“Ɗan maliyo maliyo”
Shiru ya yi bai ce komai ba takaici duk ya cika shi tsohuwar na son kaishi bango.
“Ba za ka yi ba?”
“Maliyo”
“Ya je ina ne”
“Maliyo”
“Ya je ilori”
“Maliyo” Cewar Imran yana amshi yana rawa ransa sai ƙuna yake yana jin kamar ya mammake Inna ga takaicin nauyin baccin Sadiya da ya addabeshi.
“Kake zazzakuɗa wa mana” Cewar Inna da ke ɗan tafi ƙasa-ƙasa.
Ɗuwawu ya shiga zazzakuɗa wa yana yi hawaye na zuba gashi ba ya so micijin ya tashi, amma ya fahimci da gangan Inna fa sa yake rawa wai har da wani zazzakuɗa wa kawai dan ta sanyashi a bala’i.
Yana cikin rawar sai jin inna ya yi ta sauya baitin waƙar.
“Mu kama sana’a mata macen da bata sana’a aura ce, lale-lale maraba da ke zinariya”
Ai kawai Imran da ya lura Inna dan ta yi ta sanya shi rawar ne ba wai za ta rabashi da micijin bane sai kawai ya saki wani kuka mai ƙarfi wanda hakan ya sanya Sadiya tashi ba shiri, ta tashi a firgice jin kuka Imran tana tashi ta yi arba da Inna da ke tsaye kan Imran ta daddage tana tafi da waƙa.
“Ikon Allah yau kuma me yake faruwa wane irin dogon bacci na yi ne da ake wannan bidirin ban sani ba” Ta faɗa a ranta tana saurin sakkowa daga gadon.
*Masu fitar min littafi ku sani haƙƙina ne, ku ma masu karantawa baku biya ba haƙƙina ne, kowa ya san Allah na gafarta zunubai gabaki ɗaya amma ba ya gafarta haƙƙin wani a kan wani! dk mai so ta biyabta karanta 300 kacal*
09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
*I* ➡️ *J*
” Subhanallahi Abban twins lafiya” Cewar Sadiya lokacin da ta sakko idanunta a kan Imran. Kafin Imran da ke kukan zuci da sarari ya yi magana Inna ta yi karaf ta ce.
“Haba Halima yo kya yi maganar lafiya ma kina ganjn mijinki a wannan hali na durƙuso, ƙura’ani ni duk tunani na naƙuda yake ashe wai duk labarin ƙanzan kurege ne mutum a dudduƙe ya zo cewa yake Innarmu, Innata” Cewar Inna tana sakin dariya. Da mamaki Sadiya take kallon wani uban gumi da hawaye ratata a fuskar mijin nata.Ga miciji a cikin singlet ɗinsa sai wani nishi yake fitarwa kamar wanda aka biyo da gudu.
“Ya Allah ni dai ina ganin abubuwan da na kasa gane ko fahimtar inda suka dosa shin wai meye tsakanin Inna da Imran ne?” Sadiya ta jefawa kanta tambayar a zuciyarta tana miƙa hannu za ta fara ƙoƙarin cire masa Hassan ɗin.
“Haba Sa’adiyya wai me yasa kika raina ni ne ya za a yi in yi ta maza in bar baccina dan in taimaki mijinki kina can kina baccin asara, muka ƙayyade zai min rawa da amshi ina masa waƙa amma yanzu ki zo za ki cire masa micijin nan salin alin, so kike ki barni da haƙƙin rawar da ya mini ban cire masa micijin ba ai ni ya kamata na cire masa…
“Sadiya umarni nake baki idan kina son ki shiga aljanna ki cire min micijin nan dan Allah” Imran ya katsewa Inna maganarta dan ya ga jan maganar za take ta yi shi kuma numfashi ma dakyar yake iya yi dab komai yake da faruwa da shi.
“Ke dan Allan can bani wuri ni ɗin da ya rainawa hankali ni zan cire masa, in banda ma fallasa auren bashi ai da tuni ma an yi komai an gama ba tare da kin sani ba, amma saboda girman kai rawanin tsiya irin na Imirana ya ƙi taka rawa da kyau, saboda ya gama ganin makwancina wato ga ƙaramar danga me daɗin tsallaka shi ne yanzu kuma ya ce ki cire masa” Cewar Inna tana ture Sadiya gefe. Sadiya tana shirin magana amma Inna bata, bata dama ba, ta hana ta, hannunta ta kai bayan Imran ta daddage ƙarfinta cike da mugunta ta sanya faratanta ita ala dole singlet ɗin za ta cire tun daga farkon bayansa ta fara karta faratan ta har wuyansa tana ɗago singlet ɗin haɗe da farcen nata, ta kusa gama ɗago singlet ɗin wani uban raɗaɗi ya ratsa Imran na farcen da Inna ta karta masa amma haka ya daure dan burinsa kawai a rabashi da micijin.
Haka ta haɗo da micijin da singlet ɗin ta cire amma ko lokacin da ta zo cirewa daga wajen kunnesa sai da ta haɗa da kunnuwan duka biyu ta murɗe yadda zai ji a jikinsa ba tare d Sadiya ta lura ba, haka dai ya danne har wani ɗan daddaurewa yake.
” Yanzu na san na yi wai mahaukaci ya taka kashi, to Halima sai gareki kuma tun da an cire ai ta faru ta ƙare an yiwa me dami ɗaya sata, har a ce ina nan a bar Imirana cikin damuwa ai idan da kara akuyar gidan sirika ma iya ce da ke dashi ai duk ɗaya ne a wurina ba banbanci” Ta faɗa tana miƙawa Sadiya Hassan da singlet ɗin gabaɗaya.
Wata uwar ajiyar zuciya ya sauke yana jin raɗaɗin bayansa da Inna ta kartawa farce da kuma kunnuwansa suna zafi amma babu yadda zai yi sai dai ya ƙuduri wani abu da ban, sai yanzu ya gama fahimtar cewa babu makawa Inna ce ta kai masa micijin nan.
“Lallai tsuhuwar nan al’amarinta ya girmi tunani na “Ya faɗa a ransa yana mamakin irin ƙarfin halin Inna.
” Yau dai na ga abin da ya turewa buzu naɗi yo banda dalili mai sa a leƙe gindin sirika wai yau ni Imirana ke kira Innata” Ta faɗa tana dariya.
Wani takaici ne ya ziyarci Imran lokaci guda abubuwan da ya sha faɗa cikin gushewar hankali da tsananin tsoro suka rinƙa dawo masa haushin kansa ya rinƙa ji da kuma hashin nauyin baccin Sadiya ai da ta tashi da wuri da bai nemi taimakon Inna ba wanda hakan gashinnan ya zame masa abin gorantawa. Amma dama ya san duk wanda ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa.
“Yo kuma ai sai ka tashi daga tsugunnen ka tafi masallaci tun da dai ka yi abin kunya yau” Cewar Inna.
“Dama tashi zan yi” Cewar Imran yana ji kamar ya kwaɗe Inna.
“Ba niyya ango ya kwana da wando, yo kana durdurƙusar da kai alamun kunya ka kasa tashi za ka ce wai dama tashi za ka yi, ai fa ka sanyawa zuciyarka dangana Imirana faɗan da ya fi ƙarfinka kake midashi wasa sai ka zauna lafiya da mutane, ai zama lafiya ya fi zama ɗan sarki”
“Wai kamar ya Inna” Cewar Sadiya da ta fara fuskantar wani abu kenan dai Inna ce ta haddasa komai.
“Abin da wancan ya ce shi na ce kirarin mai tsoro, wato ke uwar ƴan son miji shi ne kike bin ƙwaƙƙwafi, kawai ki barni da Imirana dan kura ce kaɗai ta san gidan mai babbar sanda” Ta faɗa tana niyyar fita daga ɗakin.
“Sadiya miƙo min riga a drower” Ya faɗa yana jin haushin Inna na ƙara azalzalashi a kan ƙin yin da na sani a kan abubuwam da ya aikata mata a baya da ma wanda zai aikata mata nan gaba, duk da dai ya san ramin ƙarya ƙurarre ne, kuma rana dubu ta ɓarawo ɗaya ce tak ta me kaya.
“Maza miƙo masa rigar ya tafi masallaci kar ya yi saki na dafe, na ga sai wani hararata yake abin da na masa bai gode ba yo Allah na tuba ban da dai abin kirki bai gaji kare ba in ya yi ma dukansa ake duk taimakon da nake yiwa Imirana a gidan nan ba ya gani kawai dan na sa ya min rawa na ce yake ɗan zazzakuɗa mazaunai yana kaɗa kai shi ne laifin da na masa” Cewar Inna tana kallon Imran fuskarta da alamar dariya, wata uwar harara ya doka mata.
“Wai tsohuwar nan ni za ta yiwa kissa, amma ba komai ki dai bi a hanakali kar tura ta kai bango, dan wanda bai ji bari ba zai ji hoho” Ya faɗa a ransa. Sadiya kuwa Hassan ta mayar kan gadonsa ya ɗakkowa Imran rigar dan gabaɗaya kanta ya kulle da abubuwan nan ko kaɗan Inna da Imran babu wanda ya ke tunanin halin da Hassan ke ciki, wai yana cikin halin ne ma har ya zama ana ɗaukansa dan cika wani buri, gashi kullum cikin ka ce suke ta ka gane dalili musamman ma shi Imran da, ko damuwa da bai yi ba da yawan magana amma yanzu sai take jin har magana yake yadawa Inna a wayance ta kasa gane bakin zaren.
Inna dai juyawa ta yi ta fice daga ɗakin ta je ta ɗauro alwala. Ta dawo tana ɗakko abin sallarta daga cikin jakarta sai ga Imran ya fito daga bedroom ɗin.
“Masallacin ne Imirana sauka lafiya” Ta faɗa tana ƙushe dariyarta ganin ya fito sai muzurai yake. Bai tanka mata ba ya cije leɓe ya sanya kai ya fita ya ɗaura alwala ya tafi masallaci dan zuwa lokacin ma har an kusa kaiwa raka’ar farko.
*HAJIYA*
Tun da ta baro gidan Imran bata zame ko ina ba sai gidan wani Malam Isuhu mai almajira ta daɗe tana jin labarinsa to da yake ma babu nisa sosai daga gidanta amma can sama da su yake. Tana zuwa ta tambaya aka ce yana cikin gidan da sallama ta shiga gidan bayan sun gaisa da matan aka faɗa masa ya yi baƙuwa, bayan an mata iso ta nufi ɗakin nasa tare da matarsa uwar gidansa ita ce ta raka ta har turakar Malam ɗin. Ɗakin cike yake da manyan qur’anai da littattafan addini a gefe guda, ga wasu carbuna manya manya da ƙanana hawan hawa. Zaune yake a kan darduma ya sanya gabansa gabas ga wani ƙaton carbi yana ja. Matar da ta rako ta tana shiga ɗakin ita kuma ta koma. Malam kuwa da ke ɗaura rubutu a leda rubutun cikin bokitin fenti babba, wanda ruwa ne kawai aka zuba tawada a ciki sai a ƙulla a leda ana baiwa mutanen da suka bayar da kuɗi a musu rubutu.
Dan haka ba ya rubutun tawafa kawai yake zubawa a ruwa yana ƙullawa jin an ce ana masa sallama shi ne ya rufe bokitin ya ɓoye wanda ya ƙulla ɗin. ya koma ya zauna a darduma ya fara jan carbi yana mismis da baki.
Sai da ya kai ƙarshen carbin Hajiya tana zaune sannan ya juyo gareta ta fara gaishe da shi tana masa ya fama da kuma ƙoƙari da jama’a, nan ya masa komai lafiya.
“Malam dama wani aiki ne nake so ka min a kan iska…
“Ai mun gama sanin me yake tafe da ke, duk na gani cikin mafarki tun jiya na san da zuwanki, dan haka indai ƙwanƙwamai ne babu abin da ya gagaremu ku da su sai dai ku ji ana labari” Ya katse Hajiya daga abin da take son faɗa masa a kan Hassan da take so ta ce ya je ya masa addu’a ko za a dace ya dawo mutum amma kuma shi sai ya nuna ya san komai ya hana ta ta masa bayani.
” To babu komai nawa ne abin sadaka?”
“Ai abin sadaka sai mun je muke faɗa, kuma yau ina da baƙi ba zan samu zuwa ba sai gobe da yamma”
“To babu damuwa, Allah saka fa alkairi”
“Amin” Cewar Hajiya, tana jin daɗi za a yiwa jikan nata magani.
“Ai kar ki damu mu nan fitar da mutsa mutsai ba komai bane indai muka karanta ayoyin qur’ani to tabbas Allah zai amsa”
Sosai ta ji daɗin maganar tashi, sai da za ta tafi ya ce
“Baki faɗa mini gidan ba”
“Yo ai na ɗauka har gidan ma ka sani a mafarki “
“A’a ki faɗa kawai an za a faɗa min gidan sai na falka daga bacci kin ji dalil”
Nan ta shiga masa kwatance daga ƙarshe ma dai sai ta gane ya san gidan Imran ɗin, dan ya faɗa mata wani gida da ke maƙotaka da gidan Imran ɗin dan haka sai ta ce masa maƙota ne da gidan da ya faɗa mata, sai da ta tabbatar ya gane sannan ta mas sallama ta tafi abinta.
” Wa ya ga taɓɗi ai ban da kin ce iska babu abin da na sani game da zuwanki amma yanzu ai na kama ki a hannu” Ya faɗa a zuciyarsa bayan fitar Hajiya yana janyo leda da bokiti ya cigaba da ƙulla maganin, rubutun, yana murnar samun aikin nan, kuma ma ya ce mata sai gobe yau yana da baƙi ne dan kar ta raina shi ta ce ba a kawo masa aiki.
Hajiya haka ta koma gida tana ta farincikin samun mafita dan haka ma sai ta ja bakinta ta yi shiru ko su Imran ba za ta faɗa wa ba sai gobe.
Wajen ƙarfe ɗaya da wani abu Inna tana zaune a ƙasa a falon tana cin abinci dan yau ita ra dafa abincin ma Ashrof bata zo ba, wai kanta na ciwo ko haka ne ko kuma saboda tsoratar da ta yi Allah kaɗai ya sani. Imran da ya ci abinci a bedroom ya fito jin ƙaran wayarsa da take caji a falo.
“Assalamu alaikum barka da rana Hajiya” Ya faɗa lokacin da ya kara wayar a kunnensa.
Amsawa ta yi tana tambayarsa mutanen gidan bayan sun gaisa, nan kuma ta ce.
“Imran na je wajen wani Malami Malam Isuhu zai zo da yamma. Shiru ya yi bai ce komai ba Inna da fa kasa kunne tana iya jiyo maganar da ake daga cikin waya, ba handsfree take ba amma dai volume ɗin a ƙure yake.Shiru ya yi yana son gama jin abin da take so faɗa masa.
“Gwara dai ya zo kam Amina dan yau ma micijin nan a wajen Imirana ya kwana a cikin rigarsa” Hajiya ta jiyo muryar Inna ta cikin waya hakan ne ya ƙara tada mata hankali. Wata harara Imran ɗin ya jefawa Inna da ke gatsina mas gefen hanci, haushi ma ya sanya bai ce komai ba jin Hajiya na faɗa a kan me yasa ya kwana da miciji kuma zuwan Malam Isuhu babu fashi dan haka sai ya zo. Hajiya na gamawa ta kashe wayarta ta bar Imran riƙe da wayar sai muzurai yake ya maida cajinsa ya koma ɗaki ya kwanta yana ta nazari tabbas ficewa zai yi daga gidan dan ba zai zauna a maida masa twins ba.A a zo wani maida masa ɗa miciji bayan Allahn da ya baiwa yaron baiwar zai dawo dashi a duk lokcin da ya so ita kuma mahaifiya ce a wajensa babu yadsa zai yi da ita. Sadiya da ke zaune tana shayar da Husaini ta kalli Hassan da ke kan gadonsa rufe da bargo, tana jin tausayin yaron har cikin ranta.
Imran ko da aka fara kiran sallar la’a sar sai gashi ya fito zai tafi masallaci, ya sunkuya zai ɗauki wayarsa daga caji Inna ta ce.
“Wai ni Imirana wannan uban lemukan robar da ka kawo aka jibge ba za a ɗauka min wanda idan Aminiyata Tsahare ta zo gobe ba zan bata da kuma wanda zan bata saƙo ta kaiwa jama’ar garinmu ƴan uwa da abokan arziƙi, ni kuma in yaso idan na gama ZAMAN WANKA zan tafi sai in tafi musu da namn sunan da zan sanya shi a kitse” Ta faɗa tana kallon Imran da ya ɗago riƙe da wayarsa tsabar mamaki ma ya rasa bakin magana, wai ashe har wata aminiyarta ce za ta zo suna lallai tsohuwar nan da ɗora hau take a gado baki kawai ya taɓe bai ce komai ba ya juya ya fice zai yi alwala.
“Uban shegen mugun halin tsiya, yo Allah na tuba meye a lemon roba ban da tsiya ma abu da bai fi a bani sinƙi biyar (cartoon biyar)ko shida ba in bayar a mini bajinta da shi a ƙaunyen kafin in koma” Ta faɗa tana kallon lemon da aka jibge wasu kan wasu.
“Haba Inna wai ke dai bakya ƙi ko gudun abin magana, yanzu lemon da za a raba na ƴan suna shi ne za a baki har katan biyar kuma ma maimakon ki tambayeni sai kika tambayi Abban twins, sannan Inna har Iya Tsahare kika gayyato”
“Halima wallahi ba na son kinibibi ki fita idona in rufe, kuma ni nan Azumi wallahi ban iya munafurci ba shi yasa kika ga ina tambayar abu kuma abin da yasa na tambayi Imirana na ga dai shi ya siyo ba ke kika siyo ba, in tambayeki in tambayi wofi, kuma nawa sinƙi biyar yake da har za a ce na yi zari, sannan Tsahare kuma kamar ta zo sunan nan ta gama dan takanas ta kano na tura ɗan acaɓa ya faɗa mata na tafi Kano kin haihu ta sameni a nan”
“To shikenan Inna amma ai dai kin ga yadda wurin kwanan ma yake aiki ne a gidan nan amma kika gayyato ta”
“Na shiga aljanna na maƙale saboda na ga wurin zama babu fitowa, yanzu Sa’adiyya ni Azumi da na haifi ubanki kike faɗawa wannan magana wurin kwanan banza da wofi wallahi a kan Tsahare za mu ɓata da kowa saboda ita ce ta gaban goshi kuma sai ta zo ta kwana dan wallahi ban gaji rashin arziƙi ba da zan ruge ido in ce ta koma inda ta fito a ranar da ta zo dan rashin tausayi ta yi doguwar tafiya ta koma a ranar to ba da ni ba gaɗa a hurumi, kwana daram sai dai mijinki ya nemi akurkin kaji ko ma zabbi ke wallahi ko na tattabaru ne sai dai ya je ya kwana in ba haka ba mu haɗu mu uku mu kwana a gadon ni ke da kuma aminiyar tawa, in ba za ki kwana damu ba sai ki je wajen mijinki ku kwana a falo, dama burinsa kenan ya jiki a kusa dashi, ko yau ya ɗauka Hassan ke ce baki ga yadda ya ƙwaƙumeshi ba kamar mayunwacin zakin da ke jin yunwa ya samu abinci kai ai wannan yaro da jaraba yake”
“Inna ya aka yi kika sani ke da ya tasheki a bacci ta yaya kila san ya rungumi Hassan ɗin” Cewar Sadiya tana kallon Inna da mamaki.
Imran kuwa da ya taho zai wuce masallaci bayan ya yi alwala ya jiyo Inna na wannan bayani hakan ya ƙara bashi tabbacin ita ce ta kai masa Hassan kai kawai ya gyaɗa ya sanya kai ya fita abinsa.
Inna kwa yatsina fuska ta yi ta taɓe baki ta sanya hannu ta turo ɗankwalinta gaban goshi tare da kauda kai, babu yadda Sadiya ta iya sai ƙyaleta ta yi.
*Masu fitar min littafi ku sani haƙƙina ne, kuɗin karatu kawai kuka biya, ke ma da kike karantawa baki biya ni ba haƙƙina ne duk ina so ku san da haka!*
09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
*Q* ➡️ *R*
“To Allah raya ya kuma ɗayyaba, ai sai na baku addu’a ma kafin na tafi wacce za a yi taro lafiya a gama lafiya” Cewar Malam yana ƴar dariya.
“Amin ya rabbi, ni kuwa zan tuna maka idan za ka tafi” Cewae Inna a fili a zuciyarta kuma ta ce.
“Tabbas lokacin da za ka tafi ba lallai ka tuna da takalmanka ba ma bare addu’ar da za ka bayar”
“Kar ki tuna min ai ni na ce zan bayar kuma ba sai kin tuna min ba dan ba na mantuwa”
“Ah to in kwa haka ne na yi katsalandan” Inna ta faɗa tana ƴar dariyar wasa.
Sa’adiyya ki zauna a nan ni zan raka su wajen marar lafiyar” Cewar Inna tana ƙoƙarin yin hanyar bedroom.
“Kamar ya Inna cikin ƙuryar ɗakin za ki kai su…
“Ikon Allah wai kina nufin marar lafiyar kuka haɗa ɗaki ɗaya da jaririn nan da aka fiddo? Kenan yana cikin ɗakin nan ba kwa tsoron faruwar wani abu?” Cewar Malam cikin mamaki dan shi ya ɗauka ɗaki aka ware wa marar lafiyar.
” Ah jikin ne dai yau da sauƙi amma ko jiyan nan gidan nan sai da kowa ya nemi mafaka har da masu shiga tukunyar jego, da masu shiga ƙasan gado, kai har ma da masu hawa saman bishiya, dan nan marar lafiyar yake bin kowa a guje” Cewar Inna cikin nuna tausayawa.
“Allahu akbar kin ga abin da ake gudu ko in ce dai ba makami yake ɗauka ba, ai wannan aikin manyan baƙaƙen aljannu ne” Cewar Malam yana kallon fuskar Inna da ya kasa gane kamar dai tana nuna alamar dariya.
“Ka dai bari Malam ai idan abin ya motsa sai dai du’a i”
“Yau kuwa za a yi maganinsu yau bacci zai yi har da munshari su kuma mu fatattake su, su bar jikinsa ba za mu ƙyalesu ba sai mun dangana su da kukar bulukiya, ko ma mu aika su bangon duniya, ke wasu ma har ƙasar sin muke aika su”
“Kai gaskiya gafarta Malam ka iya aiki yo irin wannan aiki ai ko miliyan aka baka ba a faɗi ba”
“Shi ya sa ai raina ya ɓaci da kika musa wato kika nuna na muku tsada in aka haɗa da ƙoƙarin da zan muku ai abin sadakar ba wani mai yawa na a zo a gani ba na faɗa”
“To ba komai ” Cewar Inna tana yin gaba.
“Ai ba da ke za a shiga ba mu kaɗai za mu shiga dan ba ma son kowa ya shiga saboda idan muna dukan aljannu kar a samu mutum” Cewar Malam yana kallon Inna.
Sadiya saurin miƙewa tsaye ta yi jin an ce wai za a yi duka. Wata harara Inna ta doka mata ta ce.
“In ba a nema masa lafiyar ba haka zai yi ta zama”
“Rabu da ita mana a mata bayanin da hankalinta zai kwanta, ba fa shi za a duka ba aljannun za a duka kuma da zarar mun ga sun fita za a dakata da dukan ki kwantar da hankalinki, ina ga ma sai an rufe ƙofa in muka shiga saboda ƙara da kururuwar alajannu kar ma ta yi zaton marar lafiyar ake duka ta zabura ta je ɗakin ko kuma shi ya fito a guje ya je ya ji muku ciwo kun san aljannu da shegen ƙarfin tsiya dan ma dai na taho da Ƙasimu da Habu” Cewar Malam yana kallon almajiransa da suka washe baki jin an ambace su dan suna da ƙarfin danne mai aljannu.
“Koma ki zauna” Cewar Inna tana kallon Sadiya. Komawar kuwa ta yi ta zauna duk da ta san dai tun da ta ga Inna tana ɗan kanne mata ido a ɓoye tabbas akwai ayar tambaya.
“Ƙasimu ku ɗakko kayan aikin maza” Ya faɗa yana gyara zaman rawanin hiraminsa.
Inna ce a kan gaba sai Malam sannan ƴan rakiyarsa, sai da suka gama shigewa cikin ɗakin Inna ta tsaya a jikin mudubi, Malam kuwa ajiye carbunansa ya yi a ƙasa yana cewa.
