Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 12

Sponsored Links

Chapter 12

   “Anna yanzu tafiyan zanyi nafaɗa kaman zan mata kuka?”eh tafiya zakiyi ta amsamun kanta tsaye ba tare da tadamu da yanayina ba,sake maimata tambayan nayi amsan de ɗayace eh dole ba dan naso ba saka hajibi na naɗauki jakata inada canji naira ashirin namikawa khadija nace idan kunje islamiya kwasayi sweet amsa tayi tanamun godiya hakama mubaraq suka dauki jakar makarantar su suka fita.

Sai sannan anna ta kalleni tace”jeki mana Aisha kinbar bawan Allan nan da jira”amma Anna yanzu fisabilillahi kinsan natsani wannan wanki musamman na hajiyar nan amma sai kika yarda kice naje,ai da naje can gidan nata gwara sukawo kawai nayi anan tunda kin fison….katseni tayi tana cewa”a’a Aisha idan kinga kaman da taƙura yi zamanki dama nace mata idan kin amince zakije idan kinƙi kuma bazan tilastaki ba.

Aisha shi rayuwa ɗan hakurine kowa dakika gani yayi nasara a rayuwa to sai da yahaɗa da hakuri dakuma jajircewa kafin yakai ga cin nasara dan haka inason koda yaushe kika sance mai hakuri a rayuwa dan masu iya magana kance mahakurci shikan dama dutse har yasha romonsa,ki koyi shanye damuwarki ko yaushe karki zama mai korafi ko saurin fushi kikuma iya sarrafa fushinki sannan komai zaki gani ki kalla da idon basira idan kuwa zakiyi abu ki auna amizanin addini dakuma al’ada jeki Allah yamiki albarka”amin na amsa mata nace sai nadawo Anna adawo lafiya ta mun.

“Ahmad wai lafiyanka kuwa?Ammin sa dake zaune a gefensa tamasa wannan tambaya”lafiya Ammi wallahi kawai tunani nake kan wasu kaya da ake neman su nan da kwana uku wallahi gani nake kaman sabbin ma’aikatan da muka ɗauka bazasu iya ba wallahi,hmmm Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace”in banda abunka ahmad ai sai kamusu bayani tunda dukkansu sun yarda zasuyi aiki dakai kuma kwararrune to meyasa bazaka tuntuɓe suba,kagade yau asabarce ranan litinin idan mai duka yakaimu sai ka tarasu duka kai musu bayani dakuma basu order shikenan abu mai sauki amma kawani tsaya tunani abunda baka taɓayi ba kenan kode wannan karon surukuwa ta acikin su take tunda ana kunyan su tayi maganan cike da zolaya kwafa kawai yayi yana kikewa ya fita daga main falo baki ɗaya dariya ƙannensa sukai bayan fitan sa ganin yanda yayi kicin kicin da fuska.

“Mummy kin tabbata yau wannan yar rainin zata zo kuwa tayi maganan tana yamutse fuska?”mai ze hanata zuwa bayan suna da bukata da kudin zata zo yanzun nan…sallamata shiya hana hajiya karasa maganarta juyawa tayi suka kalli juna da basma sai kuma suka kwashe da dariya tsayawa nayi daga bakin ƙofar shiga falon sai da sukai mai isarsu sannan suka tsagaita”shigo mana naji muryar hajiya mariya namun magana ba yanda na iya na shiga ciki gaidata nayi ba tare da na duƙa mata ba,kallona sukeyi a wulakance kaman bazata amsamun ba sai kuma ta amsa tana taɓa baki dacewa haka aka koyar dake ki gaida na sama dake?
“hakanma nayi kokari hajia tunda na iya gaisuwan wasukan ai hakan ma basu iya ba,na amsa kaina tsaye a fusace basma ta miƙe tace”kee ni sa’ar kine da kike neman kawomun rai.hmm murmushin dauke a fuskana nace”in banda abunki anty basma na ambaci sunane yanzude ba tare da bata lokaci ba”miƙomun kayan wanki nafara da wuri dan inada wasu aiyukan da nabari a gida uhmm karkuma ki mance ki haɗomun da sabulu kinsan ba saba haɗawa bawa sai kuma robobin wanki sai ki nunamun bakin famfo na kare maganar ko akwalata ban kuma damu da irin kallon wulakanci da suke jifana da shi ba,na juya zan fita waje naji tana cewa”waye ze kwaso miko kayan komo kizo kishiga dakina bayan kin gyaramun bedroom ɗina ki kuma wankemun toilet sai ki dauko kayan wanki a dustbin kizo laure zata nuna miki wajen wanki.

