Auren Wucin Gadi 9
Chapter 9
Bayan ficewar malam ilu da muƙarraban sa ƴan kallo ɗago Anna nayi daga ɗuƙen da take muka shiga ɗaki da ita maman manu da muke gida ɗaya da ita tashigo har ɗaki ta zauna ta kalli Anna da har lokacin takasa koda ƙwaƙƙwaran motsi sai ajiyar zuciya da take saukewa dama muddin kaga Anna a irin wannan yanayin to lalle ranta yakai ƙololuwar ɓaci dan haka cikin sanyin murya maman manu ta buɗe baki tace”maman Aisha dan girman Allah kiyi hakuri da abunda malam ilu yazo yayi miki karkisaka abun arai ballema yazo ya dameki ya hanaki sukuni a ranki.
Sai kuma taɗanyi shiru ɗan muskutawa nayi nace”amma maman manu tsakani da Allah yanzu duk zaman da mukeyi da mutane a nan anguwar amma arasa wanda ze dakatar da irin cin mutunci da wannan mutumin yakewa Anna magana ashe duk taron yuyuyu taron kuɗaji marasa amfani muke zaune dasu bamu sani?wannan yanuna koda cutar damu za ayi a unguwar nan ba wanda zaiyi magana wallahi maman manu da zaran nasami albashin wannan watan wallahi ɗaukar uwata zanyi mubar nan unguwar da ba wajen zama bane ba.
“Haba ƴar nan katseta nayi raina a mugun ɓace nace”kinga maman manu tashi kawai ki fitar mana a ɗaki dan dukkan ku halinku ɗaya banga wani abun kizo kina mana karamar murya bayan kowa ya watse ba,ai wannan duka gulmace kiji mai zamuce kisami na barbaɗamu.
“Yi hakuri maman manu rabu da Aisha ai kinsan sha’anin yaro ba kowani ɗan halak ne zaiga ana wulakanta masa iyaye yayi shiru ba cewar Anna da har lokacin bata kalli inda maman manun ke zaune ba tayi maganan.
Washe baki maman manu tashiga yi tagyara zama tana cewa wallahi maman aisha ai wannan maƙwabciyartamu mai ɗan wake ita ke kai gulma wajen malam ilu dake shikuma ba hankaline da shi ba shikuma yazo yana ta tada jijiyoyon wuya kawai dan baku biya da kuɗin wannan wata ba,rainane yasake ɓaci jin wai mai ɗanwake ce ta haɗa wannan tarzomar yasani cewa ai wallahi sai namata rashin mutunci.
Saurin dakatar dani maman manu tayi tace”haba keko aisha daga ganin ɗan fawa sai miya tayi zaƙi haba de ai basai kinje ba kinama zaune zata ciyota ta zo tasame ku nan zaune.
Daga haba ba wanda yasake yin magana haka ta karashe zaman ta harta tashi tatafi ƙofarta mude bataji ta bankin mu ba kamqn yanda Anna tajamur burki nima shirun nayi.
Saboda ɓacin randa nake ciki wallahi sai na nemi ƴunwar dakuma gajiyar da na ƙwaso duka narasa.
Dadare muna zaune ina sake kwantarwa da anna hankali sai ga fadila kaman anjehota ta faɗo mana ɗaki tana ta huci ko sallama babu tashiga cewa yanzu dama wannan mara mutunci mutum haka yazo yamiki anna wallahi sai yasan yataɓoki hukumace zata rabamu da shi wallahi.
Murmushi mai ciwo anna tayi tace”yo mai natada jijiyoyin wuya ai idan mukace zamu rama abunda yamana mun zama ɗaya kenan barin shi da Allah kawai zamuyi shine ze bimana hakkin mu dan Allah ba azzalumin bawa bane saide bawa ya zalumci kansa,Allah yana gani tunda nazo nagarin nan bantaɓa yi da kowa ba,to mai zetada mun da hankali dan ɗan kwaya irin malwm ilu yamun tijara kawai de naji ba dadine gani yanda yan anguwa suka zama ƴan kallo akarasa wanda zece da ilu abunda yayi ba daidai bane ba.
Amma duk da haka nagode Allah haihuwa tamun rana tunda yanta tazo ta tsayamun haka yarba gidan cike da kunya harda su masu kallon.
