Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 10

Sponsored Links

Chapter 10

Saurin maida hawayena nayi dana tuna maganan Anna inda take cewa dani karki bari mutum yasan dalilin kukanki idan yasani gobe shi zesaki kuka,
“Ok tom kawai nace dashi ba tare dana ko kalli inda yake ba nayi hanyan waje a raina ko cewa nake kajimun da ɗan rainin hankali,ai ko makaho ne ya laluɓa yasan kayan nan ta ɗinku amma jishi har dawani cewa kin ɗanyi ƙoƙari yana yauƙi kamar ta mace abunda bata sani ba duka maganar tata afili tashi kuma yajita cizan lips dinsa na ƙasa yayi aransa yana cewa zannuna miki rashin hankali na kuwa.

Fadila zaune take a office din Alhaji sunusi bisa jagorancin Alh shehu kallon ta kawai Alh sunusi keyi yana kara nazartarta yace”fadila ko?
Sauri ɗaga masa kanta tayi dan ita duk a tsarge take ganin irin kallon da yake binta dashi”,zaki iya aiki damu?
Zan iya da yardan Allah ta amsa mishi baki na ɓari gyaɗa mata kansa yayi yana juyi a saman kugeran sa sai can yace menene dalilin ki nason aiki damu?
Fadila ba tare data tsaya janbaki ba tace”saboda nagaji da rayuwar talauci kullum mu kenan bawani canji daga miyar kuka sai wake da shinkafa wannan ɗinma sai wata ran wata ran,dan haka sonake abani aiki yallaɓa komai wahala zanyi shi matakur zan sami farare bugun habuja inci shawarma anci pizza in ɗaura kaza a duk sanda naso in riƙe babbar waya nasanya kayan da nakeso na gammu cikin daula wannan shine babban burina.

Ƙyalkyalewa da dariya sukai baki ɗayansu jin abunda tace”yarinya inde wannan ce damuwar ki,
To kaddara damuwarki tazo karshe zamu baki aiki sannan zaki shiga ƙungiya wajibi ne akan duk wani member dake cikinta halartan meetin a duk inda zamuyi kuma koda wani lokacine bamason kawo mana yashashen uzuri sannan buɗe sirrin mu gawani wanda ba cikin mu yake ba kaman wasa kike da rayuwarki,ki tashi ku tafi kabata duk abunda take da buƙata kafin zuwa ranan meetin.

“Da to Alh shehu ya amsa duk girman Alh shehu saboda girmamawa kaman zeyi sujjada wa Alh sunusi saboda biyayya,godiya tayi masa sannan suka fita,
A hanyar su ta tafiya gida Alh shehu ya tsaya a wani haɗaɗɗen wajen suya yasiyo mata kaji danƙwala danƙwala har ƙunshi biyu sannan pizza da shawarma da lemunkan gora masu ɗan karen sanyi fadila tunda taga yashigo da ledar kajin nan take yawunta ya tsinke Allah Allah kawai take aranta yace ta ɗauka tasoma ci.

“Aisha nikan ɗinkin wannan kaya kaman baya baki wahala?
Cewan shamsu dake zaune shima saman kugeran keken sa daura da ni”,hmm shamsu kenan bawai dan baya bani wahala bane ba kawai de dan bayan da zanyi tunda mai abun yace su yakeso yaga ina ɗin kawa.

Sai yamma lis muka tashi nan na fahinci karfe biyar ake tashi a ma’aikatar dan da muka fita naga dandazon mutane kowa na kama gaban sa,sai na tsinci kaina da matukar farin ciki dakuma son aikina koba komai nasan rufin asiri gareni da Anna ta da ƙannena.

“Fadila ina kika sami kudi harkika iya sayo danƙwa danƙwal kaji haka?
kinsan fa banson ɗauko magana muna zaune ƙalau bamu rasa ci ko sha ba,amma saboda dan banzan baƙin halinki na kyamatar talauci zaki kai kanki ga halaka.