“Sai ni Malam Isuhu mai maganin duk wani shegen aljani, ban fito ba sai da na shirya gaba salamun baya salamun” Ya faɗa yana wani sunkuyawa ya ɗan naɗe ƙafar wandonsa, su ma sauran tattare hannuwan rigarsu suka yi tare da na ƙafar.
“Ina yake ne?” Cewar Malam yana kallon ɗakin da mamaki ganin bai ga marar lafiyar ba.
“Aifa sai kun yi da gaske dan yana ƙasan gado can yake shigewa ba ya son ma a zo kusa da shi” Cewar Inna tana kallon Malam.
“Allah sarki duk fa ba yin kansa bane, amma komai zai zo ƙarshe yau, jeki waje, inda hali ma rufo mana ƙofar dan wannan aikin ba na wasa bane” Cewar Malam.
“To shikenan bari na je daga wajen a yi aiki lafiya, to kuwa zan rufe muku ƙofar kamar yadda ka buƙata har mukulli ma zan saka” Cewar Inna tana ɗan juyawa da sauri ta fito daga ɗakin.
“Ƙasimu ku taho mu san yadda za mu fito dashi daga ƙasan gadon nan dan da alama aljanun nasa ma kafirai ne tun da basa son mutane” Inna ta tsinkayo muryar Malam lokacin da ta sanya mukulli ta rufe ƙofar.
“Habu ɗauki galan ɗin ruwan addu’ar ɗora shi bisa mudubi kar garin artabu a hankaɗar da shi, gwara in mun samu nasarar fito da shi sai a ɗakko shi idan za a fara ruƙiyyar” Cewar Malam da ke wajen drower yana ƙoƙarin sunkuyawa ya leƙa ƙasan gado.
“Malam kar fa garin janyo shi a ji masa ciwo, gwara a ɗage katifar yadda za a fito dashi salin alin” Cewar ƙasimu cikin girmamawa.
“Eh to kai ma ka kawo shawara gwara a ɗaga katifar” Cewar Malam yana mai fasa leƙa ƙasan gadon. Sai da Ƙasimu da Habu suka fitar da katifar suka jingine ta sannan suk shiga ɗaga filankin gadon, suna cire na ƙarshe sai ganin wani ƙaton miciji suka yi a kan wani lallausan bargo na yara ya fasa kai alamar sara.
Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Malam da almajiransa ai kan ka ce kwabo Malam ya kai bakin ƙofa cikin ruɗewa.
Ƙasimu ma sai gashi yana neman shan gaban Malam, Habu kuwa har bugar kafaɗar Malam ya yi. Amma Malam ya ma manta matsayinsa da yadda suke bashi girma burinsa kawai ya riga kowa fita daga ɗakin. Tsalle ɗaya Hassan ya yi sai gashi a gabansu ya ƙura musu ido gabaɗaya suka jingina a jikin ƙofar duk da wurin ya musu kaɗan amma a haka suka cakuɗa.
“Waye a kusa ne a zo a buɗe ƙofa” Cewar Malam da ya daddage ƙarfinsa kamar yana magana da waɗan da ke ƙofar gida. Inna da ke zaune kan kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ta saki dariyar mugunta ta kalli Sadiya ta ce
“Kin gani Halima ko ai ba mai taɓa miki ɗa da har kina damun kan ki yo Allah na tuba ina suka ga ƙarfin gwiwar taɓa miciji” Ta faɗa tana kallon Sadiya da ta saki baki galala tana kallonta, mamaki take duk tunaninta Inna ta wuce wurin lallai Inna gwana ce ta bugawa a jarida.
“A buɗe Malam mai sittin wata kan wata ne ke magana” Cewar Malam da ya dage ƙarfinsa yana tura ƙofar kamar zai karya ta almajiransa suna taya shi.
“Gafarta Malam har an fitar aljanun? Ka kai shi birnin sin ɗin?” Cewar Inna cikin ɗaga murya yadda za su ji.
Malam na shirin bada amsa miciji ya ƙaraso kusa da su hakan ya sa maganar da Malam ke ƙoƙarin yi ta sarƙe sai zare ido suke shi da almajiransa.
Cikin hanzari ya wani bangaje su Ƙasimu tsalle ɗaya ya yi sai gashi a kan gado, da yake an ɗage katifar sai ya faɗa kan filankin da ba a ɗage ba ji kake ƙumm ya bugu da jikin katako, wani zafi ne ya ratsa kansa da ya bugu ga mazaunansa da suka yi zaman ƴan bori a kan katakon idanu ya runtse ya buɗe a hankali aikuwa ya sauke su a kan Ƙasimu da Habu suna neman wajen mafaka sai zare ido suke ana kallon kallo.
“Wannan an yi gardawan banza wallahi, in ce dai nan kuke danne mai aljannu ƙaton gardi da ƙarfin tuwonku amma kun gagara mana maganin miciji ɗaya maimakon ku damƙeshi in samu ni da nake gaba daku in fita in ya so ku kwa san yadda kuka yi kuka kuɓuto” Cewar Malam yana zare ido cikin takaici da jin haushin almajiran nasa.
Babu wanda ya kula shi bare ya tanka masa dan basu da nutsuwar da za su tuna matsayinsa a wurinsu kowa ta kai ta kai yake kamar a filin ƙiyama. Ganin micijin ya ƙurawa Habu idanu Ƙasimu ya yi wani tsalle ya hau gadon inda Malam yake sai gashi ya faɗa kan Malam ɗin, ji kake gwaraf,ƙasusuwa da kayuwansu sun bugu wuri ɗaya, Malam na shirin yin ihu dan jin ƙaton gardi a kansa sai ya ƙara jin wani uban nauyin da ya fi na farko ashe Habu ne shi ma ya yi wata alkafira ya faɗa kan Ƙasimu da ke kan MALAM gabaɗaya sai suka yi ɗaya a kan ɗaya Malam ne a can ƙasa.
“Ku ɗaga ni mana kun min talibge fa, Malam ne fa Baban Jamila da Jamilu Malaminku ne ko baku shaidani ba idan a ɗimuwa kuke na ganin miciji ku dawo hayyacinku dan zan iya yin addu’a yanzu ku koma alade gabaɗayanku” Cewar Malam dakyar dan ji yake kamar an ɗora mas manyan duwatsu.
“Ka dawo da waccen marar lafiyar da yake a miciji sai mu samu salama gabaɗaya” Cewar Habu cikin kuka dan micijin ya nufo inda suke kuma shi ne daga sama ya san shi micijin zai fara kaiwa hari kafin su.
“Habu, Habu ni kake ƙurewa, wato taƙure zaka mini, har ni kake faɗawa magana ko, dan ka ganni a wani hali to wallahi kar ka kuskura in ɗauki jarbuna na masu dubu-dubu dan wallahi zaka yi da na sanin faɗar hakan” Cewar Malam. Habu kuwa bai ma san me Malam ya ce ba dan lokacin micijin ya fara sulalowa kan gadon dan haka sai kunnuwan Habu suka bada wani dimmm ba ya jin komai. Ganin micijin ya gama hayowa kan gadon ya fasa kai a saitin su Habu ya yi ta maza ya faɗa gefe guda sai gashi jingine jikin katifar da aka jingine ta, ai yana ɗaga Ƙasimu sai shi ma Ƙasimu ya hangi micijin dan dama Habu ya rufe masa har saitin idanunsa, shi ma gefe ya yi cijin zafin nama ya zama na sai Malam kaɗai ya yiwa micijin ƙurii da ido shi ma miciji kallonsa yake. Cikin jajircewa da kuma ƙarfin hali Malam ya yi yaƙi da bakinsa da ke son gagararsa yin magana ya ce
“Dan Allah ku dawo ku danne ni Habu ku min talibgen wallahi ƙwara nauyinku sau dubu da wannan ganin tashin hankalin”
Babu wanda ya ce uffan. Habu ne ya lallaɓa a hankali ya sauka daga gadon shi ma Ƙasimu ya take masa baya suka sauka daga kan gadon su duka sai Malam da miciji. Neman wurin ɓuya kawai suke a ɗakin amma kuma sun kasa samu sai rarraba ido suke.
“Ashe haka duniya take wato ka yiwa mutum rana ya maka dare tun baku san ciwon kan ku ba kuke hannu na amma yau ni kuka kasa taimako na ko Ƙasimu?” Cewar Malam cikin zubar hawaye kamar an kunna famfo.
” Haba mai maganin aljannu kai da kake maganinsu ka fitar da su amma kuma kana neman taimakon almajiranka” Cewar Inna da ke jikin ƙofar ɗakin tana dariyar mugunta.
“Dan Allah matar nan ki buɗe ƙofa na san dai wuyarta ki buɗe ƙofa dole za mu san yadda muka yi muka tsere daga ɗakin, ni kuma na miki alƙawarin za mu raba duk abin da aka bani, dubu hamsin ɗin ce kawai zan baki dubu biyar amma ƙwaryar nono ke ɗaya ni ɗaya, ta zuma ma rabwa za mu yi, ƙwaryar dabino ma raba dai dai za mu babu wani abu da nawa zai fi naki sai kuɗi kawai” Cewar Malam yana ɗaga muryar kamar ai ari baki, ganin micijin ya juya kansa yana kallon su Ƙasimu da suka takure a waje ɗaya sai salati suke.
“Hahahaha na dawo in ji ɗan yawon duniya gaskiya Isuhu ka iya duniyanci yo Allah na tuba ni Azumi wane dare ne jemage bai gani ba ai wallahi sai dai ranar mutuwarsa ce kaɗai za ta masa gagarar ya ganta, har ni za ka zo wa da rainin hankali wato za ka bani jaka ashirin da biyar (5K) To sai ka bari har sai ka yi aikin sannan idan an baka kuɗin sai ka yi wannan in ce dai ga ka nan ga wanda za ka yiwa aikin kana roƙon a rabaka da shi to yaushe za ka masa aiki kuma?”
Wani kuka Malam ya saki mai ƙarfi sai ka ce jiniyar ƴan sanda, ganin miciji ya matso da bakinsa kusa da na sa.
“Ni kike kiran suna na tsirara babu Malam a jiki, sai ka ce wanda… Maganar ce ta katse ganin micijin ya dawo kusa da shi ya miƙa bakinsa kusa da na Malam ɗin
” Kar ka min kiss dan Allah, wallahi kana sa bakinka a nawa na san mutuwa zan yi ga tsoro ga kuma dafin da ke cikin bakinka ka min rai dan Allah ba zan sake zuwa gidan nan ba ni na ɗauka mutum ne mai aljannu ashe abin ya fi ƙarfin Malam Isuhu” Cewar Malam yana zazzare ido.
“Kai ana dara ga dare ya yi” Cewar Inna tana da dariya abinta sai nishaɗi take dama ta san a rina wai an saci zanen mahaukaciya dama tana sane wai karuwa ta taka matar aure, ta san sai an yi artabu dama. Sadiya kuwa kallonta kawai take ita dariya ma Innar ta bata ganin irin abubuwan da take ita kullum Inna ta san ta kan mugunta, sai dai hakan ya yiwa Sadiya daɗi dan ba a cutar mata da ɗa ba.
Habu da Ƙasimu kuwa suna nan a durƙushe a takure wuri ɗaya ganin micijin a wurin Malam sai Habu ya ware jikinsa daga jikin Ƙasimu cikin zafin nama ya tashi tsaye Ƙasimu bai ankara ba sai jin Habu ya yi ya taka gadon bayansa, kafin ya ɗago ka ce me Habu ya kama drower ya ƙanƙameta cikin sakan biyu sai gashi ɗare-ɗare a saman drower, har wani murmushin jin daɗi ne ya kuɓucewa Habu ganin ya sha, dan ya san dai miciji iya ƙasa zai tsaya ba zai hau sama ba kuma ma jikin drower ɗin santsi gareshi miciji ba zai iya hawa ba. Wani haushi ne ya kama Ƙasimu ganin Habu ya tsira ya barshi.
“Habu ya ka min haka tun muna yara muke tare ko bara muka je in baka samu abinci ba nawa nake baka mu ci tare amma yau za ka mini halin ɗan adam yanzu da ka taka ni ka haye ni kan wa kake so in taka in hayo?” Cewar Ƙasimu kukan takaici na fito masa.
“Taka Malam ka hayo shi dama ai ya ci duniyarsa saura mu tun da ya tsofe ko yanzu ya mutu to dai dai ne” Cewar Habu har wani fito ya saki dan daɗi. Ƙasimu saitin Malam ya kalla amma ya ga Malam bai ma san me suke cewa ba bakinsu na kusa da na juna shi da miciji kawai ruwan hawaye kake iya hangowa daga idanun Malam suna rige-rigen sauka, ga majina sai zuba take rawanin nan ya kalle gabas maso yamma bakinsa kuwa kamar an kunna inji sai zuwa yake yana dawo wa. Ganin haka Ƙasimu sai dibara ta faɗo masa dan yana so shi ma ya haye wurin Habu su bar Malam tun da dai hankalin micijin na wurin Malam ƙwara ya haye kafin micijin ya ankara. Da sauri ya tashi ya hau kan mudubi ganin wuri ya yi nisa da drower ya sauka, wani uban tsalle ya yi sai gashi ya ɗane jikin drower a haka ya daddage ya haye suka rungume juna da Habu dan daɗi. A hankali micijin ya ja baya kaɗan ya waiwaya bayansa sai gani ya yi babu kowa a wurin da su Ƙasimu suke. Ja da baya ya fara yi har ya sauka daga kan gadon wata uwar ajiyar zuciya Malam ya sauke yana sanya hannu ya ciro rawanin hiraminsa da hularsa ya yi wurgi da su.
” Haba Isuhu mai sittin wata kan wata ya da cire rawanin ban girma kuma” Cewar Inna da ke tsaye a window tana dariya duk abin da ake a kan idonta, dan gani ta yi tsayuwa a jikin ƙofa ba zai mata yadda take so ba shi yasa ta dawo daga window take gani muraran a kan idonta. Malam kuwa jin muryar Inna a saitin windown da yake kusa da gado ya juya aikuwa suka yi ido huɗu da Inna tana masa dariya, ji ya yi kamar ya shaƙo ta ya shigo da ita ɗakin ita ma ta ɗanɗani bala’in da suke ciki. Amma babu hali ɗauke kansa ya yi daga kallon Inna dan za ta iya sa zuciyarsa ta buga kan miciji ya maida ya ga ya bashi baya ya tsaya cak kuma bai waiwayo ba bai kuma cigaba da tafiya ba. Malam sai ya fara tunanin ina almajiransa suke ganin bai ga ko ɗaya ba. Wani tsoro ne ya ziyarceshi dan duk tunaninsa micijin ne ya haɗiye su a taka ya saki fitsarin wahala dan gabaɗaya ya gama tsurewa cewa saura ahi za a haɗiye Hannu ya miƙa ya taɓo wandonsa jin lema jagaf ya ƙwalalo idanu yana ayyana cewa shi Malam ne uban Jamila da Jamilu da fitsarin wando yau, lallai firgici ya yi firgici.
*Masu fitar min littafi ku daina dan haƙƙina ne masu karantawa ma basu biya ni ba haƙƙina ne kowa ya san Allah na gafarta zunubai baki ɗaya amma baya gafarta haƙƙin wani a kan wani!*
09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
*M* ➡️ *N*
*IMRAN*
Bayan an idar da sallar ya kira Sadiya a waya suka yi magana a kan snacks da zai siyo wanda za a raba a suna, dama saboda ma Hassan sai suka shawarta ba sai an zo gidan an yi wani abin rabo ba dan haka sai ya ce a sayi lemuka kawai in ya so sai a haɗa da snack dan hatta jakar da za a saka kayan duk ya bayar a yi yanzu zai je ya karɓo. Bayan sun gama wayar Inna ta kalli Sadiya ta ce.
“Halima ki tabbtar dai kin ɗauka min kyak (Cake) Ɗin mai yawa da dannat(Donot) Ɗin nan dan wallahi ina so Tsahare ta tafi da kayan sunan nan himili guda dan bana so ta je ƙauyenmu babu kaya mai yawa ƙwara ta je da abin arziƙin da za a daɗe ana batunsa a ƙauyen” Ta faɗa tana tashi ɗauke da kwanukan da ta ci abinci. Da kallo kawai Sadiya ta bita.
Bayan Inna ta wanki Husaini ta shirya shi lokacin Sadiya tana bayi tana wanka Imran kuma bai dawo ba, ƙaran bugun da ake yiwa ƙofar gidan da alama ma ba wai da yatsu ake ƙwanƙwasawa ba, hannu kawai aka jimƙe, ake faman doka ƙofar Inna tana zaune ta yi ɗai-ɗai tana ji amma ko alamar tashi bata yi ba bare a sanya ran za ta buɗe. Hannu ma ta sanya ta ɗakko wani lemo a frige da ta sanya wanda ta fasa ɗaya daga cikin cartoon ɗin da za a raba, buɗewa ta yi tana sha tana lunshe ido.
“Kai duniya budurwar wawa, wallahi daɗi da sanyin lemon nan har tsakar kaina, wayyo Tasalla gaskiya ana yi ba ke ni bana jin ma Tasalla ta taɓa shan lemon roba amma dai zan daure in danne kishi na in baiwa Tsahare robobi guda biyu wanda aka shanye lemon ta kai mata ta tsage ɗan ƙasan robar da ake bari da bai fi cikin cokali ba, ta suɗe in ya so ta ajiye robobin take ganin hoton lemon na jikin robar tana jin haushin ina ma tana da ƴan uwa a birni take shan lemo” Cewar Inna a ranta tana dariyar mugunta, tana ɗaga lemonta tana sha hankali kwance.Wani uban bugu da aka yi wanda ya sanya Inna zabura har lemon ya tafi wa Inna ba shiri har yana biyo wa ta hanci, robar ta ajiye ta tashi a fusace ta yi hanyar ƙofar gidan, tana zuwa ta ce
“Wai uban waye yake wannan bugun kamar wanda yake binmu bashi?”
“Buɗe ƙofa uban Jamila da Jamilu ne Malam Isuhu mai haddar izufi sittin wata kan wata” Ta ji an bata amsa. Shiru ta yi tana son gano inda ta ji wannan sunan kafin ƙwaƙwakwarta ta tuno mata ta sanya hannu ta cire jamlock ɗin a fusace ta buɗe ƙofar Idanunta ne suka sauka a kan wani ƙaton mutum da manyan kaya har da babbar riga ga wani hirami ya naɗa a kansa sai ka ce gammo ga wani carbi irin mai dubun nan guda biyu yana riƙe da su hagu da dama. Sai wasu manyan ƙartin maza guda biyu suna tsaye su ne ke bugun ƙofar shi kuma yana tsaye ya kame sai jan carbunan yake hagu da dama bakinsa yana motsi mismis. Mazan guda biyu ɗaya yana riƙe da manyan dorina guda biyu ɗayan kuma galan irin na mai da wata hula da alama wani abu ne a cikin hular.
“Ikon Allah kun yi ɓatan kai nan ai ba turu bane, ba kuma gidan maza bane(Gidan yari) Cewar Inna tana galla musu harara tare da sanya hannu a hancinta ta fato sauran lemon da ya biyo mata ta hanci dan har lokacin bata daina jin zafinsa a hancinta ba.
“Ke tsohuwa ki iya bakinki ba a faɗa mini magana” Cewar Malamin daga inda yake tsaye ya cigaba da jan carbunan kamar ba shi ne ya yi maganar ba.
“To fa lallai yau ake yinta to buɗe idonka da kyau ka gani Azumi ce ba matarka bace, har ni za ka kalla ka wani ce in iya bakina yo Allah na tuba kai har ka ma isa, yo meye a cikin ido banda ruwa”
“Ki kama bakin ki Iya” Cewar ɗaya daga cikin Mazan nan.
“Oh abin da ya sa kuka riƙo dorinai dan ku daki mutane to indai zan daku ga wurin nan, dan wallahi sai uwaku ta yi da na sanin haihuwarku”
“Ba ta duka ake ba tsohuwa muna jiye miki Malam ya fusata ya maidaki tsuntsuwa” Cewar ɗaya yana kallon Inna da ta yatsina fuska tana kallon Malam ɗin da ke ta jan carbuna, a shelaƙe.
“Ah jemage zai maidani, ko baka ji ba na ce jemage zai maidani, ko ya maidani ɗan tsako in hakan bai masa ba ma zai iya maidani tururuwa”
Gabaɗaya sai suka maida Inna kamar TV kowa kallonta yake cike da mamaki yadda ta haƙiƙice take magana babu tsoro ko ɗarr a tare da ita bayan kuma sun san Malam ɗin yana yiwa mutane kwarjini.
“Ki faɗawa masu gidan Malam Isuhu ne da ya zo cirewa Hassan aljannu wanda Hajiya Amina ta turo” Cewar Malan dan ya ɗan ji shayin Inna ya ga kuma tana neman kunyata shi a gaban almajiransa, manyan almajiransa ne da ya riƙe tun suna yara har suka girma yanzu sun zama manyan garada amma da yake ba wani karatun kirki ake a makarantar ba har yau ba su yi sauka ba, kawai ya ajiyesu in zai je yin ruƙiyya ya tafi da su suke danne masa mai aljanin saboda majiya ƙarfi ne.
Shiru Inna ta yi sai lokacin ta tuna da inda ta ji sunan wato wanda Amina ta faɗawa Imran a waya zai zo. Kallon Malamin ta yi ta ga yadda ba ya barin bakinsa ya huta da mismis ko ambaton Allah yake ko kuma dan a ce yana yi ne shi dai ya sani.Jibgegiyar babbar rigarsa ta bi da kallo sai wani baza ta yake yana wani bada faɗi shi a dole Malami. Wata ƴar dariya ce ta suɓuce mata wacce a ranta ta so yinta amma ta kufce ta fito fili.
“Dariya kuma?” Cewar Malamin yana kallon Inna dan ya ɗauka ta gane shi ba wani Malami bane kawai dai yana son a ce ya yi suna amma ko almajiransa ba wani tsayawa yake a kan su, su yi karatu ba kawai dai ya ajiye su ne dan yawanci duk su ke ci da masa gida idan sun samo abinci. Da kuma aikin ƙarfi da suke duk wajensa nemansu ke ƙarewa.
” Lah dariyar farinciki ce na yi ganin babban Malami ya zo gidan nan, ashe kai ne Malam Isuhun da ake ta labari, yo da na san kai ne ma ai da tuni kuna cikin gidan nan kuna gabatar da aikin” Cewar Inna a fili a ranta kuma ƙwafa ta yi tana fatan Allah kai damo ga harawa.
Wani uban washe haƙoransa da basa samun wanki Malamin ya yi, ya ƙara gyara zaman babbar rigarsa jin Inna ta ce ana labarinsa ai tuni ya ji kansa ya fashe ya masa wani gingirim.
“Haka ne ai duk yankin nan da ni ake ji kuma da ni suke ƙafafa a matsayin babban Malamin da ya yi fice”
“Gaskia dai na ga alama” Ta faɗa a ranta a fili kuma ta ƙara washe baki ta ce.
“Allah ja da ran Malam ai na yi komai cikin rashin sani ne, bari na maka iso dan babban Malami kamar ka ba ya shigo ba tare da an kintsa ba saboda girmama wa” Ta faɗa tana juyawa ta koma cikin gidan, tana zuwa ta ɗauke robar lemonta ta shanye tas, ta ɗauke Husaini ta mayar da shi ɗaki, shi dama Hassan yana ɗakin bata fito da shi falo ba dan ba wanka za a masa ba dan yana siffar miciji. Kallon Hassan ɗin ta yi ta fashe da dariya har da ƙyaƙyatawa ta ce a ranta.
“Yau akwai daru” A fili kuma ta ce.
“Hasanunu bawan Allah kana da baƙon Malami”
Suna nan tsaye sai gata ta dawo ta ce su shigo. Matsawa gefe samarin suka yi Malam ya shiga gaba su kuma suka take masa baya suna wani wasa shi tare da koɗa shi sai ka ce wani basarake. Har falon Inna ta shigar da su Malam ya samu wuri ya zauna a kan kujera haka almajiransa ma suka zauna a ƙasa dan girmamawa. Inna da ke ƙoƙarin zama a kujera almajiran Malam suka ce.
“Iya ba a zama a sama idan Malam yana zaune sai dai ki zauna a ƙasa”
Galala Inna ta saki baki tana bin su da kallon mamaki, shiru ta ɗan yi ta dakata da zama a kujerar ta kallesu ta ce.