Daga haka taɗauko wata hiran nan muka shigayi sai can fadila takalli ni tace”nikan yau tunda garin Allah ya waye nake ta zaune ina jiran dawowarki naji ya rananki ta farko ta kasance duk da nasan keɗin kwararriyace inde ta fanin ɗinkine banida haufin ko matar shugaban ƙasa zaki iyama dinki amma kuma kedin matsoraciyace lamba ɗaya masamman ma wajen da ba idon sani.
Dariya nayi nace bawanda yasanni sama dake da anna na nashiga faɗamusu yanda na tsorata kafin wani saurayi ya fahinci halin da nake ciki yabani kwarin gwiwa dariya sosai fadila tamun anna kan cewa tayi Allah yakyauta yarabaki da wannan tsoro naki,sai karfe taran dare fadila tamana sallama rakota mukai nida khadija nan take sanar dani ai takusan samun aiki a masana’antar sarrafa magunguna na al hakk natayata murna dakuma yi mata addu’ar samun nasara tunda tace gobe zataje dan ayi musu gwaji.
Washe gari bayan munyi sallan asubahi nayi karatun al qur’ani mai girma kaman de yanda nasaba nade sallayar nayi na maida qur’anin na ajiye sannan naje na gaida anna datake zaune take lazumin ta sai kuma nafita naɗaura mana ɗumamen abincin jiya dadare saboda ɓacin rai bawanda ya iyaci tsakanin ni da anna harma kwara mubaraq ya ɗanci nasauke na daura mana ruwan wanka sai ga maman manu tazo tana wani washe baki ita ala dole fara’a”a’a aisha kece da sassafen nan”eh nice na amsa mata a takaice.
Zata kuma yin magana nace kinga sauri nake dan zuwa human right kai karan malam ilu da mai ɗanwake dan bima Anna hakkinta na kalaman batanci dasukai gareta dan shiga tsakanin mu dasu da dukma wani mai hali irin tasu kinga maman manu bar wajen kirki ɓatan lokaci.
Yanda nayi magana cikin haɗe fuska nima kaina nayi mamakin irin jarumta da nanu,barin wajen tayi tanufi kofarta cikin sauri nikuma abincin na dauka nashiga dashi ɗaki mukaci nace maza khadija tashi kiyi wanka kafin nan nayi shara bayan duka mun shirya sai muna anna sai anjima sai anjima dan sai naraka su khadija makaranta kafin na wuce sai ga sallaman mamman saje wani dattijo makwabcin mu sai kuma ɗaiɗai kun ƴan anguwa da mai danwake.
Har kasa na zauna nagaida mamma saje dan saida nakira sunan sa ma nagaida shi saboda sukara sanin ma haushi suke bamu”Aisha humaira ina ita nafisan take?”tana ɗaki baba nace dashi tare damiƙewa na dauko tabarma na shimfiɗa masu sannan nashiga daɗi nasanar da Anna zuwa su a tare muka fito ta zauna daga baƙin kofar daki da carbin ta a hannu ta gaida mamman saje cike da girmamawa dan dattijon ƙwarai ne mutumne wanda koda wasa bayason ganin anayin ba daidai ba acikin anguwa yanzun nan zai tsawatar da babba ko yaro.
Nisawa yayi yace”nafisa wajenki mukazo bada hakuri akan abunda yafaru jiya,wallahi jiyan bana nan hakan yafaru sai can dare dana dawo mai ɗakina take sanar dani abunda yafaru,sa’ilin dare yayi shisa ban zo ajiyan ba,wallahi raina yaɓaci sosai da abunda malam ilu yayi ina kallon sa babban mutum ashe shiɗin bashi da cikekken hankali dan Allah kidubi girman Allah da manzon sa kiyi hakuri idan kinji ance da mutum yayi hakuri tabbas an cutar dashine,a kuma janye maganan human right da zakukai ƙara insha Allah hakan baze sake faruwa ba.
Sai da yakai aya sannan Anna ta ɗago tana kallon sa tace”hakika baba saje ba’aɓa muzantani kaman yanda ilu yamun jiya ba,nasan bakomai yakawo haka ba saboda kawai yana ganin bani dashi shiyasa yamun haka da ace ina da kuɗi koda a titi nake kasa haja wallahi be isa yamun koda kwata kwatancin abunda yamun ba amma bakomai gidane dama wannan wata damuke ciki kuɗinmu ze kare insha Allah karshen watan zamu barmasa gidan sa basai yazo yacimun mutunci a gaban mutane ba.