Kuka tafashe dashi tana cewa”ai dama nasan komai nayi ba daidai bane a gunki,yanzu mama fisabilillahi dan na kawo wannan abun yanzu har abun magana ne wallahi da Aisha ce takai irin wannan gidansu saide Anna tashi mata albarka amma bata ta dinga tuhumarta ina tasamu ba,takare maganan tana mai kara sautin kukanta.
“jikin mamace yayi sanyi ganin yanda ƴartata ke kuka cikin sigar rarrashi tace”ai duk uwa tagari dole ta tuhumi ƴaƴanta da kike wani cewa Aisha ai ita ba haka take ba tasan talaucinsu kuma bata adawa da shi kullum fafutuka take dayin aiki tuƙuru dan ganin sun samu abunda zasuci kefa?
to yanzu yi shiru share hawayenki faɗamun inda kika sami kuɗin tukunna kinga sai hankalina ya kwanta,jan majina tayi tukunna tace”banace miki zanje Al hakk neman aiki ba”eh kin faɗa mama ta amsa tana gyara zamanta”yauwa to can naje kuma andace sun ɗaukemu aiki shine suka raba mana dubu goma² a cewar su muyi kuɗin mota,nikuma ganin nasamu kuɗin shine fa nace yau ɗaya muma muci daɗi amma shine kike ta……sai kuma tayi shiru.

“Ayya fadila ɗiyar albarka dole na tuhumeki yanzu ba gashi nasan daga inda kika samu ba,nide fatana a koda yaushe be wuce ki zubar da wannan banza aƙida taki nakin talauci ba wallahi,nan ta sauko sukaji kaza ɗaya suna korawa da ruwan lemu mai sanyi saida suka cinye sannan mama tafito waje jinta take wasai aranta kuwa cewa tayi yaushe rabon da naci kaza a gidan nan in baci nayi karya ba sai ince tun tunna amarcina lol.

Shaƙan ni’imtaccen iskan waje nayi ina sakin ajiyar zuciya haka kawai nake jina cikin nishaɗi,hanyan waje nayi laila na biye dani tana tamun hira wani abun na amsa mata da eh ko na amsa da a’a da haka dar muka fito bakin get wata mota baƙa harta gitta mu sai kuma tadawo da baya baya ta tsaya daidai setin mu saurin ɗauke kaina nayi daga kallon sa nafara yin gaba banyi aune ba sai ganin mutum nayi yasha gabana na tsaya dan dole yasani jaa nima natsaya batare da nako kalle shi ba,anufin idan ya gaji da tsayuwan yabani hanya nawuce.

Ganin naɗauke kaina yasa shi cewa”Assalamu alaikum sanin muhimmacin amsa sallama yasani amsa masa da wa’alaikum salam na daura dacewa ko zaka bani hanya nawuce dan Allah,hmm yasauke ajiya yace”in banda kince Allah da ba abunda ze sani kauce miki a hanyan har sai na fadallasa miki sirrin zuciyata amma duk da naga kaman ba’amaraba da ni sunan usman sunusi kuma a gaskiya kinmun tunda naganki naji duk duniya ba wata ɗiya mace da tamun kamanki ina son ki,take naji zuciya ta wontsolo kaman zata faso ƙirjina ta faɗi jikina ne ya dauki wani irin ɗumi take naji gumi ya karyomun take ƴawun bakina yakafe nama kasa buɗe bakina sabida wani irin nauyi dayamun batare da na bashi amsa ko sake tsayuwa a gunba,naraɓa gefen sa zan wuce yayi saurin riƙo hannuna nayi saurin fizgan hannuna na yarfa masa mari cikin rawan baki data jiki nanushi da tsaya nace”karka sakeyin gigin kawo ƙazamin hannun ka da nufin riƙemun hannu…

Dafe ƙuncin sa yayi cike da jin haushin kansa wai yau shine yarinya ƙarama zata mara a cikin bainar jama’a,suma su Ahmad da khalid sunga marin da namasa amma basu san meya haɗani da shi ba,nufata yayi cikin zafin nama yakai hannu zai fizgoni yaji an riƙe masa hannu saurin ɗago kansa yayi dan son ganin uban waye kuma yake kokarin tsadashi dan sai ya yayyaga wa wannan mara kunyar rigar mutumcinta a idon jama’a kaman yanda tamishi.