“A min afuwa ƴan samari jikokina, ai ban sani ba, kuma ni ma na yi tunanin hakan ai girman Malam ne a masa komai” Cewar Inna tana neman ƙasa ta zauna. Malam Isuhu kuma sai ya fara wani gyara zama yana wani ƙara jan carbunansa bakin nan kwa sai mismis yake.
“A wane ɗakin aka kulle marar lafiyar? Dan yau ƙaryarsu ta ƙare sai mun fitar da kowa daga jikinsa” Cewar Malam yana wani gyaɗa kai.
“Eh gaskiya kam da ana samun irinku ai da aljannu ba za su yarda ma su zauna a jikin mutane ba” Cewar Inna tana ɗan ƙunshe dariyarta.
“Hakane kam ai nan da kika ganni ba na barin aljani sosai muka zuba artabu da su har sai sun gaji sun sakar min ragamar tare da bani haƙuri da kuma yin alƙawarin barin jikin mutum har abada” Cewar Malam yana nannaɗe hannun rigar kamar wanda aka ce za a hau dambe da shi.
“To Allah gafarta Malam yanzu za a fara aikin ne?” Inna ta faɗa cikin ɗan girmamawa.
“Haba tsohuwa ya ba a tsadance ba za ki ce a fara aiki ai sai an tsadance tukunna mun daidaita na ji nawa za a bani”
“To gafarta Malam kai kake yanke abin sadakar da za a baka kenan”
“Eh” Kawai ya ce yana wani ɓata rai ganin Inna ta ce wai yana yanke abin sadaka, ita ma Inna baki ta taɓe ta ce.
“To bari matar gidan ta fito daga bayi sai ku tsadance”
“To” Kawai ya ce ya ɗauki carbunansa wanda ya ajiye lokacin da zai naɗe hannun riga ya cigaba da laziminsa.
Suna nan zaune sai ga Sadiya ta fito daga wanka da sallama ta shigo da yake ma ta shiga da hijab wanka sai ta sanyo abinta gaishe da Malam ɗin ta yi sauran samarin suka gaishe ta, haka kawai ta ji haushin ganin su musamman da ta ga uwar dorinan da suka zo da su, ban da sirikarta ce ta turo Malamin nan da babu wanda ya isa ya shigo mata gida da sunan wani abu.
Ɗaki ta shiga ta shafa mai ta sanya kaya ta ɗoro hijab ta fito da yake Inna ta ce ita ake jira falon ta dawo tana ƙoƙarin zama a kan kujera Inna ta dakatar da ita tana nuna mata cewa Malam ni kaɗai ya kamata ya zauna a sama. Mamaki duk ya hana Sadiya cewa komai ita abin da ya fi bata mamaki ma yadda Inna ta yarda ta zauna a ƙasa kuma take wani kaffa-kaffa da su tana wani sanyaya murya sai wani baiwa Malam ɗin girma take.
” Wato jiranki dama muke tun da me gidan naki baya nan za mu ƙididdige abin sadakar da za a bayar na aikin fidda aljanin”
Wani zaro idanu Sadiya ta yi jin wai ya ce za a fitar da aljani gabaɗaya ta diririce amma kuma Inna ta mata alama da kar ta furta komai kan hakan babu yadda ta iya ta yi shiru da bakinta.
“Wato za a bada dubu hamsin sannan ƙwaryar nono mayan manya guda biyu, da ƙwaryar zuma ɗaya sai kuma ƙwaryar dabino dukansu manya” Cewar Malam yana wani gyara zama. Daga Inna har Sadiya sa kallon mamaki suka bishi, Inna ce ta yi karaf ta ce.
“Haba Malam sai ka ce wanda za ka ɗauki aljanin da hannu ka fitar dashi, in ce dai addu’a za ka yi ya fita kawai to wannan kayan ko aljanin ne zai tafi da su wato toshiyar baki za ka bashi” Cewar Inna tana kallonsa.
Wani irin haɗe fuska Malam ya yi ya fara wani zazzare ido cikin kaushin murya ya ce
“Babu wanda zai muku wannan aikin in ba ni ba ko da kun samu wanda zai muku to ba zai muku aiki kamar ni ba, ko da an fitar da aljannun to za su dawo ne”
“Ikon Allah to wallahi da sake dubu hamsin fa ga ƙwaraken nono da na zuma kai wai har da dabino, yo ai ka manta ka ce da manyan zabbi riƙaƙƙu guda bakwai” Inna ta faɗa ita ma tana ɓata ran.
“Idan baku da kuɗin mu za mu tafi”
“Yo Allah na tuba ku fi ruwa gudu mana, indai kuɗin nan da ƙwaraken abubuwan nan za a bayar wallahi ƙwara mijina Malam ya zo ya yi aikin a bashi kuɗin ni ma in san na mori wani abu nono da zumar kuwa da dabinon ma tsakurawa Tasalla a farar leda ladan ganin ido mu ajiye muna cin kayanmu, da dai a baka kai kaɗai da ranka ni ma ai matar Malam ce kai ni da kaina ma sai in yi aikin”
Wata uwar harara ya jefawa Inna ya ce
“Babu mai ja dani sai wawa, dan duk mai hankali ba zai ja da Malam Isuhu ba dan hukuncin Malam ba ya yin kyau” Ya faɗa yana kallonsu.
“Yo Allah na tuba ni zaka faɗawa haka? To kalleni da kyau fara nake ba baƙa nake ba ruwan sama ne ya wanke ni ruwan datti ya ɓata ni da zaman ƙauye ne ya mulke ni, Allah na tuba me zaka min wallahi ni Azumi matar Malam na sha tabara na sha lahaula”
“Allah gafarta Malam a bar aikin kawai” Cewar Sadiya cikin sanyin murya dan dama ita bata son wani aiki kawai an tashi an ɗakko wani Malami tausayinka sa sauƙi har da wasu uban dorinai ko wa ma za a duka da dorinan.
“Gidanku Sa’adiyya babu mai fasa aiki Malam indai aikin ka ya yi to za a baka duk kan abin da ka buƙata” Cewar Inna da ta danne fushinta tana ɗan murmushi.
Shi ma murmushin ya yi ya ce
“Yawwa ko ku fa ai duka abin da na lissafa haƙƙina ne a bani dan Allah kaɗai ya san artabun da za a yi da mu da su”
“Babu komai ai komai ma aka bada ba faɗuwa aka yi ba” Cewar Inna cikin sanyin murya. Sosai Malam ya ji daɗin maganar Inna yana wani jin kamar ya tashi ya taka rawa dan murna dan tun da yake ko aikin dubu uku bai taɓa yi ba amma gashi zai yi na dubu hamsin har da wasu kaya a ka.
“A kaimu ɗakin mu fara aikin” Ya faɗa yana gyarawa carbinsa ruƙo a hannunsa.
“To Malam bari ina zuwa sai na muku iso” Cewar Inna ta tashi Sadiya kwa da kallo ta bita dan ta san dai ba a ƙarƙewa ƙalaw da Inna. Tana shiga bedroom ɗin sai gata ta ɗakko Husaini da gadonsa ta kawo shi falon.
“Ikon Allah haihuwa ka yi a gidan ma kenan?” Cewar Malam yana kallon Husaini.
“To kenan Hajiya bata masa bayani ba ko me ?” Cewar Sadiya a zuciyarta.
“Eh haihuwa aka yi har gobe ma suna ” Cewar Inna a fili tana ƴar dariya. Azuciyarta kuma ta ce da alama dai Amina babu abinda ta sanar maka”
*Masu fitar min da littafi ku sani haƙƙina ne, kuɗin karatu kawai kika biya, ke ma da kike karantawa haƙƙina ne tun da baki biya ni ba ina so ku san da haka!*
09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
4️⃣1️⃣ ➡️ 4️⃣2️⃣
“Gasu can a saman loka” Cewar Inna da ta fahimci mai Malam ke tunani. Idanu ya ɗaga sama aikuwa ya hango almajiran nasa zaune a kan drower, wani haushi ne ya kama shi ashe dama za su iya cin amanarsa cikin ɗan ɗaga murya tare da yin ƙasa da ita dan kar micijin ya ankara da shi ya ce.
“Yanzu Habu kai da Ƙasimu a maimakon sai kun fara kinkimata kun ɗorani sannan ku samu ku hau shi ne kuka ɗare kuka barni gani a ƙasa daga ni sai micijin ga wadona jargaf da ruwan da na zauna a kai” Ya faɗa kansa a sama yana kallonsu.
“Ruwan da ka zauna a kai ko kuwa fitsarin da ka jabga a jiki, ai fa haka za ka tashi yaraf-yaraf da ruwan fitsarinka ka haye sama in ba haka ba lahira ta yi baƙo yanzun nan micijin nan yana juyowa sai dai wani ba kai ba” Ya tsinkayi Inna ta window tana faɗa. Cikin hanzari ya tashi ya fito daga cikin katakwayen fitsarin nan sai tsiyayowa yake daga jikinsa, ga kunya da ta kama shi da Inna ta faɗa fitsari ya yi almajiransa na ji, taga-taga ya yi zai faɗi amma haka ya daure ya taka katakon gadon ya fara ƙoƙarin hawa.
Amma santsin jikin drower da kuma kemar futsarin ƙafafunsa suka taru suka hana shi hawa lokar. Micijin da ya hango Malam kawai sai ya nufi wurin Malam.
“Gashi nan ya taho” Cewar Inna tana dariya ai Malam jin haka ya sa ya waiwayo ƙasa aikuwa ya ga micijin ya nufo shi gadan-gadan wani tsalle da ya doka sai ga hannayensa sun isa saman drower amma shi bai hau ba.
“Kai Ƙasimu matsa gefe ɗaya mana in samu wurin zama” Cewar Malam yana nishi dan tsantsi sai neman dawo dashi ƙasa yake amma saboda ƙarfin hali da gudun ceton rai ya sanya ƙarfinsa ya riƙe gam.
“Haba Malam kai kaɗai ma fa sai ka cinye saman lokar nan idan ka hayo, baka ganin yadda kake mu ma wurin ya mana kaɗan” Cewar Ƙasimu yana wani ɓata rai.
“Lallai yaron nan to wallahi Allah sai na hayo, Allah wadaran naka ya lalace, ban da ma yau da gobe mai sa a mari amarya, kai baka san ma an ce Malamai magada annabawa bane ina Malaminka amma kake ƙoƙarin ƙin taimakona”
Banza suka masa kuma basu matsa masa ba.
” Gashi naaaaaaan” Cewar Inna har da jan na ɗin, Malam bai samu damar waiwayo wa ba dan ɗazu ma da ta ce gashi nan ya ɗau ƙarya ne amma yana dubawa ya hango shi dan haka yanzu ko waigawar ma bai yi ba ya dafe lokar da hannu ɗaya yasa ɗaya hannun ya kamo ƙafar Habu ya fisga da ƙarfi ya miƙa bakinsa cinyar Ƙasimu ya gantsara masa wani uban cizo da ya sanya suka manne a wuri ɗaya suka bashi wajen.
Haka ya yi saurin ɗanewa ya samu ya zauna a saman drower yana aika musu mugun kallo kamar zai hau su da duka amma ba hali, saboda yanayin da suke ciki. Habu kuwa cinyarsa ya dafe da hannu saboda zafin cizon da Malam ɗin ya masa.
“Ku dai shirya dan na san tsugunne bata ƙare ba” Cewar Inna tana dariya har da yiwa Malam gwalo da ke harararta.
“Muguwa to a bakin ki ta Allah ba taki ba dan na san mun masa nisa sai dai ya tada kai ya yi kallo” Cewar Malam yana ɗan leƙo ƙasa aikuwa ya hango micijin ya cake kansa a ƙasa ya ɗaga jelarsa sama yana wulwulawa.
“Allah ƙadiran, wai kuwa marar lafiyar nan haka aljannu ke maidashi miciji dama kuke rayuwa da shi a gidan nan bakwa tsoron ya zama ajalinku?” Cewar Malam har lokacin yana kallon micijin.
“Ba fa marar lafiya bane ba me aljannu bane, jariri ne mahaɗin wanda ka gani ɗazu ka tambaya haihuwa aka yi to shi ne yake sawaya ya koma haka” Cewar Inna.
“Jariri? ” Cewar Malam yana zare ido.
“Rass kuwa ” Cewar Inna.
“Amma shi ne ba a sanar da ni komai ba aka bani komai a rufe aka barni na kawo kaina ” Cewar Malam a fili a zuciyarsa kuma ya ce.
“Shikenan garin yin zamba cikin aminci na cuci kaina matar nan jiya tana ta so ta min bayani amma saboda kar ta ga kasawata a ɓangaren malunta na ce na san komai”
Inna kuwa baki ta taɓe bata ce komai ba Malam kafin ya gama tunani sai ganin micijin ya yi ya taso wani shuuuuu ya iyo sama wajensu kafin ka ce me ya ɗare fanka, sai gashi a kan ɗaya daga cikin abubuwan fanka guda ukun nan yana reto da yake fankar a kashe take.
Malam da almajiransa sai suka fara cakuɗa waje ɗaya gashi kuma wurin ba wani faɗi gareshi ba sai suke neman faɗowa, gabaɗaya micijin ya naɗe jelarsa a jikin fankar sai ya miƙa kansa waje su Malam yana kallonsu su duka a kiɗeme suje basu dawo daga mamakin yadda aka yi ya taso sama ba, shi ba iska ba, sannan gashi ya naɗe jikin fanka wai kuma a hakan an ce musu jariri ne.
“Wayyo yau mun kawo kan mu gidan mutuwa, ni dama ban zama Malami ba bare a ɗakoo ni ruƙiyyar aljannu yau gashi na ga ta kaina sai dai addu’a da fatan Allah ya tsallakar da ni” Cewar Malam yana rushewa da wani kuka.
“Haba mai sittin wata kan wata kai ne ke da na sanin zama Malamin ma baki ɗaya haba kai da ke taimakon mutane kana cire musu aljannu ka tura su bangon duniya ko birnin sin” Cewar Inna tana dariya. Banza Malam ya mata dan ba ra ita yake ba ga kuka almajiransa ya cika masa kunne.
Inna kuwa zuwa ta yi ta ɗakko wani dogon icce ta dawo windown ta tsaya sai da ta ga Malam ya juyar da kansa can baya hango ta sai ta sanya iccen ta cikin windown ta miƙa har sai da ta kai iccen wajen wuyan Malam ta zungura iccen ya dungurewa kan Malam ta kuma caka masa a wuya, da sauri ta janye iccen ba tare da Malam ya gani ba.
Wani uban ihu da Malam ya saki duk ya kiɗime ya gigice sai wata karkaɗa kai yake da sauri da sauri yana sanya hannu yana dukan wuyansa ya ce.
“Shikenan kuma yau aljannu za su yi yaƙi a ɗakin nan, dan sun fara caka mini farcensu a wuyan da kaina sun ƙi bayyana yau kuma sai yadda hali ya yi ni da almajiraina” Ya faɗa yana ɓare baki kamar wani ƙaramin yaro, Inna kuwa tsabar dariya ta kasa furta komai har sai da ta tsagaita da dariyar sannan ta ce
“Ka cewa aljannun su miƙo maka dorinarka da galan ɗin ruwan addu’ar da kuka zo da shi da kuma waccen hular ba kai bane mai fitar da su ai sai ku shiga fafatawa”
“Rufa min asiri dan Allah wallahi ba dai ni ba, ina ni ina yaƙi da iyayena”Cewar Malam yana kuka har lokacin.
“Iyayenka kuma aljannun ne iyayenka?” Inna ta tambaya cike da mamaki.
“Au wallahi suɓutar baki na yi, ku yi haƙuri mutanen ɓoye, yo abinka da su ba ganinsu ba ake yi” Cewar Malam yana wani waige-waige dan kar aljannun su fara masa hukunci tun ba a je ko ina ba.
Ganin miciji ya daina kai kaisa wajen su Habu ya miƙo wajen Malam tuni ya manta da batun aljannu wani irin haɗiye kukan da yake ya yi yana dannewa dan kar ya yi kukan, kallon kallo ake shi da micijin Malam ji yake kamar ya ɓace ɓat ko kuma ya suma dan ya daina ganin wannan micijin a kusa da shi in yaso idan micijin ya tafi sai ya farfaɗo. Ahankali micijin ya ɗauke kansa daga kusa da Malam ya koma da shi jikin fanka ya shiga warware jekar daga naɗewar sai da ya gama idanun Malam da su Ƙasimu sun zazzaro su har sai da suka ji jijiyoyin idanun sun ɗame duka wato babu yadda ma za a yi su ƙarawa idanun nasu fitowa saboda sun gama fitar d su har ƙarshe. Kafin meye wannan micijin ya yi wani tsalle sai gashi a tsakaninsu, dama Habu da Ƙasimu a jere suke sai Malam daga gefe, a tsakanin Ƙasimu da Malam micijin ya sauka sai Ƙasimu da Habu suka haɗe a wuri ɗaya Malam ya kasance warewa, shi kaɗai a gefe idanu ma Malam ya runtse saboda yadda zuciyarsa ke buga masa da mugun ƙarfi kamar za ta faso ƙirjinsa ta fito. A take micijin ya shiga juyi kamar mai rawa yake kawai, Inna kuwa sai dariya take cikinta har ciwo ta ji yana mata dan ta daɗe bata yi dariya haka ba, ko sararawa bata yi.
Wani uban tsalle Habu da Ƙasimu suka yi sai gasu sun diro a tsakar ɗakin sun bar Malam shi kaɗai a sama.
“Kash lallai in ba mutuwa to akwai tsofa, yau na ga ranar samartaka, in ba dan tsufa ba, ina za a barni a kan lokar nan, da lokacin samartaka ta ne ai da na riga kowa dirowa” Cewar Malam yana kallon micijin fuska shaɓe -shaɓe kamar dai ba shi ne Malam mai sittin wata kan wata ba.
“Yanzu ma lokci bai ƙure maka ba ka diro in ya so in ka karkarye sai a tattara ƙasusuwan naka a watsar” Cewar Inna da har lokacin bata bar masa dariya ba. Malam yana shirin bata amsa sai gani ya yi micijin ya ɗan tashi sama kaɗan sai da ya je saman kansa ya tsaya , Malam ba ɗaga kai ya yi ba idanunsa ne suke kallon saman kawai lumfashinsa ma ya tsaya cak, ko idanunsa ba ya so ya ƙifta tsabar tsoro da kaɗuwar da ya yi.
“Suma ka yi ko mutuwa ka yi, nanga ka kafe idanun naka a sama?” Cewar Inna sa ke kallon idanun Malam kafe a kan micijin. Malam dai babu bakin magana kawai kallon yadda micijin ke tsaye a kan iska ya miƙe duka tsawonsa.
Kafin Malam ya ankara kawai sai jin micijin nan ya yi a wuyansa gabaɗaya ya masa ƙawanya ya nannaɗe sai da micijin ya gama naɗe jikinsa tsaf a jikin Malam sai kuma ya kwallaso kansa ya dawo da shi saitin fuskar Malam ɗin ya zamana sun yi ido cikin ido. Malam bai san lokacin da ya saki numfashinsa ba wanda ya riƙe, ya maido da idanunsa daga kallon sama zuwa kallon fuskar micijin.
Irin halin da Malam ya tsinci kansa a ciki abun ba a magana shi kansa ba zai iya misaltawa ba ya san dai yana cikin gagarumar matsala da tashin hankali. Bakinsa yake so ya buɗe ko Allah zai sa ya iya tuno wata aya daga cikin qurani ya karanta ko kuma wata addu’a daga cikin addu’o i ya karanta dan neman ceton Allah maɗaukaki dan ya san yanzu shi kaɗai ne zai iya kawo masa ɗauki dan almajiransa ma sun juya masa baya, amma gabaɗaya sai ya ji bakin nasa ya masa nauyi ya kasa furta ko da kalma ɗaya ce. Cikin dddagewa ya fara iya motsa laɓɓansa suka fara ɗan motsawa kaɗan amma ba komai yake cewa ya, da ya fara ƙoƙarin maganar ma sai ya ji babu wani sauti da ke fitowa daga bakinsa. Abin da kawai ya sani yana iya jiyo saukar hawayensa daga idanunsa tamkar wani ne ya cika buta da ruwa yake kwararo masa a fuska haka yake jin zubar hawayensa da gudu ko ƙaƙƙautawa babu.
Haka dai ya rinƙa yaƙi da bakinsa dan karanto addu’a amma ina bakin Malam dai ya yi mirsisi tusar ango, babu alamar ma zai bashi wata dama da zai furta komai a fili bare kuma a zuciyarsa, zuciyar da tun da micijin ya naɗe wuyansa ya ji ta doka da uban ƙarfi har zuwa lokacin bata tsagaita ba da bugawa bare ta bashi wata dama ko ta samu natsuwar da za a yi addu’a a zuciyar.
“Ɗiɗiiiiit, jiiiiiin” Cewar Malam dan komai ya kwance masa shi yasa ya fara hourn ɗin mota. Ƙasimu da Habu duk da halin sa suke ciko sai da suka fashe da dariya.
“Minjaye” Cewar Inna da ƙarfi dariya na cin ta dan ta lura addu’ar ma ta gagara a wajen Malam, Malam kuwa da ke cikin halin neman taimako jin abin da Inna ta faɗa bai tsaya wata-wata ba ko tunanin me Innar ta faɗa na sai jin bakinsa ya yi kamar wanda aka yiwa dabaibayi a bakin aka kunce, haka ya ji, saurin fisgo maganar ya fara faɗar abin da Inna ta faɗa dan sai ya ji tamkar ta sanya shi a hanya ne ta sama masa mafita. A take ya fara biya abin da ta faɗa.
“Minjaye, mi’ara, ba ta ɗauri ba, baba kenan” Cewar Malam yana kuka yana fitar da maganar kamar wani ya masa dole. Tun da ya faɗa yake ta faman maimaitawa ko tsayawa ba ya yi Inna kuwa kamar ta samu Tv haka ta maida Malam babu abin da ke bata dariya iron yadda ruwan hawayensa ke kai komo, a fuskarsa kamar wanda ya wanke fuskar, gabaɗaya hankalinsa a tashe yake da yadda micijin yake har lokacin nannaɗe a jikin wuyansa kansa kuma a wajen fuskarsa.
“Wa maa ƙadarullaha haƙƙa ƙadrihi” Cewar Habu dariya na cinsa ai kuwa Malam ya kama ayar gagam ya riƙe sai maimaitawa yake yana kuka.
Dan a take ya saki waccan jiniyar motar da yake yi ya kama wacce Habu ya faɗa masa. Sai da ya maimaita kusan sau hamsin ko dakatawa ba ya yi sannan a take ya tuno da wani karantun ya fara.
“Wallaili iza yagshe, wannahari iza ta jalle, wama kalaƙazzakara wal unsee, inna sa’ayakum lashatte,wa ammaa man a’aɗawattaƙe” Haka ya rinƙa janyo ayoyin yana kuka, amma daga ya je iya ayar da ya karanta sai ya dawo farko ya kasa ƙarasa surar har zuwa ƙarshe. Yana cikin yi sai Ƙasimu ya ƙara ɗora shi a kan wata surar.
“Wadduhe”
“Wallaili iza saje, ma wadda aka rabbuka wama ƙale” Cewar Malam cikin sauri-sauri dan duk wanda ya ji ya janyo masa aya sai ya saki wacce yake karantowa ya kama wadda aka karanto ɗin dan shi kawai so yake ya kamo ayar da za ta masa sha yanzu magani yanzu. Su Ƙasimu da Habu da kuma Inna da suka shagala da masa dariya ya yi dibara ya sauke idanunsa ƙasa ya hangi yadda suke dariya wani haushi ne ya turnuƙeshi ji yake da zai iya sai ya fita ya shaƙo Inna ta ƙarfin tsiya ya shigo da ita ɗakin ya sanya musu micijin a wuyansu ita da su Ƙasimun su ji yadda ya ji.
“Allahu, Arrahmanu, Arrahimu, Almaliku Alqudusu Assalmu” Malam da ya runtse idanunsa da ƙarfi dan ya daina ganin takaicin abin da almajiransa da Inna ke masa da kuma ganin fuskar micijin a kusa da tashi ya kamu sunayen Allah yake karantowa. Idanunsa na rufe ya fara jin riƙon da aka yiwa wuyansa ya sassautu, a hankali ya ɗan ƙyalla ido ɗaya ya buɗe aikuwa sai ya ga babu kan micijin a kusa da fuskarsa kawai sai ya buɗe ɗaya idon ma a take ya fara gani ashe micijin ne ya shiga warware jikinsa daga wuyansa, daɗi ne ya ziyarci zuciyar Malam yana ganin micijin har ya bar jikinsa ya yi wani uban tashi ya sauka daga kan drower ya je ƙasa wurinsu Ƙasimu ya nufa da ke yiwa Malam dariya ko lura basu yi da micijin ba sai ji suka yi ya nannaɗe wuyansu lokaci guda su biyun ya haɗa wuyansu ya kanannaɗe su.
