Hausa NovelsMai Maganin Mata Hausa Novel

Mai Maganin Mata 7

Sponsored Links

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*

*Zahra Surbajo*

Bisimillahirrahmanirrahim.

*HARIJA CE,sabon littafine dazan yishi akan kuɗi 500 kacal,karku bari abaku labari,yazo da salo na musamman shima meso ze iya turo kuɗinshi yanzu ta acct kawai zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*

*meson karanta paid book ɗina tsawon shekara guda batare daya sake siyaba to 1500 ne register dani,meso seta tuntuɓeni a 07044600044*

*7*

 

Koda gari ya waye da wuri suka kimtsa zuwa asibitin.
Koda suka isa basu tadda layi sosaibadan haka na ciki na fita suka shiga.

Duk wani abu daya dace shine aka musu inda ƙarshede xakamakon ya nuna matsalar daga fadilane.

Wayyo Allah kuka ta fashe dashi me tsuma zuciya yayinda shiko labeeb kukan nata ke ɗaga masa hankali, rungumota yayi jikinshi yana rarrashinta.

Likitanne yace”hajiya haƙuri zaayi kici gaba da zuwa asibiti ana bincikawa maybe mu gano sanadin daya hanaki haihuaa,amma for now bamusan abinda ya janyo mahaifarki bazata iya ɗaukar cikin ba,wanda in aka gano maybs wanda ze magantune.”cewar likitan.

Godiya sukai masa suka baro asibitin rai babu daɗi,dan hankalin fadila inyayi dubu ya tashi.

Koda ya tashi sanar da hajiya cemata yayi matsalar daga gareshi take

Sosai ta nuna taji tausayin shi yayinda kuma azuciyarta ta lashi takobin sashi ƙara aure dan ta tanbatar da gwajin.

********

Duk da ɓoyewa hajiya aynihin sakamako da akayi fadila hankalinta be kwanta ba dan tasan komai daɗewa asiri ze tonu.hakanne yasa ta kira ƴar chadi taji ko akwai mafita.

Bayan sun gaisane fadila ta zayyane mata duk matsalolinta,cikin kuka.

“wannan ay hajiya fadila ba abun damuwa bane inhar na bada shawara zaa ɗauka”cewar ƴar chadi.

Cikin zaƙuwa fadila tace “kowacce irin shawarace ƴar chadi zan ɗauka inde hakan ze samamin salama azuciyar sirikata”

“To inde hakane yazama wajibinki ki aurawa mijinki aure,da wata bisa sharaɗin in ta haihu ɗan nakine batare da kowa ya saniba”

“Aurefa kikace ƴar chadi,taya da hankalina zan bada gudunmawar aymin kishiya ay abune dakema kinsan baze yiwuba”.

“In na baki shawara kidinga ɗauka,nasan fa abinda nakeyi,to ce miki akayi zama zasuyi na har abada,ko ɗaya,auren ana ɗaurashi in tayi ciki seya saketa,in ta haihu ta baki ɗanki,ki biyata kuɗin aykinta ki sallameta ke kuma ki riƙe ɗanki amazaunin kece kika haifa va tare da kowa yasaniba ciki kuwa harda uwar tashi,ni kuma anan zan haɗa miki haɗin kulle bakin kowa,dan karma azo ana maganat daga baya,a kabari ake sashi ta yadda har abada bamejin gaskiyar maganar”

Ajiyar zuciya fadila ta sauke sannan tace”to wacece zata yarda ayi wannan wasan da ita ƴar chadi?”

“Akwaisu anan sosai wanda ko mahaifar kika buƙaci siya zasu siyar miki bare auren kwangila”

“To na gamsu da shawararki ki samo yarinyar daga yau zuwa gobe,kuyi ciniki,seki min bayanin sannan ki turamin hotonta ta yadda zan nunawa mijin nawa muyi shawara”cewar fadila ba tare da tunanin komaiba.

Daga haka sukai sallama fadila nata jinjina lamarin amma tunda ƴarchadi tace zatayi maganin matsalar ta yarda zatayin.

******

Ƴar chadi suna gama waya ta buga wata uwar guɗa gamida fara tiƙar rawa atsakar gidanta.

Da sauri farida ta fito daga ɗakinta dan ganin abinda yasa uwar tata shiga jazaba haka.

“mama lafiya me ya faru haka kike rawa da guɗa?”

“Farida mijin aure kika samu asadaka kinga ko dole nai rawa na godewa Allah,”Cewar ƴar chadi

Faraace ta bayyana a fuskar faridan tace”mijin aure kuma mama a ina yake?”ta faɗi tana murmushi

Natsuwa ƴar chadi tayi sannan tace”acikin masu siyan kayanane wata bata haihuwa shine mijinta yace ta nemo masa matar aure,shine tace tunda gaki meze hana ayi haɗin gida.”

Murmushi farida tayi sannan tai ƙasa da kanta dan Allah yasani ta jima tana son aure amma halin mamanta nabin bokaye yasa ko anzo neman auranta sai afasa.

Kumude je zuwa.

*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*

*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*

FREE NE HAR ƘARSHE

07044600044

Leave a Reply

Back to top button