“Cool down bro Ahmad yayi maganan cikin hucky voice ɗin sa,ɗago da jajayen idanun sa yayi dasuka gama jirkice saboda ɓacin rai yayi yazuba cikin na Ahmad,take yaji yamasa ƙwarjini yabude baki cikin ɓacin rai yana nunani yace”wai yaushe nayi lalacin da wannan kucakar yarinyar zata saka hannu ta mareni kawai dan tace nabata 50k mu haɗe a hotel nikuma nace 20k zan bata.

Tunda nake a rayuwata ban taɓa sanin inda hotel yake ba amma kaji sharri muraran bansan sanda nadawo gaban sa natsaya ba,ina kuka irin mai cin ran nan fuskana duk yaɓaci da hawaye nace”kaji tsoron Allah yaushe nataɓa ganin ka in ba yanzun nan ba dahar zaka jefeni da sharri na juya ina kallon oga Ahmad nace wallahi Allah bansan shi ba shi ya tsaya yace yana sona ban kula dashi ba nafara tafiya shine yariƙe mun hannuna nikuma bisa kuskure namare shi danjin haushin riƙemun hannu da yayi amma wallahi oga ka yarda dani ni ba ƴar iska bace ba,da har zanyi kuɗi da wani….ɗagamun hannu oga Ahmad yayi hakan yasani shiru amma fa idona be fasa tsiyayar da kwallan bakin cikin da wannan sharrin da ɗan talikin nan yajefeni da shi ba.

“Ki bashi hakuri na tsikayo muryarsa ba alaman wasa a cikin ta maida idona nayi ga wannan bawan Allah dana mara watsomun da wani mugun kallo dayasa hantar cikina kaɗawa murya na rawa nace”dan Allah kayi hakuri bisa kuskure hakan tafaru kuma bazan sake ba.

Hayayya kowa kaina yayi kaman ze kaimun bugu oga Ahmad ya tare sa yana cewa”ai ta baka hakuri ko?”amma ai katseshi khalid yayi cikin hargowa kaman zasu haɗa ƙirji yace”inaga abun naka rashin kunyace dama ba komai ba bara nanuna maka muma mun iya irin wannan ɗanyen kan wazaka nunawa tsageranci ɗan akuya kawai rikosa Ahmad yayi yana cewa”haba mutumina ba fa girmaka bane hakan kana abu gaban ma’aikatanka,dan dole usman yashiga motarsa yabar wajen bayan yamun nuni da idon sa mukut na hadiye miyawo.

Kallona khalid yayi bayan tafiyan usman yace”Aisha kidena saurin yanke hukunci irin haka nan gaba sa’an ki ɗaya nan ne da a wani wajen kika masa hakan ze iya yimiki komai yatafi yabarki kuma kece da kunya matsayinki na ɗiya mace dan daka ki kula kinji,share hawayena nayi nabuɗe baki daƙyar nace nagode murmushi yasakarmun yawuce yashiga mota juyawa nayi da nufin nama oga Ahmad godiya amma ina juyawa ya watsamun wani mugun kallo da yasani maida kaina ƙasa kwafa yayi batare dayace dani uffan ba shiga mota khalid yaja suka tafi.

bayan barin su gurin kuma sai tsoro ya shigeni dakyar nasamu na daidaita kaina na tari napep na hau tunda muka fara tafiya na lura wannan motar biye damu da alama bina yake yaga anguwarmu ko gidan mu kenan kirjina na shiga dukan uku uku take nashiga danasanin marin da nasama…

 

ALLAH YASA MUDACE
[5/2, 8:34 AM] Xeenat: 💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

Leave a Reply

Back to top button