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
3️4️⃣3️⃣➡️4️⃣4️⃣
“Duk kun sauka kun barni, aikuwa inda ba ƙasa nan ake gardamar kokawa, in ka ji kana ba za ka iya ba bai kama ka bane” Cewar Malam ya rintse ido ya diro daga saman, duk da ya ji zafin faɗowar amma haka ya jure tare da daurewa ya miƙe tsaye cikin hanzari, wurin window da Inna take ya nufa idanun nan jajawur da su, duk da yana jin kururuwar su Habu amma saboda abin da suka masa sai bai bi ta kan su ba duk da dama ko da ya bi ya kan nasu babu abin da zai iya kusu.
“Dan Allah dan darajar iyayenki da ƙaunar manzo S.A.W ki buɗe ƙofar nan wallahi wannan tashin hankali bashi ma da daɗi ji bare daɗin gani” Cewar Malam cikin sanyin murya tare da haɗe hannuwa alamar roƙo.
“S.A .W, aikuwa dai tun da ka haɗa ni da Allah da kuma manzonsa, da kuma iyayena, to zan buɗe amma da sharaɗi…
“Wallahi kowane sharaɗi ne zan bi, matsawar dai za ki buɗe ƙofar” Malam ya katse Inna cikin hanzari.
“Wallahi fa ka ce”
“Eh haka na ce wannan alƙawari na ɗauka, ko da cewa kika yi in baki gabaɗaya ladan aikin da za a bani wallahi duka zan baki ba zan ɗau komai daga ciki ba”
“Sai cewa kake ladan aiki wai shin ka yi aikin ma? Kai kan ka baka da nutsuwar da za ka yi aikin, kawai sharaɗi zan gindaya maka”
“To, to, to na yarda”
“Duk abin da na ce ka yi ba za ka mini musu ba”
“Wallahi indai ba saɓon Allah bane zan yi”
“Ɗakko hiraminka da carbunanka ka tsaya daga jikin ƙofar” Cewar Inna tana wani murmushi Inna ta yi tare da barin windown ta dawo falo ganin Sadiya zaune ta buga uban tagumi ta taɓe baki tare da ɗauke kan ta, ƙofar ta nufa ta buɗe. Malam yana jikin ƙofar riƙe da carbunansa, su kuma sauran har lokacin suna haɗe kamar yadda micijin ya haɗe su ta hanyar laulaye wuyansu da ya yi, sai kuka suke suna zare idanu.
“Bani su nan” Cewar Inna da bata wani buɗe ƙofar duka ba, sai da ya miƙa mata,ta ce ya durƙusa ya miƙo mata wuyansa. Mamaki ne ya cika Malam amma sabodanba ya sp ya musa mata ya kasa cika alƙawari, sai kawai ya zubar da gwiwoyinsa a ƙasa, carbunan wannan duka biyun ta saƙala masa a wuya da yake dama suna da girma, sannan ta saƙala hiramin ma a wuyansa ta ƙulle, yana durushe dai yana jiran tsammani.
Ɗan leƙa kanta ta yi sai ta ga Habu ya ci nasara micijin ya saka masa wuya sai Ƙasimu kawai ya naɗewa wuya, zo ya ka ɗan nan taho da rarrafe cewar Inna tana kallon Habu da sauri ya taho har yana ɗan neman faɗuwa, yana zuwa Inna ta ce to tashi yau za a rama maka abin da ka yi na shekara da shekaru, da kake riƙon aljani, tun da dai Malaminka ne ya gayyatoka wannan gida to bisa adalci shi ne zai fitar da kai” Cewar Inna su kuma sai kallonta suke burinsu kawai su bar ɗakin basa buƙatar wannan dogon zancen nata.
“Tashi ka hau bayan Malam” Cewar Inna tana kallon Habu.
“Bayan Malam kuma” Habu ya faɗa yana kallonta.
“Hau Habu babu komai ka san alƙawari kaya ne na kuma riga da na ɗauka cewa zan mata duk abin da ta buƙata. Cikin cika umarni Habu ya tashi ya ɗare bayan Malam, Malam ji ya yi kamar an jibga masa buhun hatsi biyu a bayansa, amma haka ya daure har da cije leɓe.
“To Isuhu za ka fara hamimiyar doki ” Cewar Inna tana riƙe da hirami da kuma cabunan da ke wuyan Malam tamkar ta samu linzamin doki.
Haka ta ƙara janyo ƙofar ta rufe tana jan hiramin wuyan Malam yana ta hamimiyar doki a haka suka fito yana ɗauke da Habu a gadon bayansa yana rarrafawa irin yadda yara ke wasan doki dakyar yake jan gwiwoyinsa amma haka ya daure dan kawai fatansa ya fita daga gidan ma baki ɗaya ba wai ɗakin kaɗai ba.
Sadiya kallonsu kawai take Malam ya daddage sai hamimiya yake ko hutawa ba ya yi, dariya haɗe da tausayi ne suka haɗewa Sadiya lallai Inna ita ce maganin kowane ɗan guguwa, a haka suka je har bakin ƙofar gida suna zuwa Inna ta ce Habu ya sauka haka ya sauka ta nuna masa gabas aikuwa da uban gudu ya zuba ko waiwaye ba ya yi. Sannan ta ƙara janyo Malam yana ta hamimiya ta dawo da shi falon ta tsayar da shi a wajen ƙofar bedroom ɗin ta buɗe ƙofar a hankali ta leƙa aikuwa sai ta ga micijin ya saka wuyan Ƙasimu ya kwanta a ƙasa da alama bacci ma ya yi, sai Ƙasimun yana rarraba ido.
“Ƙasimu” Cewar Inna.
“Na’am” Cewar Ƙasimu.
“Taho ka sha goyo” Cewar Inna tana dariya.
“To” Ya ce yana ɗan lallaɓawa ya kewaye micijin cike da tsoro ya nufo ƙofa ya fito haka shi ma Inna ta sanya ya haye bayan Malam ɗin duk da ba a san ransa ba, a haka ya hau Malam takaici ne ya cika masa ciki wai yau almajiransa da ke matuƙar girmama shi su ne a gadon bayansa kuma ma dan wulaƙanci yana hamimiyar doki, wannan abu ya ƙona masa rai sai dai ba yadda zai yi. A haka suka fito daga falon suna shirin nufar zauren gidan sai ga Abid da Imran suna ƙoƙarin shigowa kowa riƙe da kaya. Imran ya haɗu da Abid ne a wajen gyaran machine ɗinsa da ya lalace masa a hanya shi ne ya tsaya za a gyara a nan suka haɗu da Abid ya ɗaukeshi a mota suka bar machine ɗin a wajen gyara tare suka je suka siyo duk kayan da za a buƙata na rabon sunan. Da mamaki, bakinsu ya kasa furta sallamar da suke ƙoƙarin yi dama shi Imran ya yi mamakin ganin ƙofar gidan nasa jingine a jikin bango an barta a buɗe, gashi kwata-kwata ya ma manta da cewa Hajiya ta sanar da shi za a yi baƙon malami mai ruƙiyya. Abid kuwa baki ya saka galala yana kallon Inna riƙe da lunzamin wuyan da ta yiwa Malam da hirami da carbi shi kuwa ya tara gumi gabaɗaya ga wannan garsamemen ƙato a bayansa yana rarrafe da hamimiya tamkar a filin tseren dawakai.
“Woooo Inna tamu ta amana, waye kuma wannan ya yi arangama da hukuncinki dan na san dai ruwa baya tsami banza” Cewar Abid cike da sheƙiyanci dan ya shaida Malam Isuhu saboda akwai lokacin da ya je gidan wani ɗan uwansu zai yiwa wata budurwa ruƙiyya tana fama da aljannu haka kawai ya je suka yi ta libgarta da dorinai ashe ba wani ilimin azo a gani gareshi ba sai cin kuɗin mutane kamar masifa da shegiyar ƙafafa shi ala dole malami.
“Abida, kai ne yau a gidan namu lallai wata sabon gani, ni wallahi har na gaji da jajenka a zuciyata kwarankwatsa na ɗauka ma ko mantawa ka yi da ni” Cewar Inna tana washe baki ganinsu riƙe da kayayyki duk da dai dama ta yi murna da ganin Abid ɗin.
“Wai Inna meye hakan ya za ki kama babban Malami ki masa wannan cin fuskar…
“Kai yaro iya bakinka ni nan wannan abin da take min ba wani abin zafi bane a wajena, idan aka kwatanta da halin da na fito babu ruwanku ni nan na san duk cikin umarni ne da cika alƙawari” Malam ya tari numfashin Imran da ya haƙiƙice yana faɗa, shi kuma Malam abu ne ya haɗe a goma da shirin saboda ya shaida Abid kuma bai manta da kuɗaɗe da kayayyakin da ya karɓa a wajensu ba kuma dai ƙarshe ba biyan buƙata dan dama ba wai ya iya ruƙiyyar bane kwai lalume yake a cikin duhu.
Yanzu dai burinsa bai wuce Inna ta sallame shi ba ya kama gabansa.
“Kai Imirana ka iya bakin ka da Azumi kake magana kura mai ban tsoro amma ba tsoro” Ta faɗa tana gatsinen gefen hanci. Wani takaici ne ya rufe Imran dan haka raɓawa kawai ya yi ta gefensu ya bar su da Abid.
” Abida yaushe rabonka da gidan nan tin lokacin da ka zo na baka labarin Sojojo ranar da ka kawo min abin arziƙin nan kai wannan yaro Allah maka albarka ba zan taɓa mantawa da abin arziƙin da ka mini ba, amma dai kuma ina ta jiranka ka zo ka sha labari labarai har sun gaji da taruwa” Ta faɗa tana kallon Malam da ya sunkuyar da kansa ƙasa tare da Ƙasimu da ya masa wani ɗogogo a baya.
“Ai ina nan Inna abubuwa ne suke shan gabana amma da tuni na zo kin ɗora min daga inda kika tsaya”
“Kai dai bari Abida
ai labari kala-kala, mutuminka fa ranar nan har da shiga tukunyar da nake dafa ruwan wankan jego” Cewar Inna tana ɗan rage murya take magana raɗa-raɗa ƙasa-ƙasa.
“Tukunya Inna?” Cewar Abid shi ma yana rage muryar dariya na cinsa dan har ya hango Imran a cikin tukunya.
“Tukunya mana, yo ba ƙwara shiga tukunya ba wallahi ranar nan idona idonsa yadda na ga Imirana da Rakiya Allah nuna min annabi S.A.W, wallahi rungumar juna suka yi saboda ruɗewa, yo kai ka taɓa jin wannan sabga aiki ɗanye sharaf siriki ya ƙaƙumi sirika” Inna ta faɗa tana ɗan waiwaya bayanta tana dariya ciki-ciki.
Dariya kawai Abid yake sosai yake hangowa kamar a gabansa komai ya gudana.
“Jeka ciki ina zuwa in sallami wannan Mololon dan ba malami bane, in zo” Ta faɗa tana jan wuyan Malam ƙiii shi kuma ya cigaba da hamimiyarsa da kallo kawai Abid ya bi su yana jinjinawa tsohuwar dan shi har ga Allah ba ya ganin laifin Inna komai tana yi a kan gaskiyarta ne kuma da hujja.
Inna kwa ko a jikinta wai an tsikari kakkausa haka ta ja Malam suka je bakin ƙofa, ta sanya Ƙasimu ya sauka ta nuna masa hanyar da zai yi haka ya fita a guje ko takalmi babu kamar yadda Habu ya tafi ya rage daga Inna sai Malam.
“Kai kuma daga nan har in daina hangoka da rarrafe za ka fita” Cewar Inna tana haɗe rai tare da kama tsantsa.
“Dan Allah ki rufa min asiri kamar yadda Allah ya rufa miki, dan Allah yanzu na fita da rarrafe gabaɗaya mutuncina zubewa zai yi kuma shikenan bare ga wandon nan nawa jagaf da shi da Allah ki taimaka mini” Cewar Malam yana durƙushe a kan gwaiwoyinsa.
Shiru ta ɗan yi tana kallonsa tare da taɓe baki ta ce
“To shikenan ka tafi da ƙafarka”
“Nagode Malama Inna Allah ja da kwananki ki daɗe ki yi ƙarko” Ya faɗa yana miƙewa tsaye dakyar dan gabaɗaya ƙafafunsa sun yi sanyi ga dila ma ya kama masa ƙafafu amma haka ya daure ya tashin yana raba idanu gashi ko takalmi bai ɗakko ba yana cikin gidan.
Ya juya yana taka ƙafar dakyar Inna ta rafka masa wani uban kira da yasa gabansa bugawa da mugun ƙarfi, yana fatan ba cewa za ta yi ya dawo gidan ba, in kuwa haka ne ba zai yarda ya koma ba da gudu zai zuba sai dai in an kamo shi a yanka shi.
“Addu’ar fa” Maganar Inna ta katse masa tunaninsa.
“Kai wannan tsohuwa da masifa take wato dan jaraba bata manta ba, bayan ni yanzu komai ma na manta a kan nan nawa bare har in tuna da cewa wai na ce zan basu addu,a” Cewar Malam a zuciyarsa.
“Cewa na yi addu’ar da ka ce za ka bayar wacce za a yi taro lafiya a gama lafiya, duk da ka ce ba sai an tuna maka ba amma dai na ga kana ƙoƙarin tafiya, babu niyya ango ya kwana da wando” Cewar Inna tana kallon Malam da kunya ta gama rufe shi.
” Da ku na cikin gidan, da duk wanda zai zo suna, ku karanta Qulhuwallahu ƙafa uku bayan kun gama sai ku ce Allah raba mu da mugun ji da mugun gani” Cewar Malam a fili a ransa kuma ya ce
“Ba dole in ce ku nemi tsari da mugun gani ba dan wannan micijin ai ganinsa kaɗai tashin hankali ne”
“Haka za mu karanta to bari na mayar da kai ɗakin ku kwana da mugun ganin mu gani” Cewar Inna tana kallon Malam da har lokacin, carbunansa da hiraminsa suna wuyansa amma ba ta su yake ba, wannan magana da Inna ta yi ta, za ta maida shi ɗakin micijin nan ta sanya hankalinsa ya tashi dan haka ya yankewa kansa shawarar zabgawa a guje dan ya tsira da ransa. Kafin ƙiftawar ido Inna sai gani ta yi ya tattare babbar rigarsa gudun hantsilwa idan yana gudu ya zangaya a guje.
” Ka manta takalmanka da na almajiranka, da hular mai kayan aikinku da galan ɗin ruwan addu’arku, kuma baka karɓi kuɗin aikinka ba da sauran kayan aikin da ka ce za a baka” Cewar Inna da ta daddage tana faɗa masa.
“Na bar muku duka halal malak” Ya faɗa da ƙarfi har lokacin yana zabga gudu ko waiwaye ba ya yi gudun kar a samu matsala Inna ta biyo shi ta mayar da shi ɗakin miciji. Daga Inda Inna take tsaye daga ƙofar gidan da ta fito tana hango yadda ya sha wata uwar kwana a sukwane ko lanƙwasa babu.
Dariya Inna ta yi idanunta a kan motar Abid ta juyo ta dawo ciki tana ƙoƙarin rufe ƙofar sai gasu sun fito Imran da Abid.
“Innna har ya tafi baƙon naki?” Cewar Abid yana maida dariyarsa.
” Ya tafi mana amma dai ba baƙona bane baƙon Hassan ne kuma ya sallame su dan kuwa sun sha baƙar azaba kwakwa dai yau an sha ta a wajen miciji” Ta faɗa tana washe baki.
“Na gane Inna” Ya faɗa yana daria.
“Ba dai tafiya za ka yi ba?” Cewar Inna da mamaki.
“Ba tafiya zan yi ba kaya za mu ɗakko a mota kin san kayan rabawa ne gobe muka siyo”
“Ikon Allah wato ka ji kaɗan ka ji da yawa, yanzu baƙin halin Imirana har ya kai haka, a ce zai tafi siyayyar amma ina garin nan muna gida ɗaya ɗaki ɗaya amma ya kasa gayyata ta na raka shi sai ya je ya ɗakko ka”.
Wani kallo Imran ya jefa mata irin na kina kai kan ki inda Allah bai kai ki ba, kafin ya raɓa ta ya wuce wurin motar.
“Au Allah wato ina maganar ma ka wuce ka bar ni wato ga karya yo in ba karya ba waye ake bari yana haushi shi kaɗai” Cewar Inna tana bin bayan Imran da harara.
“Rabu da shi Inna ba gani ba zan tsaya mu yi hira abin mu kuma kwantar da hankalinki indai kina nan to kuwa kafin ki tafi xan kai ki yawo a mota ta mu yi siyayya ki zaɓo abin da kike so in biya kuɗin” Cewar Abid yana kallon yadda fuskar Inna ta saki lokaci guda kamar an mata albishir da gidan aljanna.
“Allah Abida ka ce akwai zaɓar abubuwa masu yawa to aikuwa har sa kishiya kuka da sa kishiya tagumi zan ɗakko a wurin siyayyar”
Galala Abid ya yi jin furucin Inna dan shi dai ya ji ana cewa sa kishiya kuka ko tagumi maganin mata ne amma kuma mai Inna za ta yi da maganin mata.
“Inna sa kishiya kuka da tagumi za ki ɗauka in mun je siyayya…
“Oh Abida rufani ka saya ni, dan Allah kuke bari sai mutane sun mutu kafin ku binne su.
, yo in ba fallasa auren bashi ba har na tsaya yin maganar maganin banza da kai(Maganin mata) Magano na ce magano, to indai abin da ka yi zato to Allah tsari gatari da saran shuka, to ni ina nufin kayan ƙwalam wato kayan ciye-ciyen ne zan ɗakko sa kishiya kuka da tagumi, abubuwa ne zan ɗakko masu daɗi wanda ba za su lalace ba har lokacin da zan gama ZAMAN WANKANA in tafi da kayana gidan Malam sai in ke ɗakkowa ina ci ina jefar da takardar ko ledar yadda Tasalla da ta gani za take rafka uban tagumi da hannu bibbiyu, idan ta shige ɗaki kuma ta yi ta rusar kuka saboda baƙinciki, shi na ce zan ɗakko kar ka kai ni inda Allah bai kai ni ba ka sa ni a bakin duniya” Ta kai ƙarshen maganar tana kallo Abid da ke ta faman dariyar maganar ta.
“Na gane manufarki Inna, sai Inna ta mu ta Malam bada kan ki a sare ki je gida ki ce ya faɗi”
“Rass kuwa Abida ai ni ce ɗaya tamkar da miliyan a wajen Malam, kuma wallahi da ka ce Inna tamu sai ka sani wata ƴar bazawarar dariya dan ka tina min da daren jiya” Cewar Inna tana ƴar dariya tana kallon Imran ta gefen ido dama ganin ya kwaso kaya a mota ya taho ta faɗa.
“Mai kuma ya faru daren jiya Inna?” Cewar Abid yana dariyar shi ma
“Hummm kai dai bari Abida wallahi daren jiya ne abokin ka Imirana ya shiga wani hali na a zo a gani, sai ji ka yi Imirana yana, Innarmu, Inna ta” Ta faɗa tana sakin dariya irin mai ƙular da mutum ganin Imran ya zo wajensu zai fice, wani irin haɗe rai ya yi tare da wurga musu wata uwar harara. Abid kwa kawai dariya yake dan har ya hango abokinsa tabbas ya san Imran ba ƙaramar wuya ce za ta sa ya ce Innarsa ba.
“Hehehehe na dawo in ji ɗan yawon duniya, to wallahi ban san ana yi ba kunu a maƙota, kuma ban san harara ba sai ido ya faɗo ehe” Cewar Inna tana jefawa Imran hararar ita ma har da gatsi ne.
“Ƙyaleshi Inna” Cewar Abid dariya har kasa magana yake.
“Yo dama ai ba biya shi zan yi ba da ina biya Imirana ai da zamana a gidan nan bai kawo yanzu ba, ni kuwa na faɗa masa zama daram, kuma nan gani nan bari farar tunfafiya, labari kwa dole na bayar tun da ya yi abin da za a faɗa dan labari sai ma na koma ƙauyenmu in samu abin da za mu ke maimaitawa ni da aminiyata Tsahare muna darawa yo labarin abubuwan da Imirana ya yi daga zuwana zuwa yau ai abin a bayar da labari ne, dan ba tsoronsa nake ba, bada labari kuwa farillah ne tusa a masallaci, dan wallahi ina sane wai karuwa ta taka matar aure, dan kuwa ni na san karambanin akuya yasa ta leƙa ɗakin kura” Ta kai ƙarshen maganar tana wani juya ido tare da gatsine kamar wata matashiyar budurwa.
Abid kawai dariya yake a haka ya je ya buɗe motar ya ɗakko wasu kayan da wata leda mai ɗauke da apple mai yawa fari da kore ya miƙawa Inna, ta karɓa tana ta godiya kamar ta ari baki, a haka suka baro zauren dan dama a can ne tun da ya same ta za ta rufe ƙofa suka tsaya suke maganar. Ko da suka dawo ma haka ta zauna tana ta baiwa Abid labari dan haka kuwa ya zauna yana ta dariya har da riƙe ciki, amma kuwa saboda soyayya da kuma kyautatawar da Abid ke mata, Inna bata bari Abid ya ga miciji ba, dan ƙofar ma ta kulle bayan ta maida Hassan ɗin kan gadonsa dan kar Abid ya gani ya firgita dama hausawa sun ce zuciya na son mai kyautata mata.
Bayan tafiyar Abid Inna ta buɗe jakar kayanta ta ɗakko wani abu ta saka a cikin ɗan tofinta (Siket da tsofaffi suke sakawa daga ciki wand ake ɗinka musu har da aljihu a jiki) Bayan ta sanya a aljihun ɗan tofin nata ta cewa Sadiya za ta fita ta ɗan zaga ƙafarta dan ita ta gaji da zama wuri ɗaya, Sadiya kwa ta ce a dawo lafiya dan ita ma so take Innar ta fita saboda ko kaɗan in tana gidan sai an samu wani akasin. Baki ta taɓe ta ɗauki mayafinta ta yafa sannan ta ɗauki goro guda ɗaya take ci abinta ta fita. Tun da ta fito hanyar da Malam Isuhu ya bi ta nan ta bi tana yi tana kallon sawun ƙafarsa da ya yi ta sheƙa gudu ɗazu dan sawun har wani nitsewa yake a cikin ƙasa saboda yadda ake taka shi da ƙarfi, kalla kawai ta yi tana dariya wai mai sittin wata kan wata sai gashi ko izifi ɗaya bai karanta ba a ɗakin Hassan. Tafiya take abinta hankali kwance, tana cikin tafiyar, wata mota mai baƙin gilashi da wasu ke ciki suna kallon hoto a waya ɗayan ya kalli ɗayan ya ce
“Ita ce”
Aikuwa da uban gudu motar nan ta sha gaban Inna dama wajen duk ba mutane Inna da ta tsaya kallon ikon Allah ganin mota ta sha gabanta kafin ta gama tunani sai gani ta yi an fito daga ciki an fisgeta an shiga da ita motar an banke ƙofa an kwasa da uban gudu…
Masu fitar min littafi ki sani haƙƙina ne, dan haka ke ma da kike karantawa haƙƙina ne kuma baki biya ni ba.
09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
3️ 4️⃣5️⃣➡️4️⃣6️⃣
Tun da suka saka ta a mota ta fara wurwurga idanu, mutum huɗu ne a cikin motar gabaɗaya suna sanye da kayan sojoji, ɗaya yana jan motar shi kaɗai ne bashi da kayan sojoji. Mutum biyu ne suka sanya Inna a tsakiya kallonsu take tana so ta ga ko ta taɓa ganin wani, amma babu wanda ta gane, baki ta buɗe za ta yi magana amma ɗayan ya ɗaga bindiga ya ɗora mata a kan ta hakan ne ya sanya Inna ta ja bakinta ta yi shiru dan duk abin ta bata wasa da rai da lafiyarta.
Gum ta yi da bakinta bata sake yinƙurin yin magana ba su ma kuma duk cikinsu tun da ta shigo motar bata ji wani daga cikinsu ya yi magana ba.