  Murmushi ɗauke a fuskata nace”anty basma kiyi hakuri wanki kawai hajiarki tace zanyi amma batace harda wani ƙarin ba,idan baki shirya amiki wankin ba zan iya komawa inda nafito?wani irin hayayyako mun tayi kaman zata hauni da duka yanda takemun ihu harta kai saida na ritsa idanuna dan harga Allah zan iya cewa tunda nayi wayo ba wanda yataɓamun tsawa ko ihu irin haka,”meyake going ne anan?naji wani ya tambaya daga bayana”bro wannan ƴar aikine take neman rainamun hankali ina bata command tana neman raina mun hankali”ƴar uban waye ita?da har za bata umurnin yin abu tace ba zatayi ba,cak ya tsaya daidai setin fuskana  yana karewa fuskana kallo da tunanin ina yasan wannan fuskar,bude idona nayi a hankali na sauke blue eyes ɗina cikin nasa daya sauke masa wani irin kasala na bude bakina a hankali na kai dubana ga hajia mariya dake hakimce tana zaune tana karkaɗa ƙafa duk wannan hargowar da basma kemun bata ko motsa ba balle nayi tunanin zata tsawatar mata”hajia tunda ba aiki da zanyi sai anjima dan tunda naga kaman baku shirya ba.
“to fitararriya yimun fitsara dakika saba,mamaki yakani jin abunda hajia tace wato nice ma nayi lefi duk abunda ƴarta tamun bata gani ba”yi hakuri nace da ita ance faɗan da yafi karfinka kamai dashi wasa”riƙe hakurin ki mara kunya a raina nace ganan mara kunya a gabanki amma a zahiri sai bata hakuri da nake na daura da cewa hajia kefa cewa kawai kikayi wanki amma ya daga zuwana zata tareni da wani gyaran danki da wanke bayi kinga dole ai nace bazanyi ba,kuma harda guzuri zagi nida ba maula ko neman sakada yakawo ni ba ai kinga bazan dauki irin wannan mulkin mallakan ba.
“Hohoho mummy dama ashe mai wanki ce?itan wannan saurayin da namara jiya yayi wannan tambaya dan tunda na gansa nagane shi shine bansani ba koya ganeni ko be gani ba,yana wani yatsine fuska kaman yaga wani kashi”eh ai da fari uwarta ke mana wanki kasan halin talauci da rashin cima mai kyau yunwa duka ta karya mata karfin jiki shine taturo wannan dan ta maye gurbin ta,tana magana tana nunani da hannu zuciya tazomun iya wuya kaman zan amayar masu da abunda yake cina a ciki amma na daure dan nasan idan nakoma gida nace ma Anna banyi ba bazata ji daɗin hakan ba”yauwa mummy kawai bani ita tarinƙa zuwa duk week tanamun wanki da guga dakuma gyaramun ɗaki kinga sai muyi jinga da ita biyan wata ko kullum inason ganin irin waƴan nan ƴan mata na aiki karkashina yanzun nan zan saukar mata da duk wani iya shege da takeji na yawo a kanta,kallon sa nayi na murguɗa masa baki ba tare da nadamu da kallon da hajia ke jifana da shi ba ita da basma.
“Laure laure naji basma ta kwala kira wata mata tafito daga wani ƙofa da ƴar gudunta tana dukawa gaban ta tace”gani hajia ta amsa mata yatsine fuska tayi tana nunoni kaita ɗakina kinuna mata inda kayan wanki suke zata ɗauka da to matar ta amsa jikinta sai ɓari yake”ki dauko kawai basai nashiga ciki ba ai ɗakin mutum sirrin sa be dace.
..katseni basma tayi da cewa ke kinga wasa a fuskana”nide dan Allah kuyi hakuri me wani na batawa mutun lokaci akan wanki da yanzu ai nayi rabi amma tun dazu abu mai sauki anty basma ki shiga ki miƙomun kinƙi sannan ga wacce zata ɗauko kina katseta wai idan nashiga dakin naki mai zanyi miki idan so kike naga inda kike kwanciya kikeso nayi ai basai kinyi haka ba,tun sanda na fara ganinki nasan kedin ta dabance dan Allah kinga inna laure ɗauko kawai ni yau naga ta kaina wallahi har kaina yafara ciwo.

“He hehe wannan saurayin yamun magana kallon sa kawai nayi ban ko amsa masa ba yace,gobe a roud 9am kizo zakimun wanki dakuma gyaramun ɗakina ke harma da wordrobe ɗina duka dan tayi kura sosai kallona yake kaman mayun wacin zaki kana wani lashe baki kaman tsohon maya araina nace maye saide kaci kanka kana kallon sa kasan be san kunya ba”banawa maza wanki na bashi amsa da mamaki hajia take kallona da tafa hannu tace”wace daraja ke ga talakan da talauci yama katutu da har ze zaɓawa kansa kalan jinsin da zewa aiki…..

ALLAH YASA MUDACE
[5/2, 8:34 AM] Xeenat: I just published “13” of my story “AUREN WUCIN GADI”. https://www.wattpad.com/1311711488?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=zahraaliabdullahi5&wp_originator=wpYNlAAYQ3IxPeVPRWtm5DyqJzbgM%2FvLx0yMHk%2FK2f8NkjF0ATEJkK3UhEsQPyN83XUn5liQlQV%2BV3QYloUU7dGIDKA9ptqw19b4Ns0leGWo2QY1rSR%2BYKgHDlgsYhPp
___________________
💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

Leave a Reply

Back to top button