Baba saje juyawa ga malam ilu yayi daya sinne kai kasa alamun rashin gaskiya ya bayyana ƙarara a tare dashi yace”ashe kai ilu mutumin banzane dama kai bansani ba?ashe kuɗin suma basu cinye ba kazo kamushi tijara haka wai ma akan wani dalili kaxo kasamu mata da yaranta karamata mutane kayi ta aibatata mai tama?ku kuma yanuna su malam kalla maƙwabcinmu sai baban manu sai malam ashiru yace anyi dattawan banza wallahi tirr da hali irin naku ace kuna anguwa kuna ganin irin wannan abun nafaruwa bazaku tsawatawa mai yi ba saide ku zuba ido kuna kallo kuna dariya.
Mainene aibun matar nan?dan tana zaune cikin mu tunda tazo garin nan yau kimanin shekara takwas ba wanda yataɓa ganin tayi abunda bashine ba tana zaune kalau da kowa tatsaya tsayin daka dan ganin ta tarbiyatar da ƴaƴanta tabasu ilimi,shin kanta farau hijira daga garin da kake zuwa wani gari ko kanta karau nagade dukkan mu nan zuwa mukai ba ƴan nan bane.
Hakade baba saje yayi ta musu faɗa karshe kuma yaɗaura da musu nasiha jikin su yayi sanyi sosai na suka shiga bawa Anna hakuri bama kaman malam ilu da mai ɗanwake dan cemata nayi wallahi ko kallon banza sukama Anna sai nakai mutum human right dariya baba saje yayi yace”yauwa Aishatul humaira faɗamusu suji tunda basu da hankali haka akeson ɗan halak yazama mai kishin iyayen sa.
Alhaji sunusi ne zaune da mukarraban sa yadubi Alh shehu tace”kai Alhaji shehu ya ake cikine?dariya ya kwashe dashi sannan yace”an sami tawa ƴar talakawa mai masifar son kuɗi inaga wannan za ayi tafiyan da ita nan duka suka saka dariya sannan Alh sunusi ya ɗaura da cewa”ko saurayi ko magidanci matukar aka sami mai irin wannan hali to azo dashi dan za ayi tafiyar tare dasu.
Ahmad ya ɗaga rigar da Aisha ta dinka yafi aƙirga yana girgiza kai yana ƙara jinjina ma kwarewarta khalid cike da tsokala yace”wai nikan kode rigar nan ajiye zamuyi ne kawai kadinga kallo?”mtsss yayi tsuka yace”nifa ɗinki bewani yimun kyau ba”kai kasani cewar khalid yana fita daga office dan kiran sunayen waƴanda suka samu aiki,yana doso hall din duka suka zuba masa ido kowa na addu’an Allah yasa yasamu aikin ina Aisha ishaq sunar farko daya yakira amsawa nayi tare da sujjada shukura dan godewa Allah dayasa nasami wannan aiki badan wayona ko ƙware wata ba hakan da nayi ya burge kowa hatta shikansa uban gayya da yake kallon komai ta cctv nasan cewa samun aikin nan da nayi rufin asirin mune nida anna dakuma ƴan ƙannena.
Saida yakira sunayen mu duka wayanda suka ɗauka aiki saura yabasu hakuri dakuma bawa ko wanne cikin su 5k sannan ya juyo kanmu yace musame shi a office din oga Ahmad tunda muka doso wajen sai naji zuciyata takasa nutsuwa nice farkon shiga sallama ɗauke a bakina nashiga office din wanda sanyi ac dakuma wani irin daddaɗan kamshi suka daki hanci na take yasaukar mu da wata iriyar kasala.
“Aisha ishaq³na amsa cikin sanyi murya tare da fargaban abunda zai biyo baya ɗaga rigar da na ɗinka jiya yayi sama yana kare masa kallo sai can yace ba lefi kinɗanyi abun azo a gani amma duk da hakan sai kin sake ɗinka biyu irin sa nagani kafin na ɗauke ki aiki gudun samun matsala daga baya take ƙirjina yabada sautin dam ganin ina farin cikin samun aiki ashe abun ba haka bane ba jikinane yafara rawa tsaban kiɗima har bansan sanda hawaye ya ɗan zubo daga idona ba.
ALLAH YASA MUDACE
[5/2, 8:34 AM] Xeenat: 💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