Wata unguwa suka nufa da babu hayaniya sosai a ƙofar wani get suka tsaya horn aka yi mai gadi ya zo ya buɗe ƙofar suka shiga ciki Inna kuwa sai rarraba ido take yi dan ta kasa gane dalilin da ya sa aka ɗakko ta. Tunani ta fara yi ko ƴan yankan kai ne suka ɗakkota, duk da dai ta gansu da kakin soja a jikinsu amma hakan ba zai hana ta zargesu ba saboda yanzu ƴan bindiga suna kashe sojoji su ɗauke kayansu suke sanyawa, dan dai ta san wancan karon da aka ɗakko ta daga gidan masu kuɗin wannan jeji aka nufa da ita saɓanin yau kuma da aka nufo cikin gari kuma ƙeraren gida na gani na faɗa.
Haka dai ta daure saboda bakin bindigar da ke kanta. Suna fitowa ita ma haka ta bi ayari ta fito bisa bin umarnin da aka bata, tun da suka fara tafiya zuwa ainihin cikin gidan take ta kalle -kalle har suka samu nasarar shiga cikin wani falo madaidaici mai shegen kyau. Su duka wuri suka samu suka ƙame babu wanda ya nemi wurin zama Inna kuwa ganin tsayuwar ba za ta mata ba sai ta zauna a ƙasan kafet gudun kar ta hau kujera a harbeta.
Suna nan, sai ga wata yarinya ta fito cikin wasu ƙananan kaya tana riƙe da abin wasanta, Tun da ta fito Inna ta ƙura mata ido tana mata kallon sani sai dai ta kasa tuna inda ta san yarinyar tana ta kiciniya da ƙwalƙwalwarta a kan ta barta ta tuna ina ta san yarinyar amma kafin hakan sai ganin mutum ta yi ya fito daga cikin wani ɗaki shi ma sanye da kaya amma ba na sojoji ba. Kallo ɗaya Inna ta masa ta gane shi a take ta tuna da inda ta san yarinyar ma.
“Sojojo kai ne dama nan gidan ka ne ina tsohuwar matarka mai shegen tsoron nan kamar farar kura, ko da yake ma ba ita kaɗai ce matsoraciyar ba har da…
Wata uwar tsawa da ya daka mata ita ce ta hana Inna da ta washe baki tana ta kauɗi da karaɗi ƙarasa maganar, dan tun kan ya ƙaraso ma tsakiyar falon ta fara zuba.
Cikin ɓacin rai ya ƙaraso tsakiyar falon gabaɗaya suka shiga sara masa kujera ya nema ya zauna har lokacin ransa a matuƙar ɓace yana aikawa Inna wani mugun kallo. Ƴar tasa ce ta zauna a kusa da shi tana ta raɓewa a jikinsa da alama dai bata manta da inda ta ga Inna ba.
“Ke inyamura ina uwaki take, yo ina so in miki magana amma na san bakya jin hausa, ina so in ce ki kira min uwaki tsohuwa mu gaisa ko yau ma tana can tana kwalliyar tana shafa jambaki kamar akuya ta ci dusa sai…
Ɗaya daga cikinsu ne ya ƙara yiwa Inna tsawar da ta sanya ta yi shiru sai dai yanzu tun da ta ga abokin Imran gaba yake da su, wato ogansu ne sai ta ji duk bata tsoronsu dan ta san dai duk tsiya ba lallai su harbe ta ba.
“Oh ni Azumi Allah ya tsaga min bakina amma ku hana ni magana, na rasa ma mai yasa kuka ɗakko ni duk da dai na san ruwa ba ya tsami banza amma dai da walakin goro a miya”
Babu wanda ya mata magana dan abokin Imran ya ɗaga musu hannu alamar dakatarwa.
Kallon su ya yi cikin bada umarni ya ce
“A kai ta wannan ɗakin” Da kallo Inna ta bishi tana mamakinsa amma sai ta miƙa hannunta ta taɓo saitin aljihun ɗan tofinta ta ji abin da ta ajiye yana nan hakan ya sanya ko gardama bata musu ba suka tafi da ita. Har sun je ƙofa za su fita ta juyo ta ce
“Gobe sunan Hassan dai mutuminka ina fatan za ku je” Wani haushi ne ya rufe shi yana ayyanawa a ransa tabbas tsohuwar nan yau sai ta banbance tsakanin aya da tsakuwa, dan sai ya tabbatar ta gane akwai banbanci tsakanin kiɗa da karatu. Ƙeyarta suka tisa har ɗakin da aka bada umarni a kai ta, ɗakin a can bayan gidan yake kuma a rufe yake sai da suka buɗe ɗakin suka shigar da ita ciki wani daga cikinsu wanda ya zo a kujerar mai zaman banza lokacin da suka taho a motar har ƙeya ya tallewa Inna, amma bata ce komai ba sai dai ta ayyana za ta rama ne.
Sai da suka gama harare -harare da wani tsawace -tswacensu sannan suka fito suka rufe Inna a cikin ɗakin suka sanya mukulli sai dai basu cire mukullin ba daga waje suka barshi a jikin ƙofar.
Sai da suka yi kamar minti goma da fita Inna ta tashi ta yi dibara ta ɗan buɗe windown sai da ta tabbatar babu kowa a kusa sannan ta buɗe windown duka, wani dogon icce da ta samu a ɗakin ta ɗauka ta sanyo shi ta windown a hankali cikin dibara ta saƙala iccen a jikin ƙarfen key holder na jikin mukullin, cikin dibara ta cire mukullan daga jikin ƙofar sai dai tana ƙoƙarin shigo da iccen ta windown sai mukullin ya zame daga jikin iccen ya faɗi ƙasa.
A haka ta rinƙa yin dibara har dai ta ci nasarar ɗakko shi a jikin iccen, daga ƙasan ta shigo da shi cikin ɗakin, jijjiga kai kawai take tana dariya ta ce
” Ta yaro kyau take bata ƙarko, tabbas yaro bai san wuta ba sai ya taka, lallai yau allura za ta tono garma, su a ganinsu sun garƙame ni, basu san na fisu wayo ba ko dan dogaye ne dan bashaushe ya ce dogo da hankali dace ne” Cewar Inna tana ta ƙoƙarin cire mukulli ɗaya daga jikin key holdern dan gabaɗaya mukullan iri ɗaya ne hakan ya nuna duka na ɗakin ne.
Bayan ta cire ɗaya sai ta sanya a cikin aljihunta, bayan ta ɗakko wata ƙaramar farar leda ƙulle da wani abu, tana gyaɗa kai alamar za ku gani. Sai da ta adana mukullin da ta cira ta yi murmushi ta ce
” Mu je zuwa da ni Azumi kuke zancen ai ni duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha”
A hankali ta lallaɓa ta sake leƙawa har lokacin bata hango kowa ba kuma bata ji motsin kowa ba ga la’asar ta yi lis haka ta sanya mukullin ta buɗe ƙofar a hankali ta fito daga ɗakin, tana fitowa ta maida ƙofar a hankali ta rufe bayan ta rufe sai ta bar mukullin a jiki, cikin sanɗa ta fara tafiya tana ta waiwaye abinka da marar gaskiya ko cikin ruwa gumi yake. Cikin ikon Allah har ta ƙaraso ɓangaren da suka fara zuwa ita da sojojin nan wato inda ogan nasu yake abokin Imran. Shigewa ta yi dan a hankali ta tura ƙofar har ta ƙaraso falon babu wanda ya lura da ita. Laɓewa ta yi a jikin bango wani ɗan loko take leƙo falon yana zaune ya rungume ƴar sai matar ita ma daga ɗaya gefen nasa ta zauna ta kwantar da kanta a kafaɗarsa ta yi wani turum da tsohon cikinta.
” Wai da gaske an samo matar nan ta gidan abokin ka?” Cewar matar cikin gurɓayacciyar hausarta.
“Eh wallahi har nan aka shigo da ita amma saboda ƙarfin hali har tambayarki take tana miki wulaƙanci wai ko kina can kina shafa jambaki bakin ki kamar akuya…
” Haba wato kaima maimaita abin da ta ce za ka yi, tabbas yau bayan ka hukunta tsohuwar nan sai ni ma na mata hukunci mai tsanani za ta san da ni take magana”
“Ayyo to ke ma ashe shegiyar kan ki ce da ban yi niyyar miki komai ba shi kaɗai zan yiwa to tun da ke ma mummunan ƙudiri ne a ranki har ke zan haɗa, ƴar taku ce dai ba zan yiwa ba saboda ƙanƙantar ta, dan kar in ɗau alhaki” Cewar Inna a zuciyarta.
“Ayya ba dan na ɓata miki rai ba na yi baby, amma tabbas yau za ta karɓi hukunci dan kuwa zan ɗauke idanuna daga kallon tsufanta in manta alaƙarmu da Imran duk da shi ma ya ce min ta addabeshi, amma yau sai ta san wa ta yiwa abin da ta yiwa ranar nan wai dan wulaƙanci ni take cewa sojojo sai ka ce wani ɗan ƙwaya” Ya faɗa cikin gurɓatacciyar hausarsa.
“Ai kawai ka bari tsohuwar nan za ta gane kurenta, ai na gode Allah da ka aamu hutun sati biyun nan jiya gwara da ka sa aka ɗakko ta mu ga tsiya” Cewar matar tana dariya.
“Za mu ga wanda zai gane kurensa ni da ku ai ni duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha, kuma iya gani iya ƙyalewa ni Azumi zan nuna muku ɗan hakin da ka raina shi ke tsone maka idanu” Cewar Inna a zuciya.
A hankali ta since farar ledarta wacce ta zubo ƙaiƙayin hatsi ta haɗa da barkono ta daka ta zuba a leda ta ƙulle. Ya daɗe a ajiye a cikin jakarta dan tun kafin cikin Halima ya tsufa ta ajiye saboda idan za ta je ZAMAN WANKA ta ajiye saboda shirin ko ta kwana. Ledar ta since ta lallaɓa cikin falon da suke da yake sun baiwa ƙofa baya ne basi san me ke faruwa ba idanunsu a kan TV. Sai da Inna ta je bayansu kawai sai ta ga matar za ta juyo da sauri ta durƙusa Allah ya sa ma matar bata ganta ba sai da ta bari ta ɗan jima ta ji suna ta hirar yadda za a azabtar da ita, ta tashi ta zuba musu ƙaiƙayin nan mai barkono a cikin wuyan rigarsu sai da ta barbaɗawa mata da mijin ta lallaɓa ta fice. Ta baya ta bi tana yi tana laɓewa dan so take ta gano inda sauran sojojin nan suke wanda suka ɗakko ta. aikuwa ta hangosu zaune a kan benci sun bata baya suna cin wani abu haka su ma ta lallaɓa ta je sai da ta zubawa kowane a cikin wuyan rigarsa cikin hanzari ta bar wajen ta koma ɗakin da aka ajiyeta. Ta maida mukullin yadda suka ajiye shi a jiki ta rufo ƙofar sai dai bata kulle ba.
Sojojo suna kallo bai ankara ba sai ganin ya yi ya miƙe tsaye zimbet yana zazzare ido dan raɗaɗin barkonon da ya ziyarci fatar bayansa ya haɗe da ƙaiƙayin ya bashi wani azababben zafi da raɗaɗi. Yatsina fuska matar ta yi tare da taɓe baki ganin abin da mijin nata yake yi kamar wani mahaukaci sabon kamu. Tana shirin masa magana sai ita ma a take ta ji wani raɗaɗi ya ratsa fatarta kamar wanda aka tsatstsaga mata fatar bayan da wuƙa ko reza aka zuba gishiri ko yaji haka ta ji a take ita ma ta miƙe suka shiga zarzage -zazzage sai idanu take zarewa kamar ta yi ƙarya an zo mata cakar ƙarya.
A take suka shiga zirya a falon babu wanda ke iya taimakawa ɗan uwansa kowa ta kai ta kai yake kowa ɗauki yake nema sai ife-ife da soshe-soshe suke kamar za su karce fatar jikinsu amma kuma ƙaiƙayin ƙaruwa yake . Su sa suke hannu bibbiyu dan shi mijin ma ya yi xaman ƴan bori a ƙasa sai susa yake amma kamar ya yi hauka ga ƙaiƙai ga raɗaɗi , ita ma matar da ta gaji sai zaman dirshan ta yi ta miƙe ƙafa tana sosawa shi ya kalli gabas ita ta kalli yamma sun raba jaha mijin da matar, can ya gaji ya kwanta a ƙasa yana gurza bayansa a ƙasa amma ina jin abin na neman wuce gona da iri sai ya fara kiciniyar cire riga, yana gama cirewa ya cigaba da soshe soshe ƴarsu na musu sannu.
Hakan bai masa ba sai da ya tuɓe kayansa duka daga shi sai gajeren wando, tashi tsaye ya yi sai zagaya falon yake yana wani dira ƙaƙafu, matar ma kiciniyar cire riga ta fara ganin tana neman cire kayan ya doka mata wata uwar tsawar da ta sa ta suka shige ɗaki ita da ƴarta shi kuma ya yi hakan dan kar wani cikin yaransa ya shigo duk da dai basa shigowa sai ya musu izini amma dai idan wani uzurin ya tashi zasu iya shigowa bare yau da ya san ya ajiye Inna a gidan ya san ba za a rasa nono a ruga ba.
Suna shigewa ɗaki da ya ji bala’in ya yi bala’i a sukwane ya fito daga part ɗin nasa ya fito yana ƙwalawa yaran nasa kira, daga inda suke suna ta tutumurtu suka rugo wurinsa a guje cikin son cila umarninsa ganinsu su duka a tuɓe da gajerunan wanduna kowa hannu a jiki kowa na susa kamar su yi hauka.
Shi ma yana susar ya kalle su yana wani zare idanu.
“Meye hakan kuma kuke yi kuna min yawo a gida a tuɓe?” Ya jefa musu tambayar yana soshe soshe. Sara masa suka yi suna ta susar kowanne idanunsa jajur.
” Oga wallahi kawai muna can baya a zaune sai kowa ya fara jin ƙaiƙayi da raɗaɗi mun rasa menene” Suka haɗa baki wurin bashi amsa har lokacin kowa susar yake har ogan.
Yana shirin yin magana ai da ya ji wani azababen ƙaiƙai sai ya manta da basu amsa tun yana yi a tsaye har ya kwanta reran a ƙasa sai birgima yake su ma maimakon su taimaka masa sai ƙaiƙan ya ci ƙarfinsu suka kwanta a ƙasan daga gefe duk da halin da suke ciki amma sun san Ogan su ne basu jeru da shi ba, yana gefe yana birgima da gurza bayansa a ƙasa suma suna gefe suna yi kamar yadda yake, sai da suka ji ƙaiƙan ya ɗan lafa suka dakata Oga ne ya fara tasho sai wani cin magani yake yana wani harare-harate shi a dole kar a kawo masa raini cikin haɗe rai ya ce.
“Ina tsohuwar nan?”
“Tana ɗakin da ka ce a kai ta”
“Kun kulle ta kuwa”
“Eh Oga da mukulli ma”
Sai lokacin ya ɗan ji ya daina zargin Inna dan ya san dai babu yadda za ta yi ta fito ɗaki a kulle amma da ba zai taɓa yadda ba ita ce silar shigarsu halin da suke ciki ba sbd ya san za ta iya yin komai sai dai ai babu wanda ya ga wanda ya aikata wani abu kowa ya tsinci kansa ne a halin dan haka sai aka dangana hakan da ko aljannun gidan ne suka musu hakan.
Ɗakin da Inna take suka nufa domin a je a mata hukunci tun yau za ta fara karɓar hukunci dan ya yi alƙawarin sai ta kwana uku suna azabtar da ita sannan za a maidata sunan da damun mutane da shi ma ba za a yi tana nan ba sai dai a bata labari haka ya ƙudurta a ransa.
Inna da ke cikin ɗakin tana ta addu’a a kan Allah ya fitar da ita daga gidan sojojo lafiya dan ta sha jin ana cewa sojoji basa ragawa mutane babu ruwansu sai su zartarwa mutum hukuncin da ya musu, tana kuma fatan kar su gane wani shiri da ta musu dan ta san shirin shi kaɗai ne zai ƙwace ta daga uƙubarsu, tana nan zaune tana ta jan sunayen Allah sai ta fara jiyo maganarsu, hakan ya sanya ta cigaba da addu’a, suna zuwa ɗaya daga ciki ya sanya hannu ya murɗa mukullin bai lura cewa a buɗe mukullin yake ba, dan haka shiga kawai suka yi.
Inna da tun da suka shigo ta kafe su da idanu dariya na cin ta yadda gabaɗayansu suka yi ankon gajerunan wanduna ga wata ƙasa tun daga kan su har bayansu. Cikin izza Ogan ya kalli Inna zai fara magana sai kuwa ya ji ƙaiƙayin ya dawo sabo dal, kamar an haɗa baki su ma sai suka ji hakan a take suka layu a jikin bango suna susa da jikin bangon kowa yana goga bayansa dan lokacin ma sun manta matsayin Ogan nasu a wajensu kowa ta kai ta kai yake.Inna sadda kanta ƙasa ta yi tana dariya ƙasa-ƙasa ganin duk sun haukaci lokaci guda.
“Oh ni Azumi ko ina matar sojojon take, tana can ita ma tana fama ga ƙaton ciki ga susa, ai dama in zaka gina ramin mugunta ka ginashi gajere wato kun kawo ni za ku azabtar da ni gashi nan ido ya juye da mujiya. Cewar Inna a ranta.
Sai da suka ɗan dakata da su sar sai kawai idanunsu ya sauka a kan wani miciji da ke can gefe kusa da Inna sai dai ba su yake kallo ba ya basu baya, sai dai ya fasa kansa. Gabaɗaya sai suka sha jinin jikinsu, gashi ko bindiga babu a wurinsu lokacin bare su ce za su harbeshi, a take Inna ta gane tarkonta ya kama su.
” Kuna gani na haka to wallahi ni lunbu-lunbu wutar ƙaiƙayi ce, kuma murucin kan dutse ce ban fito ba sai da na shirya, wa ya faɗa muku barno gabas take ai wallahi faɗa da aljani ba daɗi, wai ku nan wayon a ci an kori kare daga bakin ɗinya, ai iya gani ƙyalewa” Cewar Inna a zuciyarta tana tashi tsaye daga inda take zaune da ta fahimci tarkonta ya kama tsuntsu.
Sai da ta ɗaure mayafinta a tsantsa sannan ta turo ɗankwalinta gaban goshi ta taka a hankali ta isa wajensu da suka takure a waje ɗaya su duka dan gabaɗayansu Oga ya basu labarin micijin gidan Imran da ya faɗa musu jariri ne yake zama micijin, dan haka kuma abin da ya ƙara ɗaure musu kai sun san dai su suka kawo Inna ita kaɗai suka kulle ta a ɗaki ita kaɗai amma yanzu ga miciji tunaninsu micijin aljani ne dama shi yasa ya biyo ya ceci Inna. Tana zuwa gaban abokin Imran ta kama tsantsa ta ce.
“Sojojo har ni za ka sa a kamo a kawo gidan nan a kulle ni dan ka cutar da ni, to ga Hassan nan ya biyo ni zai cece ni dan haka sai ku shirya artabu da shi”
“Dan Allah ki taimaka mana ki ce ya tafi wallahi za mu maidaki gida yanzu ba tare da mun taɓa lafiyarki ba” Suka haɗa baki wurin faɗa. Wata dariya ce ta zo wa Inna ganin yadda suka yi buɗu-buɗu da ƙasa kamar wanda aka tono daga cikin rami wai duk garin susa suka zama kamar wasu fatake, danne dariyar ta yi ta kallesu ta ce to ni zan tafi na barku tate da shi a sha gumurzu lafiya ai kai sojojo ina fatan baka manta ba da karonku da shi”
Gabaɗaya sun ruɗe da maganar Inna dan haka suka shiga ihu da kururuwar bata haƙuri ba ga Ogan ba, ba ga yaran nasa ba.
“Ai ya faɗa min ba zai juyo gareku ba sai na bashi umarni dan haka yanzu zan bashi umarni ya cika aiki” Ta faɗa tana ɗakko mukullinta daga cikjn ɗan tofinta dan Ogan da suka shigo sai ya kulle ƙofar ya cire mukullin dan haka mukullin yana hannunsa.
“Ka ga mukullin da Hassan ya kawo min yanzu da ya zo” Ta faɗa tana nuna musu mukullin hannunta tsabar tsorata sai jikinsu ya shiga karkarwa dan sun yarda aljani ne.
” Bani mukullin hannunka sojojo ko yanzu lahira ta yi baƙo” Ta faɗa tana miƙa masa hannu ya damƙa mata, dan wanda ta cira a jiki ta yi amfani wajen buɗe ƙofar ganin ƙofar ta buɗe sai suka ƙara tabbatarwa, tana fita kuwa ta kullo ƙofar ta sa mukulli dan ta ga sun iyo ayari a guje za su biyo ta, ganin ta kulle sai suka koma inda suka baro suna takurewa a waje ɗaya.
“Tun da na fito yanzu nan zan bashi umarni ya cika aiki” Cewar Inna da ta leƙo ta window tana kallonsu har hawaye sun fara musu zarya a fuska.
” Haba sojojanni marmari daga nesa duk jarumtarku ku fara kuka tun yanzu?”
“Haba Inna ya zaki rufe mu ɗaki da wannan abun ki ce ba za mu yi kuka ba, a haɗa ka ɗaki ɗaya da mutuwarka wato ajalinka” Suka faɗa suna hawaye yaraf-yaraf.
“To in bakwa so na bashi umarni sai kun yi abin da na ce”
“Faɗi ko menene za mu yi” Suka haɗa baki wajen faɗa.
” Hassan kar in ga ka juyo ka tsaya a yadda kake kamar gunki kar ka kuskura ka motsa sai na baka umarni” Cewar Inna tana nuna Hassan da yatsa.
“To ya amince, babu abin da zai muku sai dai wanda ya ga baya yin abin da na saka ku zai zo wajensa wataƙila ma ya haɗiye shi”
“Zamu yi ma”
“To ku hau layi ku daina cakuɗewa a waje ɗaya a hau layi, sai a fara yiwa nigeri’a kirari amma duk inda sunan nigeri’a ya fito kar wanda ya kuskura ya ce nigeri’a Azumin Malam za kuke sawa a duk inda aka ambaci nigeri’a”
Kallon kallo suka fara amma ba yadda suka iya, haka suka ƙame suka fara taken nigeri’a (National anthem) Kuma duk inda aka ambaci Nigeri’a a cikin national anthem to sunan Azumin Malam suke sawa, bare duk basu hausa sosai Ajimum Mayan suke cewa amma a haka suke ta yi suna dawo wa farko har sai da Inna ta gaji ta ce su dakata.
“Yanzu kuma abin nan da kuke cewa leee ray(left right) Wanda kuke yi kuna ɗaga ƙafa dama da hagu kuna bugawa a ƙasa wanda da ake cewa mai tsumman (letf) Marar tsumman(right) Shi za ku yi amma a maimaikon leee, ray, sai kuke cewa Azumi (left) Malam (right).
Babu yadda suka iya haka suka fara bin umarnin Inna suna buga ƙafa suna kiran sunanta da na Malam a maimakon left right.
Tun suna yi da ƙarfinsu har sai da suka gaji sun jigata sosai, sannan Inna ta dakatar da su, ta ce su fito su kalli gabas za ta shiga ɗakin su yi magana da Hassan ta bashi haƙuri ya ɓace, bayan sun mata alƙawarin mayar da ita gida ba tare da ko lakuci ba, har rige-rigen fitowa suke daga ɗakin da ta buɗe ƙofar suna fitowa suka kalli gabas wato sun baiwa ɗakin baya tana shiga ta kulle ƙofar sai da ta tabbatar basa gano ta sannan ta ɗaga micijin robar da ta tsinto a wannan gidan da ƴan kidnapping suka ɗauketa, lokacin tana ta zagayawa a cikin gidan ta ganshi, da farko ita ma ta tsorata amma daga baya sai ta gane ba na gaske bane saboda matuƙar dai baka taɓa shi ba ba za ka gane ba haka yake kamar micijin gaske sai ka taɓa za ka ji wani latsotso kamar wata leda mai laushi amma ba roba bane.
dan haka sai ka ɗaga wajen cikinsa a nan ne tillar da ake hura micijin take a rufe da murfinta, dan haka da sauri Inna ta buɗe tillar ta sace micijin ta linke ta mayar ɗan tofinta ta zige zip ɗin. Dama tun lokaci da ta gani a gidan ta ɗakko dan idan ta koma ƙauyensu take hurawa tana tsorata Tasalla, to ganin ranar nan daga fitowarta ana sace ta a matsayin wata dan haka ta ce yanzu duk inda za ta je da shirin ko ta kwana za take tafiya saboda tsaro ba dan tsoro ba. Shi yasa ma ta taho da ƙaiƙayinta mai barkono da ya daɗe a ajiye a jakarta ashe kuwa da walakin goro a miya sai gashi sojojo ya sa an ɗakko ta sai ta yi amfani da su ta dan ceton kan ta gashi kuwa sun mata rana.
Sai da ta tabbatar ta gama ta ce su shigo su gani, ai daga window ma suka leƙa dan a tsorace suke, ganin babu micijin babu dalilinsa sai suka ƙara shan jinin jikjnsu.
Haka ta ce sai abokin Imran ne ma zai kai ta gida haka ya shiga ya sako kayansa babu yadda ya iya ya buɗewa Inna mota ta shiga ya rufe kamar yadda ta buƙata. A hanya ma haka ta sa ya tsaya ta rinƙa sa shi siyayya ta babu gaira babu dalili har sai da ya ji ya yi da na sanin, sanin Imran ma ba ma da na sanin ɗakko ta kaɗai ba, har ƙofar gida ya kawo ta, ta ce ya shiga su gaisa da su Sadiya ya ce mata a’a .
“To sojojo ka gaishe da matarka tsohuwa mai shafa jambaki kamar akuya ta ci dusa” Cewar Inna da ke tsaye riƙe da ledoji hagu da dama riƙi-riƙe da kayan siyayyarta. Wani kallon takaici ya mata ganin sai dariya take ya ja motar ya bar wurin a sukwane.
” Sai ni Azumin Malam wallahi ni gaba ta kai ni gobarar titi” Cewar Inna tana juyawa ta shige gida abin ta.
Masu fitar mn littafi ku ji tsoron Allah, da tsoron haƙƙina.
09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
3️4️⃣7️⃣➡️4️⃣8️⃣
*TASALLA*
Gabɗaya ta kasa zaune ta kasa tsaye saboda tsananin murnar tafiya birni suna, sunan da ba a san da zuwanta ba kyma ba wai shiri suke dz wacce za ta je sunan domin ta bane kawai dai ƙarfin hali ne ɓarawo da sallama. Tun da aka ce yau alhamis take ta shirye shirye saboda Tsahare ta faɗa mata cewar da sassafe za su tafi sunan wato ranar sunan kenan ranar juma’a. Kuɗaɗe masu yawa ta karɓa a wajen Malam dan ta ce masa kar a je suna babu wani abin a zo a gani dan jaka ta yaudareshi kuɗaɗen da suka fi wanda za ta yi amfani da su yawa.
Fura dakan mai ta ce za a yi, ta sha sugar da man shanu dan haka hatsi ta auna ta bayar da duk abubuwan buƙata na aikin furar da ladan masu yin furar dan akwai gidan da ake yin furar in mutum yana so sai ya biya a masa. Galan kuwa ta samu ta ɗure nono a ciki wanda za a kai gidan sunan haɗe da furar duk tana yin hakan ne dan kar Inna Azumi ta kunya tata, tana ganin in ta je da ɗan abin arziƙi ko ma menene zai zo da sauƙi.
Ƙafar nan ta sha ƙunshi kamar ba gobe sosai lallan ya kama aka ɗauki wani baƙin gishirin ƙunshi aka sanya, ga ta tanadi kayan da za ta saka idan za su tafi da kuma wanda za a ta sa ranar da za su dawo washe garin suna duk da ba haka ta so ba da son samu ne ta fi so ta zauna ta taya Inna ZAMAN WANKAN ita ma ta ɗan murmure sannan idan Innar ra tashi dawo wa sai su dawo tare . A ɓangaren Malam ma murna yake da tafiyar da Tasalla za su yi zuwa suna saboda yana ganin wannan ne abin da zai shirya tsakaninsu, yana kuma addu’ar Allah haɗa kawunan su komai ya zo ƙarshe a tsakaninsu na rashin jituwa.
Hakan ne ya sa Malam yake bada duk abin da ta buƙata kuma shi daɗi yake ji da ya ga tana murna, dan da abin har haushi yake bashi yawan fitar ta zuwa gidan Tsahare wani lokacin ma baya sanin ta fita sai ta dawo idan ya tambaya daga ina take sai ta ce ta je tambayo Tsahare ne ya shirye shiryen tafiya, ko gajiya bata yi da zuwa gidan Tsahare zancen tafiyarsu dan idan ana maganar tafiyar ba ƙaramin daɗi take ji ba, duk ta bi ta bama yaɗawa cewa za su tafi birni. Dan haka yanzu komai ya haɗu gobe kawai ake jira a ɗau hanyar Kano suna.
*INNA*
Tun bayan da ta dawo Sadiya ta gan ta da kaya riƙi -riƙe lokacin suna zaune da Imran dan har magriba ma ta kusa yi, haka ta shigo da ledojinta tana ta washe haƙora bakinta ɗauke da sallama
amsa mata suka yi kowa na kallon hannunta da mamaki, haka ta shigo ta zauna abinta tana ta fito da kayayyaki tana washe baki.
“Inna ina kika samu wannan kayan?” Cewar Sadiya tana kallon Inna da mamaki.
“Kai haba Sa’adiyya wannan tambaya ina dalili sai ka ce wata budurwa tsofai-tsofai da ni ki zauna kina mini tambayoyi kamar wata budurwa, yo Allah na tuba ai budurwa ya kamata a yiwa wannan tambayar in an ganta da wasu baƙin kaya a tare da ita, dan gudun kar ta ɓaci amma tsohuwa da ni kike min tambayar ƙwaƙwa” Cewar Inna tana kallon Sadiya tare da maida kallonta kan Imran ta ce.
“Ko ba haka ba Imirana, ai gaskiya na faɗa ko?” Cewar Inna tana kallonsa.
Haɗe rai ya yi ya kauda kai gefe.
“Ikon Allah ni ma mai ya kaini tambayarka dan na san ko dai dai na faɗa ba zaka faɗi gaskiya ba uban mugun halin tsiya haushi kake ji na baiwa Abida labarinka to ya za ka yi da ni ai ni na ci dubu sai ceto” Ta faɗa tana cigaba da fito da kayayyakin.
“Wai dan Allah Inna wa ya baki kayan nan, ranar nan kin ce wanda suka ɗauke ki ne suka baki yau kuka fa”
“Oh ni Azumi na ga ta kaina, yanzu Halima dole sai kin tambaya saboda niyya, to yau ɗin ma ɗaukeni aka yi” Ta faɗa hankali kwance.
“Haba Inna kullum dai kika fita sai an ɗauke ki sai ka ce kuɗi”
“Ke dalla can yau sojojo ne abokin Imirana ya aiko sojoji suka ɗauke ni a mota suka kai masa ni, shi ne na yi yadda na yi na ƙwato kaina”
Gabaɗaya kallonta suke da mamaki sun san sai tabbas Inna babu yadda za a yi ta haɗa wannan maganar”
“Wai da gaske Inna” Cewar Sadiya tana kafe ta da ido shi ma Imran ɗin kallonta yake.
“Yo ƙarya zan miki ɗiyar nan wallahi da gaske, aikuwa sun ga tijara gaba da gabanta aljani ya taka wuta, hummm ai ni Azumi an buga an barni”
Nan Inna ta kwashe labari kaf ta faɗa musu, daga Sadiyar har Imran ɗin dariya suke yadda Inna ta yi wasa da hankalin sojojin kaɗai ya isa ya baka dariya, basu sha dariya sosai ba sai da ta fito da micijin nan ta hura ta ajiye shi suka yi ta dariya suna jinjina ƙoƙari da kuma ƙarfin hali irin na Inna.
Tun da aka yi sallar isha’i Inna ta kwaɓa lallenta dan ta ce da shi za ta kwana a ƙafarta dan ya kama sosai. Haka ta jiƙa lallen ta tanadi ledoji tana ta rawar ƙafa za ta yi ƙunshi gobe suna. Bayan ta kwaɓa lallen suna zaune da Sadiya suna ɗan taɓa hira Imran ya fita lokacin, Inna ta kalli Sadiya ta ce.
“Ke yanzu Sa’adiyya ina iliminki na mahammadiyya a ce kina da ilimin addini amma kin bari ana kawo miki Malamin da bashi da wani ilimi gida duk da dai ba da son ranki aka kawo shi ba, ai kamata ya yi ki zauna ki tofe ɗanki da addu,’a dan matsawar yaron nan yana siffar miciji to kuwa ƙwara ma ki haƙura da taron sunan dan duk wanda ya ganshi to tsoro zai sa ya gudu wasu ma ko tunkaro gidan ba za su yi ba.
” Cewar Inna tana kallon Sadiya da ta yi shiru tana saurarenta.
“Hakane Inna bari to na gani” Cewar Sadiya cikin sanyin murya, ta tashi ta ɗakko Hassan ɗin daga bedroom ta kawo shi falon inda suke. Gadon dama kawai ta ɗakko
Sadiya ta yi bismillah ta fara karanta ayatul kursiyyu, falaq da nas da sauran ayoyin kariya cikin hikima ta ubangiji tana cikin yi sai yaron ya fara sawaya a hankali a hankali da haka ya koma mutum sak, a take a wurin aka shiga bashi nono ya sha aka wankeshi aka musu shirin bacci.
Inna sai da za ta kwanta ta ƙunsa lallenta ta ƙulle da leda ta kwanta da shi.
*DARE*
Gari ya yi tsit baka jin komai sai haushin karnuka a sauran abubuwa. Imran da dama bakam ya yi babu alamar bacci ma a tare da shi ya tashi ya janyo ledar da ya shigo da ita ya ɓoye a ƙasan kujera ba tare da kowa ya sani ba. Kaya ne ya siya baƙaƙe riga da wando sai wata wacce ake ɗorawa daga sama wata buɗaɗɗiya haka ya sanya baƙaƙen kayan nan.
Sai da ya tabbatar ba ya jin motsin kowa sai tashin munsharin Inna da ke cika ɗakin. Cikin sanɗa ya ƙarasa ɗakin yana fara da addu:a kar a gano shi. Kan gadon ya tsaya ƙarewa kallo ta hasken wata ganin kowa baccinsa yake hakan ya sanya ya tabbatar har ya gama abin da zai Sadiya ba lallai ta tashi ba saboda nauyin baccin ta.
Inna da ke ta shararar baccinta na gajiya sai sakin munshari take abin ta, a hankali Imran ya yi dibarar cire mata bargon da ta rufa da shi dama ko fuskar bata rufe ba. Hannu ya kai jikin ƙafarta mai ƙunshi ya ɗan ja ƙafar shiru bata motsa ba har lokacin tana ta bacci tare da sakin munshari, ƙara jan ƙafar ya yi zuwa lokacin ta ɗan motsa cikin bacci ta ɗan janye ƙafar. Ganin bata tashi ba sai ya ƙara jan ɗaya ƙafar lokacin ne ta ɗan kai hannu ta doke inda take jin an taɓa amma idanunta a rufe suke. Duka Imran ya sakar mata ɗaɗe ai jin zafin dukan nan Inna sai gata a zaune tana rarraba ido. Kafin ta tantance abin da ke faruwa, da kuma waye wannan mai baƙin kayan Imran ya kausasa murya yadda ba za ta gane shi ba ya ce.
“A yau ne za ki koma ga Allah, za a tambayeki duk abin da kika aikata a duniya dan haka yanzu ranki ne kawai za a zare”
Wani uban bugawa ƙirjin Inna ya yi lokaci ɗaya gumi ya baibayeta, cikin tashin hankali cikinta ya bada ƙululuuuuu.
“Wayyo Allah na mala,ikan mutuwa ne, ni Azumi kenan kwanakina sun ƙare wayyo shikenan tafiya zan yi ko sunan ƴan biyun bana nan za a yi, gashi zan barwa Tasalla Malam” Cewar Inna a zuciyarta har lokacin gabanta na mugun bugawa.
Ba ƙaramin tsorata ta yi ba ganin Imran da baƙin kaya dan ƙafarsa ɗaya ya ɗora a kan gadon sai ya ɗan ranƙwafo tare da baza baƙar rigarsa hakan ya sanya Inna da ke a tsorace ta ga wani girmansa ƙiba da kuma faɗi. Gabaɗaya jikinta karkarwa yake dan a duniya Inna tana tsoran mutuwa kuma a ce yau gata ga mala,ikan mutuwa zai ɗauki ranta, babu abin da ke ɗaga mata hankali sai kwanciyar kabari wannan abu yana matuƙar tada mata hankali idan ta tuna kenan yau ita ma za ta kwana cikin kabari, yau za ta tafi inda ba a dawo wa yau za ta tafi inda iyaye da kakanni suka tafi.
Hannu Imran ya miƙa wajen ƙafarta mai lalle. Inna da tunaninta ya bata cewa ranta zai zare bata san lokacin da ta haɗiye yawun da ya taru a bakint ba ta fara ƙoƙarin haɗa kalmomi sai kawai ji ta yi ta yi ƙarfin halin cewa.
“Da lalle a ƙafar, ƙunshi ne” Wai tunaninta idan ya ji da lalle ko za a ɗaga ɗaukan ran nata wataƙila ma ba ɗaukan ran mutum idan yana da ƙunshi, amma a tunaninta.
“Ba ma son magana ki koma ki kwanta ki miƙe” Cewar Imran a fili a zuciyarsa kuma ya ce
“Ashe kina tsoron mutuwa to kuwa yau sai na tsurar da ke gabaɗaya kamar ydda kike surar da ni ki tsoratar da ni ki sani cikin bala’i da miciji”
Jirif kake ji Inna ta koma ta kwanta jikinta gabaɗaya ya saki, tana zazzare ido sai hawaye da ya fara kwaranya daga idanunta ganin ga ta ga Sadiya amma za a ɗauki ranta Sadiya bata sani ba. Ita kanta ji take kamar ta tashi ta gudu sai dai ta san ba a tserewa mutuwa duk inda ka je tana biye da kai ko yau ko gobe ko ɗazu ko yanzu ko anjima.
“Sa’adiyya gaki da nauyin bacci da na tada ki kin ga tafiyar kakarki Azumi mai ƙaunarki ina ƙaunarku Sa’adiyya ke da Asharofa da Malam amma zan tafi in barku fatana ake min addu’a bayan mutuwata” Cewar Inna a zuciyarta tana zubar da hawaye. Imran kuwa dariya ce ke neman ƙwace masa yadda yake ganin Inna na rarraba idanu ta saki jiki gabaɗaya ita ala dole mai mutuwa.
Ganin ya miƙo gannunsa sai jikinta ya fara karkarwa tana raya wa a ranta shikenan ita kuma tata ta ƙare shikenan ranta zai zare.
“Kai gwara dai ki miƙa hannu ki tashi Halima ai gwara dai a ce da wani a kusa da ke lokacin ɗaukan ranki lokacin da za ki bar duniya, oh ni Azumi duniya budurwar wawa duk ƙaunarka da duniya haka za ka koma ka barta to Allah kasa can ta fi nan” Cewar Inna a zuciyarta tana ƙoƙarin kai hannunta na hagu mai lalle wanda shi ne daga gefen da Sadiya ke kwance, tana ƙoƙarin miƙa hannunta kan Sadiya Imran ya lura sai da sauri ya ce.
“Ba a son motsi in ba haka ba za a zare miki ran da ƙarfi”
Da sauri Inna ta janye hannunta tana ta addu’a a ranta kar a zare mata rai da ƙarfi saboda ta san an ce fitar rai akwai azaba bare kuma a ce da ƙarfi.Hannu Imran yake miƙowa yana ƙoƙarin kai hannun jikin Inna ita kuma sai ɗan takure kan ta take tana ɗan ƙoƙarin matsawa ji take kamar ta tashi ta gudu sai dai ba dama.
Hannunsa ya miƙa ya kamo hannunta na dama saitin dantsen ta ya riƙe gam sai ya sanya ɗaya hannun ya kamo yatsanta na tsakiya, ai gabaɗaya sai Inna ta fara wata karkarwa, karkarwa take gifgifgif gadon har jijjigawa yake ita ala dole an zo mawar zare mata rai.
“La’ilaha illalahu, muhammadur rasukullahi, S.A.W” Cewar Inna tana kuka gabaɗaya ta sanya a ranta shikenan ita da duniya kuma an yi ban kwana tana ta fatan ta samu dacewa a can.
Wannan karkarwar da take da salatin da take ita ala dole shirin ɗaukan ranta ne da ake take yi dakyar Imran ya iya danne dariyarsa saboda bai taɓa ganin Inna ta shiga ɗimuwa da tashin hankali haka ba ya so akwai haske yadda zai ke ƙare mata kallo amma ina.
“Kai ni Azumi ashe haka tafiyar za ta zo, ashe haka mutuwa za ta zo mini ban shirya ba, duk da dai dama babu wanda yake mata shiri haka kowa ke tsintar kansa haka take zuwa ba sanarwa bare sallama, Allah sarki ni Azumi ko wasiyya ban bayar ba, shikenan sai tafiya mutuwa haka take zuwa shi ma tashin ƙiyama an ce haka zai zo bagatatan” Cewar Inna tana runtse idanunta hawaye na kwaranya.
“Saura sati biyu ne ashe ba yau bane dan haka ki rufe idanunki sai kin daɗe sannan za ki buɗe” Ya katse wa Inna zancen zucin ta.
“Allah na gode maka ai har na bayar sa wasiyya in nemi yafiyar jama’a” Cewar Inna a zuciyarta.
“Kuma ba a baiwa kowa labari ki ja bakin ki ki yi shiru”.
“Bakina ƙanin ƙafata” Cewar Inna cikin rawar murya.
Ai Inna da ta rufe idanunta gam, ko alamar ɗagawa bata yi ba, har Imran ya lallaɓa ya tsugunna ya fice daga ɗakin da rarrafe amma Inna ko fitarsa bata ji ba. Har lokacin gabanta bai daina faɗuwa ba jikinta kuma bai bar karkarwa ba, sai da ta kwashe tsawon awa guda sannan ta miƙa hannunta na dama ta taɓo hancinta jin iska na fita daga hancin ta tabbatar bata mutu ba a hankali ta shiga buɗe idanunta cike da tsoro tana so ta tashi Sadiya ta faɗa mata sai dai tana tsoro kuma an ce kar ta faɗawa kowa.
*IMRAN*
Tun da ya fito daga ɗakin ya dawo falo ya cire kayan ya maida wanda ya cire ya sanya su a ledarsu ya mayar ƙasan kujera ya ajiye yana so da asuba sai ya fice da su in zashi masallaci. Tun da ya kwanta yake ta dariya ƙasa-ƙasa ba abin da je bashi dariya irin yadda idanun Inna suka yi ƙulu-ƙulu ita ala dole za ta mutu, ga karkarwar da jikinta ke yi kamar mazari shi kaɗai ya isa ya sanya cikinka ya yi ciwo saboda dariya.
“Ko a ina ta taɓa jin mala’ikan mutuwa yana manta wa’adin mutum har ya zo ɗaukan ran mutum amma kuma ya fasa ya ce sai wani lokacin, har ya faɗa maka lokacin ka.
“Kai ruɗani bai yi ba wallahi” Ya faɗa yana ƙyalƙyala dariya a ɓoye.
Tun da ta buɗe idon nata ta ji wani fitsari ya cika mata mara, ga tsoro da fargaba duk sun tarar mata sai kuma karkarwar da take. Jin fitsarin na neman zubowa ta ƙoƙarta ta tashi zaune ta fara kiciniyar sakkowa daga kan gadon saboda gabaɗaya bata gama dawo wa dai dai ba. Da dibara ta sakko daga gadon amma ko ta kan ƙunshin ƙafarta bata bi ba dama tun lokacin da Imran ya ja ƙafarta ta haɗe ƙafafun waje ɗaya duk ta caɓe lallen amma ba ta shi take ba, ita dai yanzu burinta ta yi fitsarin. Haka ta tako da ƙafafunta tana jin yadda lallan ke mata santsi a ƙafarta duk ta take shi lallan da ta ci uban buri a kan sa za ta yi ƙunshin fita kunya da suna, lallan da ta taho da shi tun daga garinsu amma kuma gashi za ta ɓata shi a banza, lallan da ta yiwa mai ƙunshin nan kuri cewa ya fi wanda take ƙunsawa su Ashrof kyau amma sai gashi abu ya zo mata a hautsine, dan tun da ta ga mala’ikam mutuwa ya zo ɗaukan ranta duk da bai ɗaukan ba, sai ta ji duniyar ta fice mata a rai komai na duniyar ya ginshe ta. A haka ta taho ko fitilar ɗakin bata kunna ba saboda tana ƙiyasta, da an ɗauki ranta da gobe da safe za a sanya ta a kabari duhun kabari kuwa ya fi na duniya sai dai fatan Allah rabamu da shi.
Haka ta fito tana taka ƙafarta dakyar dan duk ta yi sanyi, ko kallon inda Imran yake kwance bata yi ba ta zo ta wuce, shi kuwa yana kallonta har wani ɗan doro ta yi. Inna kuwa ko takalmi bata tsaya sakawa ba dama ga ledar lallan a ƙafar sai kawai ta tafi bayin a haka tana gama fitsarin ta yi tsarki ta fito, ledar lallan ta fusge ta watsar ta ƙarasa ta kunna famfo ta wanke ƙafar bata damu da ganin ko ya kama ƙunshin nata ba ko kuma ganin ya caɓe ita ba wannan ne a gabanta ba ita da za ta bar duniyar ma baki ɗaya nan da sati biyu to menene na damuwa da ƙafar da ta kusa komawa cikin ƙasa.Imran yana kallonta ta dawo ta shige ɗaki abinta jim kaɗan sai ya ganta ta kunna fitilar wayarta ta fito ɗauke da bargonta tana sanɗa, haka ta zo ta cikuikuya bargon ta saka a jakarta ta ɗakko sallayarta da hijabi a kan kujera su ma ta cusa su a ciki ta ɗakko mayafinta a kan kujera ta cusa ta ɗakko takalminta a ƙofar ɗaki ta cusa ta zige jakar. Duk abin da take Imran na kallonta kuma ya fahimci mai take shirin yi.
Sai da ta gama ta janyo jakarta a hankali.
“Wallahi guduwa zan yi daga gidan nan, na fasa ZAMAN WANKAN ƙwara in koma in mutu a ɗakina, na gwammace mutuwa ta ɗauke ni a ɗakin mijina a kan ta ɗauke ni a wani waje da ban, ƙwara in koma gida in roƙi yafiyar Malam dan dama ina zargin kamar ba da zuciya ɗaya ya barni na taho ba, dan tun da na zo birnin nan abubuwa suke faruwa da ni daga wannan sai wancan” Cewar Inna a zuciyarta tana sanya hannu ta share hawaye duk Imran yana kallonta. Sai da ta kai jakar ƙofar ɗaki ta dawo ta shige bedroom yana kallonta tana haske -haske a ɗakin da alama Sadiya da su Hassan take yiwa kallon ban kwana.
“Sa’adiyya ki yafe min na zo gidanki na hana ki sakat da sakewa da mijinki yau zan bar muku gidan ma baki ɗaya ko ma mai zai yi Imiranan ya je ya yi in ma kin samu wani cikin kin yi ciki da goyo Allah ne ya baki, kuma shi zai taya ki riƙonsu domin Allah ba ya ɗorawa bawa abin da ba zai iya ba Allah raya miki tagwayenki da ma wanda za su zo nan gaba na san wannan ne haɗuwarmu ta ƙarshe sai kuma in kin je jana’iza ta, ba zan iya tashinki daga bacci ba ki hana ni tafiya guduwa zan yi in ya so in kwana a tashar mota da asuba in samu mota in tafi gida. Kai ma Hassan ka yafe min saboda na maidaka abin zolayata kowa ya yafe min sai wata rana” Cewar Inna a hankali yadda ba za ta tashi Sadiya ba.
Duk abin da take faɗa Imran ya kasa kunne yana jiyo wa, sai da ta gama sai gata ta fito ta zo saitin katifarsa ta tsaya.
“To Imirana abokin karawata ka yafe min na tafi na bar maka gidanka da iyalinka Allah baku zama lafiya ya kaɗe fitina, in an samu labarin mutuwata nan da sati biyu a je jana’iza a min addu’ar samun dacewa mu tamu ta ƙare za mu tafi inda Baban Halima da su uwata mai daddawa da mai barkono suka tafi” Ta faɗa muryarta na karkarwa tare da juyawa ta nufi ƙofar ɗaki inda jakarta take duk Imran na ganinta.
Jakar tata ta kinkima dakyar ta ɗora a kan ta, sosai abin ya baiwa Imran dariya haka ta fara tafiya dakyar ga sanyin jikinta ga nauyin jakarta ga hawaye yana zuba ta nufi zauren ƙofar gida.
“Ai yadda kika hana ni tafiya lokacin da na tsinci kaina cikin tashin hankali zan bi Hajiyata haka ke ma za ki dawo ki zauna” Cewar Imran ya tashi da sauri ya kunna fitilar falo da ta tsakar gida, Inna da ta kama jamlock ta cire ta fara buɗe a hankali, ta ga hasken fitilar ya mamaye tsakar gidan, da sauri ta fasa buɗe ƙofar dan kar a ganta ta dakata dan ta sa wataƙila Imran ne ya tashi fitsari ƙwara idan ya koma ya kwanta bacci ya ɗauke shi sai ta tafi. Imran fitowa ya yi ya fara sa takalmi Inna tana jinsa, ƙofar da ta cirewa jamlock ta ja ta bata gama buɗewa ba ce ta yi ƙara.
“Shikenan Imirana zai ganni” Ta faɗa a zuciyarta.
“Waye a nan? Waye a zaure?” Cewar Imran cikin maida muryarsa irin ta masu bacci ya nufi zauren.
“To Imirana an falka” Cewar Inna tana wayancewa.
“Inna lafiya ina zaki da daren nan?” Cewar Imran yana haske Inna da fitilar wayarsa da ya fito da ita, ganinta ya yi ta yi hirim da uwar jaka a ka, wata dariya ce ta kusa kufce masa amma sai ya maje.
“Kai dai bari Imirana wai da yau kwanan tashar mota zan yi saboda murna”
“Murna kuma?”
“Eh mana murnar tarɓar aminiyata Tsahare shi ne zan je in kwana a tashar in jira zuwanta gobe dan na san da wuri za ta taho, sai mu taho tare duk da ta san gidan dan kar ta yi ɓatan kai”
“Kuma da tsohon daren nan sannan kuma har da jakarki za ki je taryen nata?”
“Eh, eh, eh mana”
“A’a Inna ki dai bari sai gobe kya je” Ya faɗa yana ƙarasawa ya rufe ƙofar ya maida jamlock ɗin, yana yaƙi da bakinsa kar ya kunya ta shi ta hanyar dariya dan gabaɗaya Inna tana cikin yanayin da dole sai ka yi dariya.
“Haba Imirana ya da haka kuma, ya za ka shiga tsakani na da burina, za ka shiga tsakani na da tuba na, ya za ka shiga tsakani na da mutuwa a ɗakin mijina” Cewar Inna a zuciyarta tana jin kamar ta saki kuka ko ta samu sassauci.
“Ai fita cikin dare haɗari ne ga karnuka gashi baki san da wa za ki haɗu ba a hanya duniyar nan da ta ƙi daɗi ki je ma masu yankan kai su ɗauke ki su yi watanda da namanki” Cewar Imran yana kallon Inna da ta turɓune fuska.
“To, to, to, to” Cewar Inna a fili da ke ta furta to, har babu adadi dan ji take kawai Imran ya gama da ita.
“Ko ban samu masu yin watanda da namana ba ai sha huɗun rana i ta yau na daɗe a ƙiyama, un ma gudun mutuwa ake” Ta faɗa a zuciyarta.
“Yawwa ko ke fa, kawo jakar taki” Cewar Imran yana miƙa hannu ya saukewa Inna jakar daga kanta. Haka ta barshi ya sauke jakar ba dan ta so ba haka ya juyo cikin gidan da jakar a hannunsa tana jin kamar ta juya ta buɗe ƙofar ta gudu ta bar masa jakar.
“Shiga gaba mana Inna ai kamar ba girmamawa in barki a baya” Cewar Imran yana matsawa gefe Inna ta wuce gaba ba dan ranta ya so ba, sai dan babu yadda za ta yi kuma ma bata son yin hayaniya dan tana ganin kwananta ya kusa ƙarewa bata da lokacin ɓatawa.
Haka ta shige falon jiki sanyi ƙalau. Imran kuwa sai da ya tsaya ya ɗan matse dariyarsa sannan ya shigo ɗauke da jakar Inna ya ajiyeta a inda take ajiyewa. Kallonta ya yi ya ga ta zauna a ƙasa ta rafka uban tagumi.
“To Inna ya ga kujera kuma za ki zauna a ƙasa?”
“Yo ai da na ga ƙarshen alewa ƙasa”
“Kamar ya Inna?”
“Yo duk mai rai mamaci ne kuma dai da ƙasa aka halicce mu kuma cikinta za mu koma sannan daga cikinta za a ƙara fito damu” Cewar Inna tana tuna nan da kwana goma sha huɗu tana cikin ƙasa hakan ya sanya ta share hawayenta tana jin bata da wani abu da ya wuce ta cigaba da kusanta kan ta ga Allah har ranar da mutuwarta za ta riske ta.
” To Inna ai kowa ya san da hakan amma ai manzo S.A.W ya ce, ka zauna a cikin duniya kamar matafiyi, sai hakan hakan ba yana nufin ka bar komai na jin daɗin duniyar ba” Ya faɗa yana kallonta sai ya ji duk tausayinta ya kama shi.
“To haka ne Allah dai ya sa mutuwa ta zame mana hutu, Allah sa mala’ika mutuwa ya zare ranmu a hankali, Allah raba mu da duhun kabari, azabar kabari nauyin ƙasa ya bamu ikon amsa tambayoyin kabari ya sanya aljanna maɗaukakiya ta zame mana makoma kuma madawwama” Cewar Inna cikin sanyin murya.
“Amin dan alfarmar annabi da alqur:ani” Cewar Imran yana neman wuri ya zauna a kan katifarsa.
“Amma Inna ki tashi ki koma ki kwanta mana tun da yanzu fa dare ne”
“Ina ni ina runtsawa Imirana ai sai dai ko na tashi na rinƙa nafilfili har asuba ta yi sallar asuba sai na zauna lazimi har garin Allah ya waye”
“To ikon Allah abu mai kyau gaskiya hakan ma ya yi Inna Allah dai ya ja da kwana ya sa ki yi tsawon rai dan ki yi ibada mai yawa”
“Kayya Imirana ni da wa’adina ya kusa cika ina zancen dogon kwana sai dai a ce Allah sa mu cika da kalmar shahada”
“Wa’adinki ya kusa Inna ta yaya aka yi kika sani kuma?”
“Uhmm da wasa nake kasan ɗan adam ana so ko yaushe ya kasance cikin shirin tafiya, in ya wayi gari ya sanya a ransa ba zai kai yammaci ba in ya kai yammaci ya sa a ransa ba zai wayi gari ba haka ne kawai ya sa na faɗi hakan” Cewar Inna cikin wayincewa dan ta ga ta kusa yin ɓaran ɓarama sai kuma ta tuna mala’ikan ya gargaɗeta.
“Eh kuma fa haka ne”
“Bata sake tanka masa ba ta fita ta ɗauro alwala dan bata so ma zuciyarta ta cigaba da kissima mata dalilin sakkowar Imran har yana biya ta suna magana yana kuma nuna mata kulawa da tausayawa, ga sakin fuska, dan ita yanzu ta kanta take bata ma so ta fara tunanin wani abu ita da za ta bar duniyar ma dan me za ta damu kanta. Haka ta zo ta wuce ta ɗauki sallayarta da hijab a jakar ta nufi ɗaki.
“A sanya mu a addu’a Inna ” Cewar Imran yana dariyar zuci.
“To Imirana” Cewar Inna a fili a zuciyarta kuma ta ce.
“Yo ni ina ma na ga lokacin yiwa kowa addu’a yau ai yau kawai nafsi – nafsi, ta kai-ta kai, kaina kawai zan yi ta roƙawa gafara da neman dacewa a lahira”
09030283375
*MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
3️4️⃣9️⃣➡️5️⃣0️⃣
*LAST PAGE*😿😂
Barkanmu da kasancewa a ckn watan rahma watan ibadah RAMADAN MUBARAK😍
*RANAR SUNA*
Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, Tasalla dai yau yadda ta ga rana haka ta ga dare, dan gabaɗaya bacci ya kasa zuwar mata, tsaf ta nemesa ta rasa bacci ya ƙauracewa idanunta sai zumuɗi take d murnar a kan gari ya yi ya waye su ɗauki hanyar birni, tun kiran sallar farko ta tashi ta yi alwala ta zauna tana lazimi, ita kana murmushi sai ƙwace mata yake ita kaɗai ta san irin daɗin da take ji da irin farincikin da take ciki.
“Kai Allah da ikonsa komai sai Allah ya nufa shi yasa wasu ke cewa kishiya in alkairi ce Allah tabbatar da alkairi to ni dai gashi kishiya ta wani wajen ta zame mini alkairi tun da gashi sanadin kishiya (Buk ɗina, labarin yadda sanadin kishiya ta haɗu da ƙalubale gidan aurenta tun daga ranar da ta sanya ƙafarta a gidan aure ta fara arba da bala’i kala-kala har makancewa sai da ta yi sanadin kishiya) Duk da dai ta wani wajen Azumi ba kanwar lasa bace amma dai yau ta mini rana har da yammaci ma” Cewar Tasalla da ta tashi daga kan abin sallah tana linkewa da hijabinta.
Babu ɓata lokaci ta shiga wanka ta fito ta shiga shiryawa cikin atamfarta mai kyau, tana cikin sanya kwalli sai ga Malam ya shigo ɗakin nata daga masallaci yake, ganinta zaune da ƙaramin madubi a hannu tana gwale ido yake kallonta da mamaki, washe haƙora ta yi tana kallon Malam da ke mata kallon mamaki.
“Malam har an dawo daga masallacin”
“Eh na dawo” Ya faɗa yana kallon wani jambaki sabo da ta fito dashi daga wata baƙar leda ta daddage za ta shafa.
“Tasalla menene hakan kike yi dan Allah” Cewar Malam yana kallonta.
“Wai a ina ?” Ta faɗa tana kallonsa.
“Wannan ba gazar bane da yara ke sanyawa?”
“Au wai wannan? Ba gazar bane Malam jambaki ake ce masa fa”
“Ko ma dai menene, ba dai sawa za ki yi ba”
“Shafawa zan yi mana Malam, saƙo na yi kasuwa aka siyo mini saboda na shafa, ko so kake in tafi birni suna dangin kishiya ake nuna ni da baki ana gulmata ko kwalliya ban iya ba bare kuma dama Azumi da ke min kallon ban taɓa zuwa birni ba ta faɗa musu cewa babu abin da ma iya wallahi ba zan juri baƙinciki ba gwara dai na cancaɗa adona da kwalliya yadda babu mai mini kallon raini alqur’an”
Ta faɗa tana wani shafa jambakin tare da haɗe laɓɓanta waje ɗaya ta daidaita jambakin.
“Ni na ga ikon Allah saboda zuwa birnin ne za ki shafa gazar da girmanki da komai tsofe-tsofe da ke saboda gudun magana za ki shafa, kuma ma da kike cewa Azumi za ta faɗa musu magana a kan ki bake kika ce mini ita ta gayyaceki ba, kin ga Tasalla wallahi bana son tashin hankali kar fa ku je cikin mutane kuke raba jaha ke da ita ij kin san da matsala kamar kullum kawai ki yi zamanki dan ni ba na son haɗin gurugudu”
Wani uban bugawa ƙirjin Tasalla ya yi da ƙarfi jin Malam zai shiga tsakaninta da burinta na zuwa birni, sai yanzu ta gane ɓaran ɓaramar da ta yi na cewa Azumi za ta faɗi magana a kan ta ai da sauri ta washe bakin nan na tsohuwa da ya sha jambaki ta ce.
‘Allah sarki Malam ni fa ba haka nake nufi ba ka dan san mu mata ba ma rabuwa da gutsuri tsoma dole dai idan aka haɗu a gidan suna ko biki sai an yi da mutum tun daga suturar da ya saka zuwa kwalliyar da ya yi kai hatta tafiyar mace ma sai an saka ido musamman kuma aka ce maka kishiya ce ya je dangin kishiyarta to qur’ani hatta ƙasan zanen da ta saka sai an duba an ga wace irin atamfa ce ko leshi shi yasa ka ga na faɗi hakan, kuma jambaki da na shafa ai ba haramun bane ko Malam, in kuma kana ganin na goge sai na goge, dama na siya ne dan kar a kawo maka raini”
“A kawo mini raini?”
“Eh mana wallahi idan ban gyara jikina ba na fito fes muna zuwa za a ke cewa baka adalci a tsakanin matanka banbanci kake nunawa a tsakaninmu wata tafi wata a wurinka” Ta faɗa cikin sanyin murya tana wani karkata kai kamar ƙadangaruwa ita a dole kissa.
“Kuma fa haka ne da gaskiyarki to in kwa haka ne ki gyara abinki fes ki fito ɗoɗar da ke” Cewar Malam yana washe baki dan yadda Tasalla ta yi magana da kissa sai ya ganta kamar Azumi dan ita ce mai irin wannan yanzu za ta sanya shi yin abin da bai yi niyya ba.
“Ka ce fa ai dama na ce bari in gwada yadda Azumi ke yi, dan ko ranar da za ta tafi birni ZAMAN WANKA haka ta shaƙe murya ta rinƙa karairaye murya har sai da ka barta ta tafi, shi yasa na ce ni ma yau dai bari na gwada sa’a ta” Ta faɗa a zuciyarta tana wani jin ita ma yau ita ce.
” Aikuwa zan gyara ɗin dan ba na so a yiwa Malam ɗina kallon marar adalci a tsakanin iyalansa” Ta faɗa tana rufe fuska da tafin hannunta, alamar kunya wai ta ce Malam ɗinta. Shi kuma wani irin murmushi ne da dariya suka haɗe masa lokaci guda yana jin wani kansa na neman fashewa.
“Wayyo daɗi kasheni wahala ta huta, ashe dai ni ma da saurana a fannin soyayya ashe dai matata bata ganin tsufana take ce min Malam ɗinta duk da dama masana fannin so sun ce soyayya bata tsufa sai dai masu yinta su tsofe” Cewar Malam a zuciyarsa yana jin zuciyarsa fes.
Haka dai ta cigaba da shirinta ta shirya tsaf ta shafa turare ta ajiye bokitin da ta zuba fura a ciki da galan ɗin nonon da za ta kai gidan sunan. Tana gamawa lokacin Malam ya shiga ɗakinsa ta fito ta galgala wuta ta ɗora ɗumamen tuwo, tana ɗorawa kuwa ta barshi kafin ya yi zafi ta tafi gidan Tsahare tun daga nesa ta fara hango Tsahare tana haɗa kan ita ce a murhu ko wanka bata yi ba wani takaici ne ya cikata tana ji a ranta dama da a ce ta san birnij nan da tafiyarta za ta yi in ya so ita Tsaharen ta taho daga baya, dan ta ga aminiyarta ce Azumin shi yasa take mata wani jan aji.
Da sallama ta ƙaraso a bakinta kana kallon fuskarta za ka fahimci cewa ranta a ɓace yake. Amsa mata sallamar Tsahare ta yi ta ɗago daga sunkuyen da take tana ƙarewa Tasalla kalko. Babu inda ya ɗauki hankalinta haɗe da bata mamaki irin bakin Tasalla da ya sha jambaki gashi ta zana jagira da kwalli sai ka ce wata ƙaramar yarinya.
“Haba Tsahare wai ma baki shirya ba kuma na ga kina ƙoƙarin haɗa wuta ga wani ƙullin ƙosai a gefe in ce dai wata za ki barwa ta soya miki” Tasalla ta katsewa Tsahare tunanin mamakin da take na mai ya kai jambaki bakin Tasalla har da su jagira da girmanta da komai.
“Wai kamar ya wace irin magana kike haka, kawai dan zan tafi suna sai in kasa yin sana’ata shin kin manta ba a ƙafa za mu je ba kuɗin mota za mu biya daga nan ma zuwa tasha sai mun biya kuɗin machine, a can ma in an sauke mu sai mun hau adaidaita sahu, ga kuɗin gudunmuwa mutum ba ya je baƙiƙƙirin ba” Ta faɗa tana kallon ƙafar Tasalla da ta sha wani uban vasiline sanye da takalmi ɗan madina kore.
“Haba Tsahare yanzu dan wannan ne zaki yi sana’a yau so kike sai shinkafar da za a dafa ta suna ta ƙare bamu je ba gaskiya dai baki kyauta ba”
“Dan Allah ki rabu dani da wani zancen shinkafa yunwa za mu je, da za a ke tunanin shinkafar rabo, duk wannan abin da kike fa har yanzu a ƙarfe bakwai saura ake dan Allah ki koma gida duka ƙullin ma na kwano guda ne yanxu zan gama kinsan dai na kwano uku da rabi nake yi kullum”
“To ai shikenan ya na iya da abin da ya fi ƙarfina ni da ko hanyar ban sani ba ai dole na jira ki” Cewar Tasalla tana taɓe baki ta juya ta tafi.
Da kallo kawai Tsahare ta bi bayanta tana mamakin irin kwalliyar yaran da ta yi a fuskarta, gashi har yanxu ta kasa daina mamakin wai Azumi ce ya gayyaci Tasalla suna, dan ta san dai basa ga miciji da juna.
Sai wajen ƙarfe tara suka baro ƙauyen, zuwa lokacin sawun Tasalla ya fi biyar gidan Tsahare a kan ta yi ta shirya su tafi ƙarshe dai sai da suka yi faɗa a haka dai suka samu mashinan da suka kai su Garki L.G inda suka samu motar Kano suka hau. Tun da aka fara tafiya bakin Tasalla bai rufu ba ta ce wannan ta ce wancan tun Tsahare na biya ta har ta gaji ta yi shiru dan ta ga abin nata ba na ƙare bane, kuma kamar ma duk murna da zazzaɗin zuwa birnin ne ya sanya bakinta ya ƙi rufuwa. Tun da motar ta shigo garin Kano ta dabo tunbin giwa sai kuma gabaɗaya Tasalla ta ruɗe bakinta ko rufuwa ba ya yi ta sake shi galala saboda kallon motoci da kuma gine-gine kai ba ma su kaɗai ba hatta mutanen da ta gani masu yawa kowa yana harkar gabansa suj zame mata TV saboda ita bata taɓa zuwa gari kamar Kano ba iyakacinta ƙauyukan wajejensu kawai.
Tsahare da ta ɗauke kanta ta mayar gefe daga kallon Tasalla saboda nune -nune abubuwa da ta dame ta da su, ta ji Tasalla ta saki kuka cikin sauri ta waiwayo wajenta take tambayarta dalili dan har lokacin fa basu sauka daga mota ba kawai dai sun shigo garin Kano ne, motar tana tafiya zuwa tasha ne dan ta sauke lodi.
“Dole na yi kuka Tsahare wallahi dole na yi kuka, kawai ki barni kar ma ki baiwa kan ki wahala wajen lallashina dan ba shiru ba zan yi sai na yi mai isata na ji zuciyata ta yi sanyi”
“To ikon Allah” Cewar wasu daga cikin motar da suka haɗa baki wajen faɗa.
“Haba ke kuwa baiwar Allah ana zaune ƙalaw muna murna Allah ya kawo mu lafiya saura mu sauka, kawai za ki fashe da kuka kuma ki ce wai ba za ki saurara ba sai ka ce wata ƙaramar yarinya, kuma mu babu wanda ya ga kin ɗaga waya bare a ce ko mutuwa aka faɗa miki” Cewar wani mutum da ke gefe.
“Wallahi bawan Allah ba mutuwa aka faɗa mini ba, kawai takaici ne na abin da ka mini, ni nan da kake gani ina da shanaye da dabobi da nake kiwo ina dai da abin hannuna amma a ce a duniya akwai gari ya Kano amma ban taɓa zuwa ba? Kuma ko bani da kowa a Kano wallahi da na san haka take da ko iya tasha ne na biya kuɗi na zo na ga gari na koma amma aka barni a can ƙauye a garƙame, kuma dan baƙin hali irin na kishiyata, bata taɓa gayyata ta garin nan ba wajen ƴan uwanta ai ko, dan na kashe ƙwarƙwatar idona a faɗa min Kano haka take”
Gabaɗaya motar dariya aka kwashe da ita kowa yana jin abin da Tasalla ke faɗa sai ya yi dariya, abin nasu sai ya sosa mata rai dan haka ta ɗauke kan ta gefe ta cigaba da baiwa idonta nama. Kowa ya fita daga motar Tasalla kuwa tun da ta fito sai idanunta suka kasa samun matsaya ta kalli can ta kalli nan, da yake bakin titi aka sauke su a tashar ba a shiga cikin tasha ba. Sosai Tsahare ta yi da na sanin zuwa da Tasalla saboda babu abin d take sai kalle-kalle, a haka dai ta samu dakyar ta tsayar musu da ɗan sahu suka shiga suka nufi gidan suna murna fal cikin Tasalla dan har lokacin ma a ɗan sahun kalle-kalle take.
“Taɓɗi shi yasa ashe ake cewa hankali shi ne gani wai wani ya je Kano bai ga mota ba, yo in ba haka irin motocin nan na garin Kano kwantsam kamar jamfa a jos duk da ban taɓa zuwa Jos ɗin ba, amma gaskiya yawan motocin Kano ya ɓaci yadda ka san ba mutane kaɗai ke hawa motocin ba har da aljannu” Cewar Tasalla da ke ta kalle -kalle. Daga Tsahare har ɗan sahun babu wanda ya tanka mata a haka suka cigaba da tafiya.
A daidai ƙofar gidan aka sauke su, suna sauka sai Tsahare t tsaya tana baiwa ɗan sahun kuɗinsa, Tasalla kwa dama ta biya shi, dan haka sai ta ɗan tsaya daga gefe take jiranta kusa da wasu mata guda biyu da ke ƙusƙus.
“Wallahi fa nake faɗa miki miciji sak Hassan ɗin ke zama ya yi ta firgita mutane, in kika ji irin uƙubar da mutanen gidan ke fuskanta za ki yi mamaki” Cewar ɗaya daga cikin matan da ke tsaye gefe, Tasalla da ke saurarensu cikinta ne ya bada wani ƙululuuuu ta fara zare ido a take ta ji gabaɗaya Kanon ma ta ginsheta ji take kamar ma kar ta shiga gidan.
“Ikon Allah shi kuma irin tashi baiwar kenan, to gaskiya dole mutane suke tsorata yo ina kai ina miciji”
“Himm ke dai bari kuma fa a haka suke kwana da shi ɗaki ɗaya har kakar mai jego kin jo sunanta Inna Azumi”
Ai sunan Azumi da aka ambata shi ya ƙara tabbatarwa Tasalla da jariran ƴan biyun da suka zo sunan ake.
“Mu je mana ga gidan fa kina gani mutane sai shige da fita suke ni wallahi na ƙosa na sanya amini a idanuna ” Cewar Tsahare tana kallon Tasalla da gabaɗaya jikinta ya yi sanyi ƙalaw kamar dai ba ita ce ta ishi mutane da surutu ba ɗazu.
“Kai ai ni unguwar ce duk sai na ji kaina yaba juyawa da alama mutanen ɓoye na ne ke son tashi shi yasa, idan kika sa ni a ɗan sahu za su maida ni tashar mota in koma gida” Cewar Tasalla dan duk son da take yiwa birni gabaɗaya ya fice mata a rai dan gabaɗaya hanjin cikinta ya hautsina.
“Ki koma gida kuma garin yaya wato sai da kika zo har ƙofar gida sannan tsoron mai zai je ya dawo ya zo miki, ai ni dama na san babu yadda za a yi Azumi ta ce ki zo sunan nan” Cewar Tsahare tana yiwa Tasalla wani kallo.
“Eh bata gayyace ni ba da Allah yi maza ki sama mini ɗan sahu ya maidani tasha” Cewar Tasalla dan gwara Tsahare ta ce mata komai a kan ta shiga gidan da miciji yake.
“Ai fa tun da kin riga kin zo to komai ta famjama fanjam jam” Cewar Tsahare tana kaɗa kan Tasalla suka tasarma cikin gidan.
*INNA*
Tun sanda ta fara nafilfilin nan ko hutawa bata yi haka take bari sai ta yi raka’a huɗu sannan ta sallame ta rinƙa jero addu’oi ta rinƙa kuka hawaye na zuba tana ta neman yafiyar ubangiji.
Haƙiƙa Inna tana cikin tashin hankali domin ba ƙaramin abu bane a ce ka san ranar mutuwarka duk da zai kasance za kake neman yafiya kafin lokacin amma tabbas za ka shiga tashin hankali, shi yasa yana daga cikin hikima ta ubangiji da ya ɓoyewa bayinsa sanin ranar mutuwarsu, da a ce kowa ya san ranar da wa’adinsa zai cika tabbas zai cigaba da rayuwa a cikin tashin hankali to wannan halin shi Inna ta shiga. Tana jin sanda Sadiya ta tashi tana shayar da yaranta da suka tashi amma ko ɗaga kai bata yi ta kalleta ba. Har sai da aka kira sallar asuba tana nan tana ibada amma kuma ko alamar bacci babu a idanunta dan gani take ita da ke shirin barin duniyar ma baki ɗaya to bata da wani lokacin jin daɗi a cikinta.
Haka ta tashi ta je ta tsaya a kan Imran tana kiran sunansa, ya tashi ya tafi masallaci Imran kuwa dama shi ma bai koma bacci ba dan gabaɗaya sai ya ji tausayin Inna har ma yana da na sanin mata abin da ya mata, dan tun lokacin da ya kama hannunta irin yadda ya ga ta rikice da kuma bayyanar tashin hankali a tare da ita shi yasa ma ya yi saurin cewa sai nan d sati biyu amma da niyyarsa sai ya dinga ja mata rai yadda za ta tsure sosai amma ganin ta tsorata sosai shi yasa ma ya ƙyaleta. Kuma yanzu yana tsoron ya fito ya faɗa mata gaskiya ido ya kuye da mujiya dan ya san Inna ba kanwar lasa bace dole za ta yi shirin ɗaukan fansa dan haka sai ya bar maganar a zuciyarsa yana fatan Allah sa ta saki ranta ta yi rayuwa cikin salama a kwanaki sha huɗun da yace za ta mutu duk da ya san da kamar wuya gurguwa da auren nesa amma yana fatan hakan.
Tana kiran sunansa sai alerm ɗin wayarsa ya shiga ƙara dan haka sai ya yi kamar ƙaran wayar ne ya tashe sa.
“Inna har kin tashi ke ma” Ya faɗa cikin sanyin murya dan duk da a gabansa take tana kiran sunansa amma in ta kirashi sau ɗaya sai ta ja carbin da ke hannunta bakinta ya motsa sannan za ta ƙara kiran nasa abin ya so bashi dariya sosai amma sai ya ji tausayin ya danne dariyar.
“Kayya Imirana ni dama ina nan ido biyu ai ban ko yi gyangyaɗi ba”
“Allah sarki Inna ki ce dai yau duk mun sha addu’a mun more?” Ya faɗa dan ya ɗan jata da hira ta saki ranta ko yaya ne dan ya ji daɗi dan yana ganin ya tauyeta, saboda ita duk abin da take masa na iya duniya ne ma’ana bata masa abin da zai nuna barinsa duniya ba duk da miciji ma abin halakarwa ne amma ya san daga an raba shi dashi to zai daina jin tsoro ita kuma y mat abin da a ko yaushe za ta kasance cikin tsoro mai tsanani.
“An muku kam ba laifi, fa kaina kaɗai name yiwa amma daga baya sai nake yi da sauran al’umma ma dan addu’ar da ka yi a jama’i tafi saurin karɓuwa a kan wacce ka yiwa kan ka kai kaɗai”
“Allah sarki Inna mun gode, bari na yi sallah a je a shigo da abin yanka na suna wanda tun ranar da kika zo kikr yi da bakin ki cewa ba a kawo ba” Cewar Imran lokacin da ya tashi yana ƴar dariya duk dan ya sanya Inna farinciki.
“To Imirana” Cewar Inna cikin halin ko in kula ɗin nan. Haka ta shige ɗaki ta barshi dan bata so ta yawaita magana lokacinta ya tafi a banza ba tare da ta yi istigfari ba.
Haka dai Imran ya yi shirin zuwa masallacin zuciyarsa duk ba daɗi bai taɓa jin ya yi da na sani ba a kan abin da yake yiwa Inna sai yau, duk da a da ya ɗauka cewa duk abin da ta masa sai ya rama har ma yana ikirarin ramuwar gayya ai tafi ta gayya zafi, amma kuma yau ya ji ba daɗi sosai. Yana dawo wa daga masallaci ya samu suna ɗan zantawa da Sadiya amma har lokacin carbinta yana hannunta, haka Inna ta fito dan ɗora ruwan wanka a lokacin ne kuma Imran ya ɗauki kayan nan da ya yi amfani da su ya ɓoye a drowersa kafin gari ya waye ya fice d su dga gidan.
“Wai ni Inna dama kin san bakya iya kwanciya da ƙunshi kika yi kika kwanta, kalli yadda kika ɓata ƙafarki ai dama baki yi ba da dai wannan caɓe ƙafar da kika yi, kuma gashi ya kama sosai sai dai gabaɗaya kin caɓe shi” Cewar Sadiya da za ta tafi ta shiga wanka tana kallon Inna da ke ajiye ruwan wankan za ta fara yiwa yaran wanka. Kallon ƙafar kawai Inna ta yi ta sauke wata ajiyar zuciya tana rayawa a ranta cewa ƙafar da saura kwana sha uku a binne ta a cikin ƙasa menene ma na damuwa da caɓewar kunshi. Sadiya jin Inna bata, bata amsa ba sai kawai ta kaɗa kanta ta fita dan ta lura Inna shiru ya fiye mata yau ko magana bata so ga babu walwala a tare da ita bare ma ita da ke murna aminiyarta za ta zo yau amma sai ta ga yau ko murna fa maganar Tsaharen ma bata yi kawai ko yaushe bakin motsi yake alamar tana karanta wani abu ta kasa gane dalilin yin hakan. Ta san halin Inna dai bakinta baya shiru baya rabuwa d abin faɗa amma kuma yau sai ta ga Innar ta canja mata.
Bayan Sadiya ta yi wankanta shirya abinta tsaf lokacin har Mama da Ashrof sun zo ga kuma ƴan uwan Mama duk sun fara zuwa haka zalika Hajiya ma da maƙotanta da wasu dga cikin danginta sun iso gidan dai sai san barka amma gida ya fara cika, kuma sai maganar miciji ta kwanta kamar ma babu ita dan kowa sai sabgar gabansa yake. Ashrof da Mama da Hajiya kai da duk wani wanda ya san Inna kawai mamakin ta yake yau dan akwai wasu daga cikin matan nan da suka zo ranar da aka musu ƙunshi ƴan uwan su Imran amma ganin Inna shiru yau su ma sun fahimci akwai damuwa a tare da ita kowa sai ya tambaya ko lafiya sai ta ce lafiya lau wasu dai sun danganta hakan da cewa ko wani abu ke damunta kuma bata so ta faɗa. Dan dakyar ma ta yi wanka ko shi ma sai da Sadiya ta matsa mata, ko da ta fito babu abin da ta shafa kawai atamfarta ta ɗauka ta sanya ta ɗaura ɗankwali ta ɗauki carbinta ta zauna a kan kujera take lazimi tana kallon shige da ficen mutane ana ta hada hadar yin abubuwan suna. Dan ko lokacin da aka shigo da raguna manya -manya guda biyu da tinkiyoyi su ma manya guda biyu Inna tana gani aka shigo da su, jim kaɗan aka fita da su aka dawo da su a yanke aka rataye amma ko ci kan ka inna bata ce ba. Imran ma lemuka katan uku ya siyo mata da cake irin mai biyun nan ƙanana guda hamsin dan ta yi farinciki ya ce ga kashinya ta rabawa wanda take so amma haka ta karɓa ta yi godiya da fatan alkairi ta ajiye amma ba wai dan ta ji abin ya birgeta ba sai dai kawai ita yanzu komai na duniyar ya fice a ranta tafi so kawai ta ganta a gidan mijinta hankalinta zai fi kwanciya.
Tana nan zaune kamar an ce ta ɗaga kai sai kawai ta hango aminiyarta Tsahare riƙe da kaya ta shigo, tabbas ta ji daɗi a ranta amma ba kamar yadda take zaton ji ba a baya.Kafin ta tantance sai kawai ta hango Tasalla da wani bokiti da galan da wata jakar kaya madaidaiciya a hannnunta. Ai Inna da ta wani ajiye carbi a gefe ta ji wani takaici ya turnuƙeta ai cikin hanzari ta tashi tsaye kafin ka ce kwabo ita ma bata tantance ba sai kawai ganinta ta yi a bakin ƙofa ta taho a fusace kamar kumurcin miciji.
“Yau ake yinta lallai Tasalla kin ga makwancina har ni za ki zo wa sunan jika ban gayyaceki ba? Ni saboda bana son ki raɓeni na fi so kullum hawainiyarki ta kiyayi rama ta shi yasa ko da bikin Halima ban gayyaceki ba amma shi ne yanzu saboda ƙoƙari faɗawa mijin baya tariya, kika ɗakko ƙafa kika zo, duk da cewa na san ruwa baya tsami banza, amma ki sani sara da sassaƙa bata hana gamji toho, kuma wallahi iya gani iya ƙyalewa, wannan abin da kika yi wayon a ci ne an kori kare daga gindin ɗinya, amma ki bar murna dan karenki zai kama zomo, amma duk da haka na san ba za a tambayi kalwa zaƙin miya ba sai dai a tambayi barkono a sha labari, tabbas yau allura za ta tono garma, domin kuwa ba wahalalle sai mai kwaɗayi, duk da kin cika burinki na zuwa birni dama hausawa sun ce buƙatar maje hajji sallah, amma yau zan nuna miki zafin nema baya kawo samu, kuma duk esnda ya ce wutar kara ta kwana tana ci, to tabbas bai yi bacci ba, Tasalla yau zan nuna miki wanda zai je sama ya taka leda to haƙiƙa ya ci ƙarfin tafiya!!!” Cewar Inna a zuciyarta lokacin da ta taho a fusace gadan -gadan ta iyo wajen Tasalla.Tasalla wacce dama gabaɗaya zuwa birni take da na sani duk da cewa da na sani ƙeya ce amma kuma ita babban tashin hankalinta micijin da aka ce akwai a cikin gidan wanda ta ji labari cewar ɗaya daga cikin tagwayen ne yake komawa, ga kuma hango Inna ta taso kamar wata kububuwa ya ƙara tada mata hankali wato dai bokitin furarta da galan ɗin nono da take sa rai za su kankaro mata mutunci a wajen kishiyarta ta ba haka bane dan kwata-kwata bata ga kyan wuri a kunnen jaka ba, shikenan yanzu Azumi za ta kunyata ta a cikin jama’a duk da ta wani ɓangaren tana jin ƙwara dai ta kwaɓe tsakaninta da Azumin ko ta samu damar barin gidan dan ta san dai in suka kwashi ƴan kallo to tabbas ko dan neman masalaha a ce ta koma inda ta fito, ita ma Tsaharen za ta bata goyon bayan hakan wanda ta ƙi bata a ƙofar gida dan da ta barta ma da tuni ta kai tasha ko da kuwa a ƙafa ne dan sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba, duk da ta san ba lallai ta iya zuwa ba sai dai za ta yi tambaya dan matambayi baya ɓata.
Tsahare ma ganin aminiyarta ta, ra doso su sai jikinta ya bata yau za a cancanre dan dama ta san da walakin goro a miya,dan ta san ko menene tsakanin Azumi da Tasalla to shigo-shigo ba zurfi ne, dan komai za a yi sai dai ya zamana bita da ƙulli ne dukan kabarin kishiya, dan dama ita ta san za a rina wai an saci zanen mahaukaciya. Inna kuwa da sai da ta zo dab da su sai zancen mala’ikan mutuwa ya faɗo mata na saura sati biyu ta mutu kuma dai yau ma tun da gari ya waye har ta ci kwana ɗayanta, saura sha uku, dan ita lokacin da ta hango Tasalla gabaɗaya sai ta ji wani kishi ya turnuƙeta a take ta sha’afa da halin da take ciki dan bata ma san lokacin data ajiye carbinta ba kawai dai ta ganta ta tunkaresu cikin zafin nama, amma tuno da mala’ikan mutuwa da kuma cewar in ma kishi take to wanda take kishin za ta mutu ta barshi da kishiyarta ta, ita tata ta kusa ƙarewa to ma menene na ɗaukan duniya da faɗi ita da za ta barta ma nan da kwana kaɗan.
Wani uban washe baki Inna ta yi na ƙarfin hali dan ita yanzu in ba larura ba bata ƙaunar ma a ga haƙorinta saboda ai wanda ke cikin farinciki shi ne zai yi dariya, amma kuma yanxu ya zama dole ta saki fuska da jama’a har ma da Tasalla dan an ce shimfiɗar fuska tafi ta tabarma kuma ta haka ne mutane za su yafe mata da mata addu’a in sun samu labarin mutuwarta, kuma wannan dama ce da za ta yi amfani da ita wajen gyara ma’amalarta da kishiyarta, wanda dama ya dace tun a baya hakan ya kasance dan ko da a ce mutum bai san ranar mutuwarsa ba to fa ya sani tabbas wannan ranar akwai lokacin da za ta zo ko ba daɗe ko ba jima sai kowa ya kwanta dama dan haka yana da kyau ka mu’amalanci mutane da mu’amala mai kyau, dan shaidar mutane ita ce ta ƙiyama, iya yabon da za a yiwa kyawawan halayenka iya yadda mutane suka ji daɗin mu’amalantarsu da ka yi ne, dan haka kyakkyawar mu’a mala tana da kyau.
“Gasu, gasu, sannunku da zuwa mutanen arziƙi sannunku da ɗabbaƙa zumunci ” Cewar Inna tana ƙarasowa wajensu fuska a sake take kallon Tasalla da Tsahare. Ba Tasalla ba hatta Tsahare ta yi mamakin wannan tarɓar da Inna ta yi, kuma ta kasa gane dalilin yin hakan dan ta ga a yadda ta zo amma bata san ya ka yi ido ya juye da mujiya ba, dan ta saa halin aminiyarta Azumi babu tsoro kuma ba munafurci dan ta san Azumi dai bata san cewa wai dan tana ganin mutane ta ɓoye abin da ke ranta ba ita haka take fitowa ta nuna gaskiyarta, ita dama ƴar gaskiya ce. Tasalla mutuwar tsaye ta yi ganin Azumi ta sauya daga yadda ta nufo su da farko, sai gabaɗaya ta yi fosta mamaki al’ajabi suka dirar mata lokaci guda dan ita da a ce an wulaƙanta ta a bainar jama’a gwara ta bari in ta koma gida bayan ta gama ZAMAN WANKAN ta mata duk abin da za ta mata, sannan si ta ji daɗi da kuma buri d lafahrin yadda kishiyarta ta ta tarɓeta sai kawai ta ji babu abin da ya fi zaman lafiya daɗi, da a ce haka suke zaune tun farko da tuni ta yi zuwa Kano ba adadi dan da Azumi za ta gayyaceta wurin danginta in suna zama lafiya, kuma ko da a ce bata gayyaceta sunan nan ba sa zaman lafiya suke ba za ta ji ɗar ko shayin zuwa ba. A take ita ma Tasalla ta saki murmushi tana kallon Inna Azumi ai gabaɗaya sai suka zame wa Tsahare TV ta kalli wannan ta kalli wannan.
“Ke kallon ya isa haka” Cewar Inna cikin zolaya tana kallon Tsahare da ta saki murmushin jin daɗi lokaci guda dan ita ma ta ji daɗin yadda aminiyarta ta, ta tarɓesu.
Haka Inna ta shigar da su tana murna, dan ita ta karɓi bokitin furar gannun Tasalla ma, tana zolayar Tsahare wai ba za ta karɓi kayanta ba kayan ƴar uwarta Tasalla za ta karɓa. Haka sai ta musu masauki tare da gabatar musu da abin kaiwa baka. Nan Tasalla ta gabatarwa Inna nono da fura a matsayin abin da Malam ya ce a kawo ita kuma ta fito da riguna da dubu biyu ta bai wa Inna wai a baiwa mai jego, aikuwa Inna ta yi godiya sosai amma ta ce ba za a karɓi kuɗin ba dan wahalar ta isa ita kuma ta rantse a kan ba za ta karɓa ba tun da ta yi niyya kuma ba Innar ai ta baiwa ba jikarta da ƴaƴanta ta baiwa, sosai Inna ta ji daɗin kyautar da Tasalla ta yi, dama zuciya tana son mai kyautata mata, kuma sai Inna take cewa ashe haka zaman lafiya yake da daɗi. Tsahare ma turmin atamfa da riguna biyu ta kawo haka dai aka sha godiya da fatan ƙara samun danƙon zumunci.
Sai da Tasalla ta tafi yin alwala Inna da Tsahare suka samu keɓewa.
“Wai amini mai yake damunki ne, ke da kika zo birni dan ki murmure abinki sai kuma na zo na ganki duk a wani firgice?”
“Ke dai bari wallahi ZAMAN WANKAN nawa ne ya zo da wani salo”
“Kamar ya?”
“Yo Hassan ɗin ne miciji yake zama, tun da na zo a harƙalla ake dan wataran ma ina ake zama a ci abinci ana ta gudun famfalaƙi gugun ceton rai duk fa hankali ba a kwanceka yake ba, dan ma dai ina da ƙarfin hali ma da wallahi ba lallai ki same ni yadda kika ganni ba” Nan Inna ta shiga baiwa aminiyarta labari tun daga ranar farko da ta yi arangama da aljani har kawo yadda aka sha artabu da miciji da jama’a babu abin da ta rage mata amma dai bata faɗa mata labarin mala’ikan mutuwar da ya ziyarceta a daren jiya ba wanda shi ne silar dawowarta yadda ta ganta ba ta dai faɗa mata gabaɗaya hankalinta ya yi gida so take ta tafi in son samu ne gobe idan za su tafi ta bisu.
Sosai Tsahare ta sha dariyar artabun mutane da micijin da Inna ta bata musamman zuwan Malam mai sittin wata kan wata, da zuwan su Mama ranar da Imran ya sha yiwa Nigeri’a ranar da ya shiga tukunya kai ta sha dariya a wajen da Inna ta ce an rufe ta a freezer, da yadda suka yi artabu da ajani a bayi duk cikin labaran babu na yarwa dan dariya dai ta sha ta. Sai da ta tsagaita ta ce.
“Akwai dai wani abi da zai sa ki tafi dan na san miciji ba zai sa ki tafi ba da zai sa ki tafi da tuni kin bar gidan menene wannan wanda ya sanya har kika nunawa Tasalla ƙauna da kulawa haka? Lallai wannan ba ƙaramin abu bane”
Shiru Inna ta yi tana so ta faɗawa aminiyarta tana tsoron mala’ikan ya ce kar ta faɗa Haka dai ta ce mata babu komai.
Da yamma haka su Tsahare suka sauya kaya, dan gidan suna ya cika taf, yadda ba a yi zato ba dan duk an ɗauka ba za a zo ba saboda micijin to kuma cikin ikon Allah sai ma Hassan ɗin ya zauna a mutum bai zama miciji ba ranar sunan. Haka aka sha kiɗe kiɗe har da ƴan kiɗan ƙwarya, dakyar dai su Tasalla suka ja Inna wurin kiɗan ƙwarya ta ɗan taka rawa dan har da liƙi Imran da Abid da Sadiya da Ashrof suka mata sai dariya jama’a suke da yadda Inna take rawa da kuma yadda ake zuba mata kuɗi kowa yana murna dan gabaɗaya hankalin mutane sai ya dawo wurin kaɗan ƙwarya dan sosai Inna ke ba mutane dariya.
Haka dai taro ya watse kowa da kayan rabo masu yawa sai dai fatan Allah raya yara. Haka Imran ya koma gidan Hajiya ya kwana saboda baƙin Inna dan daɗi yake ji da ya ga ta ɗan saki jikinta ma.Haka suka yi hira sosai amma suna yin bacci Inna ta tashi ta kalli gabas haka ta kwana sallah da kazimi.
Washe gari haka aka yiwa su Tsahare sha tara ta arziƙi lemo Tasalla da Tsahare kowa katan Inna ta basu cake guda ashirin ashirin. Sannan ga wanda Sadiya ma ta basu sosai Inna ta so binsu amma Imran ya hanata dan yana so ta zauna a nan ita kuma ta zauna a nan dan yana ɗauke mata kewa haka dai ta zauna ba dan ranta ya so ba. Bayan suna da kwana biyu Imran da Abid suka zo da wani Malamin sunna ya shiga yiwa Hassan addu’a ya daɗe yana yi sannan aljanin ya bayyana kansa ya yi magana, a nan ya faɗi cewa tun lokacin da aka haifi yaran ya shigi Hassan, dan ko yadda bayan Hassan yake alamarsa ce ba wai a haka aka haifeshi ba duk da ana samun a haifi tagwaye da baiwar zama micijin amma shi na Hassan aljani ne. Haka aka fitar masa da shi sosai kowa ya yi farinciki da murnar hakan.
Inna dai ta ci gaba da rayuwarta wurin ƙanƙan da kai da komawa ibada da kasancewa da mahaliccinmu ko yaushe tana bauta masa, a haka ta cika kwana sha uku ana gobe kwananta sha huɗu za su cika sosai aka kasa gane kan Inna haka ta wuni kuka da neman yafiya kuma taƙu faɗar dalili, har Malam ma sai ta kira sau ba adadi tana neman yafiyarsa.
Ranar da kwanaki kuwa suka cika Inna bata magana sai ta bebaye dan kawai a sallaya take sai dai ta tashi ta sako alwala ta cigaba da sallarta. Kai har gari ya waye Inna bata mutu ba kwanaki sha huɗu sun cika har da kwana ɗaya amma shiru kake ji wai malam ya ci shirwa sosai Inna ta yi mmaki tana ta tunanin shin su ma mala’iku suna mantuwa ne? Ko kums yawan ibadarta ne ya sanya aka ƙara mata kwanaki, a haka dai ta ɗan saki jikinta amma kuma yawan ibada da lazimi ya gama shige mata jiki sun zame mata jiki duk da dama kasancewarta mau yawan ibada amma dai ta ƙara fiye da sanin mutum ga zuhudu (Gudun duniya) da ya ƙara shiga zuciyarta sosai. A haka ta yi kwana arba’in ɗinta ta haɗa kayanta ta je yiwa Hajiya da su Mama da Ashrof sallama suka haɗa mata sha tara ta arziƙi haka ta baro Sadiya da jariranta cikin ƙoshin lafiya duk da tana jin ba daɗi da za ta rabuwa da su Imran da Abid ne suka kaita har gida a motar Abid sosai su ma suka ji ba daɗi lokacin da za su baro garin su Inna sabo tirken wawa.
Imran ya nemi yafiyar Inna kan abubuwan da suka faru, har dai ma sai da ya bayyana mata cewa shi ne aljaninta kuma shi ne mala’ikanta.
“Kai Imirana amma ka iya shegantaka wallahi, yo Allah na tuba ai ka tsurar danu gabaɗaya ka sanya ina jiran ranar mutuwa ta” Cewar Inna tana dariya shi ma da Abid dariyar suka yi , aikuwa Inna ta ce ta yafewa Imran shi ma ta nemi yafiyarsa, suka baro Inna suna kewarta dan har suka shiga garin Kano labarin Inna kawai suke suna dariya irin yadda ta sha yin abubuwan abin dariya da cikin mutum zai ƙulle.
Tun da Inna ta koma gidan Malam zaman lafiya ya wanzu tsakaninta da Tasalla sosai Malam yake jin daɗin zama da su yanzu. Inna kuwa kullum ta tuno Imran ne silar gyara rayuwarta sai ta ji daɗi ta rinƙa sanya masa albarka.
“Ina son ku masoyan ƳAR ZAMAN WANKA KWANA ARBA’IN, musamman ƴan paid grp wanda suka biya kuɗinsu domin cigaban labarina da na Hassan da kuma Imirana, yo Allah na tuba ai ba zan manta da ku ba” Cewar Inna tana ɗagowa masoyanta hannu🙌
Alhamdulillahi kasiran, ina godewa Allah dabya nuna mini farko da ƙarshen littafin nan, ina godiya ga masoyana a duk inda kuke musamman wanda suka biyani kuɗi dan bibiyar labarina na gode sosai da sosai son so fisabilillahi!
Ina neman afuwar dj wanda na ɓatawa a ckn rubutun nan da ya yafe mini ko ma ba a kan rubutun bane ina neman afuwar kowa, dama ɗan adam ajizi ne😿🙏
ALƘALAMIN MMN AFRAHH BA YA RUBUTA SHIRME😍🙋♀️
Allah bamu ikon gabatar da ibadunmu lafiya Allah sa a sallace da mu muna raye lafiya🙏
🙋♀️🙋♀️🙋♀️